Showing 42001 words to 45000 words out of 135321 words

Chapter 15 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

513

ba kukan nan yayi ba mancewa takeyi yana da tunani da kwakwalwar yara, haka nan badan taso ba kamar zatayi kuka ta dan duqa kadan har hannunta na karkarwa ta soma kama igiyar wandon nashi, gaba daya ma ta burkice ta rasa yanda ake zuge wando, shi kuwa mai zaiyi banda mazari don a matse yake sosai daman suna tsaye ne shida uncle bayan futarta ya dameshi akan saiya dauko mashi puzzle dinshi, futar uncle din keda wuya ya fado toilet din don daman duk safiya abunda yake farayi Kenan pee,

 

Wannan tazugen wando dai ta kyar aka warwareshi, daga shi har ita kamar marasa wayo babu wanda yayi tunanin sauke wandon kawai gaba daya instead of warware tazugen, shi daman idan har zaiyi using toilet kamar yanda hidaya ta koyar dashi saiya warware mazugin wandon kafin ya sauke shi kasa.

Sabeeha na gabanshi harta samu ta kunce wando, tana kwancewa kuwa yayi saurin sauken wandon kasa ba zato ba tsammani, cikin hanzari ta koma baya  saura kiris ta fadi tana mai runtse idanunta, allah ya taimaka da shorts a jikinshi kuma ta rufe idanun nata gam.

 

Shi baima bi ta kanta ba ya nufi hanyar wc, ita kuwa tuni ta bama kafafunta iska kamar ana ingizata ko waigowa batayi ba ta fuce daga bathroom din, closet room ta nufa ta fito mashi da kayan sawanshi kafin ta fuce zuwa kitchen.

 

Anaste ta fara harhada mashi breakfast dinshi, just one boil egg ne sai ruwa, tana gamawa ta gyagyara inda ya kamata kafin ta dauka maganinshi ta koma bedroom din.

Lokacin data shugo harya gama shiryawa ya zuba ma kofar dakin idanu yana son ganin first love, ganin sabeeha yasa yaji babu dadi,  don tunda safen jiya daya ganta bai sake ganinta ba kuma hakan na itching dinshi sosai, memory din abunda ya faru a daren kuwa ya rigada ya goge a kanshi.

Da sallama a bakinta ta karaso tana mai kokarin goge abunda ya faru dazu daga ranta, ganin shi looking sad yasata tsugunnawa gabanshi tace ‘friend!!’’

Dago da jajayen idanunshi yayi ya zuba mata still fuskanshi na bayyanar da baya cikin walwala yace ‘’yes!’’

‘’why are you sad?me kake so’’

Kamar jira yake kuwa saiga hawaye na yawo akan kyakyawar fuskarshi ‘’first love, I missed her so much’’

Wani irin tausayinshi ne ya kwanta mata a zuciya kamar tayi kukan itama, yan karamin tafin hannunta ta sanya ta soma goge mashi hawayen ‘’zatazo yanxu kaji?, don’t be sad please okay’’

 

‘’da gaske?’’ ya fada exicitedly

Girgiza mashi kai tayi ‘’yes da gaske nake yanxu kasha maganinka sai nab aka breakfast sai muyi wasa’’

 

Haka ta lallaba shi ya karba maganin yasha kafin ya danyi relaxing, kitchen din ta koma ta dauko breakfast ta kawo mashi yaci,

‘’friend!!’’

‘’naam, friend’’ ta amsa shi

‘’first love zata zo?’’ ya sake tambayarta

‘’yes zatazo yanxu’’ ta amsa shi

Bayan yan mintuna kalilan sai ganinshi tayi kuma yana hamma, taimaka mashi tayi ya kwanta ko minti biyu ba ayi bay a soma sauke ajiyar zuciya ahankali sai barci.

 

Sauke ajiyar zuciya sabeeha tayi tana kallon innocent handsome fuskanshi, yana da cikar gira sosai baki wuluk,ga bakinsa mai dan girma lebensa yayi jaa kamar jini zai futo,ga jaw line dinshi da idan ta kafa ma wajen idanu bata son cire idonta a wajen, yana da attractive structure so cute irin ta cikakkun maza masu aji da class, samun kanta tayi da dan duqawa tayi mashi addua kafin ta dauka cup din daya sha ruwa dashi ta fuce dashi bayan ta jawo mashi duvet ta rage mashi haske dakin nasa.

 

Kofar part din ta bude ta futo a natse, lokacin wajen karfe goma daidai, hidaya dake kokarin haurowa saman fadwa na biye da ita ne suka tsaya gaba dayansu suka zuba mata idanu, sabeeha bata lura dasu ba saida ta rufe kofar ta juyo nan tayi arba dasu, lokaci guda cikinta ya duri ruwa don bata manta marukan data sha ba

‘’ke uban me kike yi anan? Are you insane har kinada guts din presenting kanki a cikin gidan nan after what you’ve done?’’

 

Da mamaki fadwa ke kallon hidaya jin abunda take fada sai a lokacin ta gane cewa wannan din maid ce daman don ta ganta babu uniform ne yasa ta kasa gane wacece wannan hidaya ta bari har take shiga dakin Taj, ko suma ba barinsu take suna shiga ba dukda suma basu nuna sun damu da shiga dinba.

 

Muryar jamid da sukaji ne yasa suka maida dubansu gareshi, hannunshi na rike cikin na barad sun fito daga part din su.

‘’what she did was a mistake saboda batasan cewa ba a skipping maganinshi ba,’’

Rai a bace hidaya ta maida dubanta gareshi, yanda take kallonshi haka yake kallonta yana hango fire din dake cikin idanunta.

Fadwa dai hannayenta na harde tana kallon ikon allah don sai yanxu ta soma gane kan zancen nasu.

‘’you can go’’ ya umarci sabeeha.

Kamar munafuka haka ta sauke kanta kasa ta nufi hanyar sauka kasa, tana sauka shima suka sauka shida barad daman zasu fita outings ne yau weekends.

 

Cije lebe hidaya tayi kafin ta nufi hanyar part dinta,fadwa na ganin haka tabi bayanta.

A sitting ta tadda ta ta daura kafa daya kan daya, skin dinta a bayyane don rigar data saka ta zaman gida ce wadda bata saukar mata har kasa ba, rigar ya amshi jikinta don bata da qiba kwata kwata.

 

Zama gefenta fadwa tayi kafin ta soma Magana ‘’ukty are you okay?’’

Murmushin takaici ta sauke tana mai dubanta tace ‘’yes,what where you saying dazu?’’

 

‘’daman!! Maganar bilal ne’’ (mijinta)

Wani irin kallo hidaya ta mata tana sauraronta da kyau

‘’ukty please, meysa bazaki yi accepting dinshi ba? Wallahi he love me so much and he’s..’’

‘’shiii…..,fadwa na hanashi zama a gidan nan ne?’’ ta jefo mata tambaya

‘’no ukty but ina ganin meyzai hana shima ki barshi ya fara aiki anan taheel company’’

 

Wata iriyar dariya tayi kafin tace ‘’yaushe zaku girma ne keda afiya?,’’

‘’ukty please, muma munada share a cikin company nan, we can choose to work there’’

‘’ke badan na tsaya mana ba kin isa kiyi tutiya da wannan company din? Kinsan to what extend na kai har yanxu cikin company? Did you know what I had to do just to keep our legacy?kinsan sacrifice din danayi?..please idan bakida wata maganar mai muhimmaci ki futa kawai I need some space’’

 

Mikewa tayi ta wuce daki tabar fadwa anan zaune, rai a bace,

Meysa ukty ke masu haka ne?, why dole saida ikonta za ayi komai, wannan abun yana damunta sosai.

Haka nan ta futa daga dakin rai a bace.

 

Bangaren sabeeha tana komawa dakin su ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya kamar wadda tayi tsere, lokacin data shugo babu kowa a bedroom din don haka ta shiga bathroom tayi wankanta ta shirya tsaf cikin uniform dinta.

 

 

California…

‘’maya maya’’ nannybee ta soma kwala mata kira hankali a tashe, cikin bathroom ta sake lekawa hankali a tashe, ‘’ina yarinyar nan ta tafi ne?’’

Rufo mata dakin tayi ta sauka kasa, tunawa da maganar daddyn daya umarci ta saka mata idanu sannan ta dunga updating dinshi akan absence dinta yasa ta nufi wajen landline badan taso ba, direct line dinshi ta soma dialing daidai nan aka bude kofar shugowa cikin gidan, hayaniyar su ce data karade gidan yasa nannybee ajiye wayar ta nufi inda suke, sanye take da kayan barci data barta dasu a jikinta kafin ta sauka dauko mata breakfast dinta, kawayenta na biye da ita su kusan hudu, kowannen su yasha kananun kaya sun dame.

 

‘’hello nanny bee’’ haka suka soma gaisheta daya bayan dayansu, murmushi kawai tayi masu tare da welcoming dinsu tana kallon maya,

Cikin gidan suka karaso suka yada zango a sitting room, kan kace me parlorn ya karade da ihun su da hirarrakin sun a yan mata,

‘’go and frenshen up mana kafin su karaso its about to go down today’’ kloe ta fada tana kallon maya

 

‘’ku jira ni yanxu zan sauko please’’ maya ta fada tana wucewa sama.

 

Orders din da sukayi aka soma deliverying, kayan ciye ciye daban daban kamar waenda zasuyi house party.

 

Within few minutes saigata ta sauko cikin riga da wando wanda suka amsheta pink sai gashinta datayi packing dinshi a tsakiya, duk da bata da wani qiba da shape hakan baisa kayan sunyi mata kyau ba.

 

Tana shugowa parlor suka miqe gaba dayansu suna Shewa, ‘’ouu let the party begins’’

‘’oh yess’’ ta amsa su

Katuwar speaker dake nan parlorn su ta kunna masu suka fara rawa, kidan gaba daya ya gama karade wajen block dinsu kamar gidan party, nanny bee dai babu yanda batayi ba akan su rage saboda mutanen neighbourhood din basa son kara bayan wannan ma throwing noisy party a neighbourhood din is prohibited, haka suka wuni suna sha’anin su kwata kwata babu wanda yaji knocking din da aka dunga yi.

 

Sai wajen karfe biyar wutar gidan ta dauke gaba daya, rai a bace maya tace ‘’what the hell is going on?, kodai electricity bill din ne ya kare’’

 

‘’gaskia call your parents, kofa gamawa bamuyi ba gashi su tom basu zo ba’’

 

Knocking din da akayi yasa suka tsagaita da surutan da suka fara, ‘’who’s knocking kuma, daddy baya nan mummy kuma sai wajen midnight zata dawo’’

‘’let me check’’ kloe ta fada tana nufar hanyar kofar entrance din.

Saurin yin baya tayi ganin police a bakin kofar, ‘’who’s the owner of this property’’

Cikin saurin kloe tace ‘’maya, come over’’

Tasowa maya tayi ta karaso inda police din suke, ‘’are you the owner of the property?’’ suka sake tambayarta

‘’yes, I’m the daughter of the owners’’

 

‘’you’re under arrest for violating the regulations of this compound’’

Hankali a tashe maya ta kallesu tace ‘’what have I done, who reported me? For what?’’

 

Bai amsata ba yasa sauran officer din suka shigo suka saka su a gaba zuwa cikin moto, nannybee bata san me ake ciki ba saida ta fto lokacin ana shirin saka su cikin motar, turawa fa basu daukan wargi, dan report kawai neighbourhood din suka kai kusan guda biyar wanda haka yasa dole police suka zo suka tafi dasu.

 

Hankali a tashe nannybee ta soma kiran line din mummy, kiran duniya ta dunga mata bata sameta ba saboda suna cikin operation room, dan dole haka ta soma dialing number daddy, kiran farko kuwa ya daga wayan, lokacin yana kokarin barin san francisco zuwa ga los angeles daman tafiyar 30mins ce gaba daya, saboda akwai wani case da yake handling dole saiya bar garin zuwa wani garin ya samo concrete evidence.

Yana ganin call dinta kuwa ya tabbatar da ba lafiya ba, cikin sauri ya dauka call din.

Hankali a tashe ya ajiye wayar, ga ranshi yayi mugun mugun baci sosai, haka nan duk importance din aikin nan nasa ya barshi ya juya zuwa san diego.

A gurguje ya nema flight zuwa san diego allah ya taimaka akwai jirgin da zai tashi don haka ya nemi ticket a gurguje.

Bashi ya iso ba sai wajen karfe shida lokacin garin ya soma duhu, daga airport zuwa police station dinma akwai traffic sosai, ba karamin bacin rai ne kunshe a ranshi ba, allah kadai yasan me zaiyi ma maya, abubuwanta gaba suke karayi kusan kullum.

 

7 dot ya iso police bureu dake cikin san diego city, a gurguje ya bada sunanta ga officer din dake counter din wajen ‘’maya Majeed please, I’m her father’’

 

Ciki suka shiga inda suka bashi waje ya zauna, officer daya kawosu ne ya soma mashi bayanin charges da report din da aka shigar da kudin damage din da zai biya ga electry line dinsu da aka kashe gaba daya dole saiya biya tax.

Yana daga zaune saida ya kashe over 4000 dollars akan minor mistake na maya, at that point ko ganinta baya son yi, bai taba saka tunanin dukan yaro a cikin rayuwar shi ba, saidai yau yana jin kamar ya mata duka sosai.

Saida ya biya komai suka rakashi har inda aka kullesu, koda suka karasa tana daga zaune idanunta yayi jaa sosai tasha kuka, gaba daya friends dinta sun kira iyayensu sunzo ita kadai ta rage.

 

Fito da ita sukayi suka wuce gida, taxi ya tsaida masu suka shiga don motarshi na gida saboda daga airport ya biyo nan din.

Suna isowa mummy ta iso itama gidan,already ta kirashi bayan taji daga wajen nanny bee, dady ne ya fara futowa kafin itama ta futo daga taxi din, da gudu ta karasa wajen mummy dake tsaye hankali a tashe tana jiran fitowarsu, rungumeta tayi tsam tana hawaye, ‘’mummy I’m sorry please’’

Ko kallon inda suke majid baiyi ba ya wuce cikin gidan daman tunda suka shiga cikin motar bai ce mata tak ba har suka iso, babu abunda take kuwa sai kuka kuma yana jinta yayi banza da ita don har zuwa lokacin yana processing irin hukuncin da zaiyi mata daidai da ita.

 

Kallon fuskanta da tayi gaja gaja mummy tayi kafin ta kamota zuwa cikin gidan, gaba daya ranta a dagule yake da alamarin, tasan wannan karan kam bazasu kwashe ta dadi ba da daddy don ta hango tsantsan bacin rai akan fuskanshi.

Koda suka shiga nanny bee na tsaye hankali a tashe, gaba daya laifin kanta take gani na qin hana maya, son da takeyi mata ne ke sawa take hana ta yin wasu abubuwan saboda tausayinta da takeji, iyayenta are very busy parents, basuda time din ta saboda aiki, wannan yasa ta taso da kadaici da rashin kusanci da iyayen nata musammam daddy.

 

Har cikin bedroom dinta mummy ta rakata tayi wanka nanybee ta kawo mata abunci taci kafin mummy ta bata maganin ciwon kai.

Saida ta tabbatar ta natsu kafin ta kashe mata wutar dakin nata ta koma zuwa bedroom dinsu.

 

Da sallama ta shiga dakin, a zaune ta taddashi har zuwa lokacin ranshi a bace yake,karasowa tayi inda yake bakin gado ta zauna gefenshi kafin ta soma Magana cikin hikima  ‘’daddy!!’’

Dagowa yayi ya kalleta idanunshi yayi jaa sosai, ‘’majeed dan allah kayi hakuri, yarinta ke damun maya,’’

 

‘’yarinta? Bahijja yarinta fa kikace? Are you listening to your self kuwa, where’s she?’’

‘’na sata barci, ‘’

Ta bashi amsa kai tsaye.

 

Wani irin mugun kallo yayi mata kafin yace ‘’barci? Bahijja wani sa’in kina bani mamaki?,kinsan asarar da yarinyar nan ta jawo mana? Kin san me zatayi nan gaba, after all she has done kin sata barci?wallahi kinji na rantse bahijja wallahi this time around I’m going to deal with maya, duk abubuwan da takeyi ina Kauda idanu this time around bazanyi ba, and don’t even think of saying a word kinji na fada maki’’

Yana kaiwa ya miqe ya fuce daga dakin, tana ganin futarshi tabi bayansa, dakin maya ya nufa kai tsaye ya bude kofar ya kunna lights din dakin, barcinta take

hankali kwance kamar ba itace tayi aika aikar nan ba, ‘’maya!!!’’ ya doka mata uwar tsawa, tashin farko ta mike zaune zumbur,

‘wani irin furgici ne ya durar mata ganin daddy nata a tsaye, daidai nan mummy ta karaso cikin bedroom din, ‘’step out now’’

 

‘’daddy please I’m sorry bazan sake ba please’’

‘’shut up your dirty mouth, I said out to, don’t make me repeat my self, ‘’

 

Ya karshe hannunshi har karkarwa yake tsabar bacin rai,

‘’mummy please talk to dad dan allah, wallahi banason zuwa displine room dan allah’’

 

Tana kaiwa nan ta karaso inda mummyn take ta boye a bayanta, ‘’daddy please, for god sake laifi tayi kuma tayi nadama, maya is not a kid fa da za a kulleta a daki, she will be 18 in a month’’

 

‘’bahijjaaaaa!!!!,’’

‘’majid please….’’

At that point ranshi ya gama baci sosai, ba maya ba hatta mummyn ma ta gama bata mashi rai sosai.

 

Kasa cewa komai yayi kawai ya fuce daga dakin cikin bacin rai sosai, shi kadai yasan meke cikin ranshi da matakin dazai dauka akan sus u duka ma.

He’s trying so hard to understand bahijja, wani sa’in yana kauda ido sosai akan rashin jin da maya keyi saboda maya kadai ce yarsu, kuma bazasu sake haihuwa ba saboda matsalar mahaifa da bahijja ta samu bayan haihuwar maya.

 

Wannan rana dai cikin bacin rai sukayi gaba dayansu daga daddy har mummy, haka suka kwashi wajen sati guda babu wanda ya kula wani cikin su, maya kuwa harkarta ta cigaba ba tare da damuwa ba, ita dadinta daya mummy ta bi bayanta, saidai ta gindaya mata sharuda sosai tare da warnings akan cewa idan ta sake ta sake maimaita abunda tayi bazatabi bayanta ba.

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 21-22

Update

NIGERIA ABUJA

Santuraki family…

Yau family an tashi da jimamin mutuwar babban aunty amarya (matar uncle sameer), gaba daya cikin shiri suka fito inda zasu je gidan gaisuwa, already uncle Sameer ya wuce da aunty amarya chan gidan gaisuwar don tunda asuba aka kirashi aka shaida mashi, lokacin ma ba’a bangarenta yake ba yana bangaren anty Laila don kwananta ne ya zagayo a ranar, anne ce da nanna suka fito cikin shiga ta mutunci da alfarma sai sauran matan gidan, anty fadila da yaranta mazan, hamad da laily karama sai sufyan da abil, kananun ne kawai aka bari a gida wajen nannies dinsu.

 

Gaba daya suna tsaye a compound din har kowa ya futo gaba dayansu banda anty Laila,

Anty fadila ce tayi saurin cewa

‘’mamanku fah’’

Anty fadila ta fada tana mai duban su abil,kallon juna suka fara yi shida sufyan, ‘’tace driver zai taho da ita’’

Tabe baki antie fadila tayi kafin ta shige cikin katuwar lexus inda hamad ke driving motar while sufyan ke driving dayar motar dasu anne ke ciki.

 

Cikin anguwar GRA dake cikin maitama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login