Showing 30001 words to 33000 words out of 135321 words

Chapter 11 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

500

‘’eh yanxu na shugo’’

Tana kaiwa nan ta mike ‘’bari na sauka kasan’’

Nanna ce kawai ta amsa ta da toh, anne kuwa hankalinta na kan pappers din dake gabanta, anty fadila na kwantar da mubin ta dubi hanyar futar da anty Laila tayi kafin ta tabe baki tace ‘’hmmm’’

Kallonta nanna tayi fuskanta ya dan sauya tace ‘’haba fadila, har yanxu dai bakwa jituwa da yayar taki?’’

 

‘’nanna bazaki gane bane, Tsakani na da ita waye ya kamat ya gaisar da wani?’’

Rai adan bace nanna tace ‘’lallai fadila, karkiga wai don tare kuka taso, matar wan k ice kuma uwar yayansa, dole ki bata respect dinta, anne kina kallon wannan shashanci da girmansu’’

Sai a lokacin anne ta dago ta kallesu cikin glass din dake fuskanta ‘’ay sun san daidai basai nayi Magana ba, and besides ita da take babba itace ya kamata taja girmanta’’

 

‘’anne please karki goyi bayan kowa a alamarin nan saboda wani abu chan daya faru a baya wanda ya zama tarihi’’

Kallon yar uwar tata anne tayi tace ‘’hajara!!’’

 

Jin yanda anne ta kira nanna yasa anty fadila fucewa daga dakin, tana futa kuwa anne ta kalli nanna tace ‘’bana son a sake maimaita maganar nan, bana bin bayan kowacce a cikin su, laifin shi Sameer dinne daya bar hakan ta kasance shiyasa bana Magana akai’’

 

Nunfasawa nanna tayi kawai kafin ta maida hankali wajen abuncin da take ci.

 

Fadila na futa daga dakin kuwa ta sauko kasa zuwa kitchen, a tsaye ta tadda anty mubina da masu aiki suna ta hidima, karasowa tayi har inda suke tayi kafin tace

‘’amaryar babban yaya, baki koma daki kin hutaba?, kije ki huta tunda mubin yayi barci nakaishi dakin anne’’

 

Juyowa mubina tayi hannunta duk flour gashi tasha apron da alamu dai aykin takeyi bil hakki da gaskia, ‘’anty fadila ay mun kusa gamawa, cake dinne kawai ked an daukan lokaci’’

 

‘’toh shikenan, bari naje na dubo ko hamad sun dawo daga kai sadakar tunda naga an sauko daga masallaci, wannan yar banzan yarinyar ashe guduwa tayi ta barki’’

Dariya kawai mubina tayi kafin ta maida dubanta ga ayyukan dake gabanta.

 

Anty Laila kuwa bayan ta futo kasan ta sauko ta hakimce akan kujera, tana nan zaune fadila ta sauko ta wuce kitchen harta futo daga kitchen din ta sake komawa sama, su inti da amla da kareem sai wasansu suke….

 

Basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara da rabi bayan kowacce taje tayi ma anne sallama.

Part din anty Laila yana opposite na anty mubina, sai part din anty fadila dake chan nesa dasu sosai, sai kuma wani part din daban, duk sun zagaye bangaren anne dake a tsakiya…….

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 15-16

Update!!!

Saudi Arabia…!!!

Washe gari da safe kamar safiyar jiya haka alarm din bangaren ma’aikata ya soma qugi, agurguje kowa ya tashi duka maaikatan harda sabeeha, lokacin wajen karfe biyar daidai.

Sabeeha na zaune cikin hijab dinta kamar ko da yaushe, saida suka gama kafin ta shige bathroom din tayi wanka tare da dauro alwala, saida ta gama ta maido da hijab dinta ta futo daga bathroom din.

Agurguje tayi shirinta cikin uniform lokacin kusan duk maaikatan dakin duk sun fuce, aggagauce itama ta gama saka kayan nata ta tada kabbarar sallah, tana idarwa ta cire hijab din ta ninkeshi a gefe kafin ta zura mask dinta ta fuce daga cikin bangaren nasu.

 

Anatse take tafiya kamar wadda kwai yafashe ma a jiki, jikinta duk a mace game da wannan sabon almarin cikin rayuwarta wanda ya hanata sukuni, tunani iri iri daban daban nayi mata yawo akai ga tsoro ga fargaba.

 

Lokacin data shugo main house babu kowa a kasan hakan ya bata damar tsayawa don yin nazarin inda zata bi kafin taje saman,tana cikin wannan tunani sauran masu gyaran main house din suka shigo suma, bin inda suke bi itama ta soma yi harta gane inda zata nufa.

 

Lokacin data karaso saman bin wajen ta soma yi da kallo, nan take idanunta ya sauka dayan bangaren nan, wani abu ne yazo ranta kafin ta yaqice ce ta nufi part din da zatayi aikinta.

 

Tana zuwa bakin kofar ta tsaya ta saka pins din tare ba bude handle din kofar ahankali kamar mara gaskia, tana budewa ta sa kai ciki.

 

Tana shugowa wajen ya bade da haske, sanitizing hannunta ta farayi kafin ta cire takalmin dake kafarta ta zura crocs kamar yanda head ta nuna mata jiya, tana gamawa ta wuce cikin parlor.

 

Bin ko’ina ta soma yi da kallo kamar yaune ta taba ganin wajen, babu digon datti ko daya saima kamshi dake tashi, kwata kwata batayi gigin kallon wannan kofofi guda biyu ba saima dayar kofar dake wajen dining data nufa wanda haka ya tabbatar mata da nan ne kitchen, hanyar tabi ta shige cikin kitchen din a natse kafin ta sanya hannu ta tura kofar.

Gasping breath dinta tayi tare da sauke ajiyar zuciya saboda yanda kirjinta ke bugawa tunda ta shugo cikin part din wanda ta alaqanci hakan da fargabar da take ciki, dan yanxu ta qayyade koma menene a nan saman to abun cutarwa ne saboda tunawa da maganar da yar Ghana tayi mata akan cewa previouse ma’aikatan da sukayi aiki anan din ko kwana biyu basayi suke barin aiki anan saman shiyasa kowa ke tsoron nan din, ga yanda aka zuba uban dokoki.

 

Sauke ajiyar zuciya tayi tana mai addua aranta na neman tsari ga allah, ta dan dade a tsaye tana rarraba idanu kafin ta yunkura ta fara duban ko’ina, time table din abuncin da zatayi yana nan an mannashi jikin fridge sai wani dan box din medication da date harda time a jiki, saidan karamin timer dake reading time komai dai cikin sauqi.

 

Neman abun shara ta soma yi da mopper, tana ganin komai ta kwaso ta koma parlor ta soma gyara, allah ya taimaka ta iya gyaran ma sosai saboda gidan data baro bayan aikin kula datayi har da gyaran daki tana yi, agidan wannan tsohon kuwa har abunci tana dafawa irin nashi wanda matar gidan ta koya mata musammam idan ita bata gidan.

 

A gurguje ta gama komai saboda babu datti ko digo sai yar kurar da baza a rasa ba, dakin activity room ta shiga, nan ma saida ta gyara ko’ina ta goge kafin ta fito, duk wannan abubuwan da takeyi cikin natsuwa takeyi gudun kartayi wani kwakwara motsin.

 

Mamakin kayayakin wasa dake dakin activity ta soma yi, wasu abubuwan wasan ma tun tasowarta bata taba ganin su ba, yaran larabawa dai suna shan gata.

 

Kitchen ta koma ta soma preparing abunda ke rubuce a timetable din, duban date ta fara yi a jikin time table din, yau Wednesday, abunda ke rubuce ne a wajen ya dan bata mamaki don ruwan zafi kawai ta gani da just 1 apple for breakfast, wakeyin Karin kumallo da ruwan zafi zalla bama ruwan shayi ba sai kuma slice of apple, sanin bata da hurumi a cikin dokokin da aka bata yasa ta bude fridge din,  babu wani abun kirki a cikin fridge din na ci saidai fruits da chcolate sai vegetables… Apple din ta zaro guda daya ta soma slicing kafin ta jona ruwan zafi a heater kettle lokacin wajen karfe takwas tana gamawa ta samu waje anan kasan kitchen din ta zauna ta tankware kafafunta.

 

Duk bayan yan mintuna qalilan haka zata dubi time gudun kartayi kuskure har barci ya soma dibanta a nan zaune, haka nan ta hana kanta barcin nan har wajen karfe takwas rabi daidai.

8 dinma nayi alarm din kan timer dinnan yayi ringing, a furgice ta miqe tsaye jikinta na bari ta nufi wajen kettle din ta sake reboiling ruwan, tunawa da saiyasha magani a cewar matar nan yasa ta bude wannan box din ta zaro pack din magungunan ranar kafin ta dauka ruwan dake jere a wajen ta fuce daga kitchn din.

 

Daidai bakin kofar dakin ta tsaya, sai a lokacin taji wani sabon tashin hankali ya tunkarota, she’s just so anxious haka kawai.

 

Kai tsaye ta bude ahankali gabanta na bugawa kafin ta shige cikin dakin, dakin duhu babu wani haske kwata kwata daga inda take tsaye, dagowa tayi ta fuskanci cikin dakin, sai a lokacin ta dan hango hasken rana dake haskowa daga wajen labulen dakin.

Takowa ta soma yi anatse ba tare da tayi making any movement sound ba har ta karaso tsakiyan dakin, shuru ta danyi tana yin nazari nan take haske ya zagaye ko’ina ya gauraye dakin, duban ko’ina ta soma yi da kyau, daki ne babba sosai mai

dauke da gado dayasha beddings sai carpet a tsakiya, ko tv babu sai gefe kuma wata kofa ce kamar wani dakin daban kuma.

 

Duban gadon tayi ganin babu kowa akai kuma babu alamun da akwai mutun a dakin yasa ta danji sauqin fargabar da take ciki, ‘’toh ay babu kowa nan’’ ta fada aranta

 

‘’kila yaron yana bandaki’’ ta sake fada aranta, don daga yanda wannan matar ta fada cewa karfe takwas yake tashi, shuru shuru dai tana tsaye har wajen minti goma babu wani motsin, hakan yasa ta tunanin anya lafiya kuwa.

‘’first love’’ furucin data faraji Kenan, tabbas taji anyi magana saidai ta kasa gane daga ina ne tajiyo wannan sound din dake futa ahankali, dube dube ta soma yi har idanunta ya sauka wajen labulen nan dake facing dakin, chan kuma ta hango tudun abu ta wajen labulen wide glass din dakin ahankali ta soma takawa zuwa wajen,

 

tsugunnawa tayi daidai wajen curtains din sannan ta fara yaye labulen, tundaga yatsun hannunshi daya ajiye agefenshi zuwa bayanshi that is so wide zuwa sumar kanshi da take akwance kamar gashin jariri da alamu an aske mashi gashin ne ma amma ya fara fitowa,zaune yake ya tankware kafafunshi ya hade su waje guda ya zuba ma windown fararen idanu babu ko kiftawa.

 

 Afirgice ta koma da baya, hankalinta atashe azuciyar ta fara karanto addu’oin tsari kamar an kira sunan shi kuwa ya juyo ya kalleta, shima saida yadan razana.

 

Lafiyayyan saurayi ne zankadede a zaune, fari tass dashi, yana da yalwan gashin jiki da gashin baki daya cika mashi round innocent face dinshi, akalla zai kai shekaru talatin da yan kai a doran duniya, yana da wani irin kyawu da cikar haiba masha ALLAH gashi da girman jiki na mazan taka(masculine) dukda a zaune yake.

 

Kallon juna suka soma yi tsakanin shi da ita,sabeeha dai kasa dauke idanunta tayi akanshi, saboda kamar anyi magneting idanunsu waje guda babu abunda take tambayar kanta sai wannan ne sir din? Shi wannan din mutun ne? tsabar furgici ma kallon shi take kamar aljani saboda kyawun shi ya wuce musali.

 

Shikuwa ganin tana kallonshi yasa ya zuba mata idanu shima, jikinshi harya soma jaa, take yanayin fuskanshi ya sauya zuwa na furgici har jijiyoyin kanshi sun bayyana rado rado, sanye yake da wata farar riga mai dogon hannu sai wando shima fari tass masu laushi,, zumbur ya mike tsaye wanda yasa ta dago da kanta sosai kamar tana kallon sama don yana da tsayi sosai, saita zama kamar wata yar dwarf a gabanshi, bakinshi ya soma juyawa kamar wanda ke son yin Magana ‘’who are you?’’ ya fada a hasale, wannan kalmomi sune kalma ta biyu daya furta da kunnenta ya jiyo mata,

 

Inda take ya soma dosowa kamar wani zaki, ‘’who are you?’’ ya sake fada yana binta daf da daf, tana ganin haka ta koma baya cikin sassarfa har tana harde kafafunta, saida suka karaso tsakiyar dakin ya fara dube dube da alamu yana neman abunda zai dauka ya buga ne a kasa, ganin babu komai a kusa yasa shi kwala uwar kara wanda yasa sabeeha burkicewa sosai, take ta saki maganin da ruwan duka a kasa, ‘’na shiga uku’’ta furta bakinta na karkarwa,

 

wata uwar tsawa daya sake doko mata yasa ta zubewa a kasa sai hawaye wiwi, tata ta kare, wannan mai kama da aljanun ko mahaukaci ne? shiyasa ake ta tsoron hawa sama kenan,abunda yazo ranta Kenan.

 

‘’dan..dan allah kayi hakuri, karka min komai dan allah’’ ta karashe tana mai hade hannenta waje daya tana rokonshi, hwayenta kuwa basu bar tsayawa ba kuma daga gani ta torota sosai.

 

Wannan kukan nata ya sashi sarewa anan take kawai, sai yaji wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyarshi kamar an zuba mashi ruwan sanyi a kirjinshi, he was never soft towards kowa sai first love dinshi, baitaba yarda da kowa ba sai first love dinshi don duk wanda aka kawo don kula dashi tsoronsu yake ji kuma baya son ganin su kwata kwata, shi a ganin shi saboda su ne first love bata zuwa wajen shi kuma bata kulashi, sai gashi a karo na farko yaji wani iri game da wannan din.

 

Nan take ya tsugunna a gabanta kamar wani dan yaro dan shekara goma, musculine hannunshi ya dago ya dora shi akan fuskanta dake cikin mask, nan take ta bude idanunta data runtse ta sauke shi akan fuskanshi, ‘’í’m so..rry don’t cry’’

Mamakin yanda yake yi da fuskanshi da yanda yake goge hawayen idanunta take yi, wasu abubuwa yake yi kamar wani dan karamin yaro, hawayen fuskanta kuwa basu bar kwaranya ba dukda yana goge su don kamar tunzurata yake yi dayin hakan,

‘’don’t cry for me please’’

Ya sake fada yana mai hade fuskanshi abun tausayi kamar zaiyi kuka shima, ai kuwa kan kace me shima yayi zaman dirshen a gabanta ya soma kuka wiwi kamar karamin yaro, mamakin hakan ya sata dan tsagaitawa nan take kuwa ya soma bugun kasan tiles din da kafafunshi har yana zungurinta, tashin hankali, nan take itama ta zabura sai kuka jikinta har rawa yake yi tsabar furgici, ita abun da ya tayar mata da hankali shine, ya za ayi ace dingiqin zabgege mutun dinnan ne yake kuka kamar yaro, haka suka dunga kuka daga shi har ita kamar kananun yara suna nan zaune aka budo kofar dakin kamar za a balla kofar, maido da dubansa yayi ga kofar nan take kuwa ya miqe cikin sassarfa ya nufi wajen kofar baiyi wata wata ba ya rungume hidaya data shigo dakin hankali a tashe kamar an wullota.

 

Kankameta yayi sosai jikinshi na rawa, yanda ya rungumeta kamar wani dan karamin yaro, itama dai sai ta zama wata yar kif a gabanshi, hidaya dai kasa

motsawa tayi tana mamakin wannan al’amarin, bubuga bayanshi ta soma yi don ya saqalo hannayenshi a arms dinta tana mai duban maid din ranta a mugun bace.,

 

Yana nan a jikinta ta soma jan shi zuwa bakin gadonsa ta zaunar dashi, sabeeha dai tunda ta dago sau daya ta kallesu bata sake dagowa ba haka zalika kukan nan nata bata dainayin shi ba.

 

Hidaya na zaunar dashi ya matso kusa da ita ya kwantar da kanshi kan kafadarta, ‘’first love, she’s crying, for me tell her to stop crying’’

Ya karashe yana nuna sabeeha dake zaune dabas a kasa, kallon inda take hidaya tayi kafin ta maida dubanta gareshi, ‘’clean those tears’’ ta bashi umarni nan take, shi kuwa yana gama sauraronta ya goge fuskan tass, yana mai kallon ta yana murmushi sosai saboda dadin ganinta, shidai idan kaganshi yayi murmushi to sai idan yaga first love dinshi.

Miqewa hidaya tayi tsaye, kamo hannunta yayi da sauri kamar zaiyi kuka irin yanda kananun yara keyi, ‘’sit down and let go of my hands’’ ta bashi command, ay kuwa tana karashewa ya koma ya zauna ba tare da ya sake koda motsawa ba.

Tana ganin haka ta nufi hanyar futa tana mai kallon inda sabeeha ke zaune, ‘’ke kuma fito’’

Tana kaiwa nan ta futa daga dakin, miqewa sabeeha tayi tana mai kallonshi, yanda kasan baya fidda nunfashi yanda ya zauna ya natsu sosai, futa itama tayi daga dakin kafin ta janyo kofar.

 

A sitting room ta tadda hidaya dake zaune cikin shiri da alama office zataje, ta daura kafa daya kan daya fuskannan babu annuri, karasowa sabeeha tayi dan nesa da matar kafin ta tsugunna anan wajen har kasa.

 

‘’ke are you stupid? Bakida hankali ne kema aka kawoki ko kina da mentality, where are you from? Wani agency ne suka kawo ki?’’ abunda hidaya taso fada mata Kenan, saidai ta hana kanta da fadin hakan don yanxu dole ta hakura da duk maid din data dauka don kula dashi saboda bazaiyiyu a barshi shi kadai ba koda yaushe gashi ita kadaice a gidan ya yarda da ita sosai,wannan yasa ta hadiye duk wani abun dake bakinta ta soma Magana with so much class.

‘’whats your name’’

 

‘’sabeeha’’ ta bata amsa

 

‘’I’m sorry for that, patient ne,wannan da kike gani brother nane, he’s battling with amnesia caused by brain damage, nasan kin tsorata da shi, he’s not harmful at all sannan baya yin anything weird or strange, he’s just mentally unstable’’

 

Tunda ta fara Magana kan sabeeha na kasa bata dago ba haka zalika itama hidayan ita take kallo dukda bata ganin fuskanta saidai kwayar idanunta,

‘’brain dinshi ke controlling mind dinshi, shiyasa yake acting kamar 13 year old child, which was the neurological effect of the amnesia, ba wani abun zakiyi mashi ba fa ce kula dashi da maganinshi sai movement dinshi that’s all’’

 

Sai a lokacin sabeeha ta dago don da farko bata gane bayanan matar ba sai a yanxu,ko ba a fada mata ba tasan wannan itace madam din da head tace bazata samu ganinta ba, nan take taji wani iri aranta, a nata tunanin da farko ta dauka mahaukaci ne ganin yanda shima ya dunga kuka saida wannan matar ta mata bayani ta gane cewa ashe ba mahaukaci bane, larura ce dashi.

 

Nunfasawa madam din tayi don this is the first time ta zaunar da wata kaskantacciyar caregiver tayi ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login