Showing 93001 words to 96000 words out of 135321 words

Chapter 32 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

531

bedroom dinta.

Bangaren taj wunin yau a sama yayi yaqi saukowa kasan,daman hidaya haka takeso, koda jamid ya tambayeta dalilin rashin saukowarsa nan ta shiada mashi shi yaqi saukowa don haka ta aika mashi da breakfast in bed, bai kawo komai a ranshi ba don haka ya fuce daga gidan don akwai wani muhimmin aiki da zaiyi.

Bayan ya danci abuncin da hidaya ta aiko mashi yayi wanka ya saka kayansa masu kyau ya zauna bakin gado, dakin gaba daya yayi mashi wani fadi sosai gashi barad baya nan daman shike zuwa yana tayashi zaka suyi wasa, tunanun sabeeha ne ya fado mashi arai, itake yawan zuwa wajen shi a daidai wannan lokacin tana debe mashi kewa, saidai yanxu baya son ganinta ma kwata kwata, “i hate her” ya furta da dan karfi.

Komawa yayi bakin gadon ya nade kafafunshi yana tunani.

A hankali a hankali ya soma jin zazzabi na neman lulubeshi, kwanciya yayi har barci ya tafi dashi.

Wasa wasa zazzabi ya rike taj sosai, gashi babu wanda ya leko dakin, daman yanxu barad ne ke shugowa sai hidaya, toh yau duk cikin su babu wanda ya leko bedroom din, Tun wajen karfe biyar na yamma daya farka yake hawaye, jikinshi duk ya mutu gaba daya har wajen karfe tara na dare, hidaya data dawo daga office tama manta dashi gaba daya, barad kuma yana preparatları na exams, daman idan zasu fara exams baya wasa karatu yakeyi sosai, wannan yasa baije bedroom din taj ba, jamid kuwa cikin kwana biyun nan ayyuka ne sukayi mashi yawa a coffee factory dinshi.

Har sukayi dinner gaba dayan su babu wanda ya kawo batun taj, sabeeha dai yana ranta throughout the day gashi ta kasa samun natsuwa akan haka, wajen karfe takwas na dare ganin babu kowa a kasan yasa ta wuce saman

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 47

UPDATE

Saida suka gama shagalinsu kafin ya fita yabar dakin afiya ba tare da jin wani darr ba ko tunanin wani zai ganshi.

Jamid na fitowa daga bangaren sabeeha ya wuce sama direct zuwa part dinshi da hidaya rai a bace, yana shugowa ya tadda ta a zaune tana latsa system da alamu aiki takeyi, rai a bace ya soma magana “hidaya, why? Why? meysa saikinje to this extent don ki kori yarinyarnan, why,?”

Wani irin banzqn kallo ta mashi, “ban gane ba? What do you mean? Kaga nafa gane take taken ka? You’re trying to protect criminal kuma barauniyar yarinyar nan…”

Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa “karki sake kiranta da barauniya, tunda baki kamata da komai ba, inason ki sani duk abunda kike ina sane dake, kuma nasan duk wannan shirinki ne kuma bazan taba bari kici galaba akanta ba”

Yana kaiwa nan ya fuce daga part, saqe tayi tana kallon shi harya fuce daga bedroom din, cije lebenta tayi kafin tayi kwafa.

Cikin motarshi ya shige ya fuce daga gidan gaba daya, saida ya tabbatr ya futa daga tahlia street din kafin ya ganganra gefe yayi parking, kallon gefen seat dinshi yayi inda ya ajiye office bag dinshi, bude jakar yayi ya zaro sarkar da kudin, ranshi ba karamin baci yayi ba tunawa da abunda hidaya taso yi dazun, wayarshi ya zaro yayi dialing number khaal, bayan sun gaisa ya mashi bayannin komai da yanda yayi overhearing conversations din afiya da fadwa kan yanda zasu kulla ma sabeeha sharri ta hanyar sanya sarkar da kudin a kayanta, afiya ce ma da kanta ta shiga dakin sabeehar bayan ta tabbatar ta wuce sama wajen taj, inda head kuma ta tsaya bakin stairs, kwata kwata afiya bata san jamid ya ganta ba don saida ya tabbatar ta fito daga bedroom din sabeeha shi kuma ya shiga ya dauke kudin da sarkar, anan ne ma yaga waya a cikin kayan sabeeha, yayi mamakin ganin waya cikin kayanta don ba’a barin maids suna rike waya saidai a basu na aiki anan gidan idan aikinsu ya buqaci a basu waya, sanin cewa wannan zai saka sabeehar a cikin matsala yasa ya dauke wayar ma ya futo.

Saida ya gama yima khaal bayani kaf saidai bai kawo maganar wayar ba yayi shuru kafin suyi sallama akan a tafi a haka kawai.

Shuru jamid yayi yana tunani, ya kasa gane dalilin da yasa khaal yaqi yin wani abu akan al’amarin nan.

Wunin ranar sabeeha a daki tayi tana hawaye, tunda take a rayuwarta bata taba jin zafin kazafi ba sai yau, ta tabbatar da sharri ake binta dashi kuma allah ya kubutar da ita, abunda yafi bata tsoro shine wayar nan, waye ya dauke wayar? Ta tabbatar a cikin jakar nan take don da hannunta ta ajiye wayar kuka bata sake daukanta ba balle ta chanza mata waje, sannan ya za ayi ace wai ta hau sama ta dauka kudi da sarka? Saman ma bata gama tsantance ya yanayin wajen yake ba balle har ta iya daukan abunda ba nata ba, iyakacin ta da sama part din taj, shima jiyan tsautsayi yasa taje saman don dubo taj din saboda kwana biyu bata ganshi ba, shima dataje saman ta taddashi yana barci ne ganin haka yasa ta fito daga part din nashi ta sauko kasa, abunda ya kara tabbatar mata da sharri akayi niyar

qulla mata allah ya kubutar da ita shine yanda head ta dage akan cewa ta ganta ta dauko sarkan da kudi, wannan abu tsaya mata arai, haka ta kwana tana sallolin dare tana hawaye tana neman tsari ga Allah.

Bayan kwana biyu, babu abunda ya sauya saima abunda yayi gaba,zaman da take a daki har yafi na da, ko dining dinma bata futowa kwata kwata saidai idan jamid ne ya aika tazo ta hakan ne ma take ganewa idan yana gidan ko bayanan, akwai ranar da hidaya ta gindaya mata sharudan cewa karta sake ta sake hawa sama kwata kwata don bata yarda da ita ba, sannan ta hanata koda kuwa hada hanya ne da taj.

ranar tuesday da safe haka duk suka hallara a dining area din, dan dole haka ta fito saboda jamid ya aika a kirata, gaba daya ita wannan breakfast din dasu ba sabawa tayi ba, dataji kiranshi gaba daya jikinta sai yayi sanyi musamman da akace tayi satar da batayi ba, haka ta tattaro courage ta shigo inda duk suka bita da idanu, gaishesu tayi as usual babu wanda ya amsa sai jamid,kallo daya tareeq yayi mata saida ya dauka kusan minti biyu yana kallonta yana observing dinta, yaune rana ta farko daya fara ganinta tun dawowarshi, dukda baiga fuskanta ba ya lura she look naive, innocent and scared at the same time,daman shi using mutane kamarta ba komai bane a wajenshi, murmushi kawai yayi ya maida kanshi ga abunci dake gaban shi.

Zama sabeeha tayi inda take zama kullum kanta na kasa,tanason dagowa don ganinko taj na wajen saidai bata da courage in haka, maid din dake tsaye ne ta soma serving dinta tana gamawa ta koma baya, da mamaki duk suka dago suna kallon tareeq jin furucin da yayi, “good morning sister inlaw, how was your night?” ya sauke mata murmushi, dagowa sabeeha tayi ta kalleshi, bata taba ganinshi a gidan ba kuma bata san koshi waye ba amma tunda ta ganshi a wajen ta tabbatar shima family member na gidan ne.

“Good morning sir” Ta amsa gaisuwar sa,

ran afiya idan yayi dubu ya gama baci, matarshi dake gefe bata nuna komai ba amma kana ganin afiya zakasan ranta ya baci da furucin nasa, rai a bace ta fuce daga dining din ba tare da ta gama cin abuncin dake gabanta ba, tana miqewa tareeq ya bita da kallo.

tana barin wajen hidaya ma ta miqe don qasqantar dakai ne a wajenta ta zauna waje daya da caregiver, gashi ta kasa yin komai akai, saboda jamid.

kasa taba plate din dake gabanta tayi, gaba daya sai taji wajen yayi mata fadi sosai ga rashin jin dadi ganin babu taj a wajen daman anan dining dinne take samu ta ganshi, tunani ta soma yi ko meysa bai zo breakfast dinba.,

miqewa fadwa tayi  tana mai kallon tareeq’ ’zawj, ka sameni a ciki idan ka gama’’

jinjina mata mata kai ‘’okay habibty’’ ya amsa ta kafin ta bar wajen, sai a lokacin sabeeha ta fuskanci mijin fadwan ne.

Anan dining ya rage daga sabeeha sai jamid da tareeq, sabeeha dake zaune daga chan nesa dasu saida fadwa ta fita ta dan samu damar tsakurar abuncin taci kadan, jira take su gama ta tattara wajen koba komai zata danyi wani abu don zaman nan da takeyi ba dadin shi takeji ba, tafison tana aikinta, daman hidimar taj ne yanxu kuma ya hanata kusantarshi.

Miqewa jamid yayi yabar wajen shima, yana barin wajen tareeq ya Turo mata fruit bowl, in a nice way yace “Sister inlaw bismillah na lura bakici komai ba its nice”

Kallon bowl din tayi kafin ta dago ta kalleshi tace “Alhamdulillah nagode”. Murmushi ya mata very nicely ya miqe yabar wajen.

shuru tayi tana nazarin mutanen gidan, mazan gidan duk sunfi mutunci, shiyasa take daraja jamid sosai, saboda yanda ya tsaya mata, wannan ma gashi babu ruwanshi, he’s so nice, samun kanta tayi ta shan fruit din dake bowl din, saida suka bar wajen ta samu sakewa, tana gamawa ta tattara kayayyanki daidai nan head ta fito daga kitchen, ganin sabeehar yasa ta umarcin sauran maid su karbi kayan hannunta da gaggawa daman sun fito be don su kwashe kayayyakin wajen, gaisheta sukayi gaba dayansu, dakyar sabeeha ta iya amsa su don sai abun yayi mata banbanrakwai,tana kallonsu suka tattara kayayyakin tass suka wuce dashi kitchen ita kuma ta koma bedroom dinta.

Bangaren taj wunin yau a sama yayi yaqi saukowa kasan,daman hidaya haka takeso, koda jamid ya tambayeta dalilin rashin saukowarsa nan ta shiada mashi shi yaqi saukowa don haka ta aika mashi da breakfast in bed, bai kawo komai a ranshi ba don haka ya fuce daga gidan don akwai wani muhimmin aiki da zaiyi.

Bayan ya danci abuncin da hidaya ta aiko mashi yayi wanka ya saka kayansa masu kyau ya zauna bakin gado, dakin gaba daya yayi mashi wani fadi sosai gashi barad baya nan daman shike zuwa yana tayashi zaka suyi wasa, tunanun sabeeha ne ya fado mashi arai, itake yawan zuwa wajen shi a daidai wannan lokacin tana debe mashi kewa, saidai yanxu baya son ganinta ma kwata kwata, “i hate her” ya furta da dan karfi harda murguda baki.

Komawa yayi bakin gadon ya nade kafafunshi yana tunani.

A hankali a hankali ya soma jin zazzabi na neman lulubeshi, kwanciya yayi har barci ya tafi dashi.

Wasa wasa zazzabi ya rike taj sosai, gashi babu wanda ya leko dakin, daman yanxu barad ne ke shugowa sai hidaya, toh yau duk cikin su babu wanda ya leko bedroom din, Tun wajen karfe biyar na yamma daya farka yake hawaye, jikinshi duk ya mutu gaba daya har wajen karfe tara na dare, hidaya data dawo daga office tama manta dashi gaba daya, barad kuma yana preparatları na exams, daman idan zasu fara exams baya wasa da karatu, wannan yasa baije bedroom din taj ba, jamid kuwa cikin kwana biyun nan ayyuka ne sukayi mashi yawa a factory dinshi.

Har sukayi dinner gaba dayan su babu wanda ya kawo batun taj, sabeeha daman bata joining dinsu dinner saboda jamid baya nan, tsoron ma haduwa take da yan gidan, saidai taj yana ranta throughout the day gashi ta kasa samun sukuni haka kawai, wajen karfe takwas na dare ganin babu kowa a kasan yasa ta wuce saman zuwa bedroom dinshi, kamar yanda ta saba daman bata bari ya ganta saidai ta lekashi haka idan ta hangoshi saita fuce ba tare da ya ganta ba.

yanxu ma haka lekawa ta somayi a hankali ganin babu wani haske sosai a dakin, mamaki ta somayi ko yayi barci ne da wuri don yanxu schedule din barcin shi ya chanza sosai ba kamar lokacin da take kula dashi ba, karo kofar tayi a hankali ta karasa cikin bedroom din a hankali kamar wata barauniya, tana karasowa tsakiyar dakin ta soma jin saukar nunfashinsa ahankali, hakan ya tabbatar mata da barci yake yi, jiki a mace ta juya zata fuce daga dakin tajiyo muryarshi a jigace kamarma kuka yakeyi ‘’help, please help me, first love’’

chak sabeeha ta tsaya tana sauraron shi, sai a lokacin taji sautin nunfashinsa ya sauya sai kuma hakoranshi da suke neman hadewa da juna, tattara courage dinta tayi ta karaso bakin gado don ganinshi da kyau, hasken bedside lamp ne ya bata damar ganinshi da kyau, ya shige cikin duvet sai faman karkarwa yake gashi fuskanshi yayi jaa sosai bakinsa na motsawa a hankali.

hankali a tashe sabeeha ta karasa bakin gadon ta yaye bargon gaba dayanshi, ‘’innalillahi wa inna ialaihi rajiun’’ ta furta a hankali ganin yanda yake rawar dari, idanunshi a rufe sai faman kakkame jikinshi yakeyi saboda sanyin da yake ji.

cikin gaggawa ta tsugunna gabanshi ta taba goshinsa, zafin dataji ne yasa ta saurin zame hannunta ta miqe tsaye, ‘’subhanallah youre burning up’’

sama sama yake jin magana saidai yanayin da yake ciki ya kasa tantance koma waye a kanshi, sai faman kiran first love dinshi kawai yakeyi.

A.C dakin tayi gaggawar kashewa ta maida shi heater sannan ta janyo mashi duvet din ta lullaba mashi kafin ta fuce daga cikin dakin, kitchen ta nufa wajen first aid ta bude ta zaro panadol da bottle water kafin ta dawo bedroom, har zuwa lokacin yana nan yanda ta barshi,sai faman karkarwar yakeyi sautin kukanshi na karuwa sai faman kiran hidaya yakeyi, gabanshi ta karaso ta tsugunna, tana mai tausayinsa tace  ‘’sir ka daina kuka dan allah,sunan allah zaka dunga kira zakaji sauqi kaji’’

hannun nata ta sake maidawa kanshi don jin yanayin nashi, zazzabin ma yafi na dazu don kamar karuwa yakeyi any minutes, hannunshi ya sanya ya kama hannunta yana neman sauqi.

wallahi tana masifar tausaya wannan bawan allah, kwata kwata bata son ta ganshi yana jinya, dukda baya son ganinta kullum fatanta ya kasance cikin lafiya, don idan ta ganshi yana jinya zuciyarta karaya take sosai.

Gashi jamid baya nan balle taje ta sameshi, gashi tsoron haduwa take da hidaya don ta yanka mata warning kan cewa karta kara haurowa saman nan don kallon barauniya suke mata.

wata dabara ce tazo mata, mikewa tayi ta wuce bathroom dinshi ta debo ruwa mai dumi da towel ta dawo gabanshi, yaye duvet din nashi ta farayi kafin soma unbottoning din rigarshi, saida tazo karshe ta dan jinkirta kamar mai tsoro haka ta zame rigar tashi, take wide kirjinshi da kwantattun gashi ke kwance ya bayyana, cikinshi a shafe kamar bayacin abunci ga six packs dinshi kamar an zana a kirjinshi so attractive, saida ta kare mashi kallo tas heartbeat dinta na bugawa very fast,idanunta ne ya sauka akan nippie dinshi, maganar da yayi mata kwanaki ne ta fado mata arai    ‘’bibi meysa naki babba nawa karami’’, runtse idanunta tayi tana mai kokarin kauda idanunta akan surarshi da tunanin, tun bayan da abun nan ya faru ta kasa cire moment din daga brain dinta

akwai.

wannan ruwan data debo ta matse towel dashi ta soma goga mashi a kirjinshi tana mai kallon fuskanshi, har wani sauke ajiyar zuciya yakeyi, haka ta dunga goga mashi daga fuskanshi zuwa wuyanshi har zafin ya soma raguwa, saida tayi mashi wannan remedy din wajen sau uku lokacin kukan da yakeyi ma ya daina saboda relief din daya samu, tana gamawa ta mike zuwa bathroom din ta ajiye towel din ta futo, cikin closet dinshi ta shiga ta nema mashi kaya marasa nauyi sosai ta fito.

tunanin yanda zata saka mashi ta somayi, gudun kar wani sanyi ya sake shiganshi yasa ta janyo mashi bargo kawai ta luluba mashi sannan ta zauna a kasa tana mai kallon kyakyawar fuskanshi mai kwarjini.

har wajen karfe sha daya tana tare dashi watching his movement har barci ya fuzgeta, kamar da wasa cikin dare ta soma jin kuka, bude idanunta da zatayi kuwa ta ganshi zaune ya hade jikinshi waje guda fuskanshi na tsakanin cinyoyinsa, zama tayi bakin gado ta tabashi hannayenshi, saurin dagowa yayi a furgice don ganin ko waye, da mamaki yake kallonta don yana hango kwayar idanunta ya gane itace, ‘’sir are you okay? kanajin zazzabin ne har yanxu?, tell me mey kake so?’’ haka ta soma jero mashi tambayoyi yanda ta saba yi mashi idan taga bashi da lafiya lokacin da take kula dashi, fashewa da kuka ya sakeyi wanda ya sata matsowa kusa dashi bata ma san tayi hakan ba ta kamo hannunshi fuskanta abun tausayi kamar itama tayi kukan tace ‘’dan allah ka fada min meke damunka, tell me your pains, zazzabin ne? headach? ko mafarki kayi? let me know what to do bana son naga kana kuka kaji’’

muskutawa yayi dab da ita kamar wani maraya ya kamo hannunta gam cikin nashi, ‘’i’m scared, a gansu a barci na, i want to hide bana son su kamani’’

‘’waye ya biyoka? mafarki kayi?’’ ta sake tambayarshi tana mai kallon cikin idanunshi.

‘’yes,moto yayi exploding, sun tafi dasu duka, nima…nima’’

haka ya dunga mata maganganu marasa kan gado, tama kasa gane inda zancen nashi ya dosa,tunani ta soma yi tana mai kallonshi,daga ganinshi kasan a tsorace yake.

hannunshi ta kama ta rike gam, a sanyaye ta soma magana ‘’i will protect you bazan bari su kama ka ba kaji, trust me’’ haka ta dunga lallabashi harya yarda da

ita ya natsu tukunna ta soma mashi yan addu’oin data iya harya soma gyangyadi ya kwanta akan cinyarta.

kallon kanshi dake kan cinyanta tayi har zuwa lokacin hannunshi na cikin nata gashi sai sauke ajiyar zuciya yakeyi da sauri sauri, samunkanta tayi da dogon tunani akan maganganun da ya dunga yi mata dazu.

wannan dare dai sabeeha bata runtsa ba kwata kwata, saida asuba tayi ta sauke kanshi daga kan cinyarta ta gyara mashi kwanciyar nashi tana haki don akwaishi da nauyi tana gamawa ta luluba mashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login