Showing 108001 words to 111000 words out of 135321 words

Chapter 37 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

524

kai kawai,taimakon ki zanyi bayan wannan ma kin manta koke wacece?, youre nothing more than a  classless maid, so taimakon ki zanyi ke kanki’’

saurin runtse idanu sabeeha tayi batama san lokacin data daga hannu ta wankeshi da mari ba, saurin dagowa yayi ya kalleta rai abace, kasa cewa komai tayi sai hawaye, karar kofa yasa shi saurin yin baya ya matsa daga kusa da ita, taj ne ya shugo yana mai binsu da kallo, saida gabanta ya fadi ganin taj din a tsaye yana kallonsu, jikinta na bari ta matsa tana mai share hawayen dake fuskanta, ‘’bibi munata jiranki baki sauko ba’’ ya fada mata excitedly, ‘’hey uncle’’ 

murmushi tareeq yayi mashi yace ‘’nima zanzo ayi dani, kaje ka jira mu a kasa, zan yima fatima wani abu mai dadi” ya karashe yana mata wani dan iskan kallo.

Cikin jin dadi taj yace “okay uncle idan kun gama ka fito muyi ball harda kai”

Yana kaiwa nan ya futa ya barsu, harda janyo masu kofa, sabeeha baiwar allah a daidai wannan lokaci ji tayi gaba daya duniyar ta juya mata upside down, babu abunda take sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun” taj yana futa tareeq ya kalleta, ‘’you see? Mahaukacin mijinki baisan ina kanshi yake ba, he was so excited danace mashi zan maki wani abu mai dadi ke kuma you’re playing hard to get?, bazai iya maki komai ba cause he’s mental, mahaukaci ne you get? bai mayi considering dinki as a wife ba, bashida ma hankalin da zai san matsayinki’’ 

Wata iriyar dariya yayi tare da lakatar bakinta, tuni ta buge bakinshi tana kame jikinta tana hawaye, she can’t take the torture, bata taba fuskantar wannan abuse dinba sau yanxu, shi kuwa yana  kaiwa nan ya fuce daga dakin, yana futa ta tsugunna sai hawaye, jikinta sai faman karkarwa yake tsabar tashin hankali da bakin ciki, she feel disgusted, jikinta har wani kaikayi yake mata kamar tayi amai, she can feel his disgusting breath a kunnenta.

Tareeq na futa daga dakin yayi kicibus da fadwa dake haurowa saman, shugowarta kenan gidan ta hauro saman, tana ganinshi tayi saurin maida hannunta baya tana mai kallonshi da mamaki, yana ganinta ya soma dariya kamar wani banza yana kokarin cire duk wani suspicious act, fadwa kuwa kallonshi kawai tayi kafin ta girgiza kanta ta juya zuwa kasa yabi bayanta yana mamaki sauyawarta cikin kwana biyun nan, yanaji kamar ta fara ganoshi saidai babu wani alamu da take nunawa kan hakan….

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 53

Update!!

Washe gari ta kama Wednesday, da sassafe sabeeha ta tashi tayi masu breakfast, tana gamawa ta shiga wanka ta shirya, daidia lokacin taj ya farka, taimaka mashi tayi yayi wanka ya sanya kananun kaya  cotton short sleeves and pants masu kyau blue, gashinsa daya barbarze ta zaunar dashi ta taje masu, kan nashi sai walqi yake yi baki wuluk, dukda ba ayi mashi aski maj kyau ba hakan baisa kan nashi yayi kyau ba kamar ayi kitso.

Tana gamawa ta fesa mashi turarenshi da jamid ya saya mashi, babu abund ayake sai kallonta yana mumushi farraren set of hakoranshi a jere.

“Jirani na kawo maka breakfast saikaci, but you need to hurry up kar muyi latti”

Jinjina mata kai yayi yace “okay bibi”

Fita tayi cikin yan mintina kalilan sai gata ta dawo da tray a hannunta.

A gefenshi ta ajiye mashi tare dayi mashi bismillah,“let’s eat”

“Ni naci ay” ta amsa shi, turo mata dan bakinsa yayi yace “I won’t eat alone”

Tasan halinshi idan har ya kafe akan abu, ganin jayya zai iya saw suyi latti yasa ta daukan spoon din ta fara bashi, yanaci zai karba spoon din itama ya bata a baki haka suka dunga cin abuncin har suka cinye kafin ta fice daga tray din.

Wayar da khaal ya vata ta zare daga charge, tare da kashe socket din, kwata kwtaa bata iya operating wayar ba saidai ta latsata ta ajiye.

Futowar dayayi daga bedroom din yasa ta maida dubanta gareshi, “muje” ta fada tana mai bin hanyar futa daga bedroom din ta bude mashi kofa.

Atare suka sauka kasan tana biye dashi, anan compound suka jira jamid harya karaso suka shiga motarshi suka bar harabar gidan.

Sabeeha na daga zaune a bayan motar taj kuma yana gaba sai famab kalle kallen hanya yake babu wanda yace uppan bayan sun gaisa har suka karaso harabar asibitin Aldhar specialist medical.

Mask jamid ya miqa masu suka saka kafin su fito daga motar suka bufi cikin asibitin, direct wajen therapy section suka nufa inda akeyi ma taj, suna zuwa already time din shigarsa yayi don haka suka zauna anan nurses din wajen suka karaso don jagorantarahi cikin therapy ward din,qin yarda yayi ya bisu saida jamid yace sabeeha ta bishi saboda yana amsa emergency calls, cikin wajen suka shiga sabeeha nata kalle kalle, yau ne rana ta farko data taba shiga tare da taj din don yawanci jamid ne ke zuwa dashi.

Sun dauka wajen awa biyi a cikin ward din, sabeeha na daga zaune a gefe tana kallon yanda suke amfani da na’urori, har aka gama wayarta daya soma ruri ne yasa ta duba screen din, number data gani ne yasa tayi saurin daga ta kai wayar kunnenta, “fatima!”

“Naam” ta amsa

“Uncle jamid ne, idan kun gama ku sameni a parking lots,”

Sai a lokacin ta lura da jamid ne, don haka tayi saurin responding “okay tohm uncle”

Ta amsa shi tare da ajiye wayar, bayan minti goma suna fito daga asibitin, duben duben compound din ta soma yi, chan ta hango motar jamid din, ba tare da tunanin komai ba ta suka wuce wajen motar hannunta na cikin na taj, anan bayan seat suka zauna ita da taj din saboda maganin da aka bashi dake neman dosing dinshi off.

“Mu tafi ko”

“Yea uncle” ta amsa shi ba tare da ta dago kanta ba saboda wani irin azababben ciwo daya soma yi mata.

Tunda suka kama hanya babu wanda yace da wani uffan har suka hau babban titi, tuni taj yayi barcinshi, sai sabeeha data dafe kanta, sama sama ta soma jin karar wayarta,kanta yayi wani dummm sai wata kasala data mamayeta, ga wayar dai a hannunta amma ta kasa moving koda inche daya ne har idanunta suka soma kullewa ruff.

Matukin matar ne ya juyo tare da kallonsu su biyu, sanye yake da sak irin kayan da jamid ya saka lokacin da suka fito, fuskanshi yana sanye da mask baka ganin komai sai kwayar idanunshi da sukayi jawur, wayarsgi dake hannunsa ya daga tare da kiwa kunnenshi, “madam i have them with me as you requested”

Daga chan bangaren ne ala amsa shi, “ good job, ka kaisu somewhere very far ka zubda su, don’t make a foolish mistake, kayi abunda na saka ka kawai”

“Yes ma” ya amsa ta kai tsaye, yana kashe wayar ya fuzgi motar fiiii kamar zai tashi, tafiyar wajen rabin awa sukayi, a hakan ma saboda with high speed yake tukin, tun suna wuce mutane har sukazo wani waje kamar dessert, babu mutane sai uban jan yashi, parking motar yayi kafin ya futo daga cikin motar yana mai yin miqa, karan sigari ya zaro ya kunna da lighter kafin ya cizge mask din take fuskanshi ta bayyana, konanniyar fatarnan tashi tasha uban mai sai kyalli takeyi ba kyan gani, said ayasha tabarshi tass kafin ya wullar da karan sannan ya juya ga bayan motar ya bude barin da taj ke zaune ya janyoshi waje ya fiddashi daga cikin motar ya kwantar dashi kan yashin, kafin yayi banging kofar, juyawa yayi wajen barin da sabeehe ke zaune itama ya bude kofar ya janyota waje kamar kaya kai kace matattu ne, kwantar da ita yayi kusa da taj din har mayafinta na zamewa kafin ya rufe kofar yana mai kallonsu su biyun yana mai yin wani tunani, bazai iya tsallake umarninta ba da tuni ya gama dasu kawai, don haka kawai ya juya ya shige motar yaja motar ya barsu anan kwance.

Ahankali ta soma bude idanunta after 4 hours of  passing out, lokacin garin harya soma neman yin duhu, saurin runtse idanunta tayi ta bude saboda dishi dishi data soma gani, saida ta dauka wajen minti biyu kafin idanunta ya soma warware, afurgice ta mike zaune kamar wata zarraiya kallon wajen ta soma yi hankali a tashe tana innalillahi, idanunta ne ya sauka kan taj dake yashe a kasan gefenta, ko takan mayafinta  dake gefenta batabi ba ta rarrafa inda yake ta soma tabashi, “didi didi wake up innalillahi wa inna ilaiahi rajiun, ina ne nan”

Bude idanunsa ya somayi a hankali harya sauke su akan sabeeha, taimaka mashi tayi ya tashi zaune yana dube duben wajen, “bibi ina ne nan?wheres uncle?”

Ya jefo mata tambaya, wajen har echo yake yi saboda babu motsin komai sai muryoyinsu da sound din tsuntsaye gashi garin ya fara duhu sosai, rasa abunda zata fada mashi tayi gudun karya furgita don haka tace “get up”

Tana fadin haka kuwa ya miqe itama ta miqe tana fargaba, mayafinya ta janyo ta daura akanta, duban gabas tayi da yamma babu komai kamarma tsakiyan desert suke, tambayoyin dake kunshe akanta babu wanda zai amsa mata, babu abunda take sai innlillahi, tashin hankali da fargaba ya gama mamayeta gaba daya, ya akayi suka tsinci Kansu anan? Waya kawo su nan? Tabbas tasan sun shiga motar uncle bayan sun shiga bata sake sanin ina kanta yake ba sai yanxu sa suka farka a tsakiyar yashi babu kowa.

Tuni idanunta sukayi jaa, kana ganinta kasan hankalinta a tashe yake, dakewa kawai tayi ta hana kanta hawaye saboda taj, hannunshi ta kama ta ruke a cikin nata kafin ta mashi murmushin dole tace “muje uncle na jiranmu acahn” ta nuna mashi hanya, ita kanta bata san ina chan din zai kaisu ba saidai tsayuwar anan babu abunda zai tsinana masu har gwamma ma suyi ta tafiya har allah zaisa suga mutane.

Haka suka dunga tafiya yana biye da ita, kaffaunsu na limewa cikin yashin, sun wuce wajen 30mins sun tafiya babu wani sign din mutane ko titi, tuni taj ya soma complain din gaji, daman jikin yan hutu baya daukan wahal, ita kuwa sabeeha kamar ana kunna mata engine,tsoron kar abun cutarwa ya kamasu yasa take janshi kawai suna tafiya, saida suka kai kusan awa guda ta lura da kamar zageye wajen suke, at that point hawayen da take kokarin dannewa ya balle mata, cikin hanzari ta goge ganin, “bibi i’m tired, where’s uncle?, na gaji mu tafi gida wajen first love”

Dakatawa sabeeha tayi ta kalleshi tana mai hana kanta kukan dake ciyota, “yanxu zamu karasa gida, kasan me, lets have a race”

Excitedly kuwa ya amsa ta da toh suka fara gudu, sun dade sosai suna gudu har garin yayi dubu sosai, tsayawar datayi ne tana haki yasa taj tsayawa shima,”bibi…na rig..”

Shuru yayi ganin tana kuka, kuka sosai kamar ranta zai futa, ta kasa hana kanta dainawa,ganin tana kuka kuwa shima ya fashe da kukan, daidai nan tsintsaye suka taho rututu wanda hakan ya tsorata su sosai, batasan ma lokacin data shige jikinshi ta kankanmeshi, shima din dai neman makafa yake a wajenta, haka suka dunga kuka babu mai kawo masu dauki ya Allah….

Chan asibiti kuwa jamid daya wuce masallacin nan asibitin yana dawowa ya shiga wajen ward din ganin basu fito ba, already yana duban time saboda therapy din na 2 hours ne, nurse din data shiga dasu ce ta shiada masa ay sun fito, shuru jamid yayi yana wani nazari kafin ya nufi waje don nemansu, duban duniya yayi ma gaba daya asibitin bai gansu ba, hankalinshi ba karamin tashi yayi ya koma ciki ya sake tambayr receptionist ko ya gansu, nan kuwa ya shaida mashi sun fita, hankalin jamid bai gama tashi ba saida ya tabbatar basa cikin asibitin gaba daya, nan ya umarci ganin cctv camera na asibitin, authorities din wajen basu hana shi ba don haka suka kunna mashi previous recordings din cikin asibitin da wajen futa, nan take kuwa ya gansu sun fito atare, har wajen parking lot, wajen parking lot din ya kurama idanu inda yafa sun shiga wata mota irin tashi sak babu wani

banvanci, plate number ne kawai banbanci, tuni hankalinshi yayi doubling wajen tashi babu abunda yake sai  innalilahi, “waye ya dauke su? Ina aka kaisu? Wace mota suka shiga?”

Tamvayar da yayi ma kanshi kenan, tambayar nurse din dayayi masu therapy ya somayi ko akwai wanda yazo ko wani abu dai daya faru befor du fita, nan ya shaida mashi babu wani wanda yazo wajensu, hankali a tashi jamid ya juya harzai fuce nurse din ya tuna an kira sabeeha lokacin da aka gama yin therapy din, and he remember tace “okay uncle”

Jin wannan kadai yasa jamid ya sake burkicewa, waye ya kira sabeeha har ta amsa da okay uncle, shidai yasan tun bayan shigansu bai kirata ba bayan wannan ma waya ya dunga yi related to business dinshi harya gama aka kira sallah ya fuce zuwa masjid din cikin asibitin.

Tambayarshi suka somayi ko wani abun ne ya fadu vaima bi ta kansu ba ya fuce daga asibitin yana dialing number khaal a furgice, yana dagawa ya shaida mashi abunda ya faru, ba karamin furgici khaal ya shiga ba shima, haka nan ya futo daga cikin gida daman bai dade da shugowa ba saboda ayyukan daya tsaya yayi a company.

Madam dinshi na tambayr lafiya baima tsaya yayi mata bayani ba kawai yace mata its urgent don haka ya fuce daga gidan with high speed, direct police station suka wuce shida jamid inda suka hadu achan suka shigar da karar batan mutane biyu wanda suke suspecting kidnap ne, suna shigarwa hukumar policey din garin suka soma aykinsu ta fannin buncike, asibitin suka fara komawa inda jamid ya masu bayanin komai daga kan lokacin da suka shigo har zuwa lokacin daya wuce masjid, cikin cctv room suka shiga sukaga abunda ya faru nan suka dauka informations daban daban kafin a tura binciken motar da suka shiga mai plate number din, koami dai sounds suspicious sannan ayanda sukayi concluding komai da wayarda sabeeha tayi looks like a planned kidnapping.

Basu gama concluding komai ba saida suka duba plate number aka tabbatar da fake ne kuma baza a ita tarciing motar ba.

Babu abunda khaal keyi sai innalillahi har hukuma ta fara questioning dinsu shida jamid ko akwai wanda yake da kudiri ko suke tunanin zai iyayin haka, kallon juna jamid da khaal sukayi suna nazari, har jamid zaiyi magana khaal yayi saurin katseshi yace “babu”

Da mamaki jamid ke kallon khaal jin abunda ya fada saidai bazai iya interfering ba don kawai yayi shuru, nan suka sake tambayr shin taj din da sabeeha relatives ne, don saboda wayar data amsa shima zasu iya daukan wannan as something to suspect, take khaal ya shaida masu mata da miji ne, wannan bazaisa bazasuyi bincike ba don komai bin didigi sukeyi.

Daga nan asibiti suka dunguma gaba dayansu zuwa headqauters din poliçeyi din, nan suka soma bincike sosai, har call investigation center dake karkashin saida suka shigo ciki, nan jamid ya bada number sabeeha daya bude mata, duk yanda sukaso su gano wani abu suka kasa saboda wayar an kashe dole saida suka bi ta ip address din wayar shima anyi blocking wannan ya kara tabbatar masu babban

case ne nan aka fara shigarda karar gaba daya station da hanyoyin traffic, nan DG police ya shaida masu idan akayi exceeding 24houra babu wani information dole zasu fidda abun pubic, khaal bai hana ba don ka’ida ne.

Har wajen midnight hankalinsu na tashe, babu wani labari, hope dinsu daya idan aka kunna wayar sabeeha tanan ne kawai zasu iya gano wani abun, manya manyan hackers dinsu babu yanda basuyi ba don ganin sun shawo kan wannan matsala saidai abun ya faskara.

Bangaren su sabeeha bayin allah, gaba daya sun gama jigata sosai, ga yunwa,kishirwa ga sanyin wajen kamar kankara, abu mafi tayar da hankali ga tsoro da fargaban kar wani abu ya cutar dasu gashi babu haske kwata kwata saina wata, tayi kukan harta godema allah shima taj din yaji jiki sosai ba kadan ba haka suka cigaba da zagayen wajen nan cikin ikon allah suka hango wani waje kamar daga chan nesa irin ginin kasa dinnan mai dan rufi, dukda tsoron da sukeji hakan baisa tayi hamdala ba, koba komai zasu samu wajen kafewa, dakyar suka karasa wajen bashida wani girma sosai kamar kogo, duqawa sabeeha tayi ta fara shiga ciki kafin ta miqa mashi hannunta ya shugo shima, duban wajen tayi don tabbatarda babu abunda zai cutar dasu kafin ta zame mayafin kanta ta kakkabe masu wajen,taj sai faman naniqe mata yake ,kakkabe wajen tayi da mayafinta kafin zu zauna, atleast yanxu abu daya yadan kau, sanyin desert din, don cikin wajen is warm ba kamar wajen ba, sai ayanxu yunwa ta soma nanuko su,

Muryarsa na cracking ya kira sabeeha “bibi I’m so hungry kibani abunci”

ya fada a wahale, saiya bata tausayi sosai, ayanxu bata kanta ma take ba ta shi takeyi, baya jure yunwa kwata kwata, shiyasa meal dinshi yake zama ready tun kafin ya nema, 

Hannunshi ta riko cikin nata tace “sorry didi, babu abunci yanxu zuwa anjima zan baka oaky?”

Girgiza mata kai yayi gwanin ban tausayi tare da daura kanshi kan kafadarta, “in baka labari na?”

Ta tambayeshi, “uhm” ya amsa ta.

Gyara zama tayi kafin ta fara bashi labari, “sunana fatima sunan babana dalhatu, bansan baba na ban taba ganinshi ba, mamana kawai na sani kuma ina sonta sosai har cikin ziciyata kuma ina kewarta, saidai ita bata sona, ada bar kayyade hakan ba sai yanxu, bansan meysa ta tsaneni ba, akwai lokacin da kaka ta ta taba cemin duk abubuwan dake faruwa da rayuwata saboda mahaifina ne kuma shiya janyo ma mamana bata samu cigaba ba arayuwarta”

“Bibi who is kaka? And why mama hate you so much” ya tambayeta cikin whisper

“Kaka is my

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login