Showing 75001 words to 78000 words out of 135321 words

Chapter 26 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

520

ya rasa me zaiyi ma gaba daya.

bai taba tunani maya ta lalace sosai ba bai taba kawo cewa zaiga rana irin ta yau ba, yau yarshi ce ke shaye shaye kuma na muyagun kwayoyi da manyan muyagun substance, innalillahi wa inna iaihi rajin un, he was so shattaered and angry at the same time, blaming kansa kawai yakeyi da upbringing din daya bata, da sangartata da mummy tayi, sai ayau yake dana sanin dawowa kasar nan da sukayi don bai amfane su da komai ba, dondai promotion da suka samu duk a banza tunda gashi diyarsu tazo ta dauki halayen turawa wanda su a wajensu is a normal thing for an adult, su kuwa ya saba addinin musulinci kuma yar musulmai.

futa kawai yayi daga dakin, haka ya kwana cikin baqin ciki da regrets.

yau ta kasance weekends, mummy na gida haka zalika daddyn ma bai futa ba.

zaune suke kan dining mummy na shirya daddy breakfast, shugowar maya cikin dining area din yasa suka kalleta gaba dayan su.

cikin murna ta karaso inda mummy take tayi pecking din kumatunta ‘’good morning daddy and mummy’’

mummy ce kawai ta amsata kafin ta zauna.

anatse sukayi breakfast suna gamawa daddy ya kalli maya, ‘’jeki haka kayanki’’

cikin murna ta dago tana kallon daddy, don daman ta shirga mashi karya kan cewa zasuje school camping, pecking dinshi tayi excitedly tace ‘’wow, daddy ka barni zanje?, thank thank daddy i love you’’

kasakarasa cin abuncin maya tayi tsabar farin ciki ta miqe zuwa bedroom dinta ta soma shirya kayanta a katon akwatinta, qananun kaya ta kwaso masu kyau da daukan hankali sai sauran abubuwan data zata buqata tana gamawa ta sauko da box din nata da laptop dinta da komai.

a sitting room ta tadda daddy da mummy a zaune, mummy ma ba karamin dadi taji ba ganin daddy ya bar mayan zata je camping din.

‘’daddy na gama’’

kallonta ya soma yi sama da kasa kafin ya zura hannunshi cikin aljihunshi ya zaro gaba daya substance dinnan nata daya tsinta a jakarta da wanda ya samu a dakinta lokacin daya shiga ya dunga tashinta, ashe saida ya buncike ko’ina ya tsinto inda take boyesu.

a kidime take kallon hannunshi dake nuna mata, wani irin dumm ta soma ji akanta, tabbas wannan usher din da taketa nema ne wanda saurayinta ya bata, dayan kuma kloe ce ta sammata, ina daddy ya samu wannan kenan.

‘’ga wannan kin manta dashi’’

kamar mara gaksia ta soma magana ‘’daddy ba nawa bane ba’’

‘’oh kinsan menene kenan huh?’’

jikinta ne ya soma kyarma don daman shike fara haskota idan bata da gaskia, kallonsu mummy ta soma yi daya bayan daya ‘’daddy whats this? whats going on’’

afusace ya miqe ‘’ga ta nan ki tambayeta bahijja, gata nan let her speak for her self’’

tuni jikin maya ya dau kyarma, shikenan yau asirinta ya tonu, ‘’ka fada min meke faruwa mana’’

rai a bace ya soma magana ‘’bahijja diyarki, diyarki shaye shaye takeyi, shaye shayen ma na miyagun kwayoyi wanda ke cutarta young youth kamarta, it has been introduce to her by her friends da saurayinta, gata nan ta fada maki’’

tuni zufa ta wanke maya, ya akayi daddy yasan da wannan, ‘’maya kin cuci kanki, tarbiyar danayi maki kenan?, how could you?, why following this wrong path why? me kika nema kika rasa a duniyanan nan? shin kinsan wannan abun how many effect zai maki?, kinsan irin illar da yakeyi? how could you?, ‘’

‘’stop daddy stop it, wani shaida kake dashi daya nuna cewa wannan din na mayan nan?, how could you even think about that?’’

‘’bahijaaa!!!!!!!!!!!

shin kina sauraron kanki kuwa? wallahi i’m beginning to blame all of this on you, laifinki ne, bakya sa ido kwata kwata akanta, a matsayinki na doctor? how can you not even tell diyarki na shaye shaye eh???what kind of a mother are you?, toh bari kiji, nine mahifin maya, na fiki iko da ita don haka tak, tak karna sake jin kin furta kiyi min shuru i will make decision on her’’

take mummy ta fashe da kuka, ganin maya ta tsugunna tana rokon daddyn ‘’daddy wallahi bazan sake ba, don allah kayi hakuri, wallahi wallahi bazan sakeba.’’

‘’get up, dauki box dinki lets go’’ ya umarceta

‘’majeed ina zaka kaita’’ mummy ta fada tana hawaye, 

ko kallon inda take baiyi ba ya fuce,maya na biye dashi a baya da akwatinta

mummy naji na gani ya futa da maya, nanybee dake tsaye a gefe itama hawaye takeyi sosai, tashin hankali kenan, keys mummy itama ta dauka tabi bayansu saidai sunyi mata nisa.

saida ta gaji da zagaye ta dawo gida ta soma dialing number majeed, gaba daya hankalinta ya gama tashi hawaye kuwa ta kasa dainawa.

bayan futarshi da awa daya sai gashi ya sake dawowa, mummy dake sama tanaji karar motarshi ta sauko kasa, anan sitting room ta taddashi

‘’majeed ina kakai min yata? haba majeed yau koda ace abunda yafi shaye shaye maya keyi bai kamat aka yanke hukunci cikin fushi ba daga baya kuma kazo kana dana sani? maya ma yata ce kuma inada iko akanta nima tunda nina tsugunna na haifeta’’

ganin duk ta burkice yasa shi janyo hannunta ya zauna da ita, lokaci guda kawai ta bashi tausayi baisan lokacin daya rungumeta ba saida ta ta soma dawowa daidai tukunna ya saketa yana mai kallonta.

‘’ki kwantar da hankalinki bahijja, ban yanke hukunci ba saida nayi dogon tunani, kina tunanin duk abunda tayi zan kaita inda zata cutu ne? haba bahijja, maya ita kadai ce diyarda allah ya bamu, kuma son da nake mata ne yasa na yanke wannan hukunci don ina ganin shi kadai zaisa ta natsu kuma ta fuskanshi alqibla’’

‘’dan allah ina ka kaita tana ina’’

baiyi niyar fada mata ba amma ganin yanda ta damu yasa shi cewa ‘’nigeria’’

cikin sauri ta mike, ‘’haba majid nigeria? ita da wa? wazai kaita?’’

‘’ita kadai, this is the first step to allowing her understanding her mistake’’

‘’haba majeed, rabonmu da nigeria tun tana nigeria, bata san kowa ba achan, yanxu ya zaayi ace ka tura ta ita kadai,’’

‘’bahijja calm down, na kira anne, zata sauka acahn’’

hankali bahijja idan yayi dubu ya sake tashi, ‘’anne?why? meysa zaka yanke hukunci ba tare da shawartata ba’’

‘’saboda nine mijinki, kuma nike da iko daku, ina da damar yanke hukunci and thats final, maya is staying with anne, ta gama zaman nan har abada’’

‘’toh wallahi nima kuwa bazan zauna ba, na gwammace nabar aikin nawa, i cant stay babu diyata’’ tana kaiwa nan ta fuce ta barshi nan zaune, daman hakan yakeso, lokaci guda kuma kawai sai yayi hamdala bai taba tunanin hakan ba, over how many years kenan yana convincing dinta akan su koma taqi, tunda suka dawo bai taba samun kwanciyar hankali ba daidai na kwana daya tunawa da shine sanadiyar samun matsala datayi da mahaifiyarta saboda ta dage sata aureshi, she choose him over her family shiyasa yake masifar sonta kamar ranshi baya iya dogon fushi da ita.

*** 

Saudi!!!

Taheel group of company.

zaune suke gaba daya manya manyan company, babu wanda ya taba expecting wannan kiran gaggawan a daidai wannan lokacin, khaal na daga zaune sai sauran shareholders kowa na jiran karasowar hakimar don jin dalilin tarasu datayi.

cikin mintina qalilan saigata ta shugp cikin hall din, walking majestically as always, mikewa sukayi gaba daya saida ta zauna kafin suma suka zauna,

ba tare da wani bata lokaci ba soma magana ‘’na tara wannan urgent meeting dinne saboda zanyi announcement’’

kallon juna suka fara yi gaba daya khaal dai tunda ya zauna ya nade hannunshi yana sauraronta, haka zalika idanunshi na kanta, daman yayi exepecting haka saidai not soon enough.

babban lawyer dake kula da harkokin compny ne ya shugo da wasu takardu a hannunshi yana zuwa ya tsaya sama wajen da suke yi announcement, copies din dake hannunshi ya miqa ma secretary din hidaya don ya rarabawa kowa, tun kafin ma lawyer ya soma magana mutanen wajen suka fara kallon juna khaal dai ko kallon paper baiyi ba.

nan lawyer ya soma bayani, ‘’according to the commercial law of companny section 288  act 102,’it is stated that mai jinya ko mai rashin lafiya bazai taba zama director ba, cutar data kama ga cutar barin jiki, matsalar kwakwalwa dadai sauransu that will enable to work, with the provision and hardwork of the acting ceo i hereby pass special resolution to mrs hidaya taheel tajudeen to be the director of this comapany as she is the only next kin to the heir and the major shareholder with 60% share, duk wanda is against this will face the trade law’’

tsit kakeji ciki ya duri ruwa waenda basa shiri da ita tuna hankalinsu ya tashi.

maido da dubana nayi ga khal, gaba daya yanayinshi ya sauya, the outcome of this ya gama bashi mamaki, yaushe hidaya ta zama the only person with hiegest share?, ina share din taj? that means ta dauke nashi kenan or what? don yasan shike da 40%, ita kuma 10% sauran 10% kuma na afiya ne da fadwa.

ashe all the time she has already prepare her self kuma tazo ne lokacin da babu wanda yayi tsammanin hakan.

lawyer ne ya sake tambayr ko akwai wanda yake against hakan, babu wanda yayi magana don haka a take aka bata mukamin wanda ta dade tana shiri akanshi.

hidaya dake zaune ko kallon inda khaal yake batayi ba, daya bayan daya shareholder suka fara zuwa suna congratulating dinta, kowa da abunda yake ransa.

saida aka gama ta wuce office hankali kwance babu abunda ya dameta, mutane kuwa dake aiki a company sai cecekuce akeyi.

tana zaune a office saika khaal ya shugo a fusace, daman tasan zaizo don haka she’s ready for him, hannunshi na karkarwa ya soma pointing dinta ranshi a bace ‘’hidaya!!! ina shares din taj? so this was your plan? daman dalilin dayasa kika bayyanama duniya lalurar tajudeen kenan, to use that don ki samu abunda kikeso? why are you so heartless?, me yaron nan ya maki?, why?’’

wani irin murmushi tayi na rainin hankali, kafin ta sauya fuska kamar bata san me yake magana akaiba ta soma rage murya, ‘’with due respect sir, babu yanda za ayi mahaukaci ya kula da wannan company din, ni kuma nazan taba bari legacy dinmu ya tafi a banza ba, wannan hardwork din abuh ne da ummuh’’

‘’sai akace maki taj din bazai samu sauqi ba? maysa zaki tureshi gefe? he’s the only heir to this company’’

idanunta lokaci guda sukayi jaa, ‘’no khal, i am the director now, i make my self the ceo so i be the heir, why cant you understand me eh? i’m doing dis for all of us and besides ni ce next of kin kuma i’m responsibie for taj, what ever decision i make babu wanda ya isa yayi questioning dina’’

‘’karya ne hidaya, youre doing this for your self, kinayi ne don kanki kawai,saidai inason ki sani i will never allow this never, and let me remind you idan kin manta bari na tuna maki, ayanxu bake kadaice keda iko akanshi ba legally, his wife!!! matar da kika aura mashi, his first legal wife nada iko akanshi fiye dake so keep that in mind’’

yana kaiwa nan ya fuce rai a bace, yana futa ta miqe tsaye ta soma zubar da abubuwan dake kan table dinta, idanunta yayi jaa sosai, hankali a tashe, bata taba

tunanin auren datayi ma taj zai zama threat a gareta ba, gaba daya tama manta da batun auren don daman tayi mashi auren ne saboda ta samu access to all his share, don bazaiyiwu tayi tranferring komai cikin sauki ba sai yana da aure wannan yasa ta yanke hukuncin tayi mashi aure’wanda hakan yazo a daidai lokacin da yayi rashin lafiya, wannan yasa ta umarci doctor ya bashi medication din dayafi karfin kwawalwarshi.

shuru tayi tana nazari, yanxu duk wannan plans din datayi idan ta sake wannan auren zai iya ruguzawa ba tare da ta ankare ba, how could she be so stupid ta kasa yin auni da dogon nazari akan wannan?

 meysa tsohonnan ke shiga gabanta ne? why why!!!’this old man, karka fara abunda bazaka iya karashewa ba’, ni hidaya babu wanda ya isa yayi threatning dina’ ta fada aranta.

nan take ta soma wayoyi daban daban ta dade tana waya kafin ta tattara komai nata ta futo daga office din.

Bangaren sabeeha, hankalinta ya kwanta sosai, tunanin da takeyi ta rage saboda ganin yanda taj ke cikin farin ciki, duk inda yake tana wajen don jamid ya umarceta akan ta dunga sa ido sosai akan taj din, yanxu ya fara sakewa sosai kamar kowa, sannan ta gama karantar kowa na gidan, daga kan afiya zuwa ga fadwa, kwata kwata basa son taj, mugunta ma suke mashi musamman afiya dake mocking dinshi a sunan tana sonshi kiri kiri, wannan abu yana yima sabeeha zafi saidai bata isa tayi magana ba, don ko jamid shima baya ce masu komai hasali fuska yakeyi kamar baisan sunayi ba, kullum zasu sauko kasa ita da taj haka zaita zagaye gidan, inda yafi son zuwa kuwa garden ne, kullum suna chan yana zaune tana gefensa yana kallon garden din ga dawisu na yawo a wajen, yanxu haka ma suna daga zaune tana kallonshi ta doka uban tagumi shi kuwa babu abunda yake sai kallon ruwa dake futa daga pipe yana ambaliya a wajen, gaba daya ta shagala da kallonsa saida taji splash din ruwa a fuskanta wanda ya sata kallonshi, dariya ya soma yi mata ‘’hahah kalli ruwa a fuskan bibi na’’

itama dariya ta soma yi, tana shirin magana ya sake splashing dinta, take kuwa ta miqe ‘’ka bari zaka cjqani’’

bai saurareta ba ya daga pipe din gaba daya ya cigaba da watsa mata ruwan, gudu ta somayi yana binta yana dariya, itama dariyan ta somayi saida ya jigata jagab shima ya jiqa kanshi, bai kyaleta ba saita ruwan ya daina zuwa gaba daya kafin ya tsagaita.

matsowa tayi inda yake tana goge fuskanta ta soma magana yi a shagwabe tace ‘’jibi yanda ka jiqa kanka, saikayi mura ko’’

‘’mu tafi ciki ka sauya kaya’’

jin yayi shuru yasa ta dago ta kalleshi, idanunshi kuri ya tsaida waje daya akanta, bin idanun nashi tayi da kallo harzuwa inda yake kallo, bata gama processing  abun da yake ma kallonba a jikinta sai jin hannushi tayi kan nipple dinta da yayi pointing out shatinsa ya futo sosai saboda jiqewar da kayanta yayi ga boobies dinnan sun fito muraran abunda take masifar jin kunya a jikinta,

daman ita ba gwanar saka bra ba, batadashi ba sai wata half vest da take dashi kuma take amfani dashi.

‘’bibi what is this’’ ya sake tabo dayan nipple din nata, 

tsikar jikinta ne ya tashi lokaci guda, a razane ta kalli hannunshi nashi, mamaki ya gama cikata bata ma san lokacin data buge hannayenshi  ba duka biyu ta juya tana furta allahumma ajirni fi musibati, wani irin tsoro ne ya durar mata don babu zato ba tsammani taji hannunshi, juyowa ya sakeyi yana mai son sake ganin koma menene a wajen tuni ta toshe da hannayeta biyu kamar ta nutse a kasa, abunda bai taba faruwa da ita ba ‘’bibi menene wannan?’’ ya sake tambayarta ita dai kauda idanunta tayi gefe ta kasa kallonshi balle ta bashi amsa, shafa kirjinshi ya soma’ ’oh!!! inada irinshi nima, but bibi meysa naki babba?’’

rasa abun cewa tayi kawai ta nufi hanyar barin wajen, yana ganin haka kuwa ya bi bayanta, afiya dake hangosu ta sama kasa gasgata abunda idanunta suka gane mata tayi.

hidaya na dawowa afiya da fadwa suka je wajenta da rahoto,saida afiya ta zayyane mata komai, da mamaki hidaya ke kallon afiya jin abunda ta fada, ‘’wai ukty bakiyi tunanin waennan abubuwan bane kika aura mashi mace?, namiji ne fah? bakya tunanin wani abu ya….’’

afusace ta kalleta ‘’shut up, dont even think about that,’’

fadwa ce ta dora da, ‘’wai ukty kinqi fada mana komai, allow us to avenge with you’’

kallonsu tayi daya bayan daya kafin tace, ‘’kudai kawai kusa ido, this is just the begining’’

‘’but ukty wannan yarinyar fa? meysa kika aura mashi ita kinsan asalinta ne? bakya tunanin wannan auren zai zama..?’’

afiya ta tambaya

‘’kina tunanin zata aura mashi mai asali ne,mteww? ‘fadwa ta fada

nunfasawa hidaya tayi sounding unbotherded ‘’gobe zata bar gidan nan,’

Wannan litaffi paid book ne, gake buqata zai iya tuntuba na ta whatapp 08032542629

Rukayya umar.

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 39-40

‘’ 

update!!

the next day!!

bugawar da zuciyarta keyi ne ya tsananta, yau tunda ta tashi take jin wani irin yanayi a tattare da ita, tsoro fargaba ya gama mamaye zuciyarta babu dalili.

da kyar ta samu ta miqe tayi wanka ta shirya cikin uniform dinta kafin ta wuce sama.

tana karasawa saman already ya tashi, saida ta ganshi abunda ya faru jiya ya dawo mata, take taji kunya ta lulubeta, taj dake zaune yana hamma don bai dade da tashi ba yana hangota daga nesa ya miqe yana mai kiranta ‘’bibi na, good morning’’

daurewa tayi tana mai kaucema ganinshi ta karaso inda yake tace ‘’good morning friend, bari na hada maka ruwa sai kayi freshen up ko’’

‘’okay bibi thank you’’ ya amsa ta yana lumshe idanunshi, satar kallonshi tayi ganin yana miqa, karaf idanunsu yayi merging, wani irin cute murmushi yayi mata har kumatunshi na lotsawa, saurin dauke idanunta tayi ta wuce bathroom domin shirya mashi hot bath,saida ta tabbatar ta ajiye mashi duk abunda tasan zai buqata kafin ta futo.

tana futowa ya shiga yayi wanka ya shirya yanda ya saba kafin ya fito parlor inda take jiranshi kullum idan ya gama.

a tsaye ya taddata cikin saurin ya karaso inda take ya kama hannunta yana sauke mata lausassan murmurshinsa dake sata shagala, ‘’let’s go bibi na’’

kokarin kwace hannunta ta soma yi ya hanata, badan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login