Showing 48001 words to 51000 words out of 135321 words

Chapter 17 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

779

wani murmushi mai kama da na taqaici kafin yace ‘’at this point ke nake tsoro  HIDAYA!!!!!!!’’

Yana fadin haka ya fuce daga bedroom din, harya fuce bata bar kallonshi ba tana mamakin abunda ya fada, ‘’me yake nufi Kenan da wannan furucin nashi?, itafa har yanxu tana jin akwai abunda yake boye mata wanda bata sani ba, shike sashi questioning dinta koda yaushe, yanda yake kallonta anya kuwa bai gano……

Saurin kauda tunanin tayi “no that’s impossible’’  ta bama kanta amsa, nan take wani irin fargaba ta durar mata,…..

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 23-24

Update!!!!

 

Washe gari da safe tun kafin alarm dinsu yayi ringing ta tashi, don yanxu ta fara gane komai na gidan da yanda alamuran gidan ke tafiya, wanka ta fara yi ta saka uniform dinta kafin ta fara nafilfilu, ta dade sosai kanta a kasa tana kiran sunan allah har alarm dinsu yayi kara.

 

Karfe biyar daidai ta fito daga part din nasu na ma’aikata kafin ta wuce sama, kamar kullum yauma ko’ina shuru babu motsi saima haske daya bade ko’ina, saman ta wuce cikin natsuwa kanta a kasa, daidai nan daddyn barad ya futo don zuwa sallah, gaishesa tayi kafin ta wuce part din taj.

 

Koda ta shiga part din batayi gigin shiga bangarensa ba saida ta gama gyaran parlorn kafin ta nufi bedroom din.

Lokacin data shiga yana daga zaune kamar kuwa jiran ta yake yi, murmushi yayi mata wanda ya sata sauke ajiyar zuciya mai nauyi, yau bata shugo ta taddashi yana kuka ba kamar kullum, “friend!!!”

“Naam friend good morning”

Ta amsa shi, murmushi kawai yayi mata kafin yace “first love batazo ba?”

Yanda yayi maganar abun tausayi, saida ta karaso ta gane yanayin da yake ciki, he looks so pale, bakinshi ya vushe sosai yayi fariii tarr kamar wadda ke jinya, ga idanunshi sunyi jaa sosai.

Haka kawai taji kamar he doesn’t sound like yanda yake koda yaushe, “friend kayi brush?, ga breakfast na kawo maka”

Daidai nan ta karaso bakin gado ta dan duqa don ajiye tray din gefen bedside table.

Kallon corn soup din yayi, take ya soma jin wani abu ya soma zuwan mashi maqogaron shi kamar amai, batama lura dashi ba ta dauka bowl ta miko mashi, daidai nan kuwa ya soma kakarin amai, lokaci guda ya burkice, amai yake son saidai cikin nashi babu wani abun arziki a cikinsa da zai amayar, ganin yanda yake struggle tare da riqe maqogaron shi yasa ta saurin ajiye bowl din hankali atashe.

“Subhanallah!! Menene? Wani abun ke damunka”

Nuni yayi mata da bowl din kafin ya kauda kanshi gefe, “bana so”

Sai a lokacin ta lura da abuncin ne baya so, gashi batasan ya zata ya ba, abunda aka rubuta kenan a breakfast timetable dinshi kenan, gashi dole saiyaci abunci zaisha magani.

“Baka son wannan?”

Ta karashe tana nuna mashi bowl din, girgiza mata kai yayi abun tausayi, “meysa baka so?”

“I hate it” ya sake fada 

“Kayi hakuri kasha kaji friend saboda ka samu kasha magani Okay?”

Juya mata baya yayi a shagwabe tare da nade hannayenshi a kirjinshi “no noo banaso”

Ya karashe kamar zaiyi kuka.

“Friend dan Allah ko kadan ne kaji? Kaga maganinka ma baka sha ba kar lokaci ya kure”

“I don’t want to”

“Idan baka sha ba first love zatayi fushi dakai” sabeeha ta fada hoping hakan zaisa ya sha, ai kuwa bata gama karashe maganr bama ya juyo ya zuba mata idanunshi, idanunshi da sukayi jaa ya zaro mata shi “zatayi fushi sosai?” 

“Eh zatayi fushi dakai sosai”

Sauke idanunshi yayi kasa irin yanda yara keyi kamar bazaice komai chan kuma ya hadiye wani irin miyau mai daci a bakinsa

Hannunsa ya miqo mata, hakan yasa ta ajiye mashi bowl din a akan lap dinshi.

Kallon bowl din yayi kafin ya runtse idanunshi ya soma diban soup din yana kaiwa baki daga yanda yake sha zaka gane baya so kwata kwata kuma baya

mashi dadi a baki, saida yasha kusan rabi kafin ya maido da dubanshi gareta yace “friend ya isheni”

“Saura kadan friend ka shanye please kaji? Bana son first love tayi fushi okay?”

Haka nan ya cigaba da sha harya shanye tas da kyar, sabeeha na ganin haka tayi saurin karban bowl din tace “yauwa friend,”

“Friend zanje toilet please i what to pee”

“Okay tohm” sabeeha ta amsa shi tana dan yin baya don ta bashi hanya ya wuce.

Kafafunshi ya soma saukewa kasa kafin ya miqe, taku daya yayi ya soma yin baya kamar zai fadi, cikin hanzari sabeeha ta karaso ta kama hannunshi, wani irin zafi taji dayasa ta sakin hannun ta kalli fuskanshi, layi taga ya soma yi wanda ya sata tsorata lokaci guda ta sake taba hannun nashi, yanda kasan daman neman makafa yake gaba daya ya sakar mata jikinshi, wani irin wahalallen nunfashi ta sauke “ wayyo allah na, zaka karyani”

Tururin da jikinsa ke fitarwa yasa hankalinta ya koma kanshi gaba daya “friend are you okay?, jikinka akwai zafi,”

Baya jin abunda take fada ma gaba daya saboda yanda gaba daya yaji wani irin dummm a kunenshi lokacin daya miqe

“Zanyi pee”

Da taimakonta suka karasa cikin bathroom din, hannunshi har zuwa lokacin yana cikin nata, koda yazo yin pee din ita ta taimaka ta zare mashi mazugin tana kauda ido kafin ta fuce daga bathroom din.

Dakin ta koma ta kwashe bowl din kafin ta fuce zuwa kicin. 

Ta dan dade kafin ta dawo cikin dakin saboda wanke bowl din datayi, da mamaki ta karasa bathroom din ganin kamar bai futo ba, knocking ta fara yi, jin shuru yasa ta cewa “ka gama?”

Nan ma shuru babu response, hankalinta ne ya soma tashi,bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta bude kofar ta sa kai ciki, ganinshi a kasa helplessly yasa ta karasowa cikin sauri, babu abunda yake sai kakarin amai gashi aman yaqi zuwa, da sauri ta karasa inda yake ta tsugunnawa, gaba daya ya gigice, babu abunda yake sai kuka, yana jinta a kusa dashi ya nanukota, jikinta har rawa yake.

Daburcewa sabeeha tayi hartama fi shi shiga tashin hankali ganin yanda yake faman tura jikinshi ga nata, aman dake maqale a moqogoron shi ne ya soma zubowa, gaba daya ya amayar da wannan soup din a jikinta wajen gaban rigarta, baiwar allah ko kyankyaminsa bata ji ba saima dabbing bayanshi data dunga yi, struggling sosai ya dunga yi wajen amayar da abunda ke cikinshi tass, ga jikinshi yayi wani irin zumm sosai.

Saida ya gama tass kafin komai ya dan lafa mashi ya kwantar da kanshi a kafadarta jiki a mace ,gaba daya ya gama batasu daga shi har ita, “friend i want to see first love please,”

Fashewa yayi da kuka don daman idan yana rashin lpy irin wannan indai ba hidaya ya gani ba  sai yayi ta kuka.

Wani irin kuka ne ya zo ma sabeeha, allah ya bata wata iriyar raunaniyar zuciya mai rauni, tana da tausayi sosai, musamman idan taga mara lpy, lokacin da aka tafi da inna asibiti kwana tayi tana kuka, duk da zaman su da inna ba wani dadi yake ba hakan baisata tausaya mata ba lokacin da za a kaita asibiti, balle kuma wannnan daya gama shiga ranta saboda lalurar shi, 

“I’m so sorry friend, wallahi bansan ranka baya so ba da bazan baka ba, i’m so sorry please kaji”

 

Sun jima anan zaune, gaba daya ta zama kamar wata yar tsana a zaune gashi ya rufeta ruff da girman jikinsa daman gata ba tsayin kirki ba ga dan jikin nan nata.

Saida taji ya daina kukan kafin itama ta tsagaita, miqewa ta soma yi ya ruko hannunta “don’t leave me please, karki barni yanda first love ta barni, stay with me, i don’t want to be alone”

Wannan furuci nashi ba karamin narkar mata da zuciya yayi ba don saika rantse mai hankali ne yayi maganar, tasan yana da rashin lpy amma kuma bata san dalilin dayasa kullum yake daki ba dukda ta yanke hakan saboda rashin lafiyarshi amma harga allah yana buqatar yan uwanshi a kusa dashi koba komai shima mutunne kuma yana da zuciya ta dan adam bai chan chanci wannnan ba, saidai tunawa da kaddarar sa kenan yasa ta jin wani irin.

Hannunshi da jijiyoyinsa da suka futo rado rado ta zuba ma idanu don fatarsa fara ce tass, samun kanta tayi ta komawa ta tsugunna a gabanshi ta riko hannunshi “bazan barka ba friend, i promise,”

Murmushi kawai yayi mata kafin ta taimaka mashi ya miqe zuwa wajen basin, wanke mashi baki tayi da kanta kafin ta rakashi har bedroom ya kwanta ta jawo mashi duvet ta rufe shi.

Toilet din ta koma ta gyara shi tsaf sannan ta gyara gaban rigarta daya bata mata kafin ta futo, lokacin data fito har ya soma barcin wahala, sai a lokacin ta tina baisha maganinsa ba, don dole badan taso ba sai dan tsoron kar abunda ya faru kwanaki yasa ta soma tashinsa ahankali, maganin ta bashi yasha kafin ya koma, 

Zama tayi daga chan gefe a kasa ta hade kafafunta a kirjinta ta zuba mashi idanu.

He look so innocent, daga yanda yake barcin ma kasan a wahale yakeyi don daga ganin yanda yake furzar da numfashi zaka san yana jin babu dadi.

Zaman awa kusan biyu tayi barci ya soma daukan ta tana gyangyadawa har ya fuzgeta, ba ita ta farka ba sai wajen karfe daya, cikin sauri ta tashi zuwa bakin gadon sa, yanda ta barshi haka ta taddashi yana barci peacefully, ko gyara kwanciyar baiyi ba yana mai fuskantar ceiling, jikinsa kwata kwata baya motsawa badan nunfashi da takeji yana futarwa ba zata rantse ko matacce ne, gaba daya jikinsa ya saki.

Taba shi ta soma yi a hankali, don jin ko da zafi jikin nashi, bataji wani zafi ba hakan ya tabbatar mata ya sauka zazzabin nashi, hamdala tayi ta dauke hannunta daga wuyanshi.

,Futa tayi daga dakin ta sauka kasa zuwan part dinsu don gabatar da sallar dhuhur.

Saida ta idar da sallah yar ghana ta shugo bangaren su, murmushi sabeeha tayi mata don yanxu sun saba sosai, “kin dawo?” Yar ghana ta tambayeta.

“Eh na dawo,mouryoum” (sunan yar ghana kenan)

“Ay nazo dazu inata nemanki ban sameki ba, ashe baki dawo ba, kinsha aiki”

Hijab dinta datayi sallah dashi ta nannade tana mai sauraron yar ghana, “ayyuka ne sukayi min yawa yau shiyasa ban sauko ba”

Kallon dakin yar ghana ta soma yi, ganin sauran yan dakin basa nan yasa ta jan sabeeha zuwa bakin gado ta zaunar da ita kafin tace “sabeeha niko inason tambayar ki wani abu out of curiosity”

Zama sukayi bakin gadon sabeeha kafin yar ghana ta cigaba da magana “dan allah menene a saman nan?,”

 Atsorace sabeeha ta kalleta tana mai kokarin karantarta “meysa kike son sanin abunda ke saman?”

“Ba komai, I’m just so curious, ki fada min kinji”

“Ni bansan menene a saman ba” sabeeha ta bata amsa tana mai kauda kanta gefe, cije lebe kawai yar ghana Tayi kafin tace “zan baki kudi in kika fada min”

Wani tunani ne ya zoma sabeeha, ta kasa gane wannan yar ghana din da yanda take yawan tambayarta da bugar cikin ta akan al’amuran dake sama, kullum zille mata takeyi ta hanyar fada mata bata sani ba saidai yanxu ta fara bata tsoro don yawan tambayar nata yayi yawa, wata dabara ce tazo mata wadda batama san ta iya ba.

“Ni gaskia ban sani ba, amma nasan head ta sani idan kinaso zaki iya tambayarta saita fada maki”

Hankali a tashe yar ghana tace “ah ah bazan iya tambayarta ba ni fa daman kawai I’m curious ne”

Tabe baki sabeeha tayi kafin ta miqe tace “ki bari toh ni zan tambayar maki ita”

“Ki rufa mana asiri, wannan maganar zaisa a koremu daga ni har ke”

Toilet sabeeha ta wuce tana kunshe dariyar data zo mata, yanxu ta kara tabbatar da wannan yar ghanar tana da gulma sosai.

Hidaya!!!!

Anatse ta futo daga office, hannunta riqe da jakarta, employees dinta gaba daya babu abunda suke sai gaisheta, ko sau goma kuwa zata sauko sai sun sake gaisheta wannan policy din da kowa ya daukar ma kanshi kenan gudun kar a koreshi, wani baqin shade ne akan fuskanta, tasha mur bakin nan yasha red matte lipstick, yau dai a bossy hidayarta tazo office din, basement ta sauka wajen private parking lot dinta, key din dake hannunta ta danna Nan take blue LV car dinta ta hau kara, tana karasowa inda motar take ta bude tare da shigewa ciki, har zuwa lokacin wayarta ruri takeyi, Jakarta ta wulla gefe kafin ta kunna motar.

Connecting wayarta da motar tayi kafin tayi reverse, maganganu ta soma yi cikin turanci, kafin call ya shiga, harkar smart digital kenan, nan take call din ya shiga, ringing daya akayi picking, “go and pick up barad” 

tana kaiwa nan ta futo da haddaiyar motar tata daga basement din, gate din futa daga wajen ma daban ne don an kebar da wajen just for ceo.

With high speed ta hau kan titi tana murza steering, kallon dash board din motar tayi ganin call na sake shigowa da wata unknown number, kara speed tayi kamar zata tashi ranta a mugun bace, tafiyar minti ashirin tayi ta karaso wani beach, sai a lokacin ta rage speed din motar tata, wata hanya tabi daga gefe inda ya kaita har wajen jiragen ruwa na cruise sai na wasu  containers, daidai wajen tayi parking kafin wasu armed guard sukazo suka amshi key din don yin parking, bata tsaya amsa gaisuwar su ba ta wuce wajen tafkeken boat dinta, mutanen dake kula da boat din na ganinta sukayi saurin karasowa suna duqa mata, “welcome ma’am” ba tare data amsa su ba tace code 5

Sanin mai hakan ke nufi yasa sukayi saurin bin bayanta, nan take suka soma kunna engine boat din cikin gaggawa,

Ita kuwa tana shiga ciki ta samu waje ta zauna, fadin irin tsaruwar cikin boat dinma bata lokaci ne yanda kasan gida, babu abunda babu aciki ga girma.

Tundata zauna take girgiza kafafunta da yasha zobunan kafa kaf kaf, shade din fuskanta na nan gar zuwa lokaci, bini bini take duban agogon dake hannunta, saida suka dauka wajen awa guda kafin jirgin ya tsaya, kamar jira take kuwa tayi saurin miqewa ta dauki jakarta ta futo cikin qasaita.

Kallon wajen ta soma yi, yau wajen wata guda kenan rabonta data zo wajen nan sai gashi wannan useless mutanen nan suna son su saka mata ciwon kai.

Island ne mai shegen girma sai wani tafkeken gidan guda daya tal da ake hango shi daga nesa, gaba daya ciyayi ya rufe gidan, wajen nada shegen girma kamar daji.

Futowa tayi ta nufi hanyar cikin island din ko tsoron wajen bata ji, ni kaina mai kawo maku rahoto saida na danji tsoro, baka jin komai sai kukan tsintsaye da ciyayi.

Daidai bakin gate faya zagaye gaba daya wannan dajin ta tsaya tare da scanning kanta, nan take gate din ya bude,inda motar dake parke a wajen ta karasa, driver dake zaman jiranta yana sanye da uniform fari kal ne ya bude mata kujerar baya, zama tayi ta hakimce kafin ya rufo kofar.

Hannu ya daga mata ya rissinar da kanshi alamun gaisuwa kamar he’s deaf baya ji, hannu kawai ta daga mashi yaja motar suka miqi hanyar.

Sun kai wajen minti biyar kafun su karaso gaban wannan babban gidan dana hango daga bakin island din.

Gida ne babba sosai ba karami ba, bata ma jira driver ya bude mata kofa ba ta futo.

Taku dai dai takeyi harta karaso bakin kofar shiga gidan, thump print dinta ta saka kofar ta bude.

Abun mamaki daga waje dai gida ne mai kyau saidai daga ciki babu komai empty, takun tafiyarta yasa suka juyo a rikice, maza ne su kusan hudu gabzaza suna zaune akan kujerun karfe suna cin abuncin, suna ganinta kuwa suka mimike tsaye sukayi layi kafin su soma sunkuyar da kansu, “welcome ma’am”

Bata amsa su ba ta tsaya a gabansu, daya bayan daya ta bisu da kallo rai a bace, daya daga cikin su ne ya dauki kujera ya ajiye mata daga gefe kafin ya koma gefe ya tsaya wajen da sauran suke tsaye.

Kallon kujerar tayi kafin ta kaida dubanta ga abuncin da suke ci, lokaci guda taji wani maqoqon bakin ciki ya zo mata, takowa tayi inda suke har gaban wanda ya ajiye mata kujera, babu zato babu tsammani sukaji tasss tass har sau uku, saurin dafe wajen yayi sauran na ganin haka sukayi kneeling a gabanta, 

“Har kuna da time din cin abunci?,shin kunsan problem din dake gaban mu idan har ya tabbata akwai wanda yasan da wannan al’amarin?”

 

Wanda ta mara ne yayi saurin duqawa shima, “we’re sorry ma’am”

“Sorry will not fix this? Wani irin useless mutane ne ku da bazaku iya aiki ba tare da kuskure ba? Looks like kuna son nayi wiping dinku ne?”

A tare suka soma cewa “no ma’am”

“Now tell me how did you handle it?”

Rarraba idanu suka somayi daya bayan daya suna kallon juna, ogan su ne yayi karfin halin cewa “madam kinsan bamu taba yi maki kuskure ba, kuma na tabbatar maki wannan karan ma bamu bar any lead da zai nuna cewa intentionally hit and run ac….”

Shade din fuskanta ta cire,bacin rai kwance a idanunta, dukda sun tabbatar mata basuyi wani mistake ba tana jin this is not right,”

Wani irin disgusting kallo tayi masu a kaskance bayan ta dakatar dashi kafin  tayi pointing dinsu daya bayan daya da hannunta “be sure of what you said, don wallahi kusan abunda zai biyo baya idan har kunyi wani kuskuren”

Tana kaiwa nan ta fuce daga cikin gidan tana furzar da nunfashi mai zafi, idanunta har wani kif kif sukeyi tsabar masifa.

Tana fita kuwa suka miqe taaye suna kabe wandunan su.

“Kai wannan matar fah kamar she’s a psychopath, zata iya yin komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login