Showing 72001 words to 75000 words out of 135321 words
barad ne dasu fadwa gabansu kuwa shaqe yake da abunci kala kala kamar mutane goma ne sazuci.
saukowa suka somayi daga stairs, sabeeha na biye dasu a baya, tunda suka soma saukowa daga stairs din taj ke kalle kalle, hannunshi na cikin na jamid ya rike shi gam, ganin ya tsaya yasa jamid cewa ‘’muje’’
exicitedly ya kalli jamid yace ‘’uncle wajen first love zaka kaini?’’
‘’yes taj muje ko’’
karasowa sukayi dining din, babu wanda ya lura dasu saida sukaji muryar taj din, ‘’first love!!!’’
damm gaban hidaya ya bayar, for a second dataji yanda ya kiranta kamar yanda yakeyi kafin ya samu wannan amnesia din, sakin spoon din dake hannunta tayi ta dago tana kallonshi da jamid a tsaye ga sabeeha a bayan su, cikin sauri taj ya saki hannunshi dake cikin na jamid ya nufi inda take ya tsaya a gabanta harda bubuga kafa ‘’good morning first love,’’
kasa magana hidaya tayi sai wani irin mugun kallo da take aika ma jamid, maids din da suke shugowa da abunci kuwa da mamaki suke kallon taj din don basu taba ganinshi ba sai yanxu, gashi daman kowa yasan da labarin cewa akwai dan uwansu mahaukaci dake zaune a gidan.
afiya da fadwa kuwa kallon juna suka soma yi don yau kam akwai drama.
kokarin rungumeta ya soma yi ta hankadashi baya, wannan abu yayi ma jamid zafi sosai aranshi, ‘’whats this? whats going on here? meyakeyi anan kasa, uban waye ya sauko dashi? da izninin wa? who dare to do so?’’
jamid dai nannade hannayenshi yayi yana kallonta,
tuni taj ya burkice yana kokarin kamo hannunta kamar mahaukaci, ‘’first love i’m sorry’’ haka ya dunga maimaitawa wanda ya sata daka mashi tsawa ‘’shut up, dukanka akayi ne?,why are you sorry?waye ya sauko dakai? kukan me kakeyi?’’
afiya ce tayi saurin cewa ‘’yoh ukty mahaukaci yasan abunda yake yi ne eh?’’
saurin mintsininta fadwa tayi taja bakinta tayi shuru,
‘’ni ne nan na sauko dashi, kuma da iznina, as from today tare damu zai dunga breakfast, babu amfanin boyeshi tunda kin rigada kin bayyanawa duniya halin da yake ciki, so there no need of keep him grounded’’
kasa magana tayi tana mai kallon jamid ranta a bace, wani irin murmushi ya sauke daga labbanshi don yasan bazata ce komi ba, kuma ko hauka take bazata taba kawo maganar magani ba kuma yasan abunda ke ranta kenan, and tasan dazarar ta kawo maganar zaiyi questioning dinta don haka ta dauki wayarta ta fuce daga dining din.
tana futa su afiya ma suka miqe suka bar dining din, jamid bai damu ba don daman yasan halin su daya, don haka ya kalli taj dake ta faman kuka ‘’kana son ayi maka dariya ko?, ka manta na fada maka kai big boy ne?, ka daina kuka okay? big boys don’t cry’’
saurin share hawayenshi kuwa yayi ya zauna kusa da barad.
sabeeha dake tsaye kamar munafuka dukta tsure, saida su hidaya suka fice ta sauke wata ijiyar zuciya, kamar daga sama taji muryar jamid, ‘’zo ki zauna muyi breakfst’’
‘’no sir nayi breakfast’’
‘’i insist please, zauna kiyi breakfast damu’’
haka nan ta zauna daga chan sako badan taso ba duk a tsorace take gashi ta takura sosai don gaba daya hidaya tsoro take bata.
bangaren hidaya tana hawa sama ta soma dialing number doctor, yana dagawa ta soma magana ‘’doctor ina son a chanza ma yaron nan medication, wadannan basa aiki, inason ka nemo very strong sedation seems like wannan daka dora shi akai ya daina mashi aiki’’
daga chan bangaren doctor ya samsa ta ‘’but madam, wanna maganin is the strongest and safest among, idan aka bashi wanda yafi wannan za a iya samun matsala’’
‘’i dont care’’ ta daka mashi tsawa,
‘’just do your job properly idan baka san matsala’’
sanin halinta ya sashi cewa ‘’yes madam’’ sannan ya kashe wayar.
Tana kashewa ya soma dilaing wata number hankali a tashe, ‘’sir you need to talk to boss urgently, abubuwa sun fara sauyawa fa, dole ku fara first move dinku’’
tsaywa yayi ya gama sauraron wanda yake waya dashi kafin ya kashe bayan ya karbi umarnin da aka bashi.
wunin ranar taj a kasa yayishi shida sabeeha da barad, haka suka dunga zagaye duk girman gidan, maaikata nata kallonsu,masu tsegumi nayin nasu, jamid kuwa yana biye dasu a baya yana kallonsu, ba karamin dadi ganin taj din a haka yayi
ma jamid, koda ya tuna expression din hidaya dazu daya sauko dashi sai yayi murmushi, shi kadai yasan abunda ke ranshi.
sai yamma liss suka shigo cikin gida, hidaya dake sama bata san abunda ke faruwa ba, fadwa daman tana bedroom dinta while afiya kuma ta futa.
washe gari ta kama sunday, yauma jamid saida ya sauko dashi kasan, ba laifi hidaya bata nuna komai ba don harda ita aka zauna akayi breakfast din, su afiya kuwa babu abunda suke sai mocking taj da abuncin yara, jamid dai yana kallonsu baice masu qala ba, sabeeha kuwa tuni ta gudu bata ma tsaya ba balle jamid yace mata ta zauna dasu tayi breakfast wanda bata fatan rana makamancin haka ta bayyana.
kiran da afiya tayi ma maid yasa suka maida hankalin su kan abunda take cewa ‘’kuje ku hado ma baby brother na cereal, irin na barad kunsan shima yaro ne’’
tana kaiwa nan ta kalli taj dake gefenta ‘’zakasha ko baby brother?’’
da murna kuwa ya amsa ta ‘’yes, i will’’
‘’yauwa good boy zanje shopping anjima zan sayo maka kayan wasa’’ ta karashe tana shafa fuskanshi,shi kuwa ya dunga karkace kai kamar yaro fadwa kuwa mai zatayi banda dariya, tun tana kunshewa harta fito fili, hidaya kam bata ce masu kala ba hankalinta nakan abunci.
misalin karfe biyar suna zaune a sitting room na kasa, sabeeha na zaune a kasa while taj da barad suna kallon cartoon a tv,sai jamid dake gefensu yana danna laptop, saukowa hidaya tayi zuwa nan sitting room din don haka kawai taji akwai abunda jamid ke shiryawa wanda ta kasa gane koma menene.
zama tayi anan kasan da mamaki kuwa ya kalle ta don hidaya dai hidayar daya sani tafi karfi tazo kasa ta zauna haka kawai saida dalili, shugowar afiya da sallamarta yasa suka dago, hannunta rike da ledoji manya, daidai nan fadwa ta shugo cikin parlorn itama ta zauna don jiran ganin abunda afiya zatayi don da gayya ta tafi yin shopping dinnan.
‘’heyy!! baby brother’’
cikin murna ya mike zuwa inda take ‘’yes’’
‘’i got all of this for you harda kaya na saya maka jeka gwada su’’
excitedly kuwa ya karbi kayan ya wuce sama ya sako su kafin ya sauko, dagowa sukayi gaba daya suna kallonshi, kayan kwata kwata basuda fasali, mixup din kayan kamar wani mahaukaci, ga hula daya kafa da wani dan gajeran wando, gaban rigar kuma an rubuta ‘’i’m a mad dog’’
gaban hidaya ya tsaya yana nuna mata’, ’first love, sister ta bani new cloth, i love it yay’’
kallon kayan hidaya tayi kafin ta danyi murmushi, ganin yanda he is so excited about kayan yasa ta cewa ‘’you look handsome big baby’’
wani irin dadi ne ya ziyarceshi lokaci guda, first love ta yaba first gift na kaya da aka bashi, har cikin zuciyarshi yaji yana son kayan, afiya dake zaune tana tauna chewwing gum ce tace ‘’wowww, its says i’m a mad dog its so beautiful, i love the print out yayi maka kyau sosai’’
sai a lokacin jamid ya dago ya kalli taj din, ba tare da ya nuna komai ba kawai ya kauda kanshi gefe.
hidaya kuwa miqewa tayi tabar parlorn ta wuce sama, fadwa na biye da ita, ganin haka yasa afiya ma tabi bayansu.
suna hawa saman hidaya ta kalli afiya rai a bace ‘’wannan childish play dinfa? shi yasa kika kirani akan na sauko kasa? you think all of this is a joke? kina tunanin wannan wasan yara ne?’’
‘’ukty i thought..’’
‘’shut the fuck up, don’t play dumb with me,karki sake yin wannan shirmen, what are you trying to implyi by doing that? ke baki iya siyasa bane? don’t you dare spoil my plan, idan kika sake any suspicious move kamar wannan zan hukuntaki stick that to you dumb brain’’
tana kaiwa nan ta fuce daga bedroom din,
dariya fadwa ta soma yi irin ta keta ‘’shiyasa nace duk cikin mu kece mai kwakwalwar kifi,’’
‘’karki fada min maganr banza mana’’ afiya ta karashe rai a bace
‘’an fada din, bakida da wayo, bakida kissa, ke kwata kwata kanki kamar an zuba dumb waste’’
ran afiya ya baci sosai, bata ma tsaya ta saureta ba ta fuce daga dakin, tana futa ta zaro wayarta ta soma dialing wani international number datayi saving da snitch, ana dagawa ta soma magana, ‘’when are you coming back, zan baka hadin kai’’
daga chan bangaren ne akayi magana kafin ta sake cewa ‘’i don’t care anymore lets do it’’
….
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 37-38
Update
San diego california.
Tun bayan abunda ya faru daddy ya saka ma maya ido sosai, yanxu bata futa kwata kwata sannan kawayen ta ma hanata mua’amala dasu, daga school sai gida take dawowa.
duk wani rayuwar jindadi yayi canceling, no parties,no bad influence friends.
Ba karamin misunderstanding suka samu ba shida mummy akan wannan don ita a ganinta kamar sun takure mayan ne,kuma girma takeyi she’s an adult tunda takai 18.
bangaren maya kuwa babu abunda ya sauya, for the mean time ta rage abubuwan da takeyi don ta lura daddy yayi fushi sosai, saidai ko wata daya ba ayi ba ta cigaba da abubuwanta data saba ba tare da sanin iyayen nata ba, daman damuwarta karya hanata allowance dinta da yake bata.
kullum zata shirya shirin school, tana futa ta shiga bus dinsu zata sauya hanya ita da su kloe, makarantar ma bata zuwa kwata kwata har suka gama final test batayi participating ko daya ba.
koda school authority suka bukaci ganin daddy da mummyn babu wanda ya bayyana saboda yanayin aikin su, bayan wannan ma basuyi tunanin wani serious issue bane, wannan dalilin yasa basu ma san meke faruwa ba.
****
Yau ta kasance 18th birthday din maya, tama manta gaba daya da ranar don yawanci haka shekarun zasu zagayo babu excitement, daman burinta bai wuce iyayenta su kasance da ita ba a ranar kamar wannan saidai hakan bai samu ba saboda koda yaushe suna aiki, basu da time dinta, wani sa’in suma mantawa sukeyi saidai mummy tana kokari don ganin she spends quality time da mayan.
kamar koda yaushe yauma saida ta sauya kayanta zuwa na uniform daga chan wajen yawonta kafin ta dawo gida.
a jigace ta dawo saboda ciwon mara dake nukurkusar ta wanda yasa tabar wajen partyn nasu ta dawo gida.
nanny bee ce ta bude mata kofa ta shigo bayan ta karbi school bag dinta.
cikin fara’a nanybee tace
‘’welcome back baby’’
‘’thank you nanny bee mummy fa?’
‘’mummy ta futa an kirata emergency a asibiti, daddy kuma ya kira daxu, he was concern about you’’
ta amsa ta anatse
cikin gidan suka shiga tana gaba nanybee na biye da ita, maimakon ta wuce bedroom dinta saita wuce sitting room tayi kwanciyarta kan 3 seater, ganin yanda ta jigata yasa nannybee ajiye mata backpact dinta a gefenta ta wuce kitchen, ko minti daya batayi ba ta dawo da glass na favourite juice dinta.
‘’are you okay baby?’’ nany bee ta tambayeta
kamar zatayi kuka tace ‘’nannybee, i’m having cramps’’
‘’sorry baby,yanxu haka bakisha magani ba ko? bari na dauko maki’’
saurin katseta maya tayi’ ‘’no nannybee, inadashi a jaka na zansha’’
‘’Happy birthday baby, i pray you stay beautiful and strong, you’re growing so fast’’
da sauri maya ta kalli nannybee, sai kawai taji hawaye na shirin zubo mata, matar nan tana kaunarta sosai kuma ta damu da ita sosai, she’s always there for her musamman lokacin datafi buqatar iyayenta akusa, jinyar rashin lafiya da dak wata damuwarta duk nanny bee ce kawai ta sani saboda itace ke tare da ita koda yaushe, ita tama manta da wani birthday dinta ashe ita bata manta ba
saurin miqewa tayi ta rungume nanny bee tana hawaye ‘’thank you nannybee, thank you for always being there for me,no one cares for me except you, ke kadai cekika damu dani, daddy da mummy basu damu dani ba’’
share mata hawaye nanny bee tayi cikin dattako da nasiha ta soma magana, ‘’no baby, babu wanda yakai iyayenki sonki da kaunarki okay?, karki sake cewa basu damu dake ba, your daddy loves you so much shiyasa yake futa don yayi providing for this family, mummy ma taimakon alumma takeyi, she’s out there saving lives which i believe kinsan that’s a very good thing kuma duk abunda sukeyi sunayi ne don ki samu rayuwa mai inganci kinji ko’’
tabe baki tayi ta koma kan kujeran ba tare da tace komai ba, girgiza kai kawai nannybee tayi harzata juya tace ‘’bari na saka maki warm water kiyi hot bath zakiji sauki okay?’’
‘’no nannybee zan huta sai anjima, bana son hawa saman yanxu’’
anan kasan nanybee ta barta ta wuce kitchen don cigaba da abubuwan da takeyi.
bangaren maya kuwa barci ne ma ya fusgeta mai nauyi, bayan awa daya wajen karfe hudu ciwon marar ya tsananta wanda ya sata farkawa cikin gaggawa laluben jakarta ta somayi,bata son sha magani saidai idan ya tsananta indai bata sha ba wahala take sha sosai, idanunta yayi jaa sosai da alamu ta fara jigata sosai, neman maganin ta somayi bata gani ba, out of annoyance kawai ta soma zazzage jakar gaba dayanta a kasa,gaba daya abubuwa dake cikin jakar ta watsar anan kasa, cikin ikon allah kuwa taga maganin, ballar guda biyu tayi ta jefa bakinta sannan ta kora da juice din da nany bee ta kawo mata.
komawa ta sakeyi ta kwanta tana jin relief kafin wani barcin ya sake fuzgarta anan kwance.
karfe biyar daidai daddy yayi parking a harabar gidan, anatse ya fito cikin shigarshi ta suit baki wadda tayi mashi kyau sosai, hannunshi rike da flower rose da wani gift box da aka rubuta ‘’happy birthday princess’’
wayar dake maqale a kunnenshi ya fara kokarin katsewa yana cewa ‘’na dawo yanxu,’’
daga chan barin mummy ta amsa shi ‘’okay daddy, nima na fito yanxu, i will stop by the bakery zan karba cake danayi order,’’
‘’okay love’’
‘’hope ka sayo mata gift as you promise?, dan allah majeed yau babu fada, lets spend qaulity time with her, ita kadai allah ya bamu dan allah’’
murmushi kawai daddy yayi ‘’anya baki fini son maya ba kuwa?, tell me wa kika fi so? ni ko maya?’’
abunda ta fada ne ya sashi dariya kafin ya kashe wayar ya danna doorbell.
nannybee ce ta bude tare da welcoming dinshi,cikin fara a ya amsa sannnan ya tambayi ko maya ta dawo, nan ta shaida mashi tana parlor tana barci.
daidai nan suka karaso parlor din, miqa mata office bag dinshi yayi don ta wuce dashi sama.
tana wuce ya maida dubanshi ga maya datayi rub da ciki tana da shakar barcinta, kallon fuskanta ya soma yi yana mai jin son diyar tashi sosai aranshi, takowa ya soma har inda take sai a lokacin ya lura da jakarta data watsar anan kasa.
gyara mata kwanciyanta ya soma yi ahankali ganin tayi nisa sosai cikin barcini don karta fadi, saida ya gama ya ajiye mata flower din da gift box din a gefenta don tana tashi ta gani.
yana gamawa ya soma kiran nannybee don ta tattara abubuwan makarantarta data watsar, kira biyu yayi ma nannybe ya dakata yana mai kallon abubuwan dake yashe a kasa, tsugunnawa yayi ya fara tattara abubuwan jakar ya hadesu waje guda har yazo kan yar takardar dake lekowa daga cikin zip din jakar,haka kawai yaji gabanshi ya fadi lokaci guda, nanndewa ya karasa yi don farin abunda ke ciki harya soma zazzagowa.
da mamaki yake kallon takardar da powder dake cikin takardar, kuma daga jakar maya, kamar wanda ke tsoro haka ya soma shinshinar powder, take ya runtse idanunshi, babu abunda yake furtawa sai innalillahi wa inna ilaihi raji’un a cikin zuciyarshi, take idanunshi yayi ja, kanshi kamar an buga mashi guduma tsabar tashin hankali.
knocking da akayi ne yasa nannybee da barci ya dauketa ta fito, cikin saurin ta karasa wajen kofar ta bude, ‘’welcome back madam so sorry na barki tsaye barci ne yadan daukeki’’
murmushi mummy tayi mata ‘’ba komai nannybee, daddy ya dawo ko baby fah?’’
‘’yes ma’am, ya dawo,duk suna ciki’’
cake din dake hannunta ta mika mata kafin ta shiga daga ciki hannunta rike da paper bag data sayo ma maya kayan zagi datafi so.
chak mummy ta tsaya ganin daddy zaune a sitting room, batama lura da maya ba saida ta karaso inda suke, ‘’yadai daddy’’
dago da jajayen idanunshi yayi ya sauke akan kyakyawar fuskanta kafin ya suake wata ijiyar zuciya kawai ya mike yabar parlor.
da mamaki mummy ke kallonshi harya fice ma ganinta.
maya na tashi kuwa taga surprises din da suka kawo mata ba karamin dadi kuwa taji ba.
washe gari da safe daddy ne ya fara futa, bai tsaya ko’ina ba sai school, ba karamin buncike yayi ba daman gashi lawyer, saida yayi buncike sosai kafin ya dawo gida rai a bace jiki a mace.
mummy dai ta kasa gane mashi don ya sauya gaba daya, daga jiya zuwa yau gashi yaqi fada mata komai.
washe gari haka ya sake futa bai dawo ba sai dare koda ya dawo ma lokacin daya dawo mummy na night duty bata gidan dagashi sai maya.
rabonda ya ganta tun ranar birthday dinta sai yau daya shiga bedroom din nata, a kwance ya taddata tana barci don haka ya soma tashinta, tashin duniya ya dunga mata taqi koda motsawa, wani abu ne yayi ringing a mind dinshi kamar ance ya dago kuwa ya kalli fuskanta, gefen bakinta wani farin abu kamar ta shafa powder, lokaci guda idanunshi sukayi jaa