Showing 78001 words to 81000 words out of 135321 words
taso ba haka ta hakura ta bishi yana janta kamar jela yana murmushi shi kadai.
Zaune suke gaba daya suna breakfast, tsit kakeji babu sautin komai sai na cokula, muryar taj da sukaji ne yasa duk suka dago, ‘’first loveeee!!’’ ya doka ma hidaya kira, dagowa tayi ta mashi kallo daya kafin ta kauda kanta, ko kallon su jamid baiyi ba ya nufi inda take ya sumbaci kumatunta while smiling, wani irin banzan kallo afiya ta mashi kafin ta maida hankalinta wajen abuncin dake gabanta.
miqewa jamed yayi don yau cikin hanzari yaci abuncin don zaiyi tafiya zuwa qatar.
‘’good morning taj, you look so exicted today’’ jamid ya fada yana mai kallonshi fuskanshi dauke da murmushi, sakin hannun hidaya yayi ya nufi inda jamid yake yace, ‘’uncle good morning’’
‘’morning tajudeen zanyi tafiya, me kake so na taho maka dashi’’
‘’humour and satire book’’
gingina kai jameed yayi yana mamakin yanda har yanxu yake son karatu,
‘’okay i will, promise take care of your self okay?’’
‘’yes uncle i will,’’
barin dining din jamid yayi, already yayi sallama da hidaya.
kallon inda afiya take yayi kafin ya nufi inda take excitedly don tunda ta saya mashi kaya yaji yana sonta sosai, har ya saka mata sunan favourite, yana karasowa inda take daidai nan ta miqe da cup din coffee da nufin barin wajen don gaba daya fuskanshi ma bata kaunar gani.
a rikice yayi baya itama tayi baya tare da kwala yar kara, tare da d’oka mashi tsawa ’what the heck, baka da hankali ne?’’
bawan allah he was so excited yazo wajenta ya gaisheta, kwata kwata bai tsammaci zata mike ba coffee din yayi spilling,lokaci guda jikinshi ya dauki kyarma, baya son yaga mutun na fushi dashi ko fada kwata kwata, ‘’i’m so sorryyy favourite’’
goge mata rigarta da coffee din yayi spilling ya somayi, rai a bace ta tura shi yayi baya zuwa kasa ‘’dont touch me’’ ta sake doka mashi tsawa,
magiya ya soma yi mata, yana tsugunne akan gwiwanshi, gaba daya ya gama burkicewa sai faman sorry yake cewa amma ina ko kallon inda yake batayi ba saida hidaya tace ‘’stop!!! tashi’’
saurin miqewa yayi tsam ya tsaya, daman idan ya kafe akan abu maganar hidaya kadai ke sanyashi chanza ra’ayi.
sabeeha dake tsaye chan sako don suna karasowa dining din bayan ya saki hannunta ta tsaya a gefe, gaba daya duk abunda ya faru akan idanunta, kuma taga lokacin da afiya tayi spilling tea din da kanta don ko matsowa dab da inta take baiyi ba balle coffee din ya zuba, take taji wani iri aranta jin yanda take daka mashi tsawa, shiko babu abunda yake sai rokonta yana kuka kamar wani dolo.
take taji hawaye na neman zubo mata daman gata da sanyayyiyar zuciya, abu kadan ke sanyata jin tausayi.
‘’madam, madam!!’’ head maid ta shugo dining din tana kwala ma hidaya kira,hidaya dake zaune tana jin duk abubuwan dake faruwa bata dago ba saida maid dinnan ta shugo, kallonta sukayi gaba daya don jin dalilin zuwanta.
‘’madam,anyi baqi’’
fadwa ce dake zaune kamar bata wajen don duk abunda ya faru a wajen tana ji saidai ko tak bata ce ba sai yanxu tace ‘’wasu irin baqi’’
‘’mutawwa un (police) sun buqaci ganin madam’’
kallon juna fadwa da afiya sukayi da mamaki, kafin su amida dubansu ga hidaya dake cin abunci hankali kwance kamar bataji abunda suke fada ba ko a jikinta, saida ta gama cin breakfast dinta kafin ta miqe, su fadwa kuwa sun qagu sosai da sanin abunda ke shirin faruwa.
taj dake tsaye tun bayan command din da hidaya tayi mashi bai daga kafa ba haka zalika bai zauna ba harta miqe su afiya sukabi bayanta.
harabar gidan suka nufa gaba dayansu harda head dake rakube a baya har zuwa inda motocin dake parke a compound din, mota biyu ce daya ta yan sanda dayar kuma ta domestic workers affairs, mata ne su biyu sanye da uniform duk suna tsaye a compound din.
daga bakin kofar entrance din hidaya ta tsaya, kanta ko hula babu sai gashinta daya sauko kasa, tana sanye da abaya, fuskan nan babu sauqi.
karasowa workers dinnan sukayi inda take kafin su soma gabatar da kansu, ‘’sabahal khair madam, mu ma’aikatan domestic workers affair ne’’
gyara tsayuwar ta tayi tana mai nannade hannayenta waje guda tace ‘’zan iya sanin meke tafe daku?’’
‘’yes madam, munada warrant arrest na for this worker da take aiki a karkashinki’’ ta karashe tana nuna hoton sabeeha a cikin wata waya.
‘’what are the charges about? wace worker kenan?’’ hidaya ta sake jefo masu tambaya.
matar ce ta sake bata amsa kamar yanda ta buqata, ‘’fake identity, and deceit of profession akwai caregiver da kikayi employing 2 months ago, mun samu bayanai akanta da yayi violating domestic workers affair, wanda bazan iya warware maki shi ba saidai muda warrant arrrest akanta for working with fake identity’’
kallon juna afiya da fadwa sukayi sai a lokacin suka dago abunda ke wakana da dalilin zuwan police din, take fadwa ta jinjina kai tana hade hannayenta a kirjinta, wato bata taba sanin hidaya hatsabibiya bace ba sai yanxu, cikin ruwan sanyi zata kauda yarinyar nan kamar yanda ta fada.
‘’okay you can have her’’ hidaya ta fada tana mai kallon head tace ‘’fito da yarinyarnan’’
‘’no ma’am ki barmu zamuyi wannan’’ matar ta sake fada tana mai mata nuni da cikin gidan, ciki suka wuce hidaya na gaba suna biye da ita a baya,
zama tayi a sitting room inda ta daura kafa daya kan daya, su afiya ma zaman sukayi suna kallon ikon allah, inda head ta jagoranci sauran workers din zuwa inda sabeeha take.
baiwar allah sabeeha da kyar ta samu ta lallaba taj yaci abunci shima saida tayi mashi dadin baki ta dunga bashi a baki kafin ya ci.
dining din suka karasa, nan kuwa suka ganta tana kokarin bama taj abunci a baki, cikin hanzari matan nan suka karaso inda take daya na daga barin hagu dayar kuma na daga barin dama haka suka sanya ta a tsakiya tare da kama hannayenta biyu, dayar matar ce ta amshe spoon din dake hannunta kafin ta soma janta, a tsorace sabeeha ta bisu da kallon don babu zato ba tsammani ta gansu a gefenta,
kasa gane ma al’amarin dake wakana agabanta tayi, taj kuwa tuni ya miqe, ganin mutanen da bai taba gani ba gasu rida rida matan irin manya manyan ma’aikatan nan waenda suke kame, tuni ya soma zaro ido ganin yanda suke jan sabeeha, janta suka dunga yi har suka karaso sitting room, tsayawa sukayi inda hidaya take kafin suce ‘’mun gode da bamu hadin kai da kikayi madam,’’
idanunta nakan yatsunta da take faman jujuyawa tace ‘’anything else?’’
‘’no madam’’ suka amsa ta kafin su ja sabeeha kamar wata criminal, cikin firgici take kallon su, babu abunda take furtawa sai innalillahi a zuciyarta, taj dake biye dasu ganin yanda ake jan sabeeha ya sashi shan gabansu yana mai kallon hidaya, don ya hango police din dake tsaye a compound ‘’first love, ina zasu tafi da bibi na?, meysa suke janta haka’’
ko kallon inda yake hidaya batayi ba tace ‘’ku tafi da ita mana me kuke jira’’
hannu biyu ya sanya ya tokare matar jikinshi har mazari yakeyi ganin sabeeha na hawaye, ‘’no ina zaku tafi min da bibi na?, bazaku tafi min da bibi na ba’’
ran hidaya in yayi dubu ya baci, afiya data gama kufuluwa ce tayi saurin miqewa zuwa inda yake ta fusgo hannunshi, firr yaqi matsawa daga wajen kamar an dasa shi, jan duniya afiya ta dungayi amma ko gizau baiyi ba ashe yana da karfi sosai take rainashi idan yana abu kamar dolo dolo,
muryar hidaya dayaji ne yasa shi cewa ‘’first love ki hanasu, zasu tafi da bibi, meysa zasu tafi da ita’’
‘’big baby move out of the way”
‘’no first love, she’s my friend bazan bari su tafi da ita ba, zasu doketa ko?’’
take hawaye ya soma ambaliya akan fuskanshi, ganin yanda idanun sabeeha dake cikin mask yayi jaa ga hawaye na sauka a idanunta, sautin kukan nata ma baya futa sosai don sai a lokacin ta tabbatar dauketa za ayi, ga police da take hangowa daga nesa, shikenan tata ta kare innalillahi wa inna ilaihi rajiun qila ma sun gane an turo ne ta leqen asiri shiyasa aka zo kamata.
ganin yanda taj ke kuka yasa zuciyarta ta karye, bata taba sanin cewa ta shiga ranshi ba kamar yanxu, don bata taba ganin hidaya tayi mashi magan daya ya kauce ma maganar ba sai yau, bangaren hidaya kuwa wannan abu ba karamin mamaki ya bata ba don tabbas zata iya rantsewa gaba daya rayuwar taj bai taba exchanging words da ita ba ko ya tsallake ma umarnin data bashi sai akan wannan yarinyar, zaman yarinyar nan kam yanxu ta tabbatar ba karamar matsala zai jawo mata ba don bata taba ganin ya nuna tsantsar damuwa akan kowacce caregiver ba dake kula dashi sai akan sabeeha, kaskantacciyar maid acikin maids din da take dauka.
mikewa hidaya tayi rai a bace ta karaso inda yake ji kake tasss, ta wanke shi ta mari, cikin sauri ya kama fuskan nashi tam yana hawaye, rai a bace ta soma magana tana kallon cikin idanunshi ‘’tajudeen!!’’
yanda ta kira sunanshi saida ya furgita sosai, tuni jikinshi ya soma kyarma, dole ya matsa gefe yana mai suake idanunshi kasa abun tausayi, bugun zuciyarshi na
tsananta, duk takun da sabeeha ta daga sai yaji wani irin zafi a ranshi, har suka nufi hanyar futa daga cikin parlor, suna fita head ta rufo kofar.
wani irin sigh of relieve afiya ta sauke kafin ta soma tafi, ‘’wonderful ukty!!!’’
ko kallon inda take hidaya batayi ba ta miqe tabarsu anan zaune suna jinjina wannan alamari.
taj dake tsaye ya kasa koda motsawa, haka zalika ko dagowa ya kasa yi, har suka bar wajen ya rage daga shi sai head maid wadda kanta itama ya kulle da wannan alamari.
Budo kofar da akayi ne yayi daidai da saukowar hidaya daga sama rai a bace, su fadwa ma tuni suka fito daidai nan khaal ya sanyo kafarshi cikin parlor, sabeeha na biye dashi sai wannan workers din da suka fita da ita, ashe suna gab da futa da ita khaal ya shugo daman kamar yasan da hakan zata faru ya taho gidan cikin shiri, baiyi mamakin ruskar workers dinnan suna shirin fita da sabeeha ba don yasan either way or the other dole hidaya saitayi san yanda tayi ta kori sabeeha daga gidan shiyasa tun farko daya gano abunda take shirin yi baiyi gigin threatning dinta da sabeehan ba saida ta kaishi bango sosai tukunna, ayanxu kuwa zai nuna mata cewa akwai wadda ta fita iko akan taj kuma babu abunda ya isa ya raba wannan auren…….
takowa khaal yayi inda taj yake a tsaye jikinshi na kyarma har zuwa lokacin bai dawo daga jin zugin da fatar fuskanshi ke mashi ba, wajen har yayi jaa yatsun hidaya sun fito rado rado, baima lura da khaal ba dake rike da hannun sabeeha wadda tasha kuka sosai,hannun taj ya kama ya rike gam kafin ya nufi sitting room dasu duka, sabeeha na daga gefe taj dinma na daga gefe haka suka gifta hidaya datayi suman tsaye, bin bayan khaal workers dinnan sukayi har zuwa inda ya zauna, gefenshi taj ne sai sabeeha dake zaune a kasa.
‘’we’re very sorry sir, bamusan cewa matar mai gidan bane, we really apologies for this’’
magana khaal ya soma, daga yanayin yanda yake magan zakasan ranshi a mugun bace yake, hidaya dake kallonshi sai taga kamar ba khaal din data saba gani bane kullum, ya rikide ya dawo kamar mahaifinsu daman yana da zafi sosai shima.
‘’how dare you step into the house and take my daughter inlaw?, waye ya baku izinin yin haka’’
shuru matan sukayi suna rarraba idanu tsoron kar wannan ya zama dalilin korarsu daga aiki,
‘’were very sorry sir, wannan mistake ne da mukayi and we deeply apologies’’
‘’youre dismiss’’ ya umarci subar wajen.
haka suka juya jiki a mace, suna fita jamid ya budo kofa, bawan allah ashe bai wuce ba, don yana gab da futa yaga waennnan social workers din da police sun shiga gidan bai kawo komai ba saida yakai aiport kawai yaji wani abu aranshi,
take yaji something looks fishy tunawa da yanda hidaya ta dunga tambayr yaushe zaiyi tafiyan ne.
yana dawowa kuwa hasashen shi suka tabbata.
cikin sitting room din ya shiga yana haki, kallon khaal yayi dasu sabeeha dake zaune taj na kuka wiwi harda majina, ga hidaya idanu ya rikide yayi jaa.
‘’ku zauna gaba dayanku’’ khaal ya umarce su
jamid ne kawai ya zauna sai fadwa while afiya na daga tsaye gefen yayarta, hidaya dai banda runtse idanu da tamke hannunta babu abunda takeyi.
‘’as of today, i asserts to give fatima (sabeeha) her rightful place as the only daughter inlaw of the family and the only legal wife to tajudeen, zatayi rayuwa cikin gidan nan ba a matsayin caregiver ba sai a matar taj ’’
tun kafin ya karasa hidaya ta hayyako tace ‘’no!!!! never!!! i will never accept kaskantacciya, mara asali a cikin wannan ahalin’’
wani irin kallo khaal ya mata, kallon mamaki ‘’da amincewarki da rashin amincewarki wannan bazai taba sauya komai ba, wannan yarinyar matar taj ce, lawfully, islamically, matarshi ce ta sunna, kuma tana da iko akanshi, a rubuce yake babu wanda ya isa ya raba wannan ’’
tarar nunfashinsa tayi idanunta yayi jaa sosai tace ‘’no never khaal,never, ni na buqaci ayi wannan auren, yanxu na warwareshi,’’
‘’saboda kin samu abunda kike so?, to have the shares to your self?,’’
ya bata amsa kai tsaye, take tayi tsit ta kasa cewa komai sai bakinta dake faman jujuyawa sai faman cicije lebe take fuskanta yayi jaa sosai tsabar bacin rai.
‘’lallai wannan tsohon is trying her patients,’’ ta fada aranta, wani irin kallon ta wulla ma sabeeha, tana ayyana abubuwa da dama aranta….
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 41-42
update!!!
‘’lallai wannan tsohon is trying her patients,’’ ta fada aranta, wani irin kallon ta wulla ma sabeeha, tana ayyana abubuwa da dama aranta….
bata gama wannan tunanin ba khaal ya fiddo da wasu takaddu na register aure na kasar da written evidence harda sadakin sabeehar.
‘’ idan shaida kike buqata gashi nan,daga ranar da aka daura aurensu title dinta na caregiver ya sauya zuwa matar taj sannan kamar yanda na fada babu wanda ya isa ya futar da ita daga gidannan and she will be treated as the daughter inlaw of this family, kuma ita ke da ikon decision akan mijinta i repeat that’’
kallon takardun hidaya tayi na yan seconds kafin ta maida dubanta ga taj dake zaune ya sauke kanshi kasa yana hawaye, kamar yasan kallonshi takeyi kuwa ya dago kanshi karaf idanunsu ya hade dana juna, yana hango tsantsar bacin rai da sauyin yanayin fuskarta wanda hakan ke tayar mashi da hankali sosai.
kwafa hidaya tayi tare da runtse idanunta ta juya da nufin barin sitting room, bata taba zama humiliated ba sai yau duk akan kaskantacciyar caregiver, taku daya tayi taj ya miqe cikin sauri ya tako inda hidayar take ya rike hannunta, chak ta tsaya ba tare da ta motsa ba, daman tasan bazai taba iya jurewa ganin tana cikin fushi ba kuma ta dalilinshi, murmushi tayi da gefen bakinta kafin ta juyo tana mai kallon hannunshi dake rike cikin nata, ‘’first love i’m sorry karkiyi fushi please’’
‘’let go of my hands’’ ta umarceshi, cikin sauri kuwa ya saki hannun nata, ‘’wuce sama’’ ta sake umartar sa kamar wani dan karamin yaro, jikinsa na bari ya wuce saman ba tare da ya sake kallon inda su khaal ke zaune ba.
khaal dai babu abunda yake sai kallon ikon allah,kallon inda khaal din ke zaune itama tayi tare da sauke wani irin murmushi mai wuyar fassara afusace ta juya ta fuce.
Tana futa afiya ta miqe ita tabar wajen rai a bace, fadwa na biye da ita.
girgiza kai kawai khaal yayi tare da sauke wata nauyayyiyar ijiyar zuciya yana jinjina kanshi,wato she’s pratically telling him that ita keda iko da taj kuma sai yanda tayi dashi, maida dubansa yayi ga sabeeha dake kuka kasa kasa, tausayinta ne ya mamayeshi sosai don yasan zata fuskanshi waulaqanci da abubuwa da dama daga wajen hidaya harma da yan uwan nata saidai har izuwa yanxu yanaji aranshi she is the best decision da yayi making kuma yana da tabbacin zata kasance jajirtacciya kuma mai amana.
maida dubanshi yayi ga jamid daya dafe kanshi tsabar bacin rai, ya kasa gane kan hidaya gaba daya, ya rasa dalilin dayasa take abubuwan nan, saidai baiyi mamaki ba don yasan zatayi abunda yafi haka kuma asannu a hankali kowa zai fahimci duk wani motives dinta wanda ya dade da observing akanta.
‘’khaal, i’m very sorry about this, ban taba tunanin hakan zai faru ba da bazan tafi ba’’
‘’its okay jamid, ba laifinka bane, this is what i’m supposed to do tun bayan auren nan, ban taba tunanin hidaya will go to the extent ba’’
‘’fatima!!’’ khal ya kira sabeeha anatse.
muryanta na breaking ta amsa shi don ta tsorata sosai da al’amarin ‘’na..am sir’’
‘’ina son ki kwantar da hankalinki kinji?, i promise you hakan bazai sake faruwa ba,’’
shuru sabeeha tayi tama rasa me zatace, ayanxu dai tashin hankalin data shiga yasata jin hankalin ta ya koma inda ta futo, idanda tana da iko data ce su taimaketa su maida ta nigeria kawai, saidai inaa hakan bazai taba faruwa ba, bata isa ta nemi hakan bama, saurin rufe idanunta tayi hawayen kan fuskanta na sauka, tunawa da taj kuma da yanda ya hana mutanen nan su tafi da ita yasa taji wani iri aranta, gabanta na faduwa ta amsa khaal.
‘’okay sir’’
‘’don’t call me with sir, ki kirani da khaal kinji ko’’
girgiza mashi kai kawai