Showing 90001 words to 93000 words out of 135321 words

Chapter 31 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

523

ne saida ya fada mashi bai bar komai, yanxu haka ma yana office ne yazo ya sameshi.

‘’jamid’’ khaal ya kirashi a natse

‘’Banason muyi komai cikin gaggawa, shiyasa nace karkace komai ka zuba mata idanu’’

‘’but khaal ni ina ganin why not mu shiga next plan, wallahi ni nasan hidaya bazata taba backing out ba,’’

‘’jamid we have come this far, bana son muyi garaje, mubi komai a sannu a hankali, allah yana tare da mai gaskiya a koda yaushe, wannan yarinyar dai ka kula da ita kawai’’

khaal ya karsshe yana bashi assurance

ba haka jamid yaso ba saidai dole yabi abunda khaal din ya yanke don haka yace ‘’shikenan khaal’’

sallama sukayi yabar office dinshi ya fuce.

karfe biyar daidai ta fito daga cikin bedroom, dube dube ta soma yi ganin babu kowa a kasan yasa ta fuce zuwa backyard, haka ta dunga zagaye backyard din tana kallon wajen har tazo garden, idanunta ne ya sauka kan pipe dinnan tuni memory din abunda ya faru kwanaki ya dawo mata, saurin kauda kanta tayi ta, muryar taj da barad data jiyo ne ya sata tsurewa ta soma dube dube tsoron karya ganta yasa ta nemi wani waje ta boye yanda bazai ganta ba.

karasowa sukayi garden din inda barad ya rike kwallo a hannunshi, gaba dayansu sunsha kayan football sai kayan yayi mashi kyau sosai dukda kayan yayi mashi kadan, samun kanta tayi da kallon taj din daga nesa, harga allah idan tace batayi mssing dinshi ba tayi karya.

samun waje tayi ta tankware kafafunta tana kallonsu suna dariya suna buga kwallon, itama dariyan ta somayi da zarar taj yaci kwallo saboda yanda yake nuna murna harda tsalle.

wullo ball din barad yayi inda take boye, ‘’uncle taj wait for me here’’

ya fada yana nufar wajen ball din, yana karasowa yaga sabeeha maqale a wajen, tsugunnawa yayi a gabanta ta miqa mashi ball yayi mata murmushi, ‘’whats your name aunty?’’

‘’sabeeha’’ ta amsa shi

‘’aunty sabeeha, daddy ya fada min you’re my aunty’’ ya karshe yana miqa mata hannu, karba tayi sukayi shaking hannu yana mata murmushi, ‘’aunty lets play together’’

shuru sabeeha tayi tana tsoron fitowa kar taj ya ganta har zata qi chan kuma ta sauke ajiyar zuciya ta fito anatse, taj dake tsaye yana jiran barad yana ganinta a hade rai sosai, ‘’you!!’’

yayi nuni da ita, ganin hannunta cikin na barad ya sashi cewa ‘’barad move, ka matsa daga wajenta, she’s wicked, zata cutar da kai’’

‘’uncle no, daddy yace babu kyau mutun ya tsani dan uwansa, she’s my friend and she’s my aunty and your’e my uncle’’

‘’no she is not, aunt fadwa and aunt afiya ne aunties dinka kawai’’

taj ya bashi amsa kamar zasuyi fada shida barad din don yana ganinshi kamar sa anshi.

‘’uncle matarka ce fa, so she’s my aunty’’

shuru taj din yayi yana nazari don ya taba jin khaal ya fadi haka ranar dayazo, da yake kwakwalwar ta yara ce hakan yasa bai san me matarshi ke nufi ba, barin wajen yayi ganin barad yaqi sakin hannunta.

yana barin wajen barad ya kalleta, ‘’aunt sabeeha i’m sorry for uncles behaviour’’

tsugunnawa sabeeha tayi a gabanshi, tana mai kallon fuskanshi tana mashi murmushi don yaron ya burgeta, yand akasan ya girmi shekarunshi.

‘’thank you barad’’

tun daga ranar nan suke shiri sosai da barad, daga shi sai uncle jamid ne kawai ke kulata a gidan, taj dai babu abunda ya sauya kwata kwata.

Yau ta cika wata uku churr a gidan, babu abunda ya sauya saima saka ta a gaba dasu afiya sukayi a gaba, dan fitowar da takeyi ta daina shi gaba daya kullum tana maqure a daki.

yau ta kasance weekends, yauma tana zaune a daki ita kwal saiga head ta shigo cikin bedroom din inda ta shaida mata madam na nemanta, jiki a mace ta futo

daga dakin tana mai bin bayan head din, suna tsatsaye a sitting room suna jiran karasowarta daga hidaya sai fadwa da afiya sai jamid da bai dade da shugowa ba shima, kallonsu yayi ganin sunyi cirko cirko suna kallon sabeeha tana karaso kanta a kasa, nuni taj yayi da ita ‘’itace’’ yayi nuni da sabeeha

da mamaki duk suka dago suna kallonshi, hidaya ce ta tako inda sabeeha take ji kake tassss, tasss tass  ta wanke ta da maruka har sau uku, a gigice sabeeha ta dago jamid kuma ya janyo hidayar gefe, ‘’hidaya!!!1 how dare you? waya baki damar…’’

a zafafe ta kalleshi, ‘’idan an kama barwo me ake mashi?’’ 

‘’barawo?’’ ya tambayeta surprisingly, ‘’yes, babu maid din dake zuwa sama wannnan policy din gidannan ne daga ni sai kai sai barad da big baby sai wannan,’’ tayi nuni da sabeeha dake rike da kuncin ta ‘’my diamond jewelry worth of billion riyals was stolen da kudi kimanin  5000 riyal’’

rai a bace jamid ya kalleta, ‘’wace iriyar shaida kike dashi kan cewa ita ta dauka,’’

‘’jiya da muka fita babu wanda ya hau sama sai ita, ga shaidu nan’’ ta nuna taj da headmaid dake tsaye.

maido da dubanta tayi ga sabeeha ‘’how dare you stole my property, bana yafiya kuma saina hukuntaki kafin na miqaki hukuma,’’

‘’that wil never happen,’’ jamid ya katseta rai abace kafin ya maida dubanshi ga head maid, ‘’tabbacin me kike dashi na cewa itace ta dauka?, kin ganta ne da kudins?’’ ya tambayi head

zare idanu head ta soma yi kafin tace ‘’yes sir na ganta da idanu na’’

‘’innalillahi wa inna ilaihi rajiun’’ sabeeha ta soma maimaitawa

‘’da kika ganta maisa baki tareta ba kin kamata hannu dumu dumu?’’

shuru head tayi ganin yanda jamid ya tsareta da idanu, 

‘’sir…’’

‘’look jamid, nothing can change the fact that ta dauka, taj ya ganta da kanshi saboda ta shiga bedroom dinshi a daidai wannan lokacin sannan bakaga tayi shuru ba she have nothing to say saboda asirinta ya tonu’’

hidaya tayi saurin shiga cikin zancen ganin jamid na neman bin didigi.

hankali a tashe sabeeha ta kalli jamid, ‘’wallahi sir ban dauka komai ba, ban taba sata ba a rayuwana, jiya tabbas naje sama don na duba taj, wallahi ban shiga ko’ina ba kuma ban dauka komai, dan allah ku fada mata ban dauka  komai ba,’’

‘’karya kike, head ta ganki kin sauko da abu kina boyewa’’ afiya ta fada tana mai kallonta cikin kaskanci

‘’wallahi sir ban dauka komai ba, ku tanbayeta’’

ta nuna head maid, ‘’ koda na sauko, anan bakin stairs muka hadu harta tambayeni ko ina buqatar wani abu nace mata ah ah’’ 

wani marin hidaya ta sake sauke mata tare da binta da cursing word nasu na larabawa,har saida jamid ya daka mata tsawa.

 

‘’aduba belongings dinta na tabbatar anan ta boyeshi don bazata iya futa da komai ba daga gidannan’’ afiya ta fada tana murmushin mugunta,badan jamid yaso ba ya bisu har zuwa bedroom din sabeeha saboda yana son ya wanketa, yana da yaqinin sabeeha bazatyi haka ba don yasan sune sukayi plotting hakan, badan umarnin khaal da yake bi ba dayayi making move a wannan junction din don abun nasu ya fara yawa sosai.

suna shiga dakin afiya ta soma fiddo da kayayyakinta da taimakon head, saida sukayi filla filla da komai har suka zo kan yar jakar nan tata da tazo gidan dashi, take hankalin sabeeha ya tashi ta soma zaro idanu tsoron kar suka wannan wayar da aka bata, dan sai a lokacin tama tuna da wayar, ‘’wallahi ban dauka komai ba, kayana ne kawai a cikin jakar nan babu komai a ciki’’

hidaya na jin haka ta kalli su afiya, ‘’anan ta boye su ku bude jakar yau asirinki saiya tonu’’

sabeeha naji na gani suka farke jakar nan tass suka soma zazzago da abubuwan dake ciki, duk wani abunta dake cikin jakar saida suka fiddo ba a sarka ba, hankali a tashe hidaya ta kalli afiya ta girgiza mata kai, sai a lokacin jamid ya sako baki, ‘’ina sarkan yake?, kunce ita ta dauka yana ina?’’

a daburce headmaid ta soma magana tsoron kar a koreta , ‘’daman sir na ganta ne ta sauko bawai na ganta da kudi da sarkan bane’’

rai a bace jamid ya kalli hidaya, ‘’you have step your boundries, bakida hurumin accusing dinta ba tareda kwakwarar shaida ba’’

 

‘’no, i can never be mistaken, itace ta dauka kudin nan kuma ta boyeshi ne, and i will definately expose her’’ tana kaiwa nan rai abace ta fuce, su afiya ma sukabi bayanta taj dake tsaye sai yaji wani iri aranshi.

‘’i’m so sorry fatima, i’m sorry for this, kiyi hakuri i promise haka bazai sake faruwa ba’’

jinjina mashi kai kawai tayi, ta kasa cewa komai sai hawayen da takeyi, 

fitowan su hidaya yayi daidai da sallamar tareeq (mijin fadwa) ‘’hello i’m back!!!’’

cikin sauri fadwa ta taho inda yake ta rungumeshi shima ya rungumeta tsam a jikinshi, ‘’hello my lady’’

ya fada yana sumbatar kuma tunta, ‘’marhaban tareeq’’

hannunshi ta kama suka karaso inda hidaya ke tsaye da afiya, daga yanda yake tafiya ma zaka san dan chali chali ne kuma dan gari ne, hannun hidaya ya kama ya sumbace ta kafin ya dago fuskanshi dauke da murmushi ya gaisheta, wani irin kallo tayi mashi tana mai amshe hannuta ta sharce inda ya sumbaceta ba tare da

tace mashi komai ba ta bar sitting room, tana barin wajen ya kalli afiya ya kanne mata idanu daya, kallonshi kawai tayi ta kauda kanta gefe tace ’’marhaban’’ kafin tabi bayan hidaya zuwa sama.

shi da fadwa ta kuma suka wuce part dinsu.

‘’ukty wallahi nayi yanda kikace a cikin jakarta na saka kudin da jewelry din, kuma babu wanda ya ganni’’ 

dakatawa hidaya tayi kafin ta juyo ta kalleta, ‘’then ya akayi babu komai a cikin jakar nata? instead of using your dumbass head you messed up big time, wai why can’t you just do this simple trap? you’re usless,’’mteww ta doka tsaki 

rai a bace afiya ta fito daga dakin, duban wayanta tayi ta soma dialing number.

bangaren su fadwa suna shiga bedroom ta zayyane ma mijinta komai da abubuwan dake faruwa a gidan gaba daya, already ta fada mashi batun auren taj da hidaya tasa akayi.

murmushi kawai yayi yana fadin ‘’interesting aranshi’’

daidai nan wayarshi tayi ringing, kallon fadwa yayi ganin tana arranging kayanshi ya sulale ya futa daga dakin, bai tsaya ko’ina bai tsaya ko’’ina ba sai part din afiya kai tsaye, yana shiga ya tsaya daga bakin kofa bayan ya rufo, wani dan iskan kallo yake mata ya soma takowa zuwa inda take tsaye tana safa da marwa tsakanin dakin bata ma lura dashi ba saida taji an rungumota ta baya, cikin sauri ta juyo baiyi wata wata ba ya rungumeta a jikinshi tare da shinshinar wuyanta yana mai yawo da hannayenshi a kwankwason ta, karkatar da kanta tayi tana mai jin saukar nunfashinsa a wuyanta ‘’tareeq ‘’ ta dakatar dashi 

barin abunda yakeyi yayi ya maida bakinshi daidai kunnenta, ‘’kefa kika sani na dawo, why are you stoping me then?, we hard a deal already harkin manta’’

‘’no ban manta ba but this is not safe, fadwa zata iya shugowa dakin nan, we can do it somewhere safe yanxu dai tell me whats your plan, lets do it once and for all, na gaji da wannan games din,’’

wata bazawarar dariya yayi yana tabata in a seductive way, ‘’kibar komai a hannu na, zan baki abunda kike nema trust me’’

murmushi afiya tayi harda sauke ajiyar zuciya,shima murmushin yayi yana mai hade bakinsu waje guda.

tareeq kenan, tataccen womanizer,da zarar ya kyalla idanu akan mace saiya samu abunda yake nema, fadwa tasan da wannan halayyan nashi saidai bata taba nuna damu akan wannnan ba, abu daya ne bata sani ba shine yana flirting da afiya.

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 47-48 

Saida suka gama shagalinsu kafin ya fita yabar dakin afiya ba tare da jin wani darr ba ko tunanin wani zai ganshi.

Jamid na fitowa daga bangaren sabeeha ya wuce sama direct zuwa part dinshi da hidaya rai a bace, yana shugowa ya tadda ta a zaune tana latsa system da alamu aiki takeyi, rai a bace ya soma magana “hidaya, why? Why? meysa saikinje to this extent don ki kori yarinyarnan, why,?”

Wani irin banzqn kallo ta mashi, “ban gane ba? What do you mean? Kaga nafa gane take taken ka? You’re trying to protect criminal kuma barauniyar yarinyar nan…”

Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa “karki sake kiranta da barauniya, tunda baki kamata da komai ba, inason ki sani duk abunda kike ina sane dake, kuma nasan duk wannan shirinki ne kuma bazan taba bari kici galaba akanta ba”

Yana kaiwa nan ya fuce daga part, saqe tayi tana kallon shi harya fuce daga bedroom din, cije lebenta tayi kafin tayi kwafa.

Cikin motarshi ya shige ya fuce daga gidan gaba daya, saida ya tabbatr ya futa daga tahlia street din kafin ya ganganra gefe yayi parking, kallon gefen seat dinshi yayi inda ya ajiye office bag dinshi, bude jakar yayi ya zaro sarkar da kudin, ranshi ba karamin baci yayi ba tunawa da abunda hidaya taso yi dazun, wayarshi ya zaro yayi dialing number khaal, bayan sun gaisa ya mashi bayannin komai da yanda yayi overhearing conversations din afiya da fadwa kan yanda zasu kulla ma sabeeha sharri ta hanyar sanya sarkar da kudin a kayanta, afiya ce ma da kanta ta shiga dakin sabeehar bayan ta tabbatar ta wuce sama wajen taj, inda head kuma ta tsaya bakin stairs, kwata kwata afiya bata san jamid ya ganta ba don saida ya tabbatar ta fito daga bedroom din sabeeha shi kuma ya shiga ya dauke kudin da sarkar, anan ne ma yaga waya a cikin kayan sabeeha, yayi mamakin ganin waya cikin kayanta don ba’a barin maids suna rike waya saidai a basu na aiki anan gidan idan aikinsu ya buqaci a basu waya, sanin cewa wannan zai saka sabeehar a cikin matsala yasa ya dauke wayar ma ya futo.

Saida ya gama yima khaal bayani kaf saidai bai kawo maganar wayar ba yayi shuru kafin suyi sallama akan a tafi a haka kawai.

Shuru jamid yayi yana tunani, ya kasa gane dalilin da yasa khaal yaqi yin wani abu akan al’amarin nan.

Wunin ranar sabeeha a daki tayi tana hawaye, tunda take a rayuwarta bata taba jin zafin kazafi ba sai yau, ta tabbatar da sharri ake binta dashi kuma allah ya kubutar da ita, abunda yafi bata tsoro shine wayar nan, waye ya dauke wayar? Ta

tabbatar a cikin jakar nan take don da hannunta ta ajiye wayar kuka bata sake daukanta ba balle ta chanza mata waje, sannan ya za ayi ace wai ta hau sama ta dauka kudi da sarka? Saman ma bata gama tsantance ya yanayin wajen yake ba balle har ta iya daukan abunda ba nata ba, iyakacin ta da sama part din taj, shima jiyan tsautsayi yasa taje saman don dubo taj din saboda kwana biyu bata ganshi ba, shima dataje saman ta taddashi yana barci ne ganin haka yasa ta fito daga part din nashi ta sauko kasa, abunda ya kara tabbatar mata da sharri akayi niyar qulla mata allah ya kubutar da ita shine yanda head ta dage akan cewa ta ganta ta dauko sarkan da kudi, wannan abu tsaya mata arai, haka ta kwana tana sallolin dare tana hawaye tana neman tsari ga Allah.

Washe gari da safe haka duk suka hallara a dining area din, dan dole haka ta fito saboda jamid ya umarceta akan dole ta dunga shigowa tana breakfast dasu, gaba daya jikinta yayi sanyi haka ta shigo inda duk suka bita da idanu, gaishesu tayi as usual babu wanda ya amsa sai jamid,kallo daya tareeq yayi mata saida ya dauka kusan minti biyu yana kallonta yana observing dinta, she look naive,wani irin murmushi kawai yayi ya maida kanshi ga abunci dake gaban shi.

Zama sabeeha tayi inda take zama kullum kanta na kasa,tanason dagowa don ganinko taj na wajen saidai bata da courage in haka, maid din dake tsaye ne ta soma serving dinta tana gamawa ta koma baya, da mamaki duk suka dago suna kallon tareeq jin furucin da yayi, “good morning sister inlaw,” ya sauke mata murmushi, dagowa sabeeha tayi ta kalleshi, bata taba ganinshi a gidan ba kuma bata san koshi waye ba amma tunda ta ganshi a wajen ta tabbatar shima family member na gidan ne.

“Good morning sir”

Ta amsa gaisuwar sa,silently suka fara yin breakfast din har ta dago ganin babu taj a wajen yasa taji rashin dadi aranta tare da tunani ko meysa bai zo breakfast dinba.

Hidaya ce ta fara gama wa kafin su afiya,haka suka dunga tashi daya bayan daya suna bari wajen, ya rage daga sabeeha sai jamid da tareeq a dining din, sabeeha dake zaune abuncin ma ba wani cin kirki tayi ba, jira take su gama ta tattara wajen koba komai zata danyi wani abu don zaman nan da takeyi ba dadin shi takeji ba, tafison tana aikinta, daman hidimar taj ne yanxu kuma ya hanata kusantarshi.

Miqewa jamid yayi yabar wajen shima, yana barin wajen tareeq ya Turo mata fruit bowl, in a nice way yace “Sister inlaw bismillah na lura  bakici komai ba its nice”

Kallon bowl din tayi kafin ta dago ta kalleshi tace “Alhamdulillah nagode”

Murmushi ya mata very nicely ya miqe yabar wajen.

Mamakin ko waye wannan ta soma yi, he’s so nice, samun kanta tayi ta shan fruit din dake bowl din, saida suka bar wajen ta smau sakewa, tana gamawa ta tattara kayayyanki daidai nan head ta fito daga kitchen, ganin sabeehar yasa ta umarcin sauran maid su karbi kayan hannunta da gaggawa daman sun fito be don su

kwashe jayayyakin wajen, gaisheta sukayi gaba dayansu, dakyar sabeeha ta iya amsa su don sai abun yayi mata banbanrakwai,tana kallonsu suka tattara kayayyakin tass suka wuce dashu kitchen ita kuma ta koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login