Showing 81001 words to 84000 words out of 135321 words
tayi ba tare da tace komai ba hakan ya bashi damar cigaba da magana, ‘’ga sadakinki fatima, last week na daura aurenki da tajudeen bisa amincewarki, basai na maki bayanin yanayin larurarshi ba don kinfi kowa sanin hakan saidai inason na sake tambayrki for the second time? are you sure about this?’’
shuru ne ya ratsa, gaba daya daga taj har jamid attention dinsu ya koma ga sabeeha don jin abunda zata fada, at that point bugun zuciyar yayi doubling, wani irin nauyi da zafi takeji aranta, batada yancin kanta, bata da right din kanta, kota amince ko bata amince ba babu abunda zai sauya, maganr wannan mutumin daya turo ta leken asiri ne ta dawo mata arai, suna kallon duk wani movement dinta kuma idan ta bijire masu zasu salwantar da rayuwarta harda ta mahaifiyarta, dukda bata samu kusanci da soyayyar mahaifiya ba batajin zata bari wani mummunan abu ya kusanto mamanta don bata kowa daya wuceta.
na biyu kuma ga taj, tausayinshi ya gama zagaye gaba daya zuciyarta, when it comes to him zuciyarta nauyi takeyi musamman yanxu data ga yanda ake treating dinshi a gidan, tun ba yanxu ba ta lura da akwai something suspicious akan rayuwarshi, batajin zata iya rabuwa dashi.
nunfasawa yayi jamid ‘’babu wanda zaiyi forcing dinki’ saidai…’’
katseshi tayi anatse ta soma magana cikin sanyi ‘’yes sir, na amince zan zauna tare dashi’’
atare khaal da jamid suka kalli junan su tare da sauke ajiyar zuciyar relief.
‘’alhamdulillah fatima, alhamdulillah, inason ki sani duk abunda zai faru ba mai dorewa bane, duk qalubalen da zaki fuskanta just keep this in your mind,it shall pass,wannan dalilin yasa banyi declaring dinki a matsayin matar taj ba amma ayanxu dole nayi hakan don taj yana buqatar taimakon ki, i trust you with him please,sannan ga jamid nan, duk abunda kike buqata you can talk to him about it’’
jinkirtawa khaal yayi don bayason yaje deep deep into the discussion don karta tsorata don haka kawai ya barta da wannan, sallama yayi masu bayan ya shaida ma jamid kan cewa a nema mata part daya cikin parts din dake kasa kafin komai ya lafa.
godiya tayi ma khaal cikin ladabi kafin ya masu sallama yabar gidan yan mai jin tausayin yarinyar har cikin ranshi sosai, yanajin kamar basuyi mata adalci ba kwata kwata, ga threat gashi kuma an barta cikin duhu.
Bangaren hidaya suna hawa sama ita dasu fadwa afiya ta soma masifa, ‘’ukty shin kinji abunda khaal ya fada kuwa? wannan ugly poke din as the only daughter inlaw of taheels? kai ina bazai yuwu ba, mey zamu cema duniya? caregiver as the daughter inlaw of this family? wannan is a disgrace to the family, ….’’
‘’malama kiyi mana shiru, we heard him, duk munji abunda ya fada basai kin maimaita mana ba’’ fadwa ta fada tana relaxing akan kujera.
ko kallon inda take afiya batayi ba ta cigaba da magana.
hidaya dai tunda ta zauna akan kujeran study dinta ta babu abunda take sai nazari
‘’wallahi duk laifinki ne ukty, yanxu ki rasa wadda zaki aura mashi sai wannan mai hakoran kamar na doki?kuma african?, why did you even make this decision ba tare da kinyi tunanin irin waennnan abubuwan da zasu biyo baya ba, what if….’’
tsit afiya tayi jin bugun table din da hidaya tayi dake gabanta na study room, tasan abunda take shirin fada don haka tayi saurin katseta
‘’shut the fuck up, ni kike fadama anyhow maganganun da suke fitowa daga bakinki? are you insane?’’
samun waje afiya tayi ta zauna don ta tsorata da yanayin hidayar, ‘’i’m sorry ukty,’’
ko kallon inda take hidaya batayi ba ta maida dubanta ga hotunan su dake kan desk din gabanta, idanunta nakan frame din abbuh, sai kawai ta sauke wani irin murmushi mai kama dana takaici tana ayyana how she will make life very hard for duk wanda ya shiga gabanta,fadwa ce kadai tasan ma’anar wannan murmushin nata don ta iya karantar mutane da abunda ke yawo aransu,
Abuja nigeria…
tunda daddy ya ajiye ta airport take kuka har jirginsu ya tashi, bata taba tunanin daddy zaiyi mata haka ba, sending her to somewhere da bata taba zuwa ba, of all places nigeria, yanda ta tsani nigeria kamar ranta don kwata kwata bata son asan ita yar nigeria ko a school, sai gashi yanxu daddy ya turo ta nan, inda bata san kowa ba batama san ya zatayi coping da rayuwar nan ba, gaba daya she’s not fit to rayuwar nigeria dukda tasan nan ne aka haifeta kuma nan iyayenta suka taso tunda mahaifarsu ce.
karfe biyar na yamma flight dinsu ya sauka a nnamdi ezikiwe international airport,wannan dan kukan datayi ya sata barci har suka iso nigeria ba tare da ta sani ba.
saukowa tayi tana bin bayan mutane dake nufar wajen arrival gate, tunda ta shaqi iskar garin taji ranta ya kara baci, dukda garin ya danyi sanyi saboda yamma tayi hakan baisa taji zafin garin ba, ta rigada ta sama ranta kyamar kasar.
clearing katon akwatinta tayi kafin ta futo daga airport din tana kalle kallen mutane dake shige da fuce kowa yana hidimarsa, taxes din dake bakin gate na ganin futowarta tana dube dube suka yo kanta, ‘’madam ina za a kaiki?, madam ga drop nan’’
saurin ja da bata tayi tana yamutsa fuska kamar taga abun qazanta, ‘’what in the f**,!! get out of my way useless f…’’,
wani irin kallo suka bita dashi kafin su zageta tass da yaren su daman inyamurai, ko kallon inda suke batayi ba ta koma gefe takaici ya gama cikata, tama rasa ya zatayi ta samu wanda daddy yace zaizo ya dauketa, iskar zata bazo mata ne hade da kurar wajen yasa ta doka uban tsuka kamar zatayi kuka ‘’i hate it here, i fucking hate it here, wayyo mummy na’’
ta karashe tana ma runste idanunta,
‘’Maya!!’’ ta jiyo kiran sunanta daga bayanta, juyowa tayi cikin gaggawa, hamid dake tsaye cikin riga da wando na shadda mai kyan gaske, kallonshi tayi daga sama har kasa irin kallon kai’ kuma daga ina?
‘’hey its me, hamid’’
tabe baki tayi don kwata kwata bata gane shi,
‘’mtewww and who d f are you?how did you even know my name?’’ ta karashe da accent dinta na chan,
da mamaki yake kallon yanda take magana da rainin hankali, hannunshi ya sanya cikin aljihun wandon shi, daman shi baya daukan wargi, baiyi tunanin haka take ba mara kunya saida tayi magana.
ba tare da ya tanka mata ba yace,
‘’i’m supposed to pick you up, muje ko’’ ya fada yana mai jan box dinta.
gaba yayi tana binshi a baya har suka karaso wajen da yayi parking motarshi, kallon motar tayi ta sake kallonta, kamar zatace wani abu kuma saita yi shuru,
tana tsaye ya bude boot ya saka box dinta ‘’guy be careful dont ruin my stuff’’
wani irin kallo ya mata kafin yayi banging boot din ya wuce wajen driver seat, seat din baya ta bude zata shiga ya mata wani irin kallo, daman shima irin miskilannan ne basa daukan rainin hankali, ‘’ke!!!! waye driver ki?’’
‘’excuse me? dani kake’’
‘’akwai deaf human beings akusa ne aside from you’’
rai a bace ta mashi wani banzan kallo ta bude seat din bayan ta zauna abunta tare da soka tsaki.
tunda ta shiga motar ta lumshe idanunta, kamar tayi kuka haka ta dunga ji, gaba daya bata son nan nigeria bata kaunar nan din, ‘’mteww wannan wani irin zafi ne, malam ka kara ac nan’’
wani irin banzan kallo hamid yayi mata daga mirror ba tare da ya tanka ta ba ya cigaba da driving, yana mai bin wani cool music dake tashi daga cikin motar.
horn din dayayi ne yasa ta bude idanunta tana mai bin gidan da kallo, samun kanta tayi ta kallon gidan kamar wata bakauyiya tana mamaki.
direct wajen parking ya nufa inda motocin gidan suke a jere gwanin ban sha’awa, yana gama parking ya fito waje, futowa itama tayi tana mai gyara dan mayafin dake kanta, boot din ya bude daidai nan ta karaso wajen, ‘’idan kin fidda stuff din naki ki rufe min motana’’
wani irin banzan kallo ta mashi shiko ko sake kallonta bai yi ba ya nufi part din anne.
cije lebe maya tayi kafin ta kinkimo box din, har zata rufe boot din ta fasa tabar mashi a bude ta nufi hanyar daya bi.
da sallama ya shiga cikin sitting room anne ce zaune gefenta kuma nanna ce suna kallon sunna tv, sallamar hamad yasa suka amsa a tare, anty fadila ce ta fito daga kitchen din anne hannunta rike da cup din kunu data damo ma annen daga gidanta, tana ganin hamad tace ‘’yana ganka kai daya’’
‘’gata nan shugowa’’ ya amsa ta kafin ya nufi inda nanna ke zaune, kunun dake hannunta ya amsa ya soma sha
daidai nan maya ta shugo cikin gidan tana kalle kalle, chak suka tsaya suna kallonta itama kallonsu ta soma yi,
shuru ne ya biyo baya saida nanna tayi breaking silence din tace ’ah ah ah lale maraba mutanen california’’
anne dai ko kallon inda maya ke tsaye batayi ba,saima yanayin fuskanta daya sauya,
gyaran murya anty fadila tayi tare da karasawa inda maya ke tsaye awkwardly tana kallonsu take tunanin yar uwarta ya fado mata arai(bahijja), wani irin farin ciki ya lulubeta gaba daya, cikin sauri ta rungumeta tsam a jikinta ‘’welcome home my dear’’
sakinta anty fadila tayi tare da jan hannunta zuwa inda su anne suke zaune, mikewa nanna tayi ta rungumeta tsam a jikinta tana mai farin cikin ganin mayan, yau ga yar bahijja a gida kai wannan abun farin ciki ne a wajensu.
kissing din kumatunta nanna tayi ‘’maraba lale mutanen abroad, ya mamaki da daddynki’’
‘’suna nan lpy, ina wuni’’
janta anty fadila tayi har wajen anne, maya na ganin anne taga kamannin mummynta wanda hakan ya tabbatar mata da wannan ce mahaifiyar mummy kenan, dukda ta taba ganin hotonta da dadewa a cikin kayan mummy din.
saurin rungumeta maya tayi ‘’grandma na’’ tana mai jin kamar ta rungume mummy ta, anne batayi tsammanin hug dinba sai jinta tayi kawai a jikinta, take ta
tuno mata da bahijja, batama san lokacin data rungumeta itama, sun dade a haka, fadila da nanne babu abunda sukeyi sai murmushin jin dadi ganin anne ta ajiye fushin da takeyi da bahijja kuma bata daurashi kan maya ba.
murnar ganinta suka dunga yi, take kuwa ta soma dan warwarewa tana mamakin ashe familyn mummy suna da arziki sosai haka, bata taba tsammani zatazo ta tadda danginta sunada arziki sosai haka ba.
hamad dake zaune kallon maya yayi tare da tabe baki daidai nan itama idanuta suka shiga nashi ta galla mashi harara harda yar tsuka.
daki na musamman mai kyan gaske aka bata a sama, wanka tayi aka kawo mata abunci taci ta koshi da kyar tayi sallar magrib, sauran waenda bata yi ba kuwa batabi ta kansu ba tabi lafiyar gado.
washe gari haka duka families din sukazo ganin maya, matan uncle sameer ‘’aunty amarya da yaranta suma duk sunzo suna murnar ganinta, anty fadila ma da ahalinta sunzo banda hamad, laila karama kuwa an samu kawa don daman age mates ne saidai laila ta dan girmi maya da shekara guda.
Anne da nanne y’ay’a ne ga Alhaji santuraki santuraki, wanda akafi sani da SS, mahaifinsu yana daya daga cikin manyan manyan mashahuran masu arziki tun tale tale, family SS ya samu tushe ne tun kafin mahaifinsu ya rasu, inda ya gaji shima sunan ubansa.
Alhaji santuraki wanda akafi sani da santuraki karami asalin dan garin zaria ne, da tasowarsa da karatunsa duk a zaria yayi tun lokacin da karatun boko bashi da qarko, mahaifinsa shine wakilin yaqi da jahilci santuraki anan garin zaria.
Santuraki karami ya samu ilimin addini dana boko ta hanyar jajircewar ubansa akansa inda ya nunawa al’umma musali akan danshi kan cewa karatun zamani yana da amfani kuma alumma bazatasan yana da amfani ba sai nan gaba lokacin da karatun zai daukaka sosai.
Tun tasowar santuraki karami mahaifinsa ya nuna kudirinshi akan yaron don yaron ya futa daban daga cikin sauran yayan wakilin yaqi da jahilci santuraki wato mahaifinsu, dukda bashi kadaine danshi ba don yana da wasu yayan hasalima santuraki karami shine auta acikin yayansa, haka kawai allah ya daura mashi son yaron sai ya zamana yaron shima yana qaunar mahaifinsa da abunda kesa mahaifinsa farin ciki.
cikin yayan nasa kuwa dukkansu yayi kokari sakasu karatun saidai abun bai yuwu ba saboda daga cikin yayan wasu iyayensu mata ne suka qi amincewa wasu kuma daga yayan ne, karshe dai ganin kamar jama’a na ganin yana masu dole ne
yasa ya kyalesu duk wanda keda ra’ayi sai yayi don ba kakanun yara bane su don sun mallaki hankalinsu.
Tasowar santuraki karami kuwa addu’ar wakili ta tabbata don shi kadaine cikin yayansa ya nuna yana qaunar yin karatu wanda hakan ba qaramin dadi yayi ma wakili ba don harga allah yana son santuraki karami don shine yaci sunansa.
Akwana a tashi kwanaki suka dunga jaa har santuraki ya fara girma yayi karatun primary harda secondary kafin a cikin wata shekara turawa suka zo kasar Nigeria don ganin yanda ilimi ya zurfafa anan, a shekarar ne kuma mutane da dama suka fara ganin amfanin ilimi musamman mutanen zaria don wakili ya kafa masu shaidar amfanin karatun akan dansa wato santuraki.
Wannan zuwan turawan yayi sanadiyar futar santuraki kasar waje inda govnment ta dauki nauyin karatunshi harya gama, wannan abu yayi ma wakili dadi sosai daga nan kuwa matsololin cikin gida suka fara bayyana, wanda yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar santuraki, mutuwar mahaifiyar sa ta girgizashi sosai inda yaso dawowa gida saidai sanin halin da ake ciki yasa mahaifinsa wakili ya hanashi dawowa don ayanxu matansa da sauran yayan sa zasu iyayi komai don ganin bai cigaba ba wanda wakili baya fatan haka.
Bayan shekara biyar santuraki ya dawo, dawowarshi ba karamin tashin hankali ya haifar ba don ya dawo ne da qwarinshi, dukda yana saurayi amma akwai shi da wayo da hazaqa da hangen nesa wanda hakan ne ya taimakeshi achan kasar, kampani da yawa sun nemi yayi aiki dasu bayan y agama karatu amma ya qi ya tattaro ya dawo don yana son babanshi yana progress din agaban idanunshi bawai yayi ma wasu aiki ba.
Lokacin da saturaki ya dawo tsufa yazo ma wakili, don yanxu baya iya tafiya saida taimako, ganin mahaifinshi a haka ya karya ma santuraki zuciya sosai don yana qaunar mahaifinshi sosai, wannan dalilin yasa ya bada himma sosai wajen ganin babanshi yaga success dinshi, anan zaria ya soma bude dan karamin kamfanin shi inda shine ya fara kirkirar kujerar karfe da marasa tafiya zasu iya amfani dashi a duk fadin duniya, santuraki ya samu inspiration din yin wannan abun ta hanyar mahaifinsa da baya iya tafiya, matsalar da santuraki a fuskanta a wannan stage din shine rashin investors don kamfaninshi karamin kamfani ne sai kuma yan uwanshi da suke son ganin downfall dinshi don kowa ganin abunda yakeyi bashi da amfani.
Bangaren mahaifinshi kuwa Wannan abu yayi mashii dadi sosai inda yayi mashi addua sosai sannan yayi mashi fatan nasara.
Bayan shekara biyu Allah yayi aikinsa, a shekarar ne kuwa turawa sukazo kasar zaria zuwa na biyu Kenan inda sukayi zaman shekaru anan kasar, ta dalilinsu allah ya daukaka santuraki don sune sukayi investing company santuraki inda suka bashi project mai girma wanda duk duniya ba ataba bayarda kamar wannan ba, tashin farko santuraki yayi blowing arziki yazo mashi ta sama da kasa saidai kashh adaidai wannan lokacin rai yayi halinsa, allah ya dauki ran wakili santuraki
mai yaqi da jahilci, saturaki karamii yayi kuka sosai na rashin mahaifinsa saidai yaji dadin cikama mahaifinsa burinsa don wakili ya nunama duniya amfanin karatun.
Bayan rasuwar wakili abubuwa da dama sun faru ciki kuwa shine daukaka santuraki datafi ta da sosai nan take kuma hassada ta soma shigowa daga cikin yan uwansa waenda yanxu gaba dayan su they are useless, kullum a wahale suke babu ilimin arabi babu na boko, wasu daga ciki iyayensu mata sun mutu wasu kuma suna raye wanda suke zugasu.
Santuraki yana kokari sosai wajen ganin ya taimaka ma yan uwansa da sauran iyayensa mata saidai basa godiyar allah kwata kwata saboda yanda suka tsaneshi ganin shi kadaine yayi karatu kuma ya daukaka.
A kwana a tashi ya fara fuskantar yanda suke son ganin baya nunfashi a doron kasa wannan dalilin yasa ya tattara yabar garin ya koma garin Abuja don daman zaman mahaifinsa yake yanxu kuwa daya rasu babu amfani zama don yan uwan nashi ba sonsa sukeba, dukda ya tafi hakan bai hanashi tallafa masu ba amatsayinsu na jinin sa.
Lokacin daya dawo Abuja anan ne ya tabbatar da shi dan gatan allah ne saboda lokaci guda ta san dashi, kasashe daban daban ansan sunanshi, arziki dai saidai yace alhamdulillahi, company kuwa sai habaka yake don babu abunda basa inventing,abubuwan zamani wanda mutane basu taba tsammanin za a iya kerashi ba, keken hawa,cookers,fridge da sauransu.
A lokacin da santuraki yayi clicking shekara talatin cirr aduniya alokacin ya auri Hajiya Amina, mace mai kamala yar babban gida, iyayenta nada arziki sosai don ita kadaice diya a wajen iyayenta, mahaifinta shine Chief Barr Jibrin, babban barrister wanda government tasan da zamanshi.
Shekarar su daya da aure allah ya albarkaceta da juna biyu, bayan wata tara ta haifi kyakyawar yarta ta farko inda taci sunan kakarta mahaifiyar santuraki habiba, habiba ta taso da soyayyar iyayenta babu abunda ta nema ta rasa, santuraki yana masifar sonta sosai don yana kallonta yake tunawa da mahaifiyarsa dukda lokacin da amina keda cikin ta ya kwallafa rai akan da namiji wanda zai gajesa.
Samun habiba a cikin rayuwar su ba karamin farin ciki ya haifar masu ba, don yarinya ce mai jajircewa sosai she’s so bold and strong bata tsoron kowa,suna masifar sonta sosai wanda hakan yasa santuraki ya tsaya tsayin daka akanta inda yake yawan cewa ‘’ko ban