Showing 9001 words to 12000 words out of 135321 words
kowa yaci’’
Kallonshi mummy tayi jin abunda yace kafin ta sauke kanta kasa ba tare da tace komai ba,
‘’okay sir’’ nanny b ta amsa shi kafin ta juya
Tsaidata tayi ta hanyar cewa ‘’nanny b, please a tado’’
‘’okay sir’’ nannay b ta amsashi kafin ta nufi hanyar stairs, sai alokacin mummy ta kalleshi ‘’daddy wani abun ya faru ne jiya?’’
Bai kalleta bay a bata amsa ‘’bari yar taki ta sauko saiki tambayeta’’
Mummy najin hakan ta tabbatar da wani abun ya faru jiya, sanin halinshi yasa bata sake cewa komai ba saima zuba hada tea data soma yi.
Bangaren maya da kyar ta tashi, don babu yanda nany b batayi ba akan ta fito daga duvet dinnan taqi, wai barcin bai siheta ba saida taji cewa daddy yace a kirata tayi saurin miqewa ta sauko daga ita said an short da bra, toilet ta wuce while nanny b ta futa daga dakin.
Brush da wanka maya tayi sharp sharp kafin ta fito, closet dinta ta bude ta fara duban abunda zata saka, tashin farko ta watsar da komai dake cikin drawer daga duban rigar sakawa, duk cikin kayan zaman gida dake cikin drawer are revealing, don bata son kaya masu nauyi kwat kwata shiyasa take kwaso su idan sunje shopping da mummy, wat riga maid an siririn hannu ta dauka ta zura, rigar rubber ce so saita kama ta sosai amma kuma tayi mata kyau don itama akwai kyau masha allah, ita kyanta ya futa daban don kamar ruwa biyu ce, ta dauko mummy ta wani bangaren kuma ta dauko daddy ta wani shashen, batada hanci dai kamar iyayen nata.
Gashin kanta datayima mini twist fixing yanda baza a ganeba ta nannade tayi bun kafin ta feshe jikinta da turaruka kamar zatayi ruwan turare.
A chan parlor kuwa har sunyi nisa wajen yin breakfast, takun tafiyarta da kamshinta da yayi masu sallama yasa suka dago gaba dayanshu daga daddy har mummy, kallo daya yayi mata ya kauda kanshi, ita kuwa tana ganin mummy aguje ta karaso dining din ta rungumeta ‘’mummyyyyyyyy’’
‘’sakeni karki ballani, bakisan kin zama katuwan baby ba’’ mummy ta fada tana dan buge hannunta data nado a wuyanta.
Dariya maya tayi kafin tace ‘’nayi missing dinky mummy’’
‘’missed you more baby, zauna kiyi breakfast’’
Daddy dai yana jinsu baice masu qala ba saima shan tea da yakeyi.
Tanan gefenshi maya ta zagayo don nan ne mazauninta don koda yaushe a tsakiya suke sakashi idan zasuci abunci.
Zama tayi anatse kafin ta dan kalli gefenshi ‘’good morning daddy’’
Saida ya karasa shan tea din dake bakinsa kafin ya amsata a gajerance ‘’morning’’
Cikin natsuwa suke Karin kumallo, babu sautin dake tashi sai na spoons da plate, daddy ne ya fara gamawa, miqewa yayi ya kalli bangaren maya ‘’this should be the last time da zaki dunga yawo babu hula akanki da irin wannan kayan a cikin gida sannan wannan hair style din ki chanza shi, ki nema decent kitso kiyi,’’
Yana kaiwa nan ya wuce sama ba tare da ya sake kallonsu ba, mummy dai mamaki y agama cikata don this is the first time yayi Magana akan shigarta da saka hula, don kwata kwata maya bata son saka hula akanta, sannan kaya shima yasan bata son masu nauyi.
Bangaren maya kujwa tunda ya fara Magana har yakai aya bata dago idanunta ba, sai aynxu ta tabbatar ranshi y abaci sosai da abunda tayi jiya saidai batayi tunanin abun zaikai ga haka ba.
Yana wucewa mummy ta kalleta fuskanta adan hade ‘’maya!!, me ya faru jiya? Kinyi wani laifin ne kuma? ‘’
Hawaye ne ya soma zubo mata tana kallon mummyn nata ‘’mummy wallahi ba wani abu nayi ba, wai saboda na dawo late jiya shine daddy ya kwace min komai nawa harda phone na’’
‘’kinyi laifin Kenan?haba maya ko gajiya bakyayi?, did’nt I warn you akan Maganar dawowa daga school?, me kika tsaya yi har kika dawo late?’’
‘’nidai mummy dan allah ki bashi hakuri ya bani wayana da laptop dina, ni motar daya bani ma ya rike na hakura kawai ya bani wayada da ipads dina’’
Kwafa mummy tayi kafin tace ‘’babu ruwana kedashi tunda bkyaji’’
‘’mummy please, ke kadai ce hope dina dan allah karki ce haka, wallahi mun kusa fara exams kuma dole zan buqaci gadget dina please’’
‘’naji’’ mummy ta amsata a gatse.
Shuru maya tayi tana rausaya kanta dukdan mummy taji tausayinta, wanda hakan ke tasiri, da zarar ta zubda kwalla shikenan, don mummy tana bala’in sonta sosai don ita kadai ce allah ya mallaka masu, tun bayan haihuwar allah bai sake basu haihuwa ba shiyasa mummy ta dauro son duniya ta maka mata dukda tana sa ido akanta saidai ita tana da soft point akan maya wasu abubuwan bata hanata saboda son da take mata, daddy ne dai baya tolerating kwata kwata don baya son ta kangare ko ta dauki aladun da rayuwar yayan nan kasar.
Saman mummy ta bishi bayan ta gama breakfast, bata tsaya ko’ina ba sai master bedroom dinshi, da sallama ta shiga bedroom din,kamshinsa ne yayi mata sallama hade da sanyin ac, dakin nashi ya hadu sosai, har book shelve ne a cikin daki.
Ganin baya nan yasa ta wuce hanyar bathroom, alamun saukan ruwa ya tabbatar mata yana wanka.
Kai tsaye ta shige bathroom ta rufo kofar, after like an hour sai gasu sun fito atare, fuskansu dauke da murmurshi, yana biye da ita a baya.
‘’wife bakya tsufa’’
Rufe fusknta tayi da tafin hannunta ‘’jarumina Kenan, allah yabarmin kai majeed din bahijja’’
Bata karasa Magana bay a janyo ta jikinshi gam ya soma aika mata wasu sabbin saqonni masu rikitarwa, nan take itama ta soma bashi wuta don itama babu dama, duk duniya majeed bayajin zai taba samun mace kamar badiyya, badiyya ta jiyaer dashi dadin da baya sha’awa a waje kwata kwata, ita din dai, musamman a bangaren auratayya tsakanin miji da mata, allah yayi mata wata baiwa da kyautar da shi kadai yasan irin yanda yake ji a tattare da ita shiyasa yake masifar sonta kamar ranshi.
Sun dauka kusan awa biyu kafin komai ya lafa lokacin har sun sake wani wankan.
Anan bedroom dinshi ta sauya kaya don daman akwai few kayanta anan incase.
Mummy ce da kanta ta taya shi saka kaya ta feshe shi da turarensa na tom ford.
‘’hubby please ayima maya afuwa, ta fada min abunda ya faru jiya, dan allah kayi hakuri majeed dina bazata sake ba I promise’’
Zuba mata idanu yayi yana kallonta tare da karantarta, shi zai iya cewa kamarma tana nuna ta fishi son maya ne, baice komai ba kawai ya kauda kanshi gefe, ganin haka yasa jikin mummy yayi sanyi.
Da mamaki taji hannunshi cikin nata ‘’wife duk abunda kikaga inayi akan maya I’m trying to do what is best for her, ki tuna fa mu baqi ne anan mu ba turawa bane, maya is trying to collide with character din turawa da abubuwan dasuke normalizing wanda kinsan haramun ne, bana son ta kangare, I want what is best for our only child, yanda kike qaunarta haka nake sonta sosai, im being strict towards her saboda idan muka zaman soft gaba dayanmu zamuzo muna regretting upbringing dinta, so please allow me to displine her don tasan cewa tayi ba daidai ba okay?’’
Jikin mummy ne yayi sanyi dajin maganar tasa don tabbas yayi gaskia ita kanta bazata so maya ta lalace ba, don haka tayi saurin girgiza mashi kai alamun gamsuwa ‘’thank you dady, kayi gaskia allah ya shirya mana’’
‘’ameen wifey’’ matsota yayi cikin kulawa ya sumbaci kumatunta.
**
MATAR TAJ(Destined with you
🩵🤍
)
❤️
🔥
Romantic love story
❤️
🔥
Written by QueenMarh
Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai…
Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba.
I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.
The suspense and the plot twist is a top notch
🙃🙃
Enjoy!!!!!
Free page
Chapter 5-6
3 months ago (wata uku da suka wuce)
FCT Nigeria……….
Dutsen habuja wani gari ne dake a baya bayan garin abuja, yawancin mazauna garin basuda arzikin zama cikin ainihin garin Abuja,sai ya kasance masu zama a cikin garin zaman rufin asiri sukeyi saboda rayuwar Abuja sai mai arziki.
Acikin garin akwai anguwar datafi fuce a cikin garin wadda ake kira da kayefi, anguwace me qunshe da tarin jama’a don anguwar a cunkeshe take da mutane, both chiristians da musulmai harma da waenda basuda addini,a bangaren culture kuwa babu wanda babu a aguwar, gwari, yarbawa, igbo, igala duka,haka zalika ginin aguwannin cikin layin kwata kwata basuda kan gado don yawanci gidaje ne na haya barkate don ko hanyar da mota zata kutsa cikin layin babu.
Yawan mutanen anguwan yasa aka samu qarancin tsafta a anguwar saboda yanda mutane ke sana’a daban daban acikin anguwar don su rufa ma kansu asiri su samu na cin yau da gobe.
Da sallama wata dattijuwar mata ta shigo daya daga cikin gidajen haya a anguwar kayefi anan bayan garin Abujan,dan karamin gida ne daga waje mai kofar karfe, labulen zauren gidan ta dage inda ta sanya kafarta cikin tsakar gidan, hayaniyar da akeyi daga ciki ne ta karade tsakar gidan inda wasu mata da mazan gidan ke hada hadan su kowanne yana abunda ya shafe sa.
Wato daga cikin gidan dakuna ne kusan guda biyar a jere, sai dan tsukeken tsakargidan da bandaki sai wata yar rumfa da alamu anan sukeyin girki.
Ragowar Goron dake hannunta ta wulla cikin bakin ta kafin ta rike sandar dake taimakonta wajen tafiya don tana da kiba sosai gashi girma yazo don kamarma dan dingisawa takeyi, sanye dattijuwar take da atamfa riga da zani sai wani mayafi kore kore.
Tana karasowa tsakar gidan ta soma tari saboda hayaqin daya bade tsakargida inda yake fitowa daga rumfar girkin su.
Matan dake zaune a tsakar gidan sunsha daurin kirji sai faman zazzaga masifa suke tsakanin,daman sun saba, don dawuya ayi wuni guda ba tare da anyi fadan nan ba kamar kaji.
Mazajensu kuwa suna kallonsu ko qala bazasu ce masu ba, mazauna gidan maqotansu kuwa babu wanda yake shiga irin wannan fadan saboda daga hakan yake jawo babbar matsala.
Takalman kafafunta ta soma zarewa ta ture su gefe guda hannunta rike da leda, ta soma takowa daidai hanyar rumfar girki kafin ta dan leka tare da daga murya tace ‘’keeee sabeeha?? wannan hayakin fah? Babbake gidan zakiyi ne?’’
Yarinyar dake tsugunne a bakin wata runfa daga chan tsakar gida sai faman rura wuta take kamar ranta zai fita don iccen kwata kwata bashida cii saboda yanayin garin yau ayi rana gobe ayi ruwa, takai kusan awa guda a tsugunne tana faman abu daya, gashi rana ta fito kwal sosai don rufin langa langa ne wanda hakan yasa zafin ya hadar mata biyu ga zafin rana gana wuta don kusan kowa ya daura tukunyar girkin rana.
Jin sautin muryar kakarta yasa ta saurin juyowa ta mike tsaye don nufin hanyar fucewa daga rumfar,gyaran mataccen hijab din jikinta ta soma yi don yayi mata yawa sosai gashi ya kode,ta wajen wuyan hijab din ta tattaro shi ya rufe rabin fuskarta, babu abunda ake iya hangowa sai hazel eyes dinta da sukayi jaa masu daukar hankali da ido, gashin idanunta sunyi wara wara saboda hawayen dake zubo mata saboda hayakin data shaqa, wajen brows dinta kuwa a cike yake da gashi har yana neman hadewa baqi wuluk dashi.
Saida ta fito sarari sosai na kalleta dakyau, daga ganinta tana da dan haske saidai wahala data kodar da ita, bata da wani tsayi sosai saidai baza ace da ita gajeruwa ba, kana ganinta kaga yarinya danya shataf don bazata wuce shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba, hijab din jikinta yasa na kasa gane yanayin jikinta saidai bata da wani qiba, kafarta sanye da baqin silifas daya soma cinyewa.
Tari ta soma yi tana mutsiqa idanunta da sukayi jaa kafin cikin ladabi ta soma Magana tana mai kokarin karbar ledar hannun inna ‘’sannu da dawowa inna’’
Kallon fuskanta inna tayi idanunta yayi jaa sosai gashi sai kaurin hayaki takeyi ga uban zufa data tsatsafo mata.
Adan fada fada inna ta soma Magana ‘’wannan hayaqin fa? Ni mai larurar idanu ay sai ki karashe min ganin nawa ‘’
Inna ta karashe tana mata wani irin kallo, shuru yarinyar data kira da sabeeha tayi tana mai sauraronta saida takai aya tukunna kafin ta soma Magana cikin ladabi.
‘’inna iccen ne ba…ya ci’’.
‘’ke har yanxu hada icce ya zame maki wani jan aiki,ina uwar taki’’
Kanta ta sauke kasa tana mai duban jar kasan dake tsakar gidan don ko sumunti ba ayi ba ,’’bata dawo ba ’’ ta bata amsa
Saurin runtse idanu inna tayi don yana yanar da idanun nata keyi cikin yan kwanakin nan yasa ganin ta ke neman daukewa dukda bata bari kowa yasan da yanayin da take ciki ba.
‘kin gama dahuwar kwan?’’ ta sake wullo mata tambaya
‘’eh na gama tun daxu, abunci rana ne nake kokarin daurawa’’ ta bata amsa a natse.
‘’zoki bani ruwa mai sanyi in kashe kishirwar dana kwaso,’’
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar dazai sadata da dakin su, kofar dakinsu na daga chan saqo, daga gefe kuma wani daki ne karami.
‘’inna ka dawo’’ wata matar gwari dake kokarin daurama yarta robar dafaffiyar masara ta sayarwa ta soma Magana.
Kallon inda take inna tayi kafin ta washe baki don ita kadaice suke mutunci a gidan dan sauran kwata kwata basuda mutunci ‘’maman chidi na dawo, ina chidin yake’’
‘’shege yaro ya tafi yawo’’ matar ta bata amsa
‘’yara daman ba’a rabasu da yawo, miqon masarar hamsin’’ ta karashe tana wucewa
‘’toh,’’
Karbar masarar sabeeha tayi kafin ta bi bayan innar har suka zo daidai kan damali kofar dakinsu inda suke yawan zama musamman idan ana kwalla rana saboda wajen akwai dan damshi damshi, tabarmar dake ajiye a wajen sabeeha ta warware ta shimfida kafin ta nufi uwar dakin su, labulen dakin ta daga tare da saka kai ciki, dakin bashida wani girma da alamu ciki da parlor ne don naga harda yan kujeru guda biyu sai ledar daki saidan fridge, daga gefe kuma wata yar yaloluwar katifa ce, ko’ina fess fess babu qazanta sai kamshin turaren tsinke dake tashi.
Direct inda dan mataccen fridge dinsu yake ta nufa ta bude kafin ta zaro pure water guda daya mai dan sanyi.
Tana fitowa a zaune ta tadda inna yanda ta barta tana bude ledar data shugo dashi, yar shinkafa ce ta auno masu ta awo kwano daya sai taliya itama wadda ta auno saidan manja da maggi da kuka.
Anatse sabehaa ta tako inda inna ke zaune kafin ta zauna gefenta cikin ladabi tace ‘’inna ga..shi’’
Kurama fuskar ta ido tayi data danyi duhu, baka ganin komai sai kwayar idanunta sai dan karan hancinta,saboda yanda ta janyo wuyan hijab din daidai wajen bakinta.
Ruwan hannun nata inna ta karba tana mai yin wani tunani da yake bata mamaki tun da sabeeha ta soma tasowa.
Saida ta shanye ruwan tass kafin ta kalleta tace ‘’jeki karasa abuncin kizo ki tafi, karta dawo ta fara zazzaga masifar fitar ki data saba, ni na kasa gane wannan wani irin abu ne, yoh idan baki futa ba kema kin nemo mana abunda zamu rufama kanmu asiri ya zamuyi?, wallahi bazai yuwu ba kuwa, mun gajii nema don haka kema saikin nema na kanki wallahi,zaman banza bazai yuwu ba, ni yanxu da futa ke neman yimin wahala ga ciwon kafa’’
Cikin sanyi tace
‘’toh’’
Mikewa tayi ta wuce hanyar rumfar girki, maficin data ajiye a gefe ta dauka ta soma rura wutar, saida ta dauka kusan minti goma ta samu wutar ta kama da kyar, hamadala tayi kafin ta mike da robar shinkafar data tsince tsakuwar ciki ta juye cikin tukunyar.
Bakin rigiyar dake hanyar bandaki ta nufa ta janyo ruwa a buta ta wuce bandaki, dakyar ta karasa cikin bandaki kamar zatayi kuka saboda dattin daya yi, kuma da safe saida ta wanke shi tass kafin mamanta ta futa don duk safiya saita wanke mata idan tazo shiga,sha’anin gidan haya dai sai a hankali, shiyasa yawanci bata shiga bandakin cikin gidan, idan ma zata shiga sai bayan mamanta ta futo nan ne take samun damar yin wanka idan bata samu shiga a wannan lokacin ba haka zata hakura saita futa. Ruwan butar data debo ta tutule ta dauraye inda zatayi amfani dashi kafin ta futo.
A gurguje ta gama dafa dafadukar shinkafa, ta juye cikin kular su dukda dahuwar bataji kayan kamshi ba da nama hakan baisa kamshin abuncin yaqi fitowa ba.
Dakinsu ta nufa da kular lokaci inna ta wuce ciki, ganin bata parlor yasa ta ajiye inda take ajiyewa koda yaushe.
Cikin uwar dakin ta shiga da sallama, a kwance ta tadda inna kan gadon karfensu sai kwasar munshari take, gefenta masarar data gama ci ne ta yasar anan kan gado.
Kauda kanta tayi ta wuce wajen da akwantin kayanta ke ajiye gefen sip, budeshi tayi ta zaro wani hijabi wanda shima yadan soma kodewa, tana zarowa ta rufe akwatin ta fito daga cikin dakin zuwa parlor.
Hijab din jikinta ta soma zarewa daidai nan aka daga labulen dakin nasu, cikin sauri ta sauke hijab din ba tare da ta cire shi ba.
Kamar an wulloshi haka ya shugo cikin dakin, kallo daya tayi mashi yana sanye da riga yar shara sai wani wandon jeans daya dan yage daga kasan wandon, idanun nan nashi jajawur kamar gauta,dauke idanunta tayi da sauri daga kanshi kafin tace‘’sannu da dawowa kawu’’ cikin