Showing 60001 words to 63000 words out of 135321 words
baby abu a kunne nan take ya qalqale da dariya yace “first love ina jiranki please ki dawo”
“Okay big baby”
Shi ya fara fitowa tana biye dashi a baya saida suka zo daidai bedroom din nasu ya janyo hannunta ya tura ta cikin part din ya rufo kofar.
Hannunta ta nade a kirjinta tana kallonshi tana jiran abunda zai ce mata “hidaya, bana son wani boye boye, fadamin menene dalilinki na auren?”
“Saboda shi ne what is best for big baby?”
“In what aspect?” Ya sake doka mata tambaya
“Bakaji abunda doctor ya fada ba ko sai na maimaita maka?”
“Kina tunanin bansan abubuwan da kikeyi its for your own benefit bane? What do you want this time around?”
Wata iriyar dariya tayi kafin tace “jamid listen to me, i don’t care what you think rn, all i know is, I’m doing what is best for him, so please stay out of this”
“Hidaya kiji tsoron allah”
“In banji tsoronsa ba kai zanji tsoro?” Ta gaya mashi magana kafin ta wuce bedroom, certificate din auren data gani kan coffee table ne ya tabbatar mata anyi auren, ba karamin dadin hakan taji ba dukda bata nuna masu a fili ba, saidai wannan ne kadai last option.
Bangaren sabeeha, ta kasa gasgata abunda kunenta ya jiyo mata a sitting room, tunda ta wuce bangaren su na maaikata ta zauna samun kanta tayi da zuba da hawaye mara dalili, gaba daya ta shiga confusion, na farko ta kasa gane menene kudirin wannan mutumin daya turota leqen asiri, sannan abunda yafi daga mata hankali sosai har taie tambayar kanta shine, wanene wannan mutumin, meysa yake controlling dinta, sannan ya akayi yasan da maganar aure? Tun kafin ayi maganar har ya umarceta akan ta amince, karta yi gardama, fatanta daya da takeyi shine allah yasa hakan ba anyi shi bake don ayi amfani da ita don a cutar da friend, don sai yanxu take ganin komai is revolve around him, tasan tana kula dashi amma meysa za a aura mata shi? Mey zata ce ma mahaifiyarta? Why the need of the aure? Waima wani irin aure? Basu san ta ba bata sansu ba? Anya babu cutarwa a cikin wannan abun?””innalillahi wa inna ialaihi rahiun” ta soma furtawa, take hankalinta ya sake tashi sosai, gashi shes confuse babu wanda zai bata amsa kawai saita fashe da kuka, yaj dakin su kuwa mey zasuyi banda kallonta babu wanda yayi attempting yaje wajenta don yaji meke damunta.
Ranar dai ko part din taj din bata sake komawa ba saboda wani matsanancin ciwon kai daya saka ta a gaba.
Bangaren su fadwa, afiya babu irin zage zagej da batayi ba har fadwa ta gaji da ita
“Ke wai mene ruwanki? Why would you care?” Fadwa ta tambayeta,
“Dole na damu mana, wallahi tallahi na tsani ukty, bana kaunar ganinta akan wannan mahaukaci, yanxu ta manta ta sanadiyarshi yanda komai ya sauya mana? Farin ciki mu? Jin dadin mu da komai? Yanxu harta manga yanda muka taso cikin kunci? Childhood dinmu babu walwala babu komai dukdan saboda shi?, wallahi idan har ku bakwa kishin ummuh to wallahi ni inayi, ”
Kuka ta fashe dashi “ why would she care? Maysa zata so shi fiye damu? Meysa zata damu dashi fiye damu? Why?“
“Shiyasa nace wani sa’in kanki wallahi kamar na kifi, you’re so annoying, yanxu kukan na menene kikeyi? Ta rigada tayi deciding so sai me?”
“Malama karki fada min maganar banza, ba tun yanxu ba ke ma nasan kina bin bayanta mteww, duk abunda takeyi akanshi baki taba complain ba kamarma ke baki damu ba kwata kwata, i need fresh air i cant with all of your nonsense” tana kaiwa nan ta fuce daga dakin
****
Zaune suke cikin wani parlor babba, daya na zaune wajen masaukin baki, daga gefe kuma wani saurayi ne a tsaye, suna nan zaune saiga wani mutumi ya fito, babba ne mutumin don ga furfura ne ta mamaye fuskanshi gaba daya, yana da qiba sosai, sanye yake da farar jallabiya sai rawani da yayi a kanshi, wata baqar jaka ce a hannunshi, yana karasowa parlorn wanda ke tsaye yayi saurin matsowa ya karbi jakar.
Na zaunen ne yayi saurin miqewa yana girmama shi, kallonsa babban mutumin yayi kafin ya zauna, dariya ya soma yi “great job doctor!”
“Thank you sir”
Kallonshi mutumin ya sakeyi kafin yace, “kana da kaso mai tsoka saboda wannan labari daka bamu, akwai ticket dinka to bangkok, your new job awaits you from there”
Da sauri ya miqe ya karbi jakar “thank you sir thank you sir”
“You can go now”
Fucewa doctor yayi yana murna, don wannan ba karamin kaso ya samu ba, yayi mamaki sosai kuma akan just dan information din daya basu,wannan abu yayi mashi dadi sosai.
Yana fita mutumin ya kalli yaronshi yace “prepare babban kamfanin gidan yada labari, gobe inason a tashi da latest labari kai rikitarwa kan dan taheel kuma heir of the company is mentally unstable, zanga ta yanda za ayi wannan kamfanin ya cigaba da bunkasa, over this years sai yanxu zamu samu damar kawar dasu daga industry dinnan hahahahaha”
“But sir ya zamuyi da wannan likitan?”
“Wipe him off,kasan duk wanda yamin aiki yana gamawa bana barin shi da rai saboda threat so just finish him”
“Okay sir”
Yaron ya amsa shi kafin ya futa daga parlor, wata iriyar dariya babban mutumin yayi kafin yace “its high time” hahah
Abdullah ibn basit kenan, babban competitor kuma tantirin dan kasuwa, yana cikin Manya manyan masu kudin tahlia district sannan yana kasuwanci daban daban, duk wani harkar business da taheel sukeyi shima yanayi, yana da baban campany saidai baikai taheelz ba don shi bai dade da shiga kasuwancin ba, ba
kamar taheels ba da su kasuwancin su suka gaje sa daga wajen iyayensu har yayi accending to yayansu.
Abdullah ibn basit shine babban dan adawar taheel, tun kafin marigayi taheel ya rasu har zuwa bayan mutuwarsa, bayan mutuwarsa ya dauka kamfanin zai durkushe sai kuka yazo yafi da ma habaka, babu irin bibiya da harin da abdullah baya yi ma taheel company, amma abun yaci tura shekara da shekaru ya kasa samun abu guda daya dazai kama wanda zai sashi ya danqwafar da kamfanin a bayan fage kenan, a gaban duniya kuwa an shaida abdullah as aminin taheel kuka na hannun damanshi don shine wanda ya maida abdullah mutun a yanxu, ya dauke shi ya bashi aiki a companyn shi lokacin da bashi da kowa har ya maidashi mutun ya ajiye shi a kusa dashi.
ABUJA…
Kallon maqudan kudin dake gabansu jamila tayi kafin ta kalli mijinta, “jamila, anya wannan abun kuwa babu wata matsala? Wannan uban kudade ki duba fa ki gani?”
“Mai gida mai kake nufi kenan? Waye zai sani? Kaga ni wallahi babu abund aya shafeni, kudi kuma wallahi kashesu zamuyi muma mu shigo gari, wannan miliyan biyun ka ajiyesu kason mu ne sauran miliyan daya dake account dinka kuma zamu dinga bawa hadiza da kadan kadan karta fuskanci wani abun”
“Amma hadiza bamusan fah wani hali yarinyar nan ke ciki ba, an kira mu ne kawai an bamu kudi kuma ance saboda ita, Basu fada mana mene kudinrinsu ba fah? Da dalilin turo kudin? nidai tsoro nake ji wallahi”
“Kai matsalar ka kenan in kasan haka ne meysa kayi karyar kaine mariqin ta kuma maisa kayi karyar iyayenta duk sun mutu ? Ay naga son kudin ne kaima yasa kayi karyar, saida muka karba kuma zakace wani tsoro kake ji?, amma dai tsaya yanxu da gaske daga chan kasar saudiyyan aka aiko? To saboda me? Kai koma dai saboda menen oho chan ta matse masu, koma mey ya sameta achan ko sayar da ita akayi wannan ba damuwata bace ba, ita kanta uwarta ba damuwa zatayi da hakan ba dukda bazan fada mata ba”
“Toh shikenan” mijin jamila ya amsa ta.
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 29-30
Saudi Arabia…..
Monday morning!!!
Washe gari ta kama monday, wannan rana ta kasance rana wadda mutane da dama suke jiran zuwanta, hidaya tun wajen karfe bakwai ta bar gida don ko breakfast batayi ba.
Jamid ne ya kai barad school kafin ya dawo, lokacin daya dawo wajen karfe takwas na safe, abubuwan da suke faruwa tsakanin jiya da yau sun tsaya mashi arai ga fargaba da yake ji, anan compound din soma jin hayaniyar ma aikata sun hade waje daga, da mamaki yake kallonsu don sunbar ayyukan da sukeyi.
Kauda kanshi yayi daga kansu kawai ya wuce cikin gidan, bai tsaya ko ina ba sai hanyar dazai sadashi da stairs zuwa sama daidai nan fadwa ta fito daga bangaren ta, batama lura da jamid ba ta nufi wajen tv ta kunna news wayanta na hannunta, daman kiranta mijinta yayi ya shiada mata abunda ke faruwa.
Rasa ma wace tasha zata shiga tayi .
Headline din da jamid yaji ne yasa ya tsaya chak bai sake daga kafarshi da niyar tafiya ya yayi saurin maida dubanshi ga tv din, ga headline nan a kasa anyi rubutu da manyan harufa, “ reported news; heir of taheel groups has been grounded and hidden to the world because of amnesia”
Saurin chanzawa fadwa ta sakeyi ta shiga wani news channel din, nan ma cece kuce akeyi akan wannan breaking news din, akan company taheel, da gudu jamid ya sauko kasan baima san sanda ya warce remote din hannunta ba ya soma kara volume don jin abunda ake cewa,
Nan take kuma aka sauya headline din zuwa sabo, inda aka hasko hidaya a zaune zatayi press conference, dabas jamid ya zauna akan kukera yana kallon tv babu ko kiftawa,
Intoduction ta farayi kafin reporter din suka fara mata tambayoyi, “ madam shin da gaske ne heir din kamfanin taheel group kuma qani a wajenki yana fama da ciwon hauka? Madam meysa kuka boye wannan? Munason musan dalilin da yasa duniya bata san da haka ba?”
Saida ta gama jin tambayoyin su wasu ma sukarta sukeyi da tambayar, suna gamawa ta soma magana.
“Na farko wannan official announcement zanyi Tabbas heir din kamfanin taheel group yana fama da critical traumatic amnesia wanda yasa bayyanashi ya zame mana babban threat a gareshi da mental illness dinshi”
“Does that mean grounding dinshi kukayi for your benefit ko saboda kada tattalin arzikin kamfanin ku sauka?”
“Noo, i can’t publicly explain why but saboda health dinshi ne”
Wani reporter ne daya rufe fuskanshi da mask yace “does that mean situation dinshi is critical kenan meaning hauka yakeyi kenan?”
Shuru tayi suka zuba mata idanu sai faman haskata ake da cameras, jamid dai kasa dauke idanunshi yayi akanta yana jiran jin abunda zata ce, to his surprise sai yaji tace “ yes, situation dinshi is critical, i dont want to use the word hauka but i can say something similar cause he’s like good for nothing”
Wannan statement datayi ba karamin hargitsa komai tayi ba mutane sunyi mamaki sosai don kamar tayi destroying komai,
Wani ne cikin reporters yace “yanxu a wani mataki taheel group yake ciki? Zaku sayar da kamfanin ne? Ko zaku bari wannan ya zama downfall din legacy din? As we all know babu yanda za ayi companying yayi running without the heir”
Murmushi hidaya tayi kafin ta kalli wanda yayi magana tace “bazamu bari gumin iyayenmu da a sacrifice din da sukayi mana ya tafi a banza ba,“
“Babu yanda za ayi mahaukaci yayi rulling company madam…”
Hannu ta daga masu, kafin ta sauke ta dago wata yar paper, tana daga zaune ta mike tsaye, “i Hidaya taheel, the present acting ceo of the taheel group will take over responsibility of the company as the legal ceo”
Nan take aka soma hotuna masu zooming suka soma zooming documents din, kowa da abunda yake son fada.
Wannan reporter daya tambayeta kan cewa taj mahaukaci ne ya sake jefo mata tambaya,
“How is that possible? A yanda muka san law din business industry dinku babu yanda za ayi mace tayi ruling musamman idan akwai heir?”
Kai tsaye ta amsa shi, “you mean heir din da is not stable? Well there is, papers don’t lie, i am legally the chief executive director of the taheels, my brothers sickness bazaisa mubar abunda iyayen mu sukayi building ya lalace ba,we’re sorry for hiding this from the world, we did it for the sake of our only brother for his protection, thank you”
Tana kaiwa nan ta fuce daga conference room din, babban lawyer kamfanin taheel na biye da ita a baya, reporters kamar mayu haka suka soma kiranta madam madam madam, harta fuce.
Bayan ta shiga motarta tare da lawyern ta sauke wani sigh of relieve,” weldon madam your decision of hitting 2 birds with a stone is absolutely incredible”
“Thanks barr” ta amsa shi.
Wasu papers ya miqa mata tayi sighning duka kafin yace “madam you’re the current president of taheel groups, congratulations”
“Thank you, ka ajiye copy din zan karba original document din”
“Okay ma”
Gaba daya paper documents din ya tattara ya bata kafin su wuce office.
Jamid daya gama kallon tashin hankali, miqewa yayi cikin sauri ya wuce gidan khaal, koda yaje gidan shi shima already yaga abunda hidaya tayi.
“Khaal na fada maka, na fada maka wallahi wallahi hidaya bazata taba chanzawa,wannan rashin lpy taj is an opportunity to her, and tayi using dinshi to her benefit,“
Shuru khaal yayi yana wani nazari kafin ya kalli jamid yace “jamid, ina ganin we wrongly accused her, intentions dinta are pure kuma protecting taheel groups tayi”
Da mamaki jamid ke kallo khaal, babu abunda yake nema sai karin bayani,
News paper dake gefenshi ya dauka ya bama jamid din, take ya soma karantawa, jarida ce da aka buga ta tun daren jiya za a fidda ta ayau, abunda aka rubuta dai babu dadin ji duk kuma akan taj, wasu irin concrete false evidence aka tattara akan cewa yana drugs wanda shine sanadiyar samun amnesia da yake dashi yanxu wadda ta zama critical sosai, wanda kowa yasan me hakan ke nufi.
Da mamaki jamid ya dago, khal ne yayi saurin cewa “wannan jaridar itace first headline data fito kafin hidaya Tayi conference, badan ta hada conference dinnan ba da tuni companyn taheel a rufe shi gaba daya, wannan yasa aka dakatar da futarda wannan news din,”
Girgiza kai jamid yayi yace “how? Waye zai yi wannan? Ni ina zargin duk aikinta ne”
“Mutun daya nake zargi Abdullah ibn basit”
Gingina kai jamid yayi kawai, sai ya kuma fara jin rashin dadi game da yanda ya dunga zarginta.
“Ni wannan abun ma yamin dadi, saboda koba komai boyeshi da akeyi zaizo karshe.
Khal ya fada yana mai kallon jamid
Ya dade sosai wajen khaal suna tattaunawa kafin ya koma gida.
Taheels residents…..
Duk abunda ya faru yau kwata kwata afiya bata sani ba, hasali ma fada suke ita da fadwa don ta daina mata magana, hidaya kuwa haushinta takeji sosai ba kadan ba.
Karfe shida hidaya karaso gida, ba karamin yaqi tayi ba a office donma tana da gagarumar shaida wadda babu wanda ya isa yayi jayyaya da takardar, a take kuwa suka soma ganin asalin rashin mutuncinta don yanxu kamfanin ya dawo hannunta gaba daya, duk wanda tayi niyar kora har cikin shareholders zata iya yi, gaba daya kowa ya shiga taitayinsa.
Lokacin data shigo babu kowa ya kasa, daidai zata wuce sama afiya ta fito daga dining room, wani irin kallo afiya tayi mata mai wuyar fasaara kafin ta doka tsaki, fadwa dake shirin fitowa daga dining room din don dinner sukayi, ganin abunda afiya tayi yasa ta zaro idanu, “ke baki da hankali” fadwa ta fada
“Eh bani dashi” afiya ta amsa ta kai tsaye, “ ni banida munafurci kamar ke,” ta karshe tana mai dauke kallonta ga fadwa ta maida kan hidaya “ukty wallahi i hate you, i hate you so much” kuka ne ya sake kubce mata, “yanxu har kin manta da halin da ummuh ta shiga? Kin manta pain din datayi suffering dashi over the years? Kin manta abunda yayi sanadiyar mutuwarta? Why ukty, why? Maysa bakya kishin ummuh? Tana kabari amma na tabbatar tana allah ya wadai da protecting wanda yayi sanadiyar mutuwarta da kikeyi,”
Idanun hidaya sunyi jaa sosai, fuskanta ma haka ta koma jaa lokaci guda tsabar bacin rai,
Jan afiya fadwa ta soma yi tana kokarin hanata magana ta daka mata tsawa “dallah kyaleni, ni ban iya munafurci ba saina fada mata gaskia, wallahi wallahi wannan hatred din bazai taba barin zuciyata ba”
Kauda kai hidaya tayi kafin ta runtse idanunta ta bude su tarr, hannun afiya ta damko ta soma janta zuwa part dinta, fadwa na biye dasu hankali a tashe, suna shiga hidaya ta saki hannunta ta wanke fuskanta da mari, saida ta mareta wajen sau uku kafin ta kalleta da jajayen idanunta ta nunata da yatsa, “how dare you? How dare you say that eh answer me, ke a tunaninki da wannan karamar kwakwalwar taki ina yin wannan abubuwan ne saboda me? Saboda ina son TAJ? The child that destroyed our family? The child that destroy our happy home with our parents? The child that brings so much sadness to ourselves? Ehhh!! Answer me” ta karashe tana girgizata da hannunta,
“Let me remind you, ranar da taj ya bayyana a gidan nan akwai wanda ya kaini shiga tashin hankali? Daga ke har fadwa bakuda hankali bakusan meke faruwa ba a lokacin, I’m the only person who knows pain din da ummuh ta shiga, baku san komai ba don bakuga komai ba, her lonely nights, her painful days, the pain in her eyes, the screams of her pains zaki iya tunawa? Eh answer me nace zaki iya tunawa?,”
Ta daka mata tsawa mai rikitarwa wanda yasa ta furgita, hawayen fuskanta na kwaranyowa babu qaqaautawa,
“tunawa da wannan kadai yakan sakani samun sleepless night, kina tunanin ina rufe ido ba tare da wannan tsohon baqin cikin daya dade kwance a zuciyata ba? How dare you say that na zabi protecting wanda yayi sanadiyar baqincikin daya kwanta a zuciyarta har yayi sanadiyar mutuwar