Showing 120001 words to 123000 words out of 135321 words

Chapter 41 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

507

so sorry”

Yakai aya yana kashe murya, sai jikinta yayi sanyi, rungumeshi tayi tace “I’m sorry bansan haka abun yake ba, i will never judge you”

Shima rungumeta yayi yana murmushin mugunta, itama murmushin tayi tana mamakin yanda yake kokari with full confidence wajen raina mata hankali, yana rungume da ita ta daga wayarta tayi airdropping video din zuwa wayarta kafin ta fito daga cikinshi ta miqa mashi wayar.

“Kabar komai a wajena, don’t tell anyone about this i will deal with her, zan saka idanu sosai akanta and i will make sure that she pays for coming in between us”

Ba karamin dadi tareeq yaji ba, dazun data kamasu gabanshi ba karamin faduwa yayi ba, allah yaso bata kamashi on action ba da babu yanda zaiyi ya wanke kanshi wannan yasa yayi alkawarin zai fita harkar sabeehar koba komai dai ya barta da fadwar kuma ya tabbatar bazata barta haka ba.

Bangaren sabeeha tana hawa sama ta zauna a parlor tana kukan baqin ciki, tashin hankalinta daya tasan zai mata sharri, kuma zai bayyana wannan video din,haka ta kwana cikin tashin hankali da furgicin abunda zai faru gobe.

Washe gari kuwa tana jiran tsamanj sai taji shuru, a tunaninta ma zataga fadwa ko hidaya sunzo da hukuma don idan suka samu wannan video din sun gama samun abunda zasuyi amfani dashi wajen ganin sun koreta daga gidan, don kamar committing adultery ne.

Tundaga ranar ta samu sauqi wajen tareeq,ko ta kanta bai sake bi ba, haka dai kwanaki suka dunga ja.

 

***

Bude kofar entrance door da akayi yayi daidai da shugowar afiya hannunta rike da luggage dinta, tayi kyau sosai har kiba ta danyi, sanye take da kananun kaya riga da wando masu kyan gaske, ta bazo gashinta kwance a bayanta.

“I’m back!!!!!! “

Juyowa fadwa da hidaya sukayi, Fadwa ce ta fara hangota fuskanta dauke da murmushi ta tako ta rungumeta, hidaya na daga zaune a gefe, fuskanta ba yabo ba fallasa, batasan ma da dawowar afiyar ba sai yanxu, rabonta da ita tun bayan data tafi, ko waya basayi sbaoda tana fushi da ita sosai akan shirmen datayi wanda ya kusa tona aisirinsu badan maid dinnan ta mutu ba adaidai lokacin.

Rungumeta fadwa tayi tsam a jikinta tace “welcome back drama queen”

“Thank you sis” karar takalmi daya biyo baya ne yasa suka dago gaba dayansu, fadwa ce ta fara hangota daga nesa, kyakyawar budurwa ce sanye da kananun kaya itama, masha allah akwai kyau da sura mai kyau, fuskanta tasha makeup ga buli datayi a wajen lebenta da hancinta itama hannunta rike da luggae walking majesticallty ta karaso tabtaaya gabansu tana murmushi, sakin fadwa afiya tayi tana ma budurwar murmushi, fadwa ce tayi saurin cewa “and this is?”

“Sonata!!” Afiya ta amsa ta kai tsaye, daga mata gira fadwa tayi hidaya ma kallonsu takeyi don jin karin bayani, 

“TAJ EX GIRLFRIEND”

Saukowar sabeeha kenan kunenta ya jiyo mata kalamn afiya, daidai nan kuwa taj da barad suka shugo cikin gidan daman suna football ne a compound din gidan, muryarshi yasa suka dubeshi, cikin sauri ya karaso inda suke, baima lura da afiya ba da bakuwar saida yazo daidai inda suke afiya tace “meet sonata!”

Chak ya tsaya bai karasa wajen hidayar ba jin sunan da aka kira, take idanunshi ya sauka cikin na sonata dake tsaye tana mashi murmushi, “sonata!!!”ya kwala mata kira, da mamaki duk suke kallonshi, ya akayi ya ganeta? Ko ya fara samun sauqi ne? Ko memories dinshi sun dawo bama wannan ba how did he remember her name, yanda ya kirata ya tabbatar masu yana da memories dinta kenan bai manta ba ko kuma ya tuna ta lokaci guda yanda ya tuna hidaya lokacin daya daura idanunshi akanta bayan ya farka daga coma.

Cikin sauri ya tunkaro inda take ya rungume ta tsam yana murna sosai, rungumeshi itama tayi sun dade sosai a haka sabeeha datayi suman tsaye ta kasa motsawa haka kawai taji wani abu ya tsaya mata a makogaro ta kasa hadiyewa tunda taji ance tsohuwar budurwar taj dince.

“I missed you Zaddy!!!”

 Sonata ta kira sunansa, “its been long, i cant believe what happened to you zaddy”

Ta karashe tana shafa fuskanshi,

Hidaya ce tayi saurin cewa “ka santa ne? You remember her?”

“Yes first love, she’s… shes my…..” shuru yayi yana nazari koma wacece a rayuwarshi, kamar an rada mashi a kunne yace “my love!”

“Love? hidaya ta nanata abun a ranta, wannan wace irin masifa afiya ta sake jajubo masu da zaisa ya fara recognizing mutane, hankalinta ba karamin tashi yayi ba a daidai wannan lokacin don ta tabbatar da tunawar abu a wajen taj yana nufin Yana recovering kenan, inba haka ba ya za ayi ya iya tuna wadda batama san tayi existing a cikin rayuwarsa ba? How is that possible? Maganar doctor dake kula da progress dinshi ce ta dawo mata inda yake  ce mata da zarar ya fara gane mutane toh that will be the first step of recovery dinshi, don lokaci guda abun zaizo mashi, gashi kuwa akan idanunta taga hakan,  ta kasa cewa komai.

Babu kunya sonata najin abunda ya fada kuma hakan ya tabbatar da ya tunata ta kama fuskanshi ta sumbaceshi a lebenshi, “i can’t believe you remember me zaddy oh my gosh”

wannan abu ya bama su hidaya mamaki sosai, dariya afiya tayi tace “shes an american so its a normal thing to her” ta karashe tana kannema hidaya idanu, sabeeha kuwa wani jiri jiri ta soma ji, tama kasa kallon abunda ke faruwa ta zuwa saman.

Duk akan idanunsu abun ya faru, afiya kuwa me zatayi banda murmushi, fadwa dai girgiza kai kawai tayi.

Taj a akama kiss a bakin kanshi kullewa yayi, hannun sonata na cikin nashi.

“Interesting” fadwa ta fada aranta tana ayyana irin chakwakiyar da za ayi a gidan.

Toh fah!!!! Chakwakiya, ga legal house wife ga masoyiyar taj? Ya abun zai kasance kenan?

Lets dive into the book…. Free page ya kusa karewa, chaper 55 will be the end of book1 by friday insha Allah

❤️❤️

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Last Free page

Update!!!

55 part 1

Fadwa ce kawai tayi welcoming sonata, hidaya kam bata mabi ta kansu ba saima tabe baki datayi, tana tunanin yanda zatayi da afiya.

Anan kasan cikin part din afiya wajen guest room aka shiryama sonata inda zata zauna for the mean time, har cikin daki afiya ta rakata kafin ta fito zuwa nata part din, tana shiga part din ta tadda fadwa a zaune, murmushi kawai afiya tayi sanin fadwa da gulma kuma tasan abunda ya kawota kenan.

“Kinsan kinyi laifi ko?, you have to answer ukty, meysa kika kawo mana stranger cikin gida?”

Karasowa afiya tayi tsakiyan dakin tana mai cire talakmin kafarta dake da igiyoyi, “haaa wayace maki she’s a stranger?well as you can see she’s not”

“Ya akayi kika santa?, nasan ba haaka kawai kika kawota gidan nan ba”

Zama afiya tayi kusa da ita tana mai murmushi tace ‘’a london fa muka hadu, coincidentally naje shopping itama taje muka hadu’’

‘’ni ba wannan nakeso na sani ba, ya akayi kikasan sunyi relationship da taj’’

nunfasawa afiya tayi kafin tace ’hmm dogon labari ne, kai fadwa da gulma, well tunda kin matsu ki sani saiki bude kuunuwanki’’’

da idanu fadwa ta bita don jin abunda zata fada, ‘’hmm ashe yaronnan mugun kudi gareshi?, kinsan how popular he is a london da england annonymously?, last year 2022 shine yaci award din world best young enterpreneurs da mechanical engeneering field,gaba daya ya rufe identity dinshi kaf babu wanda yasan shine T-ford, the face behind Fords motor company gaba daya’’

zaro idanu fadwa tayi jin abunda afiya ta fada, ‘’Ford???? T-…..ford?’’

‘’yes’’ afiya ta amsa ta kai tsaye ganin she is so shocked,  ‘’TAJ FORDS’’

zumbur fadwa ta miqe, ‘’how is that possible? ke ya akayi kika sani? ‘’

dariya afiya tayi ganin yanda ta burkice tace ‘’ni nafiki shiga tashin hankali dana gano shine mastermind behind T-FORD, kindai san t-ford basai na fada maki ba, yana cikin top 10 richest motor company duk duniya’’

‘’afiya kinsan me hakan ke nufi kuwa?,’’ fadwa ta sake jefo mata tambaya, ‘’yes niko na sani,yana nufi duk arzikin da muke dashi we cannot compete with him,’’

‘’but…but ya akayi bamusan da haka ba? ya akayi ukty bata sani ba?waima a ina kika samo wannan zancen?’’ fadwa ta sake tambayarta,

‘’sonata ta fada min,’’ afiya ta bata amsa,

‘’ke kuma kika yarda? haaa it cannot be possible,’’

wani irin kallo afiya tayi mata na kinma rainamin hankali, ‘’shikenan idan bazaki yarda ba,malama kije kawai zan huta nikam’’

futa fadwa tayi daga dakin ta nufi part dinta, maganganun afiya sun tsaya mata arai, ‘’how is that possible? ta yaya?, when and how?, duk wani movement din taj sun sani ita da hidaya, kuma sunsan yanada dan karamin motor factory,’

‘’kai inaa…cannot be possible’’ ta furta ‘’but what if da gaske ne?, that means ya fimu komai kenan?,kuma indai hakan ne maysa bai bari kowa ya sani ba?, no one knows waye T-ford, to kodai da gaske afiya take?’’tunawa da wannan yasa ta dasa ayar tambaya akan abunda afiya ta fada mata, gaba daya saita burkice,’

ay batama tsaya cigaba da tunanin ba ta fuce daga part dinta zuwa study din hidaya ganin batanan yasa ta juya har zata futa taga frame dinnan ya karkace gefe, shuru tayi tana nazari don tasan ba a karkace yakeba, takowa tayi har zuwa wajen ta tsaya gaban frames din, duk a tunaninta ma ko ya kusa fadowa ne don haka ta fara kokarin gyarashi take kuma taga ya koma kamar wata kofa ya bude saiga safe ya bayyana, da mamaki take kallon wajen don safe dinma kamar a bude yake ko an bude ba a rufe ba.

cikin hanzari ta bude safe din taci karo da manya manyan gold cube sunfi ashirin masu shegen girma, ga wasu papers daga gefe ga pounds na kudade, batama bi takan kudaden ba ta dauki papers din ta soma karantawa,saida ta duba gaba daya ta karance tass, wata iriyar zufa ce ke keto mata har jijiyoyin kanta na bayyana ganin irin arxikin da suke dashi wanda ukty bata taba fada masu suna dashi ba, ga document din kamfani gaba daya da sauran kamfanunukan data saya dolce gabana, hermes da sauransu, duk waenda ke partnership da kamfaninsu tana da share a kamfanin, harda abunda bata taba tsammani ba saida ta gani, cikin hanzari ta maida komai ta rufe safe din ta barshi yanda yake ta fito.

tana gab da fita saiga hidaya ta shugo, ganinta kamar burkice yasa hidaya cewa ‘’yadai?’’

saurin daidaita natsuwarta tayi tace ‘’na shiga ban ganki ba shine na fito’’

duban study din hidaya tayi tunawa da tabar safe dinta a bude, tama manta shaff gaba daya saboda message din daya shugo wayarta dole ta fita ta dauko burner phone (wayar da take secret phone calls a ciki).

ganin irin kallon da take mata yasa fadwa saurin cewa ‘’we have a problem’’

‘’what problem?’’

‘’ukty shin kin tabbatar zaman da taj yayi achan london bai samu wani achievement ba apart from dan motor kampanin daya bude?’’

‘’maysa kika tambayeni?’’

‘’yanxu afiya ke fadamin wai shine T-ford’’

wani irin kallo hidaya tayi mata ‘’t-ford?,’’ 

‘’yes ukty, t-ford’’ ta amsa ta

‘wata iriyar dariya hidaya tayi kafin tace ‘’kije kiyi research akan waye t-ford kafin kizo ki fara blabbering nonsense, to kodai kema kin fara zama kamar afiya ne?,’’ hidaya tayi questioning dinta, ‘’but ukty wallahi it makes sense, nima ban yarda ba sai yanxu dana tuna abunda yafi so daya shafi harkar motoci, kuma t-ford annonymous bulder ne, babu wanda yasan dashi kaf duniya,ukty what if da gaske shine?’’

daka mata tsawa hidaya tayi rai a bace ‘’shut up idan bazaki fadi alkahiri ba kiyi shuru, t-ford is an american kuma american company ne, how? kina tunanin zan taba bari ya samu cigaba har ya bude babban kamfani kamar haka? ko kina tunanin zai bude kamfani kamar haka ba tare da sanina ba?’’

shuru fadwa tayi kawai saita juya mata kai tace ‘’shikenan’’

tana kaiwa nan ta fuce daga study din, ita bama tuannin ko wanene taj ba take, abunda ta gani a cikin study din hidaya ne ya bata mamaki, gaba daya abubuwan dake karkashin sunansu ya koma nata ita kadai, daman ukty na boye mata abubuwa ne bata sani ba?, kodai she’s planning for her self ne?, kai bazatayi haka ba cause ay su yan uwanta ne’’ 

haka fadwa ta dunga saka tana warwara aranta game da abunda ta ganema idanunta.

lokacin dinner nayi duk suka sauko kasan, fadwa barad hidaya,harda sonata da suka shugo dining area din tare da afiya, tana sanye da wata jumbsuit mai gajeran hannu, blonde gashinta kwance a kafadarta.

fatar jikinta fara tass kamar abula jini ya futo gata yar figigiya saidai akwai dan shape daga gani bbl ne ma akayi mata.

zama sukayi gaba dayansu, yau mandi akayi da side snacks harda kunafa sweets dessrt, nama kuwa ba a magana zuqa zuqa a cikin shinkafar.

tsakura kowa yayi ya fara ci a natse with class, kallon sonata afiya tayi cikin harshen turanci tace ‘’babes bazaki ci ba?’’

yatsine fuska sonata tayi tare da girgiza mata kai ta bata amsa ‘’i’m on a diet keeping fit for zaddy’’

dagowa duk sukayi suka kalleta ganin yanda take wani kwarkwasa, ‘’i will just have orange juice’’

‘’okay’’ afiya ta fada tana mai bada umarnin a kawo mata, 

dube dube sonata ta soma yi ganin babu taj a wajen tace ‘’ina zaddy na ban ganshi ba’’ ta karashe cikin gwalli tana mai maida gashinta baya,

fadwa ce ta tari nunfashinta ‘’baya cin abunci anan’’

karaf afiya ta charafke, ‘’kije sama mana idan kinason ganinshi, part dinshi shine by the left side’’ ta karashe tana kanne mata idanu, murmushi sukayi a tare kafin ta mike daidai nan maid ta kawo mata juice din ta karba ta fuce daga dining area din ta nufi hanyar stairs.

daidai nan tareeq ya shugo gidan, karaf idanunshi ya sauka akan bayan sonata, saida ya dubeta da kyau don baisan ko wacece ba, kamar ya bita saman haka yaji saidai kuma ya danne don yanzu ya lura kamar fadwa na zarginsa cause a fili take nunawa.

sonata na karasowa saman ta nufi part din da take tunin nan ne part din nashi tana mamaki how rich family dinshi suke,sannan she can’t believe ya manta komai, but ya akayi ya iya tunata?, that means yana sonta kenan har yanxu?, this is the perfect time da zata kamashi a hannunta, cause she can’t afford to loose him, rabuwarsu ba karamin tashin hankali bane a wajenta, tsabar yanda yake sonta he spends so much on her dukda ya boye identity dinshi sai daga baya ta gano ko shi waye, badan ya kamata da ex dinta ba babu yanda za ayi ta bari ya barta, she can recall yanda lokacin ya rikide ya sauya ya fito a salinshi very hard guy cije lebenta tayi ta furta ‘’so sexy’’

  

tunawa da yanda suka hadu yasa ta sauke wani lallausan murmushi, ta wahala sosai kafin ya kalleta sau daya, he’s so tough da kaifi baya barin kowa ya shiga rayuwarshi hakanan, saida tayi mashi naci sosai kafin ya barta ta shigo rayuwarshi, ita zata shaidi irin rayuwar da yayi a london, da yanda yake masifar son first love dinshi wato hidaya.

yanda ya rungumeta daxu yasa taji wani yarr a jikinta, yau taga dariyarsa mai tsada, baya son dariya da wuya kaga yana dariya saidai idan yana maganar first love dinshi nan ne yake yawan murmushi, she can see how excited he was daya ganta daxu, rashin lafiyarsa da afiya ta fada mata bazaisa ta tayi kasa a gwiwa ba, abunda ya kasa bari ta samu a wajenshi yanxu saitasan yanda tayi ta samu a wajenshi no matter what.

kai tsaye ta shiga part din tana tunaninshi feeling so excited zata ganshi, dadinta ma yanxu ya manta duk wasu abubuwa da suka faru acahn baya, yanxu kam she will do what ever it takes donta sameshi, thats the only way zai zauna da ita kuma bazai barta ba.

kallon sitting room din tayi ganin babu kowa yasa ta nufi cikin bedroom kai tsaye, bin dakin ta soma yi da kallo babu kow a cikin sai kamshinsa dake kara rikitata, how can she forget zaddys scent?, 

dariyar data soma ji ne yasa ta nufi hanyar bathroom, kai tsaye ta shiga ciki bayan ta bude kofar, gaba daya juyowa sukayi suna kallonta, yana kwance a kasan bathub jacuzzy kanshi na kan lap din sabeeha tana wanke mashi gashinsa.

wani irin kallon sonata ta bisu dashi, sabeeha ma kallonta tayi ganin yanda ta shugo kamar an wullota, ‘’who d hell are you?’’ ta jefoma sabeeha tambaya, yanda tayi maganar da accent yasa sabeeha kasa gane me take fada, ‘’are you deaf?, i said who the hell are you? ’’

rai a bace sabeeha ta kauda kai ta cigaba da dauraye mashi kanshi  yana dariya, daman da zarar ta sosa mashi kan saiya kyakyace da dariya.

‘’ops maybe she’s his maid’’ sonata ta fada chan kasan makoshi kafin  ta ajiye juice din hannunta gefen marble din waje ta karaso inda suke tace ‘’excuse me i will take it from here okay?’’

tana fadin haka ta miqama taj din hannu, shiko yana ganinta ya kama hannun nata ya miqe, towel ta dauka ta soma goge mashi kan nashi tana mashi murmushi, sabeeha de saqe tayi tana kallon ikon allah, batace komai ba ta fuce daga bathroom din.

tana futa daga bathroom din ta wuce closet ta shirya mashi kayan barci da zaisa ta ajiye mashi anan bedroom din.

tana nan tsaye suka fito daga bathroom din, hannunshi na cikin na sonata, ta bangaren taj kallonta kawai yakeyi, tabbas bakinshi ya iya furta sunanta kuma yasanta saidai gaba daya bashida memories akanta.zaunar dashi sonata tayi bakin gadon shiko ya bita kamar raqumi da akala, ‘’let me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login