Showing 3001 words to 6000 words out of 135321 words

Chapter 2 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

499

dan kiff dan sirara ne basuda girman jiki.

Kwata kwata babu alamun girma na shekaru a tattare dasu saboda arziki ya danne tsufan sai ya zamana kamar yan 20s.

  

Yanda suke saukowa cikin aji kamar bazasu sauko ba, sama sama suke hira suna dariya, Wato gidan ma ya gama gajiya da haduwa, daga waje ma ba komai bane ba don saika shugo daga ciki zaka tabbatar da haka don yasha kayan alatu na zamani, duk inda suka gifta ma’aikata ne suna ta hidima kowannen su sanye da uniform daban daban, gidan dai kamar gidan sarauta don yana da girma sosai ga kofofi da yawa alamun parts parts ne.

Ko’wanne lungu da sako shaqe yake da kayan zamani, ga luxurious interiors ta ko’ina.

Hanyar second sitting dake cikin gidan suka fara wucewa kafin su karasa first sitting room wanda shine face of the house.

 

Da sallama suka shiga parlorn afiya na gaba fadwa na biye da ita abaya saboda tana receiving call din daya shugo mata saida suka zauna tayi sallama da wanda take wayan dashi inda tace ‘’bye qalb’’ kafin ta sauke wayan daga kunnenta.

 

Azaune suka taddashi idanunshi nakan news saidai kwata kwata hankalin shi ba’akan news din yake ba,babu abunda yake mashi yawo akai sai tunanin last zuwanshi da yayi cikin gidan, ba da karamin bacin rai yabar gidan ba saboda y’ay’an dan uwan nashi musamman hidaya, kwata kwata bata ganin girmashi, tafi karfinshi ma, don sai abunda tace za ayi, darajar alqawari da kuma mahaifinsu ne kawai ke sashi zuwa gidan badan haka ba da bazai sake saka kafafunshi cikin gidan ba, bayan wannan akoda yaushe idan ya zauna babu abunda yake dana sani akai sai tilasta dawowar taj da yayi, dukda ya yarda komai muqaddari ne daga allah saidai deep down yana regretting dawowarshi don shine ya tsaya tsayin daka akan dole saiya dawo, sai yake jin kamar ta dalilin nan ne abunda ya faru wata uku da suka wuce ya faru.’……

 

Muryoyin su da ya soma jiyowa ne ya sashi fargawa daga tunanin daya fada, duban tafkeken wall clock din da akayi ado dashi a parlon yayi, karfe 5 da rabi Kenan na yamma,

sallamarsu ya sanya shi dagowa ya kallesu daya bayan daya, zaman half an hour yayi a wajen sai aynxu suke saukowa, shidai yana mamaki hali irin nasu koda yake baa abun mamaki bane don yanxu kam ya saba da halayensu, .

 

kauda kanshi gefe yayi daga garesu ya maida kan tv, kowannen su sanye take da kayan zaman gida gashin nan a bude don ko rufewa basuyi ba,bayan wannan yasan su da practicing rayuwar turawa so su hakan ba komai ne a wajen su ba dukda shi dai hakan a wajenshi ba wayewa bace da girmansu kuma da shekarunsu, shigar fadwa ne ma yafi tsaya mashi arai don ita tana da aure ba kamar afiya ba amma idan ka gansu zaka dauka gaba dayan su basu da auren

.

Karasowa sukayi inda yake zaune dan nesa dashi, kan kujerun single chairs dake facing nashikafin su zauna, fadwa ne tayi saurin cewa ‘’marhaban khaal’’

Ba tare da ya kalleta ba fuskanshi adan hade yace ‘’shukran fadwa,’’

Afiya ce ta dan tabe baki don daman itace tafi rashin kunya kuma yawanci yafi sa ido akan ta musamman rashin auren da bata dashi.

‘’Marhaban khaal’’

‘’shukran’’ ya amsata kai tsaye ba tare da ya sake kallon inda suke ba.

 

Takun sahun kafafun da sukaji ne yasa duk suka dago, wani dan yaro ne ya shugo kyakyawan gaske bul bul dashi, bazai wuce 12years ba, yana sanye da kayan paw patrol sai wata yar cute jaka a bayanshi, hannunshi rike da pack of doritos chips da nintendo switch gaming pad, sai faman cin doritos din yake.

Cikin sitting room din ya karaso aguje yana washe hakora ‘’Jadd’’ (meaning grandpa)

Inda dattijon yake zaune yaron ya nufa cikin farin ciki da jin dadi, farin ciki ya gama lullubeshi,

 

Hannu dattijon ya bude mashi ya taho a guje ya shige jikinsa kafin ya rungumeshi shima dadi duk ya gama lullube shi sosai, ‘’Barad’’

Dattijon ya kira sunan yaron bayan ya fiddoshi daga kirjinshi, murmushi yaron ya soma mashi kafin ya soma gaishesa, kumatun shi dattijon ya kama irin yanda ya saba yi mashi koda yaushe‘’I missed this cute baby face’’

Turo baki yaron yayi kamar zaiyi kuka yace ‘’jadd I’m not a baby anymore, I’m turning 13 next month’’

Shafa kanshi dattijon yayi kafin ya sumbaci kumatunsa yace ‘’kaje school yau?’’

‘’yes jadd’’ yaron ya amsa dattijon.

 

 

Wani irin kamshi ne ya danno cikin parlorn mai tsada don lokaci guda ya bade parlor kamar anyi ruwan turare, takun tafiyar ta ne ya biyo baya ‘’qwas qwas qwas’’wanda yasa duk suka juyo suna kallonta banda dattijon da yayi mata kallo daya ya dauke fuska sai yanayin fuskanshi ya chanza gaba daya kamar bashine ya gama yima yaron nan dariya ba.

 

Nima dai kallota na soma yi, kasa dauke idanuna nayi akanta, wato wata irin classy matace a tsaye, daganin fuskanta kasan ta soma manyanta saidai tsufan ya boye sosai don kwata kwata bazaka iya tantance shekarunta ba dukda tana early 40s, farace tass kamar a bula fatarta jini ya futo,ya allahu, tana da kyau sosai don doguwace, sanye take da wata azababbiyar abaya baqa wadda ta haskata sosai tayi mata kyau don ta haska fuskanta data dan hade girar sama da kasa, gaba daya zubinta irin na matan nan ne da basa daukan nonsense, ga jii da kai da kudi da aji, waya ce kawai a hannunta kirar iphone 15 pro max latest, gefenta kuwa wata maid ce rike da Jakarta da wasu document tana biye da ita a baya don kusan taku uku ne tsakaninsu saboda ita ba a jerawa da ita.

Idanun matar sunsha kohl baki wuluk tayi lining idanun nata sai bakinta dayasha jan matte lips stain.

Kamaninta sun fito sosai da su fadwa saidai kamannin nata yafi zama visible da afiya don tama fi yanayi da afiya akan fadwa dukda kamanninsu ta jini itama ta fito.

 

Saida ta gitto parlorn ta hango dattijon sai kuma maganganunsa da barad data jiyo.

Chak ta tsaya tana kallonshi kafin ta tako cikin kasaita ta karaso parlorn, fadwa ce tayi saurin miqewa tana mata sannu da zuwa kafin ta bata inda ta zauna ta koma gefe.

 

Kamar an mata dole haka ta dago ta kalli maid din kafin ta bata umarnin wucewa da Jakarta zuwa sama, kallon barad tayi kafin ta mashi nuni da hanyar stairs ba tare da tace uppan ba, miqewa yayi yana ma dattijon murmushi kafin ya fuce daga parlor.

 

Gyaran murya tayi kafin tayi relaxing bayanta akan kujerar ta daura kafa daya kan daya duk akan idanun dattijon yana kallon ikon allah, saida ta dan dauka yan few seconds kafin ta soma Magana anatse with class

‘’marhaban khaal’’

‘’shukran Hidaya fatan na sameku lafiya’’

A gatsale ta yatsine fuska tace ‘’alhamdulillah’’

Shuru ne ya biyo baya, su fadwa dai kallonsu suke daga shi har ita, yanda kasan maqiya sun hadu.

A duniyar nan hidaya bata kaunar ganin mutumin nan agidannan,a yanu tana mashi kallon kamar maqiyinta dukda yana matsayin qanin mahaifinta marigayi Taheel, duk yanda taso akan ganin ya raba hanya da gidan abun yaci tura don ita gani take yana son ya shiga tsakaninta da big baby dinta ne to wama ya isa? Babu shi a doran kasa.

Bata qaunar kowa ya rabe shi kwata kwata,wannan yasa duk yanda zatayi saitayi don ganin tayi pushing uncle away.

 

Ganin shurun yayi yawa ne yasa hidaya cewa ‘’ko zan iya sanin dame kake tafe?’’

Mamakin jin tambayarta yayi da yanda tayi mashi tambayar saidai saninta da halinta yasashi dannewa kawai ya gyara zama don idan har zai bi abunda zuciyarshi ke raya mashi akan yayan dan uwan nashi marigayi Taheel to fah bazai kara waiwayar su ba, gyara zama kawai yayi ya danyi relaxing bayanshi kafin ya soma magana.

 

‘’ba komai ne ke tafe dani ba sai maganar Tajudeen,’’

Saurin rintse idanu tayi kafin ta budesu ta sauke akanshi,

Ganin haka yasa shi cigaba da cewa ‘’yanxu wata uku Kenan babu wani progress akan condition dinshi, shine nace ko zamuyi trying wasu expert health

organization da suka kware sosai ta wannan fannin na wasu kasashen daban ko za a samu dacewa’’

  Tsagaitawa yayi kafin ya nunfasa ya cigaba da Magana cikin kamala ‘’ ni ina ganin idan muka dage sosai akanshi za a samu cigaba akan matsalar tashi’’

 

Wani irin kallo take mashi mai wuyar fassara wanda yana hango tsantsar bacin rai a cikin idanunta saidai fuskanta bai nuna hakan ba shima hakan bai sashi ya tsagaita ba don hakan bazaisa yayi shuru ba.

 

Cikin muryarta mai tafe da wani irin salo mai jan hankali ta soma Magana ‘’so yanxu kana ganin babu abunda nakeyi akai ne?well likitocin nan kasar ma top notch doctors ne kuma there are one of the best in the whole world and I trust them, khaal I know what is best for him, babu wanda zai nunamin damuwa akan matsalar big baby, so please idan kazoo ne akan wannan maganar ka ajiyeta don I know what is best for him baka fini sanin abunda zai taimakeshi ba don nice komai nashi, so please..’’ta karashe tana mai kallon cikin idanunshi babu ta kunya balle ganin girmansa

 

Fadin irin bacin ran da dattijon da suke kira da khal yake ciki ma bata lokaci ne, yau yaga karshe rashin mutunci wajen yar dan uwansa, yarda aka haifa a gaban idanunsa.

 

Wani irin heavy abu yaji a kirjinsa kamar an buga mashi dutse, haka yayi saurin runtse idanu yana danne abunda yake ji.

 

Mikewa yayi tsaye ba tareda ya kalleta ba yace ‘’shikenan na barku kuyi abunda kuka ga yayi dace, saidai ina tunasar dake, ba’a wasa da amana duk qanqantarta zan samu ganinshi yanxu?’’

Cikin sauri ta dago ta maida dubanta gareshi da jajayen idanunta kafin ta maida dubanta ga agogon rolex dake maqale a hannunta ‘’I’m sure he’s asleep by now, don…’’

Kasa daukan wulaqancin yayi don haka yayi saurin katseta ta hanyar cewa

‘’ ba damuwa na barku lafiya’’

 

Yana kaiwa nan ya masu sallama ya nufi hanyar futa, harya fuce hidaya bata bar kallon hanyar dayabi ya fuce ba, tafarfasar da zuciyarta keyi kamar an zuba tafashen ruwan zafi, su fadwa kuwa kasa cewa uppan sukayi sai zuba mata idanu da sukayi suna kokarin karantar reaction dinta,

‘’tirkashi ana wata ga wata,interesting’’ fadwa ta fada a zuciyarta tana mai tunanin wani abu.

Ganin ta mike tsaye yasa suka bita da idanu harta wuce hanyar stairs anatse kamar wata dawisu.

 

Kallon juna sukayi atare kowannen su da irin tunanin dake yawo a zuciyarshi…

MATAR TAJ(Destined with you

🩵🤍



❤️



🔥

Romantic love story

❤️



🔥

     Written by QueenMarh  

Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai…

 Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. 

I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.

The suspense and the plot twist is a top notch

🙃🙃

Enjoy!!!!!

 

 

Free page

Chapter 2-3

*

Saman hidaya ta wuce anatse, tsayawa tayi tana kallon parts din dake saman, duk girman gidan nan part biyun nan yafi haduwa, daya na gefen hannun dama dayan kuma na hagu, saidai kofar part din daman yafi kyau sosai don wata iriyar koface mai shegen girma da kyau security door, handle din kofar ma automatic digital biometric lock ne irin na zamani wanda ba kowa ne ke shigan wajen ba.

 

Ta dauka yan mintuna qalilan kafin ta kauda idanunta daga wajen ta nufi hanyar dayan part din dake hannun hagu .

Chak ta tsaya ba tare da ta sake daga kafarta ba da niyar tafiya Jin karar bude kofar dayan part din, da mamaki take kallon kofar don ganin wani gwanin ne zai fito daga part din a wannan lokaciin don shige da ficen part din saida izinin ta, don ta gindaya sharudan shiga part din.

 

Da mamaki take kallon maid din data futo, ga hawaye akan fuskanta, gaba daya kana ganinta kasan she’s stressed daga yanayin yanda take tafiya, tana sanye cikin uniform dinsu na aiki, hannunta rike da tray mai kyau, asaman tray din an daura wani bowl na corn beef porridge sai glass din ruwa’.

 

Maid din na ganin madam gaban ta ya fadi, shikenan tata ta qare, daman tsoron data dunga ji Kenan na qin futowa don idon ta futo da abuncin ma matsala ne don job dinta ne ta tabbatar anci abuncin sannan kuma akwai time schedule da aka bata na musamman na yanda zata kula da abunda ya shafi part din bayan wannan ma akwai kashaidin da aka bata akan duk sanda ta tsallake rules din to fa sallamarta za ayi.

Duk inda karfe hudu tayi babu maid din dake zuwa part din kwata kwata hatta saman ma basa haurowa gaba dayan su.

A cikin gidan akwai over 10 maids daban daban banda waenda ke kula da alamuran daya shafi premises din gidan.

 

Dauke ganin ga daga kan maid din tayi ba tare da ta ce mata qala ba ta nufi hanyar dayan part din, maid din na ganin haka kawai ta sauka kasa don tasan an sallameta Kenan, ita a dadinta ma don har wani sign of relief ta sauke.

 

Hanyar walkway din dazai sadata da living room tabi, babu sautin dake tashi sai karar hills din dake kafarta na saint Laurent red color wanda ya fidda clean kyawawan yatsunta.

 

Kamshin bakhoor ne kawai ke tashi a parlorn sai sanyin ac daya bade ko’ina, tana karasawa tsakiyan parlorn ta tsaya tabi ko’ina da kallo, babu datti ko digo, har sparkling wajen keyi, parlor yayi mugun haduwa komai na parlorn black and gold ne.

 

Motsin dataji ne yasa ta maida dubanta ga hanyar kitchen din part din nata, wata budurwa ce ta fito sanye da uniform riga da wando irin na dayar maid din saidai color ya banbanta don ita wannan blue ne hannunta rike da electric cleaner da alamu gyara ta gama yi, tana ganin madam din ta tayi saurin rissinawa kanta a kasa.

 

‘’wani time ne ya kamata a gama aikin yamma?’’

Hidaya ta tambayi maid din tana mai kallonta irin kallonda zan fassarashi da kaskanci.

 

Jikin yarinyar ne ya soma kyarma kanta a kasa ta soma rarraba idanu

‘’4pm madam’’

Yarinyar ta bata amsa da harshen larabci wanda baya futa sosai saboda ba yar kasar bace yar Senegalese ce.

‘’shekaranki nawa kina aiki anan? Wani agency ne suka kawo ki nan? Bakisan rules dina bane? Duk inda 4 ta wuce bana son ganin kowa a part dina?’’

 

Yarinyar harta soma kuka don tsoron abunda zai biyo baya cikin shesheka ta soma Magana ‘’jiya aka kawo ni ma’am, ina cikin waenda akayi recruiting sabbin workers this month madam, I’m sorry madam ban sani bane’’

 

‘’you must be very stupid,you’re fired’’

A kidime yarinyar ta dago jin abunda madam din tace, sanin cewa ayanda ma’aikatan data tarar a gidan ke yawan fada bata son hayaniya yasa ta hadiye kukanta daya ciyota, don ba’a musayar yawu da ita, har a lokacin tana nan tsugunne bata motsa ba.

 

Ba tareda ta kalleta ba ta wuce hanyar bedroom dinta idanunta har lokacin sunyi jaa sosai,tana shiga dakin ta banko kofar,yarinyar kuwa haka ta mike ta fuce inda wata yar aikin daban ta fito daga cikin kitchen din part din hannunta rike da tray an daura glass jug mai shegen kyau sai glass cup da wasu vitamins a gefe, kana ganin yarinyar kaga yar india itakuma.

 

Hanyar bedroom din madam tabi tare da shiga cikin bedroom din,don aikinta Kenan itakuma duk abunda ya shafi harkar personal buqatun madam din, tana shiga cikin mintuna qalilan na soma jin karar fashe fashen abubuwa daga cikin dakin, kafin daga baya kuma aka bude kofa, yarinyar data shiga ce ta fito a rikice ta rufo kofar kafin ta sauka kasa itama.

 

Mamaki bai hana ni shiga don ganin me ke faruwa cikin bedroom dinba, a tsaye take hannunta rike da wani document data taho dashi daga office, sai kuma wayarta dake yashe a kasa don wani muhimmin call ta dunga expecting tunda safe sai yanxu akayi responding dinta sai gashi kuma abunda take buqata din bai samu ba saima wasu dogayen dokoki da aka fado mata wanda dole sai an bi dokokin ne zata samu abunda take so,Rayuwar ta yanxu gaba da baya aiki ne kawai tasa a gaba.

Babu abunda take sai zagayen dakin from one end to the another, tama rasa tunanin da zatayi, ‘’I have to do something cikin gagagwa, wannan ne kawai last chance da nake dashi to make it mine, wallahi wallahi bazan yi kaffara ba, bazan taba bari taheel groups ya kubuce daga hannu na ba, no never not now and not ever.’’

 

Hannunta ta sanya a daidai tsakiyar goshita tana wani nazari kafin ta dafe kanta ‘’dole ne nayi shiri I need to plan accordingling, bazan taba bari legacy din famyln nan da sacrifice din da Abii yayi ba to go to waste I can’t let them have it all inaa’’,

 

Haka ta dunga safa da marya tsakanin dakin abubuwa da dama sun tsaya mata arai, ga wannan matsalar data kunno mata da taso ta kasheta cikin sanyi ba tare da sanin kowa ba sai gashi plans dinta suna neman rugujewa, na biyu kuma ga maganar khaal data tsaya mata arai.

 

Gaba daya dakin ma ta haukata shi saboda bacin ran da take ciki, daman ta haka take sauke takaici akan duk abunda ta samu na anfani, nan take zata tarwatsa shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login