Showing 15001 words to 18000 words out of 135321 words

Chapter 6 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

506

tsaya mata arai sosai, ayau da ace iskanci take to fa babu wanda zai fara sani sai mamanta saboda ta santa ciki dabai, don ko kalar nunfashin da take futarwa mamanta ta sani ballatana kuma motsinta.

Ko tsoronta dake kunshe a cikin ranta bazaisa tayi iskancin bama, don a duk duniyan nan babu wadda ta zagaye rayuwarta kamar mahaifiyarta, duk wani motsinta akan mahaifiyarta, shiyasa tun bayan dawowar su Nigeria bata kara futa ba da sunan zuwa makaranta ba, gashi ta haneta mu’amala da kowa don ko qawa bata dashi, bata ma san menene qawance ba saboda she has a very dark experience lokacin tasowarta saboda halittarta, kowa is just a stranger to her hatta maqotansu da suke zaune gida daya mamanta bata yarda tayi mu’amala dasu ba kwata kwata, daga inna sai mamanta sai kawu wato qanin mamanta Kenan, shiyasa take nan kamar mai rayuwar qunci mara freedom.

Tun tasowarta da girmanta bata taba barinta ta zama socialize ba, bata taba barinta ta shiga cikin mutane ba, she hid her to the world gaba daya, tun bayan da ta fara zama budurwa, bata taba koda taka kofar gidan suba lokacin suna tsohon gidan su kafin yanayin yau da kullum yasa zaman nasu ya gagara a cikin gidan …..

 

A lokacin da suka koma gidan haya ko tsakar gidansu bata futa kwata kwata, bata isa tayi koda dogon nunfashi ba saboda how highly strict with movement dinta da maman ta take,duk wani motsinta saida izinin mahaifiyarta abun yakai hatta kalar nunfashin da zata futar da duk motsin da zatayi saida izinin mahaifiyartaa, shin wannan so ne ko kuwa wani abun ne daban? Haka take yawan tambayar kanta koda yaushe.

Free page

7-8

MATAR TAJ(Destined with you

🩵🤍



❤️



🔥

Romantic love story

❤️



🔥

     Written by QueenMarh  

Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai…

 Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. 

I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.

The suspense and the plot twist is a top notch

🙃🙃

Enjoy!!!!!

 

 

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

Free page

Chapter 7-8

Washe gari da asuba ta tashi as’usual kamar kullum, a parlor ta kwana saboda kawu bai kwana a gidan ba, daman yawan ci asabar da lahadi ne kawai yake kwana a gidan, sauran kwanakin kuma achan tasha yake yi saboda sana’arshi ta tukin motar haya, kano to Abuja line.

Saida ta fara yin sallar asuba kafin ta fara gyaran parlorn nasu inda ta tattara katifar, da dan qyallen zanin da take shimfidawa a kan katifar don katifar soso ne kawai ba bu komai a jikin katifar,sai kuma hijab din da take luluba dashi dayan kuma dashi take sallah.

Ragowar kayan wanke wanken da sukaci abunci dashi ta kwashe ta fita dasu don wankewa.

Gaba daya gidan basu tashi ba sai mazajensu dake futa aiki,wannan yasa take futowa tayi duk wasu ayyukanta da wurwuri kafin sauran matan gidan su fito, don ko dibar ruwan rijiyar gidan ma layi sukeyi.

 

Zama tayi ta soma yin wanke wanke cikin natsuwa ga sanyi asuba dake busawa, sanye take da hijab din datayi sallah dashi, hijab dai koda yaushe bata rabo dashi, kuma yana nan yanda take sakawa ta rufe bakinta dashi.

Saida ta gama wanke wanken tass ragowar omon kuma ta wanke dayan hijab dinta dashi don gaba daya guda biyun nan ne kawai take dashi kuma shi take sawa koda yaushe shiya duk suka kode saboda wanki dukda wanki ma wani san’in babu omo take yi saidai ta tsalma cikin ruwa ta dauraye shi.

 

Tana gamawa ta shanya kan qauren langa langan da take shanya  wajen, lokacin har matan sun soma futowa.

Wanke toilet din ta fara yi kafin ta koma dakin nasu, da sallama ta shiga, inna nata sharbar barcinta, mama kuma na gefenta a zaune, da alamu bata dadw da tashi ba, zaman jirata daman takeyi don bata shiga toilet din saita wanke kafin tayi amfani dashi.

 

Cikin ladabi da biyayya ta tsugunna, har kasa ta soma gaisheta ‘’ina kwana mama, an wanke bandaki’’

 

Kamar koda yaushe bata fiya amsa ta ba, saidai kawai tayi gyaran murya, yau dinma ko gyaran muryar batayi mata, ganin haka yasa ta sake maimaita abunda tace, sai a lokacin maman ta dago ta kalleta kafin tace ‘’naji’’ jikinta ne yayi sanyi don duk a tunaninta har yanxu fushi take da ita, fushinta kuwa ba karamin tashin hankali bane a wajenta.

 

Sum sum ta fuce daga dakin don daura abunda zasu karya dashi, tuwon jiya ta dumama ta juye a kular, lokacin mama harta futo tay wanka ta koma ciki.

Daga baya ma saiga inna ta futo itama,dakyar take tafiya saboda qibar da take dashi sosai, wani sa’in ma saboda qibarta cikin dare bata iya futa yin futsari saidai tayi a poo saboda tana da saurin sakin mara saboda ciwon sugar da take dashi.

 

Dakin ta sake komawa da kulolin tuwon data dumama,tana shiga ta ajiye bayan sun gaisa da inna, kafin ta wuce parlor ta zauna taci nata wanda ta zuba ma kanta.

 

Bayan yan mintuna qalilan ta koma daki ta kwashe kwanukan da suka gama ci kafin ta fuce dasu.

 

 

Kallon inna hadiza tayi kafin ta danyi gyaran murya, ‘’inna daga yau sabeeha bzata kara futa tallan nan ba’’

 

Wani irin kallo inna tayi mata tana kokarin yin sakacen hakori kafin tace ‘’saboda me Kenan?’’

‘’inna ni na haifi yarinyar nan kuma nike da iko da ita, bana son tallan nan saboda haka bazata kara futa yin wani tallah ba ko aike ma karki sake barin ta taje, nitun usuli na nuna maki bana so bansan meysa ki….’’

Saurin katseta inna tayi

 

‘’iko sai allah, yau ni hadiza kike cewa ke kika haifi yarki?shin idan taje tallan nan ba rufin asirin mu bane?, kuma idan taje tayo tallan nan ay duk rufin asirin mu ne tunda koba komai dai zamu samu nacin yau harda dumame, ke wai hadiza na kasa gane maki, wannan tsawalawan da kike yi akan yarinyar nan na menene ke a ganin ki wannan tarbiyya ce kike mata?’’

 

‘’ni ba wannan maganar nake maki ba inna, inma don ribar da kike samu ne zan dunga baki dubu duk sati’’

Shuru kawai inna tayi bata sake ce mata komai ba, don talla kam saifa ta tura ta.

 

Haka ta karashe shirinta ta fuce daga gidan zuwa gidan matar da take ma aikin abunci, matar babbar event planner ce a cikin garin abuja, sannan tana harkar abincin gidan buki da duk wasu events, da kyar hadiza ta samu matar ta dauketa aiki, inda take bata dubu talatin duk wata.

Yau Friday, yawanci ayuukan ranar sunfi yawa saboda akwai orders din abunci da yawa.

 

 

Karfe sha daya daidai kuwa inna ta sata dora dahuwar kwai, tana gamawa ta zuba a roba, saida inna ta kora mata kashedin dawowa karfe daya daya daidai kafin ta fuce, tunda ta fita gabanta ke faduwa babu dalili.

 

Bata kai karfe dayan bama ta sayar da duka kwan kafin ta dawo gida,

ba karamin dadi inna taji ba kuwa don haka ta daura damara don bata ga dalilin da zaisa ace wai baza a tura ta tallan ba yanda suke fama da talaucin nan, ita dai ba yar gwal bace da za ace ta futa nema ba.

Saida yanma tayi likis hadiza ta dawo a gajiye, gajiyar data kwaso ma baisata ta tambayi inna ko ta bar sabeeha ta futa yau ba don tasan inna akwai taurin kai.

 

Haka suka shafe sati guda, inda hadiza na futa inna zata daurama sabeeha kwan nan, kafin ta dawo, akwai ranar da sabeeha ta futa da kwan bakin titi kamar kullum, da mamaki Jamila wadda ke shirin tafiya wajen aikinta ta ganta, koda ta ganta ita sabeehan bata ganta ba.

Jamila tayi mamakin ganinta sosai, don batayi tunanin hadiza zata barta ta sake futa ba.

Saida ta dawo daga aiki ta wuce gidan hadizan ko uniform din jikinta bata tube ba,tana zuwa gidan ta samu hadiza a uwar daki, inna kuma tana tsakar gida tana hira da maman chidi, sabeeha kuwa tana bakin murhu ta daura sanwar dare.

 

Da sallama Jamila ta shiga dakin, a zaune ta tadda hadiza, ganin ta tsaya a bakin kofa yasa hadiza cewa ‘’karaso mana jamila’’

Zama Jamila tayi tana fuskantar kafin ta soma Magana ‘’wai ni hadiza maisa yanxu kikayi sanyi ne sosai?’’

 

‘’me kika gani yasa kikace haka?’’

Hadizar ta tambayeta tana kallonta da mamaki.

‘’hmm babu komai daxu sai naga sabeeha a bakin titi gaban wata katuwar mota ashe baki hana ta tallan ba allah dai ya kauda bacin rana’’

 

A razane hadiza ta kalleta, ‘’ban gane ba, wace sabeehar ba’’

Wani irin kallo Jamila ta mata irin kinma raina ma kanki hankali.

‘’akwai wata sabeehan ne bayan wadda kika san nake magana a kanta,’’

 

‘’innalillahi, wallahi Jamila saida na fada ma inna karta kara bata tallan kwan nan’’

Miqewa Jamila tayi tare da saba Jakarta a hannu ‘’shikenan ay, idan kare na yawo zabo ma na yawo wata rana sai sun hadu, yanxu ya kamata tun wuri kisan abunyi, shawara dai dayace na baki, akaro na biyu ni kinga tafiya ta’’,

Tana kaiwa nan tayi fucewarta, tun bayan tafiyar Jamila kasa sukuni hadiza tayi, yanda kasan Jamila rura mata wutar tashin hankali tayi, haka kawai ta kasa nutsuwa, washe gari haka sukayi kacha kacha da inna kamar ba mahaifiyarta, itama sabeehar bata barta ba don saida ta daketa sosai kamar zatayi mata illa, duk dan bata fada mata kan cewa inna ta cigaba da daura mata talla ba, ita kuwa baiwar allah bata ma san ta hana inna daura mata tallan ba.

Ranar dai sabeeha taga sauyi sosai tattare da uwar tata, sauyin da tun bayan dawowar su rabon data ganshi, nan take tsoronta ya sake ninkuwa akan na da, abubuwan da suka gabata shekarun baya suka soma dawo mata, don a lokacin ne hadiza ke displine dinta acewarta don wahala dai tasha wahala both emotionally and physically wajen mahaifiyar tata tun kafin ta mallaki hankalinta, sai ayanxu asalin maman nata ya dawo, wato hadiza nada zafi sosai, bata da sauqi, she’s not soft at all, wata iriyar zuciya ce da ita, ta raini zuciyar ta tsahon shekaru da dama da hatred. 

 

 

Satin sabeeha daya a gida ba tare da taje tallan ba, inna ma dai bata sake bata tallan kwan ba saboda yanda hadizar ta dauko da zafi zafi sosai, bayan wannan ma yanxu innar tayi laushi sosai saboda yanayin rashin lafiyarta dake neman dawo wa.

 

Akwai ranar da inna ta tashi da tsananin rashin lafiya, gaba daya jikinta ya sage, ranar daga sabeeha sai inna agidan, lokacin da abun ya tsananta sabeeha na tsakar gida tana wankin kayan maman nata, saida ta gama kafin ta daura musu abunci.

Duk wannan hidimar data dunga yi bata shiga daki ba, saboda ayyuka da suka sha mata kai.

Hadiza kuwa ranar taje aiki,don ranar juma’a ce kuma akwai ayyuka da yawa da zasuyi saboda abuncin sadaka da sukeyi duk sati da ake biyansu sunayi.

Tunda suka fara aikin nan basu suka zauna ba sai wajen karfe uku na rana, dama a daidai wannan lokacin ake zuwa daukan abuncin sadakar….

 

Karfe hudu daidai ta dawo gidan gaba dayanta kana ganin ta kamar susutacciya, direct dakinsu ta nufa hankali atashe, a kwance ta tadda inna, bata ma bi takan innar ba don duk a tunaninta barci take,cikin sip dinsu ta bude tare da dage kayayyakinta da suke a ninke, chan kasa ta zura hannunta ta zaro wani tsohon hoto, yan mata ne guda uku cikin hoto daga gefe kuma sai wani sauri, ta dan dade sosai tana kallon hoton kafin ta maida hoton cikin drawer, ko tsayawa rufe drawer ma batayi ba ta futa daga dakin.

 

Bata wani dade ba sai gata ta dawo kuma, this time around tadan samu natsuwa saboda maganganun da sukayi da Jamila.

Ko takan sabeeha batabi ba da ke gaisheta ta wuce daki, sai alokacin ta maida dubanta ga inna dake kwance yashar kamar gawa ga wani kumfa kumfa dake futowa daga bakinta har ya soma bushe, hankali atashe hadiza ta karaso gaban

gado kafin ta soma cewa ‘’inna, inna, wannan kumfar fa innalillahi wa inna ialihi rajiun’’

Idanun innar a bude ga hawayen dake saukowa bakinta kuma ya soma karkarcewa gaba daya ta qame gatanan dai tana jin abunda hadizar ke fada saidai ta kasa yin komai, takasa motsawa komai na jikinta ya sandare.

 

‘’inna!!! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku ni hadiza’’ hadiza ta doka ihu hankali atashe, sabeeha data shugo da kwanan abuncin su tana jiyo ihun maman nata yasa ta ajiye abuncin anan dakin ta wuce cikin uwar daki, itama gaba daya hankalinta ya gama tashi sosai tana tsaye baki kofar shugowa dakin, juyowa hadiza tayi ta kalleta hankali a tashe ta soma Magana .

‘’ke tafi gidan Jamila ki kirawota’’

Cikin saurin sabeeha ta futa daman da hijab dinta a jikinta, gidan Jamila ta wuce direct dukda batasan gidan ba saida tayi tambaya don bata taba zuwa gidan ba, ana nuna mata gidan kuwa ta shiga da sallama, duk ta burkice, Jamila na ganin shugowarta ta saki baki don mamaki, ‘’ina wuni’’ sabeeha ta gaisheta,

‘’lafiya dai?’’

‘’mama ce tace nazo na kiraki, in…inna ce’’

Jamila najin haka ta zari hijab dinta dake baki kauren kofa kafin ta fuce sabeeha na biye da ita a baya.

Gidan suka shiga a tare, matan gidan har sun fifito saboda ihun hadiza da suka dunga ji tana faman kiran ‘’inna ki tashi karki mutu, ki rufan asiri’’

 

Dakin Jamila ta shiga, inda ta tarar da hadiza na faman jijiga inna, har lokacin idanunta a bude suke tarr, karasowa Jamila tayi don dubata, tabbas abinda tayi hasashe ne ya tabbata, ita ma gaba daya lokaci guda hankalinta ya tashi

‘’hadiza mu kaita asibiti yanxu kafin abun ya tsananta’’

Tana kaiwa nan suka fara kokarin daukan inna, kasa daukanta sukayi saida Jamila ta fita, allah yao baban chidi na nan, shine ya shugo ya goyo innar, hadiza dai babu abunda take sai kuka, haka suka fito gaba dayansu har waje, ga anguwar a chunkushe take babu motoci, haka suka fito bakin titi hankali a tashe.

Daidai nan motar taxi din kawu ta shawo kwana,daman ya dawo ne yaci abunci ya koma kan aiki, hadiza na ganinshi ta tsaidashi, bata ma tsaya yi mashi bayani ba suka shiga gaba daya cikin taxi din yaja suka wuce wani asibiti dake nan duten habujan.

 

Asibitin government ne saidai kuma yaji jiki sosai, don kwata kwata babu kayan aiki, haka suka dunguma da inna cikin asibitin.

Da kyar aka samu likita guda daya ya fara dubata, tashin farko yace masu wannan matsalarta tafi karfin asibitin da basu da ayyukan da zasuyi mata taimakon gaggawa, don kamar ta samu paralyze,jin wannan kalma ta daga ma hadiza hankali sosai, haka suka sake dungumar ta suka wuce cikin garin Abuja.

 

Daidai federal hospital suka tsaya, Jamila ce tayi masu jagora inda kawu ya goyo inna dake nan jikinta babu progress ko kadan saima idanunta daya soma rufewa alamun shima yana gab da qafewa.

 

Taimakon gaggawa aka fara yi ma inna inda manyan likitoci suka shiga da ita wani daki emergency, sun dauka kusan awa guda suna kokarin gano daga inda matsalar ta fara, saida sukayi mata wata allura wadda zatayi stabilizing system dinta kafin su fara yi mata test.

 

Bayan awa gudan nan saiga likita ya futo, nan ya soma masu bayani, inna na dauke da liver cancer wanda taci taci ta sosai, wanda dole sai an cire mata wannan hantar don ta lalace, na biyu kuma tana dauke da diabetes wanda shima yayi mata tsanani.

Cikin kidima hadiza ta soma kuka, saida Jamila ta bata baki kafin tayi shuru, nan doctor ya cigaba da yi masu bayani.

‘’kamar yanda nace, dole sai an cire mata wannan hantar zata rayu inba haka ba zata iya mutuwa Indai ta kara kwanaki talatin ba tare da an cire ba, don cancer ce kuma spreading takeyi.’’

 

‘’likita nawa ne kudin aikin?’’ jamila tayi saurin tambayarsa

‘’dubu dari takwas ne’’

Dafe kirji hadiza tayi tsabar kidima, ina zata samu dubu dari takwas yanxu, matarda ko dubu dari da zata ce nata ne na kanta bata dashi.

 

Tsabar tashin hankali zaman dirshen tayi a wajen sai Jamila c eke bata baki.

Ranar dai sun kwana cikin tashin hankali, ga kudin asibiti da kudin gado da aka kira masu kusan dubu talatin, a rana guda Kenan fah.

 

Kwanan inna uku ta farfado,gaba daya jikinta yanda suka kawo haka yake, abunci ma saita roba ake dura mata,ga chachar kudin asibiti, don tsakanin kwana ukun nan sun kashe wajen dubu tamanin.

Maganar kudin aiki kuwa babu inda zasuje su samu wannan kudin, tashin hankalin hadiza Kenan, ranar da kawu ya zauna da innar hadiza ta samu ta koma gida don ta dan huta don ita ke zama da ita tsawon kwanakin.

Sabeeha dai kullum tana zaune a gida tana jimamin rashin lafiyar inna don kwata kwata mamanta bata bata fuskar zuwa asibitin bama.

 

*

 

 

Da sallama hadiza ta shugo gidan Jamila, tana zaune a parlor tana cin taliya, ganin yanayin hadiza yasa ta ajiye taliyar gefe, ta miqe ta wank hannunta kafin ta dawo parlor.

 

‘’duk kin rame wallah, ki dai na sama kanki damuwa, insha allah zamu samu mafita.

‘’jamila wace mafitar Kenan? Wata guda fa akace? Ina zan samu wannan uban kudaden?

Nunfasawa Jamila tayi kafin ta soma Magana cikin hikima ‘’inada mafita guda daya, koba komai zatayi maki maganin matsalolinki guda biyu a duniyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login