Showing 63001 words to 66000 words out of 135321 words
ta? How dare you”
Kallonta suka somayi gaba dayansu kuka ya gama wanke masu fuska, hidaya dai idanu sunyi jaa, babu hawayen ko kadan,
“I’m sorry ukty I’m sorry wallahi na dauka….”
“Shii, shut up, ay ban gama ba” ta karashe tana kallon cikin idnaun afiya da jikinta ke kyarma.
“Kina tunanin daukanshi da nayi na reneshi? Na rufe kaff rayuwarshi daga ni sai ni gaba da baya, Na hanashi kusantar kowa, na bashi soyayyar da babu uwar datayi ma danta irinshi don ko barad dana haifa banyi mashi irin soyayyar nan ba, sannan na tura shi karatu wata kasa chan sannan nayi pampering dinshi na bashi duk abunda yake so anan duniya duk kina tunanin nayi hakan ne saboda ina sonshi? No!!!!!!!!!!!!! I only did that don na juyashi son raina, to have him on my palm,”
Nunfasa tayi kafin ta cigaba, har hannunta na karkarwa “na nuna mashi so ne fiye daku da kuke jini na saboda ta wannan hanyar ne kawai zanyi yanda nake so dashi and thats the only way i can make him miserable, inajin takaici sa baqin ciki idan na tuna wani part na jini na na running a jikinshi,”
“And lastly ina son ku sani gaba dayanku, a duk duniyar nan babu wadda naso kamar ummuh, ko abuh banyi mashi irin son danayi mata ba,
Wanda yayi sanadiyar mutuwar ta shine babban maqiyi na, kuma bazan taba bari yayi enjoying wannan rayuwar ba yanda ummuh tayi suffering over that year, i will make him miserable thousand times over and over, ko ganin sa bana sonyi, kuma na tabbatar wannan hatred din saidai idan mutuwa nayi, so you better open your eyes clearly kisan yanda akw tafiyar da rayuwa yanxu keep that in mind”
Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin rai a bace, gaba daya memories din komai ya dawo mata, all the painful moments da hatred.
Jama’a Allah ya kaimu monday zamu shiga cikin labari, by next week free page zai kare
💃🏻😭
Yanxu ainahin farkon shirin zai fara
😆💔
Sabeeha dai ta zama matar taj, hidaya ta samu abunda take so, company ya dawo hannunta gaba daya….
Shin me zai faru nan gaba? Hidaya ta daura damarar shiryama TAJ miserable life, wato a yanxu ma somun tabi ne kenan?…
Ku biyo ni don sanin abunda zai faru a cikin labarin Matar TAJ….
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 31-32
Farkon labari.
Asalin ahalin Taheel Abdullah Tajudeen.
Taheel Tajudeen babban dan kasuwa ne, business tycoon wanda ya sha’hara kuma ya zama jajirtattce a cikin fashion business industry, yayi fuce sosai a kasar saudi inda duk duniya babu wanda bai shaida nasarorin daya samu ba, yana da yaya uku tal a duniya wanda allah ya mallaka mashi, danshi na farko shine Taheel Abdullah tajudeen wanda ya gaji sunan mahaifinshi da sunan kakan sa sai mabiyinshi Abdul gaffar Tajudeen (khaal) sai Halima tajudeen.
Wannan ahali sun taso cikin soyayyar mahaifinsu har allah ya dauke ran mahaifinsu don mahaifiyarsu ta dade da rasuwa, a lokacin kowannen su ya taso da raayin abunda yakeso, Abdullah shine wanda ya ya taso da kudirin riqe legacy din familyn, inda yayi karatu bangaren business kuma cikin ikon allah yayi expanding family business dinsu har ya wuce yanda mahaifinsu yabar masu business din.
Tsakanin yan uwan nan akwai wani special connection tsakanin su musamman abdullah da khaal, saboda yanda mahaifisu ya koyar dasu son juna da kuma yarda da junan su.
Basu taba samun wani misunderstanding ba tsakanin su sabida yanda basa yima junan su baqin ciki ko hassada.
Khaal bai taba nuna son shiga harkar family business dinsu ba dan shi aikin government ya zaba, don haka koda akazo zaban wanda zai gaji taheel company as heir bai nuna disagreement ba ya cire hannunshi gaba daya daga business din ya barma dan uwanshi wato abdullah.
Shekaru sun jaa sosai inda abdullah yayi aure kuma auren soyayya,inda ya auri fattu ya ga babban dan kasuwa a bangaren southern arabia kuma abokin kasuwanci ga late taheel tajudeen, aure ne dai akayi shi badan soyayya ba saidai business inda mahaifinta ya roki alfarmar su hada hannu don taimakekeniyar
juna, duba ga hakan zai kara daukaka taheel company yasa abdullah ya amince kuma ya aureta amma badai don soyayya ba saidai kuma kasancewar shi mutun ne na kwarai kuma mai cikon alqawari da addini yasa bai tauye mata komai ba ya nuna mata so da qauna, ta bangaren fattu kuwa so take mashi sosai kamar ranta, da farko bata amince dashi ba sai daga baya,rayuwa mai dauke da kwanciyar hankali da farin ciki da kula fattu ta shimfida masu ita da abdallah, harkar company kuwa sai bunqasa take sosai.
Bayan shekara daya da aurensu allah ya albarkacesu da ya mace wadda suke kira da hidaya, hidaya ta taso da soyyayar iyayenta, musamman fattu (ummuh) fattu na masifar son hidaya kamar ranta, haka zalika hidaya itama ta taso da kaunar mahaifiyar ta sosai fiye da soyayyar da take ma mahaifinta, halayenta da dabi’un ta sak na mahaifiyarta, bata daukan raini sannan akwaita da girman kai sosai.
Tun bayan haihuwar hidaya allah bai sake basu wata haihuwar ba kuma basu damu ba har takai shekaru goma ciff a duniya, acikin wannan shekaru abubuwa da dama sun sauya inda ummu ta soma shiga harkar business din taheel company as assistant director, she was so into the business don sai alokacin ta fahimci dalilin da yasa iyayenta are so obsessed with harkar business.
Kudi dai da fame ba a magana don ya shigeta sosai wanda hakan yasa ta daura damarar rike mijinta sosai don tun farko tasan ba auren soyayya sukayi ba, but ita kam sonshi take kamar hauka, samun hidaya cikin rayuwarsu kuwa ba karamin ci gaba bane a wajen ummu,
Lokacin da ummu ta gane policy din company din kan cewa wanda zai gaji wannan comapny din dole sai da namiji ba karamin tashin hankali ta shiga ba don tana da dogon buri, anan ne hankalinta ya soma tashi game da rashin haihuwar su saboda tasan idan har bata haifa da namiji ba to fah khaal ne zai karba wannan company din idan har mijinta baya raye wanda bata fatan hakan kwata kwata wannan ne ma yasa qiyayyar khaal ta fara wanzuwa a ranta dukda tasan he’s not into the business kuma bashi da raayin haka, kanwar su halima kuwa ita aurenta ma tayi a kasar waje, tun bayan tafiyarta bata sake dawowa ba, wannan dalilin yasa suka fara neman magani ita da abdallah don sanin dalilin rashin haihuwar.
Da farko sun samu matsaloli sosai ta bangaren lafiyar fertility wanda daga baya kuma cikin ikon allah ta samu wani cikin.
Fadin irin murnar da ummuh tayi da samun cikin nan bata lokaci ne don ta kwallafa rai sosai akan cikin kuma burinta akan cikin nan ya wuce misali don ta tabbatar ma da kanta da namiji zata haifa wannan karan.
Bangaren Taheel abdullah yayi farin ciki shima da samun karuwar tasu saidai shi bai wani damu da da namiji ko mace ba duk wanda allah ya bashi shi mai godiya ne da Hakan, kulawa ta musamman dai yana yima fattu sosai don ayanxu kam zaman lafiya sukeyi sosai.
Bayan wata tara fattu ta haifi diyarta mace, ba karamin tashin hankali fattu ta shiga ba don burinta na haifar namiji bai cika ba, wannan yasa taqi amincewa da
sanin gender din babyn dake cikin mararta. Bayan kwana bakwai baby taci sunanta fadwa,
Daga kan haihuwar fadwa ne mafarin sauyawar fattu ya fara afkuwa, kwata kwata kudirinta da burinta yana ga samun power da fame,soyayyar da hidaya ta samu wajen mahaifiyarta kwata kwata fadwa bata samu ba, haka fadwa ta taso ta fara girma har fattu ta sake samun wani cikin bayan shekara uku shika da kyar aka samu cikin don sun kashe kudi sosai, wannan karan kam hankalin fattu a matuqar tashe yake don bata san yanda zatayi ba idan ta sake samun ya mace, hankalin ta kwata kwata bai kwanta da cikin ba haka dai take rainonshi saidai burin nan har zuwa lokacin yana nan.
After nine month allah ya sake bata haihuwar mace,(afiya) this time around frustration yasa tayi giving up kawai, abunda yasa hankalin ta ya kwanta ma shine ganin yanda khaal baya nuna interest akan company din hakan yasa ta fan tsagaita.
tsakanin fadwa da afiya kuwa bazan ce ga wadda ta jata jikinta sosai ba, kwata kwata bata jansu a jikinta saboda burin dataci na haihuwar maza sai kuma allah ya bata mata, matsayin hidaya dai yana nan aranta, tana masifar sonta kamar ranta.
A sannu a hankali ta soma jan su fadwa da afiya suma, lokacin data karancesu gaba daya fadwa is so smart and snicky while afiya kuma is so slow, hidaya dai har zuwa lokacin itace bold and strong among them don halinta irin na mamanta kamar photocopy.
Mahaifinsu kuwa ba karamin so yake masu ba su duka, baya banbancesu kwata kwata haka suka taso cikin soyayya da kulawa, a definition of a big happy family indeed, kwata kwata basu taso da wani hatred ko wani abu a ransu ba, daga su sai iyayensu, saima dai khaal da ummu ke janye su daga jikinsa, don shi kam ba karamin threat bane a wajenta, ganin wannan farin cikin da kwanciyar hankalin yasa fattu ta sassauta burikan da take dashi ta maida hankali kan ahalinta wato mijinta da yayanta.
A shekarar da hidaya ta cika shekaru sha takwas cip a duniya, a lokacin kuma fadwa na da shekaru takwas while afiya na da shekara bakwai.
A daidai wannan gab’a komai ya sauya masu, rana mafi muni ta bayyana a garesu, ranar data tarwatsa duk wani farin ciki da kwanciyar hankali na wannan ahali, wannan rana itace ranar da abdullah ya bayyanar da tajudeen taheel tajudeen ga yan uwansa.
Wannan rana ta kasance rana mafi muni da baqin ciki a zuciyar fattu,lokacin da abdullah ya bayyanar da danshi daya tilo wato tajideen.
Safiyar ranar lahadi..
Zaune suke a sitting room na kasa, hidaya dasu fadwa na wasansu while fattu na aikace aikacen ta daya shafi office din datake running, sallamar da suka ji ne yasa
duk suka dago gaba dayansu, Khaal ne ya shigo hannunshi rike dana kyakyawan yaron da bazai wuce shekaru shida ba gaba daya a duniya, sai abdallah dake biye dashi a baya, saurin miqewa fattu tayi tana mai kallonsu, daya bayan daya take kallonsu har ta maida idanunta kan yaron, tsantsar kamannin su da abdallah harta wuce musali saidai abdullah daya fi yaron haske sosai, karasowa sukayi cikin sitting room din, inda khaal ya zauna bayan sun gaisa da fattu, daman gaisuwar sama sama ce, kallon yaron khaal yayi kafin yace “jekayi wasa da yan uwan ka”
Wani irin damm gaban fattu ya bayar, kwata kwata ta kasa dauke idanunta akanshi, samun kanta tayi da tambayarshi “habibi waye wannan?”
Kasa hada idanu yayi da ita saima dauke ma ganinta da yayi yace “muje bedroom inason zamu tattauna akan wani muhimmin abu”
Bata musa mashi ba tabi bayanshi suka haura saman, suna karasawa saman jikin ta har bari yake, kofar bedroom dinma bata kaiga rufewa ba ta nufi inda yake.
Zuba mashi idanunta da sukayi jaa tayi kamar tasan daman akwai wani abun a kasa sai dai kuma jiran confirmation da takeyi daga wajenshi,
Hannunta ya janyo ya riqe gam cikin nashi kafin ya soma magana “habibity! I want to tell you something, please karki tayar da hankalinki okay? Kaddara ne kuma tana kan kowa”
Girgiza mashi kai ta sake hannunta dake cikin nashi yana karkarwa, “I’m listening, ina fatan dai ba wani abu bane serious, ko?”
Tunda ta soma magana ya kasa hada idanu da ita, tabbas baiyi mata adalci ba bai kyauta mata amma ta yaya zai fara mata bayanin nan? Ya za ayi ta gane? Ya za ayi ta saurare shi? Matan saudi babu abunda suka tsana kuma suka kyamata kamar kishiya, da kayi masu kishiya gwara sun bar maka gidan ka auro wadda kake so, wasu daga cikin su suna yarda da second wife saidai abunda yafi tsananta kuma yafi cin mutunci a wajensu shine mijin da yaje yayi aure a boye ba tare da sanin matansu ba, shi nashi is even worst don yayi auren ne kuma cikin sirri harda ‘da shekaru wajen bakwai da suka wuce, kuma ba tare da saninta ba.
Hannunta dake cikin nashi ta cizge, idanunta sunyi jaa sosai sai hawaye dake shirin kwaranyo mata, “da gaske ne kenan,”
Saurin dagowa yayi jin furucinta, da mamaki yake kallon bakinta dake furta, “wannan yaron danka ne?”
“Yes” ya amsa ta,
Wani irin jiri ne ya soma divanta, tuni tayi baya zata fadi ya taro ta, cikin sauri ta buge hannunshi tayi baya idanunta sunyi jaa sosai,
“I’m sorry fattu,”
“Shekara nawa kenan? Tun yaushe?” Ta jefo mashi tambayan nan
“Fattu duk wannan bashida amfani yanxu, listen to me…”
Saurin katse mashi hanzari tayi “abdallah!!!! Me kunne na ke shiri jiyo min? Wannan wani irin cin mutunci ne kayi min abdullah? Why why whyyyyy? Aure kayi a boye ba tare sa sani na ba for how many years? For 7years? Innalillahi wa inna ilahi rajiun? For good seven year? Kaci amata abdallah, ka cuceni?”
“Fattu please calm down”
Idnaunta da sukayi jaa ga hawaye kwance akai ta zuba mashi “don’t tell me calm down, you have no right to do such”
“Fattu please wannan dalilin yasa na kasa fada maki kamar yanda nace kaddara bata wuce kan kowa, i know you’ll be hurt shiyasa ban fada maki ba”
“Abdallah na gwammace na dauki wannan pain din shekaru da suka wuce akan yanxu shin Kasan abunda akayi kuwa? Kaci amanata kayi aure a baya na wannan shine d most humiliating abu da zan fuskanta a duniya, shin kasan ma’anar auren da kayi bada sanin na ba? Shin kasan tabon da kayi min a anan duniya? Ka mance da culture dinmu ne? Duk matar da hakan ta faru da ita tana da tambarin….”
“Fattu!!!!!! Abunda nayi addini bai haramta ba, aure nayi na sunnah, idan addini bai haramta ba then why abunda community zasu ce zai dameki?”
“Aure ba haram bane ba shiyasa nace daka fada min tun wuri, wannan abu da kayi is the most disgusting and evil doing, how could you? Shin kasan me hakan ke nufi kuwa? Kayi aure this all time bada sani na ba? In my entire life da tarihin iyaye na bamu taba fuskantar wannan humiliation din ba yanxu sai akaina? Kayi min babban tabo da har abada bazai goge ba?Duniya zata kalleni da wannan and the worst part shine harda da? Harda da????? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun?””””
Nan take ta sake burkicewa ta fashe da wani matsanancin kuka sosai, ihu zagi insult words babu wanda batayi mashi ba, yaci amanarta yaci amanarta ya cuce ta wannan auren da yayi ba karamin bakin fenti yayi mata ba harda da, da ace babu yaro da sauqi ita bata ma damu da sanin ya akayi yayi auren ba, amma yanxu idan duniya ta san da wannan shikenan, she can’t face the world don anan kasar sun maida abun kamar wani babban zinibi, abunda yafi tsaya mata shine gashi ita bata taba haifar da namiji ba, abu ya gama tarar mata, ga auren boyen daya boye mata, ga yaro kuma da namiji, at that moment ji tayi dama mutuwa kawai tayi akan ta fuskanshi wannan baqin tabo a gaban duniya, ita kanta to her self batajin she can accept this,
Babu yanda abdallah baiyi ba don rarrashinta amma kiff ta rufe ido, jikinta har rawa yake yi don abun ya shigeta sosai, “fattu please”
“No please get out get out bana son sake ganin fuskanka abdallah yalla yalla get out,” ta karashe da larabci
Hidaya data hauro saman babu abunda bata ji ba, saida taji motsin futowar abuh yasa ta labe a corridor don kar ya ganta, yana futa kuwa fattu tayi banging kofar, girgiza kanshi kawai yayi yana tausaya mata, dole zata shiga irin wannan hali daman yayi hasashen haka, kasa ya sauka zuwa wajen khaal,
Yana wucewa hidaya ta karasa bakin kofar, tun daga bakin kofar ta soma jin kukan ummuh, kuka sosai takeyi tana screaming da larabci, words of insult babu wanda bata rafko ma abdallah.
Bangaren su abdallah, yana karasowa kasan ya tadda yaron zaune shi kadai wajen kayan wasan su fadwa, suna wasa hardashi, jiki a mace ya karaso inda khaal yake zaune kafin ya zauna,kallon yanayin shi khaal yayi hakan ya tabbatr mashi da abunda yayi hasashe, haka nan ya fara tausasa shi yana bashi words of encouragement tunda babu yanda za ayi da wannan alamarin.
Bangaren fattu haka ta wuni a dakin nan tana kuka kukan baqin ciki, bata taba tunanin zata taba fuskantar rana irin ta yau ba, bata taba kawo hakan ba kwata kwata abun yazo Mata unexpectedly, bata jin zata taba yafema abdallah akan wannan abun da yayi mata.
Hidaya dake tsaye bakin kofa har barci saida tayi ta farka, kuka dai itama babu wanda batayi irinshi ba tana mai sauraron yanda mahaifiyarta ke kuka.
She was so shattered, dukda batasan karfin laifin mahaifinta ba but damuwanta shine kukan da mahaifiyarta keyi.
Haka aka shafe wata guda fattu na cikin kunci, abu dai gaba yake yi kullum, kullum tana kulle a daki ta rame ta jeme sosai, idanunta sunyi ciki ciki kamar ba fattu ba, duk wanda ya rabe ta korarshi take, abdallah kam bata yarda ma ta ganshi, ta tsaneshi yanda ta tsani mutuwarta, hidaya ce kadai ke samun shiga wajenta, duk sanda ta shiga dakin a zaune zata taddata ta kafa ma window idanu.
Taj kuwa yana samun kulawa wajen sabuwar maid da abdallah yayi employee wadda zata kula dashi, bangaren su fadwa da afiya basu san meke faruwa ba don gaba dayan su ba wani wayo ne dasu ba, saidai sun fuskanci mahaifiyarsu tana cikin kunci don rabon da su ganta har sun manta.
Yau dai abdalla kasa hakura yayi