Showing 123001 words to 126000 words out of 135321 words
dress you up okay? ta karashe tana duban sabeeha dake tsaye kamar gunki tana kallon ikon allah da wani sabon kalar iskanci, where’s his pajamas,’’ ta tambayi sabeeha, ‘’jimin wani kalan iskanci’’ sabeeha ta fada aranta,ganin irin kallon da sabeeha ke mata yasa ta yin yar tsuka, ‘’maysa mutane ke employing illeterate, mteww’’ ta karashe tana mai dube dube, daga sabeeha har taj din kallonta sukeyi sai wani yauqi takeyi kamar dawisu, ‘’zaddy…ina kayanka yake’’
nuni yayi mata da kayanshi da sabeeha ta ajiye anan gefen gadon, dauka tayi ta taimaka mashi ya saka kayan, saida akazo wajen saka wando ta dubi sabeeha ganin tana tsaye a wajen, yanda take kallonta haka itama take kallonta, nuni tayi mata da kofa akan ta futa kiri kiri sabeeha tayi kamar batasan me take fada a ta tsaya kyam, fuskarnan a hade kamar hadari taqi koda murmusawa, itako sonata sai surutai takeyi da accent dinta da ba ganewa akeyi ba sabeeha dai ko cikanki bata ce mata ba haka zalika bata futa daga dakinba, idan zai shirya yawanci futa takeyi saidai yau ganin wannan mai kama da balbelar da taji ance tsohuwar budurwarshi ce kuma batasan dame take tafe da ita ba ta babbake a wajen hakan yasa taqi futa.
babu kunya sonata ta nemi sauke mashi towel dinshi a sunan taimaka mashi wajen saka pj yayi saurin kama towel din yana mai duban sabeeha, tunawa da fada datayi mashi akan cewa karya dunga shiryawa gaban kowa kua ya dunga kunyar surarshi ta hanyar boyewa wannan yasa ya karbi wandon ‘’noo, i will change my self’’ yana kaiwa nan ya fuce daga zuwa bathroom, suna nan tsaye ya shirya ya futo, yana futowa sonata ta kalleshi ta sake kallonsa, bai sauya ba kwata
kwata saima kara kyau da yayi a idanunta, huge body structure dinshi na nan yanda yake saidai yanda yake magana ne ya sauya, character dinshi ma ya sauya yanxu ta lura duk abunda zaiyi sai yayi murmushi, ko ya girgiza kai sannan daga yanda yake magana gaba daya na yara ne, bata damuba don haka ta cigaba da pursuing kudirinta akanshi.
ta dade sosai a part dinshi tana manne dashi tana mashi labarai dukda tasan ba ganewa yakeyi ba.
washe gari jamid ya dawo, duk ya rame sosai ya zama shuru shuru baya magana sosai, wannan abu yana damun hidaya sosai, bata ce mashi komai ba dai ganin bai tunkareta da maganganun daya saba ba saidai tasa ido sosai akanshi, don tasan tabbas bai yarda da abubuwan da akace khaal yayi ba kuma tasan bazaiyi shuru ba, yanxu dai bashine damuwarta shiyasa bata ma bashi wani attention ba ta maida hankali wajen ayyukanta da business dinta.
bangaren fadwa bata zauna ba saida ta tabbatar taj shine T-ford, ba karamin buncike tasa akayi mata ba, private top investigators dake aiki acahn london tasa sukayi mata buncike akan rayuwar da yayi a baya, kuma basubar komai ba saida suka bunciko mata hatta inda yafi zuwa da abuncin da yake yawanci koda yaushe da activities din da yakeyi harma da relationship din da yayi da sonata da yanda tayi cheating dinshi,komai saida aka turo mata kamar faifai yanda ta buqata.
abun tambaya daya tsaya mata arai shine, ‘’ina dukiyoyin nasa?, meysa ya boye identity dinshi?,zarginta bai tsaya ko inaba sai kan hidaya, kamar yanda ta fada bazata taba bari ya samu cigaba ba, in kuma ya samu….? zata maidashi nata kenan?’’ amsar da fadwa ta bama kanta kenan.
wayarta ta janyo ta tura wani message a wayanta kafin ta ajiye wayar tana murmushi, ‘’ukty kenan, ke kike wasan ni kuma zan tayaki daga bayan fage’’ ta karashe tana murmushi, miqewa tayi da papers din ta fuce daga dakin zuwa dayan dakin dake cikin part dinta, daman dakuna hudu ne a cikin part din nata, daya na tareeq ne daya kuma nasu ne dayan kuma nata ne sai kuma wani daki da suke yawan ajiye kaya a ciki.
washe gari da sassafe ta kama tuesday, tun kafin kowa ya tashi jamid ya fuce daga gidan ya hau babban titin dharr bar, yanda yake sharara gudu kamar zai tashi sama, wayarsa dake gefe ce tayi ringing yayi saurin dagawa, “we cant meet today sir?”
“Why? “ jamid yayi saurin tambayar wanda ke amsa wayar
“Sir ana bibiyarka yanxu haka, kuma na tabbatar duk motsinka ake bi, zanyi mana fixing wani meeting din some other time”
Ana kaiwa nan aka kashe wayar, gangarawa gefe jamid yayi rai a bace ya bugi steering djn motar,ya dade sosai kanshi jingine jikin motar kafin ya dago ya juya akalar motar tashi.
Gida ya nufa kai tsaye lokacin wajen karfe takwas, lokacin daya shugo duk sun halarci wajen karyawa.
Chan ya nufa kai tsaye bakinsa dauke da sallama, dagowa duk sukayi suna kallonsa shima yana kallonsu har idanunshi ya sauka kan afiya, yayi mamakin ganinta don baiyi tsammanin ta dawo ba.
“Sabahal khair abu barad” Afiya ta gaishesa, gaisawa sukayi gaba dayansu ba yabo ba fallasa ya nufi wajen da yake karyawa ya zauna.
Hidaya na hakimce kamar kullum, Daidai nan taj da sonata suka shigo hannunsu na cikin na juna,da mamaki jamid ke kallonsu, su tareeq kamar ido zai fado kasa tsabar kallo,afiya kuwa wani murmushin mugunta tayi suna kallon juna ta kannema sonata idanu,
“First love!!!” Ya kira hidaya, yana kokari cire hannunshi daga na sonata ta riqe gam, chan kasa kasa ta soma mashi rada, “remember what you promise me?” Tunawa da hakan yasa ya tsaya bai tunkari hidayarba suka karasa hannunsu na cikin na juna
Zama sonata tayi taja mashi kujera shima ya zauna, jamid dai kasa daga chokali yayi yana neman karin bayanin shin wacece kuma wannan, afiya kamar tasan abunda ke yawo aranshi kuwa tace “oh myy babes you look good together”
Cikin kwarkasa sonata ta amsa “ouu i know right”
“Hey!!!” Sonata ta kira daya daga cikin maida din dake serving dinsu tace “hot black coffee and creamy tea for my zaddy”
Tana kaiwa nan ta dubeshi, hannunta ta sanya kan fuskanshi ta shafo fuskan nashi, shiko binta kawai yake da idanu yana murmushi, jamid dai kasa zama yayi don wanan abu yafi karfinshi, ranshi a mugun bace yake ya dubi hidaya, “let’s have a talk privately”
Yana kaiwa nan ya fuce daga dining hidaya ko saida ta gama abunda take kafin ta miqe tabi bayanshi.
A zaune ta taddashi nan sitting room, tana karasowa ya dubeta, “wacece wannan?”
Zama itama tayi ta hakince hannunta nadr a kirjinta tace “you have problem with her ne? She’s my guest”
“Kinsan ba wannan amsar nake nema a wajenki ba, why’s she with taj? Whats the too much closeness about? Yana da aure fa ko kin manta?”
Kallonshi hidaya tayi da kyau, “cause she’s his girlfriend, he noticed her at first glance, you have problem with that?”
“Yes i do, haba hidaya listen to your self manq, yana da aure fah? Da matarshi ta sunna?”
“Matarshi? You still consider wanan abar matarshi? Well i dont”
“Hidaya!!!!!!” Ya kira sunanta a natse idanunshi yayi jaa sosai, tunda ya soma magana hidaya ke kallonshi, ya sauya sosai, yanda yake mata magana ada bayayi mata yanxu, kuma tasan he’s cooking something behind doors don tasan shi sarai ciki da bai, kuma tasan buncike yakeyi akan mutuwar khaal shiyasa tayi babban shiri akan wanan, jamid bazai taba shuru ba, he will do anything kuma tasan duk wani motsinshi har futar da yayi yau da sassafe.
Dalilin dayasa ta soma tailing dinshi kuwa shine tayi finding out yasa wani abokinshi dake aiki da ssd ya bude case din cikin sirri, kuma bin didigin komai sukeyi shiyasa ta saka black ya koma hideout for the mean time kafin komai ya lafa.
Abuja nigeria….
Santuraki residence…..
Rai a bace ya fito daga cikin motar yana mai duban agogon hannunshi, karfe tara da rabi kenan, gashi time sai kurewa yakeyi, duban laila dake tsaye yayi ranshi a mugun bace, yana shirin magana ta katse shi “ya hamad dan allah kayi hakuri yanxu zata futo”
Wayar dake hannunta ta latsa tana mai kokarin kiran maya, ringing kusan hudu tayi shuru babu response, “wuce na saukeki naje nayi abund aya shafe ni” yana kaiw anan ya shige motar, daidai nan maya ta futo, tana snaye da atamfa anyi mata fitted gown tayi mata kyau masha allah chass chass tasha jan baki radau sai shade akan fuskanta baki ga wani heals data saka shima, anatse take tafiya kamar dawisu ta karaso inda laila ke tsaye, “haba maya kinsan dai baya son bata lokaci, kullum idan kika kwana part din anty laila saikin bata mana lokaci”
Tsaki tayi “malama babu wanda ya isa ya takureni fah?,ban tashi da wuri bane shiyasa”
Da mamaki nake kallonta, hausanta ya dan fara fitowa radau ba kamar lokacin datazo ba,
Sanin halinta da masifa yasa laila ta nufi wajen motar tashi cikin hanzari har yayi reverse yana shirin fucewa tsabar bacin rai da takaici.
Seat din baya duk suka zauna ya dago ya dubesu, maya dai kallon ariziki batayi mashi ba ta kauda idanu, laila ce dai datasan me hakan ke nufi ta koma seat din gaba suka fuce daga compound din gidan.
Bai tsaya ko’ina ba sai baze university, yana shiga yayi parking daga waje wajen ko duban inda suke baiyi ba yace “ku fita”
“Ya Hamad please ka dan karasa damu wajen blovk din chan akwai nisa wallahi”
Ko kallon inda take baiyi ba kamar an takureshi da yin maganar yace “get out of my car”
“Masu car manya” jakarta dake gefe ta jawo da wayarta ta bude motar ta fuce tare da bako kifar kamar yaqi rai a bace.
Laila na ganin futarta itama ta fuce ya juya mitar kamar zai tashi, ya tsani raini kuma shi yarinyar nan ke gwada mashi amma zaiyi maganinta.
Achan school kuwa suna cikin tafiya maya ta nufi hanyar cafe, kallon ta laila tayi tace “banan zamuyi class ba fa”
“Bazan shiga yanxu ba sai anjima”
“Maya its late fah? Kuma kinsan test mr tokumbo zaiyi?”
“ i don’t care, nace kije zanzo”
Haka suka raba hanya maya ta wuce cafe fuskanta dauke da bakin shade ita kuma laila ta wuce class,tana karasowa ta samu waje ta zauna taba mai latsa wayarta da nanna ta saya masu iri daya da laila iphone 15.
Kamshin daya yi maya ziyara ne yasa ta dago “hello!”
Dagowa tayi ganin dan kyakyawan fine biy yasa ta sauke dan murmushi tace “yes helo”
“Can i?”
Ya tambayeta?, “yes of course ta amsa shi”
Zama yayi nan kusa da ita suka danyi hira sama sama tanata jero mashi accent dinnan nata shima dai ba a barshi a baya ba, karya ce da kudi suka hadu don haka suka dunga yaqar juna.
Haka ta sakankance har wajen karfe goma da rabi, tana duban agogon hannunta taga time din ta miqe tare da mashi sallama bayan ta karbi number sa.
Class din ta nufa kai tsaye lokacin har ana gab da submitting papers din,ko kallan inda lecturer yake batayi ba ta nufi kujeran gaba gaba ta zauna.
Papers aka soma karba, laila data san halinta kuwa ta daure ta rubuta mata ta bata haka dai sukayi submitting bata tsinana komai ba suka fito.
Next class ma bata shiga ba ta wuce hostel wajen sabbin kawayen datayi, haka suka wuni suna chasu a cikin hostel harda plans din outing din da zasu this upcoming weekends
Sai wajen shiga ta baro hostel din ta fito suka hadu da laila, yau hamad bai dawo daukansu ba dole suka jira drivern anty laila yazo ya duakesu zuwa gida cikin hadaddiyar motarta.
Laila karama nata mamakin yanda akayi ta basu motarta kuma duk dan maya ne.
Suna karasowa gida kowa ya nufi part dinsu, maya ta nufi bangaren uwar dakinta ita kuwa laila ta nufi part dinsu tana ta gunguni.
Da sallama ta shugo tafkeken part din nasu mai kyan gaske, anty fadila na daga kitchen don daga nan sitting room tana jiyo muryarta, kai tsaye ta nufi kitchen din, “mami na dawo”
“Sai yanxu?”
“Wallahi ya hamad ne yaqi zuwa daukanmu saida maya ta kira anty laila ta tura mana driver da motanta”
Da mamaki fadila ta juyo, “ita lailan ce ta bada motarta aka dauko ku?”
“Uhm ta amsa ta kai tsayw, ita kuwa mamki baisa ta daina nanata abunda laila ta fada mata ba.
Washe gari kuwa da gangan hamad ya fuce abunshi da sassafe karka mami tace yazo yakaisu, yauma driver anty laila ne ya sake kaisu kuma ya dauko su, kamar dai kullum yauma bata shiga lecture dinba ta dunga shirirta, har lokacin tashi yayi.
The next day ta kama friday, tun daga gida ta shaidama anty laila zata kwana a hostel, bata hanata ba tace “go and enjoy your self my dear”
Cikin jin dadi kuwa da yanda anty laila ke treating dinta babu wani tsangwama shiyasa ta zamto itace number one favorite dinta kaf gidan,
Lokacin tashi nayi laila karama tayi bolt ta dawo gida, saboda maya ta shaida mata zata kwana hostel kuma tasan ba haka kawai zata kwana ba achan din, itada tana mamakin maya sosai, da abubuwan da takeyi, rayuwar turawa har yanxu bata gama barin jikinta ba.
Koda ta dawo gida bata fada ma kowa ba ta wucewarta daki.
Bangaren maya kuwa karfe takwas nayi suka shirya ita da kawayen nata cikin kananun kaya, daya daga cikin akwai mai suna fadila suna kiranta da fendi, itace mai babbar motar cikin sauran suma suna da motar saidai batakai tata ba, babanta shine governor zamfara state, itama karatun ya kawota shekara wajen biyar kenan har yau bata gama ba ta tsaya shiririta, karatun da akema shekara uku ita har biyar tayi, babu gaba babu baya saidai iyayenta suyi ta tura mata kudi tana bannatar dasu ta hanyar batanci da shirirta.
Haka sukaci kwaliya fesss fess suka fito su hudu, duk cikin kawayen fendi yanxu tafi son maya sosai saboda yanda halayyansu yazo daidai, sun jiqu da kudi sosai gasu yayan wane da wane, don saidaga baya sukasan maya daga santuraki family take,wanan yasa tasu tazo daga.
Koda suka hau motar basu tsaya ko ina ba sai the most expensive restaurant dake nan cikin garin abujan, batattaun yara ne kawai wanda basu san darajar kudi ba suke zuwa nan suyi sharholiyar su, suma suna zuwa sukayi order abunci kala kala a take dai saida suka kashe over 300 thousand for just meals kuma basu wani cinye ba suka fito suka wuce wajen flushing Cikinsu a wani hotel mai suna trancorpina the most expensive hotel a garin, koda suka iso ciki suka shiga direct maya dai na biye dasu,basu tsaya ko’ina ba sai wajen inna clubbing louge, lokacin wajen karfe sha biyu saura, ciki suka shiga kai tsaye wajen yana cike da mutane masu aji fa sanyin ac da kamshi dake tashi, wasu na kan dancing pole wasu na shaye shayensu na beers wasu kuwa badalar su kawai sukeyi allah ya shirya.
Zama maya da fendi sukayi sauran kuwa suka wuce wajen rawa, “babes mey zakisha?”
Fendi ta tambayi maya, tabe baki maya tayi tana kllon wajen tace “haka club dinku yake anan so roudy?”
“How is compare to naku nachan us?” Fendi ta tambayeta
“Not that bad!” Maya ta amsa ta kai tsaye,
Hannunta fendi ta kama tana kanne mata idanu,”babes youll enjoy it here i promise, let mw introduce you to something interesting”
Jinjina mata kai maya tayi cikin jan aji tace “okay lets see”
Order fendi tayi masu na beers da shisha sai wani dan bowl da ake kawo masu high flavours, “kinga wannan you can never go wrong with this i promise” tayi mata nuni da bowl din, daukan daya maya tabi ta bude tare da mumushi, takai daidai saitin hancinta ta shaqa kafin ya kai bakinta gaba daya, saurin kama hannunta fendi tayi tace “ke yayi yawa”
“Wow!!! Toh ay this is nothing compared to…”
Dakatawa tayi jin an dafata ta dago, wannan saurayin ne da suka hadu a cafe kwanayi,“hey maya!”
“Hey!!! Uhm nama manta sunan nata? Wa izzz your name?” Ta sake tambayarshi, fendi ce tayi saurin amsa ta “ jamal abdulsamad nera, son of the former president”
Murmushi yayi yana mai kallon fendi yace “fendi right?”
“Yes ta amsa shi kai tsaye, nuni sukayi mashi da wajen zama ya zauna gefwn maya yana mai kallonta, “can i join you guys?”
“Yes if course” suka amsashi,vape dinshi ya zari daga aljihun shi ya bude gefen wajen da ake zuba flavour ya dauki wannan wrap din da maya tasha ya zazzaga a ciki ya kunna vape din ya soma zuqa yana busarwa, gaba daya kallonsa sukeyi musamman fendi data dade ta mace akanshi. Yaron is so classy and cute saidai akwai ji dakai.
Sun dade soaai suna banke banken abubuwa harya kai ga sunje high sosai sai wajen karfe 4 sukabar wajen anan hotel din sukayi lodging suka kwana.
Washe gari.
Misalin karfe sha daya ta soma bude idanunta, sorbing from giyar datasha, bude idanunta ta sakeyi tar kafun ta miqe zaune, sai a lokacin ta soma tuna abunda ya faru da yanda tayi ending up a hotel din.
Da kyar ta samu ta miqe zindir ba komai a jikinta ta wuce bathroom tayi wanka kafin ta fito da towel a jikinta, tana tsaye gefen bedside ta hango wata paper, da dollars a kasan takardar, daukan paper tayi ta karatan kamar haka “morning beauty, yesterday’s night was fun”
Tana gama karantawa ta wullar da takardar ta maida kayanta na jiya sannan ta dauki jakarta da kudin daya ajiye mata ta fito, kasa ta sauka zuwa reception kai tsaye,zama tayi anan reception din tayi requesting bolt, cikin mintuna qalilan ya iso ta fuce daga reception din.
Daga nesa chan nanna data fito daga motarta kirar range rover ta hangota, dubanta tayi don tabbatarda ita dince ko kuwa, juyawar datayi ne yasa ta kasa tantance ita dince, bayan wannan ma me zai kawo maya wanan wajen?,”kai anya, maybe I’m mistaken”
Ta furta ahankali tare da maida dubanta ga ma’aikatanta da motocin da suka shugo