Showing 6001 words to 9000 words out of 135321 words

Chapter 3 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

498

tashi daga amfani,

Wayar ma na daya daga cikin abubuwan da suka tarwatse don da alamu tana gama wayar ta wullata kasan tiles, gefe kuma glass jug dinnan ne da maid ta shugo dashi akan wani stool, gabanta kuma glass cup ne afashe da wasu kwayoyin vitamins.

Kallon papers din take jikinta har kyarma yake kamar mazari kafin ta watsa su kan gado ta wuce hanyar wani glass petition…..

 

Zuge glass din tayi nan take bathroom dinta ya bayyana sai wata yar kofa a gefe da alamu closet ne, toilet din ta fada, saida ta dauka yan mintuna kafin ta fito daure da towel, jikinta luwailuwai kamar fatar jariri, hanyar walk in closet room tabi inda aka zagaye dakin da wajen ajiye kaya daban daban, gefe guda kayan maza ne a wajen hakan ya tabbatar min da qila na mijinta ne.

Bata tsaya ko’ina ba sai wajen kayanta, wasu kayan zaman gida ta zaro masu laushi kafin ta ajiye su kan table din dake tsakiyan closet din, tana ajiyewa ta nufi wajen wasu drawers, nan ta soma jawowa ta fiddo da kayan shafenta da kamshi, komai dai is organize ba a cewa komai, saida ta gama shiryawa tsaf ciki kayan kafin ta nufi wata drawer daban inda a jikin drawer an manna wani tag da manyan harufa ‘’first aid’’

 

Bude wajen tayi ta zaro wani roban magani da plate din daura maganin, kafin ta fuce daga closet din.

**

 

**UNITED STATES **

San Diego California 11:55pm

 

Cikin sauri sauri take tafiyar dukda hasken daya gauraye street din hakan baisa ta daina jin fargabar data fara jiba tun da ta sauka daga motar data ajiyeta, sanye take da riga da wando jeans, kayan sun amsheta don tana dan jiki, gashin kanta ya sauko a har bayanta, babu abunda take zai zabga sauri, hankalinta yayi gaba kawai wanda hakan yasa ban hango yanda yanayin fuskanta yake ba,Daidai hanyar wani street tabi inda aka rubuta Boulevard California street a jikin symbol dake nuni da hanyar ne zai kaika har street din, motar data sauketa ne kirar benz ta wuce ta gabanta inda daga gaban motar matukin ya zuge aka dago mata hannu, cikin matsuwa ta daga masu hannu itama kafin su wuce, babu abunda ke tashi sai kida wakar hip hop daga cikin motar, cikin abunda bai wuce minti biyar ba ta dunga wuce titin dake street din wanda iska ke kada bishiyoyin kan hanyar sai gidaje masu shegen kyau terrace a man manne an tsara gidajen da bricks masu shegen kyau.

Ganin ta tsaya chak nesa da wani gida yasa na zuba mata idanu,kallon hanyar dazai sadata da gidan take inda aka saqala wani symbol ajikin ginin gidan da manyan rubutu kamar haka, (Barr Majeed res flat c) maido da dubana nayi wajen inda take kallo ganin ta kurama symbol din idanu kafin ta sauke wata

nauyayyayyar ajiyar zuciya ganin babu motar dady kafin ta shige cikin gidan cikin sassarfa daman ta tabbatar bayau zai dawo ba, mummy kuma na night duty a asibiti saboda doctor ce.

Bata tsaya a ko’ina ba sai daidai stairs din dazai sadaka da kofar cikin gidan,leqe ta soma yi kamar mara gaskia ganin lights din windows din gidan duk a kashe yasa ta tsugunnawa ta cire igiyar takalminta duka biyun kafin ta fiddo da kafarta, bata da haske saidai skin dinta yana glowing don irinsu ake kira da caramel complexion, kamar bata taba taka kasa ba, yatsun kafafunta sunsha nail paint pink sai wani zoben kafa data saqala, tana fiddo da kafar tayi saurin bude back pack dinta mai kyau, wata abaya ta zaro ta zura akan rigarta kafin ta tura takalminta cikin jakar, tana gamawa ta haura stairs din da baifi guda uku ba harta tsaya gaban kofar, ta dauka kusan minti daya anan tsaye kafin ta daga hannunta ta danna door bell, tana dannawa sau daya ta janye hannunta ta tsaya chak, ta dauka kusan minti biyu a tsaye jin shuru yasa ta sake danna door bell din, daidai nan aka bude kofar, wata mata ce ta bude kofar, idanu yarinyar ta zuba ma matar ganin hankalin matar adan tashe, itama kallon ta matar ta soma yi da yanayin shigar jikinta.

Matsa mata gefe matar tayi ba tare da tace mata uppan ba harta shugo ciki kafin ta rufe kofar, tana rufewa matar ta wuce ba tare da ta sake waiwayonta ba don ta tsaya chak a tsaye kamar munafuka

‘’nanny bee I’m sorry’’

Chak matar ta tsaya jin abunda tace, karasowa yarinyar tayi ganin haka kafin ta kamo hannunta ta cigaba da Magana ‘’nanny bee bansan time ya tafi har haka ba, please I’m sorry na saba alkawari’’

 

‘’where…are.. you coming from’’

Wata kaushashiyar murya ce daga cikin sitting room ta doki kunnenta, nan take gabanta ya fadi dam batama san lokacin data saki hannun nanny bee ba, nan take idanunta suka soma kawo ruwa, yau tata ta kare, badai muryar dady take jiba, daman yau zai dawo? But mummy tace mata sai Monday zai dawo yau kuma Friday, shikenan tata ta kare yanxu tsoronta irin punishment din dazai bata saboda last warning ya bata, nan take ta soma hawaye har tsoron juyowa take ji don ta bama hanyar sitting room din baya.

 

Wani magidanci ne a zaune akan kujeran sitting room din, parlorn yayi dim saboda lights din parlor ba’a kunne suke ba sai side lamp dake kunne guda daya wadda haskenta bai gauraye parlorn ba, fuskarshi kawai na iya hangowa, fari ne sosai ga hanci kamar biro, suman kanshi a kwance cikin wata hula fara tass, yana sanye da farar jellabiya ya daura kafa daya kan daya yana girgizawa da alamu ranshi a bace yake sosai duba ga yanda yayi Magana,daman zaman jiranta yake yaga ta yanda zata shugo, dawowanshi 5 hours ago, da farko yayi tunanin ko tana daki ne, don kwata kwata daya dawo baiji motsinta ba kuma yasan time din dawowanta daga school ya wuce,  saida yaje dakin ya tabbatar da bata nan koda ya tambayi nanny bee wadda ita ke kula da ita tun dawowan su nan California tun tana karama harta girma zuwa yanxu, nan ta shaida mashi inda ta fada mata

zata je kuma  da saninta ta futa ita kuma dalilin barinta datayi ta futa shine ta shaida mata cewa zataje School prep na upcoming exams din su don shiga higher institution.

 

Saida ta wuce time din daya kamata ta dawo ya soma fada sosai saidai kuma yasan ba laifin nanny bee bane don haka kawai ya zauna anan parlor don yaga gudun ruwanta da rashin hankalin ta don ranshi yayi mugun baci kuma yayi alqawarin this time around saiya koya mata hankali don daman ya bata last warning amma duk da haka ta tsallake sharudan daya gindaya mata.

Wannan karan bazai saurarin mommyn ta ba kwata kwata daman itake hanashi displine dinta yanda ya kamata.

 

Yana nan zaune har sha biyu saura, fadin irin tashin hankali da baqin ciki hade da bacin ran da yake ciki ma bata lokaci ne, bai gama tabbatar da maya ta kangare ba sai yanxu.

 

11:55pm dot kuwa saiga karar doorbell, har nanny bee ta fito daga bedroom dinta ta bude kofa baice komai ba don bata lura dashi a zaune a parlorn ba daman itama hankalinta ya gama tashi tun bayan time din datace zata dawo ya wuce, harga allah tana masifar son maya shiyasa bata iya hanata wasu abubuwan.

‘’nanny bee excuse us please’’

Sunkuyar dakai nanny bee tayi don sai taji kunya ya lullubeta saboda batajin dadin abunda maya keyi musamman da kulawanta ke hannunta.

‘’okay sir, goodnight’’

Tana kaiwa nan ta wuce bedroom dinta, maya dai kasa motsawa tayi sai data sake jin muryarshi ‘’come here this instant!’’

 

Cikin saurin ta karaso parlorn har tana tuntube da rug din dake tsakiyan sitting room din, kyam ta tsaya a tsaye tana danne hawaye dake neman zubo mata, saida taji yace sit kafin ta zauna a kasan tana facing dinshi, har lokacin bata bari sun hada idanu ba, shima daga nan bai sake ce mata komai don tunanin yanda zaiyi dealing dinta yake bayan wannan ma kokarin danne bacinranshi yake akan don ko dukanta bai taba yi ba saidai yayi mata fada sosai.

 

‘’explain your self, and mind you, karki sake kimin karya’’  ya fada a kausashe yana mai rufe idanunshi da sukayi jaa sosai alamun bacin rai

‘’’daddy I’m sorry please’’

‘’hold your sorry maya, ay ban yanke maki hukunci ba tukunna, start speaking now!!!!!’’ ya karashe da fada sosai.

 

‘’nace daga ina kike?’’ ya daka mata tsawa

A furgice ta dago tana rarraba idanu da hawaye suka wanke mata su sharr, ‘’birth…day..partyn Zara’’

‘’what!!! Ya daka mata tsawa nan take jininta ya sake boiling, bakinta har rawa yake wajen furta ‘’daddy I’m sorry please, wallahi bazan sake ba I’m sorry please’’

 

Runtse ido yayi ya sake bude su akan ta kafin ya dan rage murya ya soma Magana cikin dacin rai ‘’maya kina mace?kina mace kika fita party sai midnight zaki dawo? Daman abunda kikeyi Kenan bada sanina ba? Gaba daya shekarunki nawa? Youre just 17 maya?,I’m so disappointed in you, and wallahi this time around zanyi maganin ki sosai’’

Ya karashe yana haki saboda tsabar bacin rai

‘’your phone, tablet, gaming pads, laptop and your keys drop them now’’ ya fada yana daka mata tsawa, jikinta har kyarma yake tsabar tashin hankali, nan ta soma fiddo su gaba daya daman a ciki bag pack dinta yawanci take ajiyewa.

Wani irin kukan baqin ciki ne ya kubce mata lokacin data zaro car keys dinta wanda ko hawa motar bata taba yi ba daman birthday present ne daddyn ya saya mata for her 18th bithrday in the next 3 months, inda ya bata amma saita shiga sha takwas kafin ta fara tuqawa, yanxu shikenan, ko hawa batayi ba zai kwace, and duba ga yanda ranshi ya baci sosai dinnan tasan da wuya ya sauko sosai don taga tsantsar bacin ran da bata taba gani ba daga wajenshi, daman yawanci mummy ke shawo kanshi yanxu gashi bata nan balle ta taya ta bashi hakuri.

 

Ajiyesu tayi tass a kasan tana hawaye saida ta gama tass kafin yace ‘’get out of my sight now!!’’ ya daka mata tsawa, cikin furgici ta miqe tsaye ta wuce hanyar stairs, koda ta hau sama wani daki ta bude daga wajen wani corridor, tana bude kofar ta banko ta tare da wulla Jakarta kan gado ta afka kan gadon itama sai hawaye, dakin nata komai pinkish nay an gata, harda tv station da makeup station, sai wani tamkeken round gado shima pink sai net daya zagaye shi gaba daya.

Ko’’ina frame din hotunan ta ne zagaye a dakin inda tayi kyau sosai da kananun kaya masu kyau, maya dai akwai kyau babu laifi, bata da haske sannan akwai ta da idanu masha allah.

 

Saida tasha kuka sosai akan gadon kafin ta mike zaune, kallon agogon gefen beside dinta tayi ganin karfe daya da rabi yasa ta mike ta soma rage kayan jikinta, anan kasa ta yasar da komai ya rage daga ita sai yar bra dinta da wani dan mini shorts pink color, toilet ta nufa direct,shima yasha adon pink, daga kan hangers dinta zuwa shower komai da toilestries komai in pink color, gashi fess fess babu kazanta saima kamshin dake tashi.

Wanka tayi ta nado jikinta da towel kafin ta futo anatse tana goge hawayen idanunta da suka kasa tsayawa, kwata kwata bataso haka ba, waya itace rayuwarta, gaba daya gadget dinta dady ya karbe yanxu ya zatayi, ta yaya zata yi communicating da friends dinta abundai ya tsaya mata sosai arai don ko kayan barci bata saka ba ta hau bed dinta ta shige cikin duvet ta kwanta.

 

Asuba nayi daddy ya kwankwasa dakinta, tana jin knocking ta tabbatar da shine nan take kuwa tayi zumbur ta mike zaune don daman idan yana nan wannan

barcin nata ajiyeshi takeyi a gefe, ‘’tashi kiyi sallah’’ daddy ya fada daga bakin kofar ba tare da ya shugo ba

‘’na tashi daddy’’ ta amsa shi da gaggawa tana goge idanunta da suka kumbura tum kafin ta mike zaune ta wuce bathroom.

Alwala tayi kafin ta fito ta wuce katuwar closet dinta, fadin yawan suturar ta ma bata lokaci ne don sunfi kala dari, anjera su fess fess, wata pink jellabiya ta dauko ta zura ta tare da janyo wani katon hijab dinta kalar milk, bata tsaya rufe closet dinba ta wuce wajen praying section na dakin nata,sallaya ta fara shimfidawa kafin ta tadda kabbara.

Cikin yan mintuna qalilan ta idar da sallah, bata ma tsaya yin azkar ba ta cire hijab din da jallabiyan ta yasar anan kan sallayan kafin ta hau kan gado taja duvet dinta ta kwanta.

 

Karfe takwas daidai daddy ya sauko daga sama, sanye yake da farar jellabiya, sai a lokacin na kare mashi kallo da kyau, kyakyawan magidanci ne fari tass ga hanci,yana da suman kai mai santsi da gashin baki wadda ya fidda kyawun fuskanshi, dining area ya wuce ya zauna daidai nan aka danna doorbell daga waje, ko ba’a fad aba yasan mummyn maya ce don haka ya gyara zama akan dining din ya soma hada tea,

Nanny bee ce ta fito daga kitchen saye da uniform dinta, saida ta tsaya suka gaisa da daddy kafin ta wuce hanyar shugowa cikin gidan,

‘’assalam alaikum’’

Nanny bee ce ta tayi amsa sallamar tata kafin ta amshe jakar hannunta da lapcoat dinta.

‘’welcome ma’’

‘’thanks nanny bee’’ matar ta amsata agajiya,

Atare suka nufi sitting room ina matar ke tambayarta ‘’ina baby?tana barci ko?daddy ya dawo’’

‘’yes ma, ya dawo yana dining area, maya bata tashi ba tukunnna’’

 

Cikin sassarfa matar ta karasa dining area inda mummy bee ta wuce upstairs zuwa dakinta don ta ajiye mata kayayyakin ta.

 

Da sallama ta karaso dining din fuskanta dauke da murmurshi mai kyawun gaske, daidai nan daddy ya miqe tsaye don daukan brown sugar dake dan nesa dashi.

Da sauri matar ta karaso ta rungumeshi ta baya tsam a jikinta tana mai sauke wata ijiyar zuciya.

Shiko chak ya tsaya bai juyo ba saima hannunta data saqalo a kugunshi daya riqe gam.

 

‘’welcome back hubby, I missed you so so much kyakyawana’’

Wani irin murmushi ne ya kubce mashi lokaci guda dayaji sautin mujryarta, sai ya nemi fushin maya daya kwana dashi aranshi ya rasa shi tass kamar an wanke mashi zuciyar.

Sakinshi tayi kafin ta zagayo inda yake ta zuba mashi mayun idanuwan nan nata masu shegen sheqi da kyau.

Kallonta yake sosai babu kakkautawa yana ayyana irin kewarta daya yi a cikin zuciyarsa da begenta.

Sai alokacin nima na zuba mata idanu don ganinta da kyau, sanye take da doguwar riga peach color mai adon dutsina a saman rigar sai tayi rolling kanta da mayafin kayan asaman kanta, rigar tayi masifar yi mata kyau don ta amshi jikinta sosai, itakam komai ma karbarta yake yi don da wuya ta saka abu baiyi mata kyauba.

Matar batada jiki kwata kwata saidai akwai shape mai jan hankali, batada hasken skin irin pauu dinnan saidai daga ganin fatarta kasan tana shan gyara don tana da healthy skin.

Tana da kyawun fuska mai kyau ga hanci itama ba laifi saidai baikai na daddyn ba, daga ganinta bazata wuce 38-39 haka ba.

 

Shafo gashin bakinsa tayi ganin ya shagala da kallonta kafin ta danyi mashi fari mai jan hankali ‘’daddy wannan kallon fah?’’

Ta karashe tana kashe mashi idanu, murmushi kawai ya sake yi kafin ya soma Magana ‘’bana gajiya da kallon ki ne my cutie, welcome back, ya aiki? Kin gaji ko’’

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta maida mashi da murmushin da yake mata ‘’wallahi kuwa daddy na gaji sosai bari naje na watsa ruwa saina sauko muyi break fast din tare’’

 

Sakin hannunta yayai kafin ya zauna yace ‘’okay’’ …..saman ta wuce direct bata tsaya ko’ina ba saida ta leka dakin maya, ahankali ta bude kofar ganin tana barci yasa ta rufo mata kofar.

 

Dakinta dake gefe kusa da wani bedroom daban ta wuce, tana shiga daki ta sauke ajiyar zuciya tare da yin miqa.

‘’alhamdulillah’’ ta furta kafin ta karasa cikin bedroom din, dakine ne mai kyau da tsari, babu wani tarkace sosai saima books dake ko wani sako na daki, dresser ta kuwa yasha kayan shafe da gyaran jiki da gashi.

Mayafin kanta ta soma warware nan take gashinta ya zubo kasa inda tasha kitson kalaba wanda ya sauko har dantse kafadarta, toilet ta wuce direct bayan ta ajiye mayafin akan gado inda nanny bee ta ajiye mata laptop bag dinta da wasu files data shugo dashi harda handbag dinta.

Cikin mintuna qalillan ta fito daga cikin bathroom sanye da towel da alamu wanka tayi sai kamshin ke tashi daga jikinta.

Agurguje ta gama shiri ta tsaf cikin wata hadaddiyar sexy riga red dukda rigar is decent hakan bai hana sexy jikinta fitowa ba.

Turarukanta masu tsada ta feshe a jikin nata kafin ta zura wata yar hula ta fito hannunta rike da wayanta inda wani call ya shigo mata related to office.

Kasan ta sauko cikin nutsuwa, kamshinta ne yayi mashi sallama inda ya zuba mata idanu kafin ya dan kauda kanshi saboda nanny bee data fito da flask a

hannu, yana ganin darajar nanny bee sosai don dattijuwa ce don zata haifeshi harma da ita matar tashi.

 

Dining din ta karaso har okacin wayan na kunnenta, saida ta gama wayar ta kalli nanny bee ‘’sannu nanny b, thank you for the breakfast’’

Murmushi nanny bee ta mata ‘’babu komai madam, akwai abunda zaku buqata yanxu? Zanje nayi ma maya breakfast kafin ta tashi’’

Dagowa daddy yayi ya kalli nanny bee din don jin abunda tace, nan take ranshi y abaci ya hade rai ‘’ba nace adaina yi mata wani special treatment breakfast ba? Idan tana buqata ta dunga futowa tana dafama kanta, ko kuma ta sauko taci wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login