Showing 39001 words to 42000 words out of 135321 words
tsaki bayan futarsu saboda tashinsu da akayi cikin tsakar daren nan wajen karfe uku, gashi zasu tashi da wuri,
Suna fitowa head ta dubi inda sabeeha take tace ‘’what mess have you caused? Matsalata da irin ku black people dinnan idan kuna abu kamar marasa kai, just simple instruction baku iya bi ba?, now what stupidity have you done?’’
Tunda suka fara tafiya head take surfa mata masifa ita kuwa baiwar allah gaba daya hankalinta baya kan maganganun head din don hankalinta a tashe yake, babu abunda take sai tambayar kanta shin me tayi? Gaba daya jiya ta fara aikin fa? Hartayi abunda ba daidai ba.
Suna karasowa part din headmaids ta fara shiga ciki sabeeha na biye da ita, zuciyarta na faman lugude tsabar tsoro, koda suka karaso bedroom dinshi head ta tsaya ‘’ki shiga’’
A tsorace sabeeha ta sanya hannunta kan mabudin kofar kafun ta shiga bakinta dauke da sallama, jamid ne kawai ya amsa sallamarta da mamaki, kallonta yayi daga sama har kasa kafin ya dauke idanunshi daga kanta.
Mikewa hidaya tayi, taj na ganin haka shima ya miqe yana mai kokari kamata da kyau, kallonshi tayi ‘’big baby seat down’’
Tana fadin haka kuwa ya zauna anan kan gadon idanunshi na kanta don baya son ta tafi, takowa ta somayi har inda sabeeha take kafin ta daga hannu ji kake tasss tass tass, ta kwashe sabeeha da maruka both sides din fuskanta, cikin sauri jamid ya karaso inda suke ya janyo hidaya baya rai a bace yace ‘’hidayaaa’’
Hannu ta daga mashi rai a bace, akan me zai jata baya tana kokarin saitama wannan dumbhead din kai, lokaci guda sai bacin ranta ya koma kanshi, bata kaunar irin abubuwan da yake mata wanda babu wanda ya isa yayi mata irin haka sai shi, Taj dake zaune kukan sabeeha na mashi eco a kunne, kasa hakura yayi dole ya miqe tsaye baima san ya tashi ba ya nufi inda suke,take shima ya soma hawaye yana jan hannun hidaya ‘’first love please I’m sorry, don’t hit her please, she’s our friend remember?’’
Haka ya dunga maganganun da baima san me yake cewa ba yana jan hannun hidaya irin yanda yara keyi, ‘’stop it’’ ta daka mashi tsawa, ‘’go back and seat down’’
Wannan tsawar datayi ba karamin abu bane a wajen taj, don baya kaunar yaga tana fushi dashi ko kadan, nuni tayi mashi da gadon shi,
Saurin sakin hannunta yayi ya nufi gadon ya zauna kanshi a kasa, har wani irin zazzabi ne ya rufe shi lokaci guda, ga wani azababben ciwon kai daya kawo mashi ziyara, jikinshi har rawa yake ga jijiyoyin kanshi da suka fito rado rado.
Saida ya zauna hidaya ta maida dubanta ga sabeeha kafin tayi kwafa ta fuce daga dakin rai a bace.
Bayan futarta jamid ya dubi sabeeha dake kuka innocently harda shesheka abun tausayi, ‘’I’m sorry about that okay?bansan me kikayi ba but Please be careful next time okay?, ranta ne ya baci sosai that’s why tayi acting that way’’
Tsagaitawa sabeeha tayi da kukan tana sauraron yanda yake Magana anatse cikin mutunci, girgiza mashi kai kawai tayi alamun gamsuwa
‘’you’re the new caregiver right?’’
‘’yes sir’’ ta amsa shi.
‘’please work on his injuries okay?’’
Girgiza mashi kai sabeeha tayi kafin ya fuce daga dakin ya barta a tsaye.
Sauran hawayen dake kan fuskanta ta goge, kafin ta maida dubanta ga inda yake zaune a bakin gadon ya runtse idonshi gam jikinshi na faman karkarwa.
Takowa ta soma yi anatse har zuwa inda yake zaune, tsugunnawa tayi a gabanshi tana mai kallon fuskanshi, kawai saita fashe da kuka ganin yanda fuskanshi yayi jaa sosai ita a tunaninta shima ko bugunshi akayi, har zuwa lokacin bata san taqamaimain laifin datayi ba saidai koma menene ta yanke shi ne a dalilinshi ne.
Idanunshi ya bude ya sauke akanta yana kallon yanda take kuka, hannunshi ya dago ya dora akan fuskanta, hannun nashi dake kan hijab din fuskanta tabi da kallon, wani irin dumi ne taji ya ratsa fuskan nata wanda ke futowa daga tafin hannun nashi ‘’don’t cry for me friend’’
Runtse idanun ta tayi ta dora hannunta akan nashi dake fusknta, wani irin zafi taji sosai kamar wuta, hannunshi is so soft kamar bai taba amfani dasu ba.
Sun dauki kusan minti biyu a haka, ta kasa sauke hannunshi daga kan fuskanta, ga wani mixed feeling dake shiga cikin jininta, lokaci guda ya shiga ranta sosai, tausayinshi ya gama yi mata katutu arai, da zuciya daya taji tana son shiga cikin rayuwar shi ta hanyar taimakonshi da kulawa dashi don iya abunda zatayi mashi Kenan.
Bakinta na rawa ta soma Magana ahankali cikin muryarta mai kwantar da hankali
‘’sir, you’re burning up,’’
Zame hannun nashi tayi daga kan fuskanta ta maida dubanta ga hannun nashi, jinin data gani ne yasa ta tuna da maganar wanda ta tarar tare da madam wanda take tunanin shine mijinta,
Mikewa tayi tsaye yana ganin haka shima ya miqe yana mai jan hijab dinta, kallon hannun nashi tayi kafin ta daga kanta don ganinshi, ‘’I’m scared friend bazan iya zama ni kadai ba’’
‘’zaka rakani?’’
Girgiza mata kai yayi kafin ya sauke mata murmushin sa mai tsada, wanda ya sata kasa dauke idanunta akanshi, yanda yake murmushi zaka rantse lafiyar kalau, he looked so matured.
Batace komai ba ta nufi hanyar fita yana biye da ita har suka wuce zuwa kitchen, bin hanyar ya dunga yi da kallon kamar yau ya taba shiga wajen, suna shiga kitchen ta nufi wajen da taga first aid box, janyowa tayi ta soma budewa kafin ta zaro spirit da cotton wool harda wound plaster.
Komawa sukayi dakin yana biye da ita a baya har suka karaso bakin gadon, ‘’seat down friend’’
Tana fada kuwa ya zauna, tsugunnawa tayi tana mai kallon hannun nashi, mika mashi hannunta na dama tayi yana ganin haka kuwa ya daura hannunshi akan nata, goge mashi hannun ta soma yi da spirit, ‘’ouch’’ ya furta
A dan furgice sabeeha tace ‘’sorry, sorry akwai zafi ko’’
Girgiza mata kai yayi, haka ta gyara mashi hannun kafin ta saka mashi plaster, tana gamawa tace ‘’ka kwanta kayi barci friend’’
‘’no I don’t want to, nasan tafiya zakiyi kamar yanda first love ta tafi, I’m scared don’t go please’’ ya fada cikin rada, ganin haka ya sata zama a kasa tace ‘’bazan tafi ba friend, ka kwanta to’’
Tana fadin haka kuwa ya kwanta, dan motsawa tayi yana jin haka yayi saurin kamo hijab dinta ya riqe gam,
Haka suka zauna yana kallonta tana kallonshi, gashi idanunshi tarr yaqi yin barcin saboda baya iya barci dole saida maganinshi shiyasa ba a skipping lokacin maganinsa, ganin kusan har karfe hudu yasa ta miqe tsaye,yana ganin ta miqe kuwa shima ya mike har yana kokarin karo da ita, matsawa tayi baya kadan kafin tace ‘’toh ka bari nayi sallah’’
Da mamaki yake kallonta yace ‘’no firnd zaki tafi ki barni ne, lets go together’’
Shuru sabeeha tayi tana tunanin yanda zatayi dashi, don taso ya barta ta futa ta koma part dinsu ko alwalar ne ya barta ta dauro saita dawo nan, ganin hakan bazaiyuwu ba kawai ta nufi hanyar bathroom dinshi a tsorace.
Yana biye da ita a baya ta tsaya tana bin bathroom din nashi da kallo, kallonda batayi ba bathroom din ba daxu, komai fari qal qal ya hadu ba kadan ba, zata iya rantsuwa akan bata taba ganin bathroom mai girma sosai kamar daki irin wannan ba,.. wajen wash hand basin ta nufa yana biye da ita, alwala ta dauro yanata kallonta hart agama, tana idawa ta juyo sauran kiris su gwaru don suna dab da juna.
‘’muje toh’’
Matsa mata yayi ta wuce kafin yabi bayanta kamar jela har suka kaarso tsakiyan dakin, da kyar tayi indicating kibla kafin ta kalleshi tace ‘’ka zauna a bed dinka toh, babu inda zanje I promise zanyi sallah ne’’
‘’Sallah’’?? ya maimaita abunda ta fada confusedly, da mamaki ta kalleshi tace ‘’yes sallah,’’
Yanda tace kuwa hakan yayi ya samu waje a bakin gadon ya zauna, bai yarda ya dauke idanunshi akanta ba harta tada kabbara, ta dade sosai tana jero salloli tana addua harta sallame.
Hannayenta ta daga tana mai kai kukanta wajen allah kamar kullum ta dade sosai tana addua.
Duban agogon dakin tayi ganin wajen kusan biyar da kwata hakan ya sata mikewa ta fara sallar raka’atainul fjir, tana idarwa ta dubi inda yake zaune, yana kallonta har wani tagumi ya doka ya zuba mata idanu.
‘’friend kaje kayi alwala’’
‘’alwala?,’’ ya sake tambayarta
Nunfasawa sabeeha tayi tana tunanin how he react, tambayr kanta ta somayi kodai bai iya bane, bata kawo wani negative thinking aranta ba ta nufi inda yake tace ‘’friend muje toilet’’
Da saurin shi kuwa ya mike suka wuce bathroom, ‘’duk abunda nayi kaima saikayi okay? Wannan ibada ne, idan kanason allah ya baka duk abunda kake so sai ka dunga yi lokacin ta okay?’’
‘’yes firnd’’ ya fada da murnarsa, alwala ta somayi yana kwaikwayonta ita kuwa tana mashi bayani har suka gama, suna idawa suka fito, anan kan carpet ta tsaya yana gefenta ‘’kaga sallah danayi dazu? Irin shi zamuyi yanxu okay?’’
‘’yes firnd’’ ya fada sounding so excidetedly,
Tada kabbara tayi yana kallonta shima ya yayi, haka ta soma karatu a bayyane shima yanayi har suka idar, suna idawa ta kalleshi ‘’kaga yanxu allah will answer all your prayers duk abunda kake so you can ask allah’’
‘’zan roki allah yasa first love kartayi fushi dani, I want to be seeing her everyday’’ ya karashe sounding childish
Murmushi kawai sabeeha tayi batace komai ba haka suka zauna, tana lazimi tana koya mashi wani abubuwan, abunda ta lura dashi kamar koyon abubuwa yake, and it looks like ya mance da wasu abubuwan daya shafi addininshi.
Suna nan zaune ya soma gyangyadawa, surprisingly don da wuya yake iya bacci idan bai sha magani ba, kan kace me sai kawai jin kanshi tayi akan shoulder dinta, saita zama wata yar dul a gefenshi, juyoda kanta tayi tana kallon tsakiyan gashinsa dake shoulder dinta, curly gashinsa babu abunda suke sai wani irin kamshi mai dadi, wani ririn murmushi ne ya subce mata kawai, saita samu kanta da tofa mashi addu’oin data iya da ayar allah.
Shiko barci ne mai nauyi ya dauke sa peacefully, sun dan dade a haka ta soma yin hannunta ya qage saboda yana da girma sosai,
Rasa abunyi tayi ganin bata da wani option yasa ta soma mashi Magana cikin rada bayan ta riko hannunshi da hannayenta gudun karya furgita ‘’friend, friend, tashi ka kwanta’’
Kunnenshi ne ya soma jiyo mashi muryarta, take kuwa ya bude idanunshi ahankali da suka soma yin jaa ya zuba mata su, a shagwabe ya tabe baki ya soma miqewa, da taimakonta ta ya kwanta a kan gadon don barci ne mai karfi ya soma fusgarshi.
Yana kwanciya ya kama hannunta yaqi saki haka nan ta hakura ta zauna a bakin gadon idan barcin nasa yayi nisa saita zame ta futa.
Tana nan zaune itama tana zabga hamma har barcin ya sureta ta lafe akan gado hannunshi na cikin nata….
Matar Taj (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍️
Free page
Chapter 19-20
Update!!!
Bangaren su hidaya, bayan futarta daga dakin rai a bace ta koma daki, babu abunda take sai sintirya tsakanin dakin, jira kawai take ya shigo bedroom din ta sauke mashi ruwan masifa kamar zata iya.
Kamar yasan jiranshi take kuwa yana shugowa ya hade rai sosai,
‘’jamid wai meysa baka da burin daya wuce ka nuna min ban isa ba?, how dare you stop me from….’’
‘’stop you from maltreating wanda ke kasa dake?’’ ya katseta,yana mata wani irin mugun kallo.
‘’shin kasan kuskuren datayi ne?,did you even know abunda zai faru idan kayi kuskuren rashin bashi maganinsa akan lokaci kuma cikin qai’da according to yanda doctor shi ya fada ba?, look duk abunda ya shafi big baby bana wasa dashi kuma bazan taba barin wata stupid caregiver ta yi sanadiyar abunda zai jawo mashi wata matsalar daban’’
Hannayenshi ya nade a kirjinshi ya zuba mata idanu yanda take Magana idonta a rufe babu mutunci, daga yanda take wannan abun yasan abunda zai biyo ba wanda baya jin zai kara barinta ta sake tafka babban kuskuren datayi achan baya dukda yasan ba kuskure tayi ba.
Saida ya bari takai aya kafin ya sauke wani murmushi wanda shi kadai yasan me hakan ke nufi kafin ya raba ta gefenta ya wucewarshi ba tare da yace mata ci kanki ba.
Ba karamin haushin hakan taji ba don takai wuya sosai, binshi tayi hark an gado ta cigaba da masifa akan big babyn nata rai a bace, yana jinta yayi banza da ita.
****
Karfe takwas daidai ya soma bude idanunshi, bin ko’ina ya soma yi kafin ya miqe zaune yanda yake yi as’ual koda yaushe idan ya tashi, saurin juyowa yayi gefen gadon jin sautin nunfashinta na sauka akan hannunshi don ta rike hannun nashi tam daidai fuskanta, baiwar allah barcin ma kamar a wahale take yinshi don a zaune take sai kanta data daura akan lausassan gadon nashi.
Samun kanshi yayi da kallonta haka kawai ya kasa dauke idanunshi daga kanta, lashes dinta da sukayi zaro zaro ya zubama idanu, maida dubanshi yayi ga hannunta dake cikin nashi, daidai nan aka bude kofar bedroom din nashi.
Daddy barad ne ya shigo a natse cikin farar jellabiya, karasowa yayi cikin dakin da mamaki yake kallon taj dake kallon caregiver nashi,
‘’TAJ’’
Dagowa yayi ya maida dubansa ga dadyn barad kafin ya washe bakinsa fararen hakoransa suka bayyana,
‘’uncle’’ ya furta kamar wani karamin yaro, cikin sauri ya fuzge hannunta dake cikin nashi ya mike tsaye zuwa inda dadyn barad ke tsaye, sai a lokacin sabeeha ta farka dalilin zame hannunshi da yayi cikin nata,duban inda ya nufa tayi kafin tayi saurin miqewa tana mai sauke kanta kasa.
Rungumesa daddyn barad yayi tsam a jikinsa yana mai shafa suman kanshi ‘’sai yanxu zaka kulani Kenan, jiya ay qin qulani kayi saida first love dinka tazo’’
Sakinsa taj yayi yana murmushi harda girgiza kai kamar yaro yace ‘’jiya?? First love? Ina first love dina, batazo ba ban a ganta ba uncle jamid, I want to see her please’’
Sanin yana yawan mantuwa wasu lokutan musamman idan abunda ya furgita shi ne da wuya memory din abun ke dawo mashi yasa jamid cewa ‘’zatazo yanxu, how are you?’’
‘’I’m fine uncle jamid, ina new puzzle box dakace zaka kawo min da da colate?’’
‘’yana nan na boye maka zan baka okay’’
Cikin murna taj ya soma shafa sajen fuskanshi tare da bitting lower lips dinshi yanda ya saba musamman idan yana cikin farin ciki ko idan ya samu abunda yake so, wannan character nashi yana nan bai sauya ba koda kuwa ya samu matsalar kai, kallonshi jamid yayi cikin tausayawa da kaunarshi,
Jan hannunshi taj yayi har zuwa inda sabeeha take kafin ya kalleta yana mai rike hannunta itama ‘’uncle kaga new friend dinmu nida first love,’’
Girgiza mashi kai yayi har zuwa lokacin mamakin taj yanda ya taddasu yake,
‘’friend uncle Zai kawo min cholate, kema kina son cholate ko’’
Sautin ajiyar zuciyar data sauke ne tare da girgiza mashi kai yasa jamid kallonta yana mamakin yanda akayi ta samu courage din kwana tare da taj din, yayi mamaki sosai don taj baitaba yarda wani ya kwana tare dashi ba ko yazo kusa dashi musamman caregivers din da ake kawo mashi don su kula dashi, baya son ganinsu kwata kwata in baa hidaya ba baya qaunar kowa a kusa dashi, shima don ya dage ne sosai yana chusa kanshi yasa yake yarda dashi wani sa’in.
Yanda yazo ya tadda su abun ya bashi mamaki, abunda ya tsaya mashi arai har yake tambayr kanshi shine shin wannan improvement ne ko kuwa yaya?, don abun yayi surprising dinshi sosai.
‘’you can go now, I will take it from here’’ jamid ya fada yana mai duban sabeeha
‘’sir zan taimaka mashi yayi freshen up, sannan time din medication dinshi yayi’’ Kamar mai tsoron Magana haka ta karashe maganar
‘’okay!!’’ ya amsa
Hannunta dake cikin na taj ta zame kafin ta wuce bathroom, duk abunda tasa zai buqata saida ta ajiye mashi ta shirya mashi bathtube sannan ta saka mashi maclean a jikin electric brush dinshi kafin ta fito.
Tana kokari daukan mashi towel dinshi sai gashi ya shugo toilet kamar an wulloshi, kallonshi tayi ganin yana faman daga kafafunshi ga gumi na saukan mashi, idanunta ne suka sauka akan inda hannunshi suke, ya rike mazugin wandonsa yana kokarin zame wandon, cikin sauri ta dauke idanunta daga wajen harta yi tsuru tsabar tsoro, ‘’friend I want to pee pee pee help me pls’’
Hankali a tashe sabeeha tace ‘’toh ka tsaya in futa saikayi’’ bakinta har karkarwa yake towel dinma har ya fadi ba tare da saninta ba
‘’friend button ….button… my trouser…. Yaqi futa’’
‘’na shiga uku ni sabeeha’’ sabeha ta fada aranta, hanyar futa ta nufa cikin tashin hankali, cikin sauri kuwa ya kama hannunta gam don ta gefenshi tazo giftawa,
gabanta ne ya bada dam, ta kasa motsawa ma, ‘’help me pls’’ itace Kalmar data doki kunenta dukda ta gama tsurewa
‘’sir ka bari na kira maka uncle saiya taimaka maka’’
Kamar zaiyi bori haka ya soma yi mata, ‘’noo please pee zai futo ki cire min’’
‘’innalillahi !!! sir bazan…’’
Baima jira me zata ce ba ya janyo ta kamar yar kaza zuwa gabanshi sai ganinta tayi yar tsulum wajen kwankwasonshi, kamar zatayi kuka ta soma Magana ‘’kai wai ina aka taba haka, da girmanka zan cire maka wando, ni wallahi bazan cire ba’’ ta karashe tana mai fiddo da manyan idanunta
Tashin farko kawai sai jin kukansa ta soma yi, sai a lokacin ta tuna lalurar sa, gaba daya idan