Showing 69001 words to 72000 words out of 135321 words

Chapter 24 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

527

harya gama kafin ya saketa, “daga ina kake? I’ve been waiting”

“Sorry for keeping you waiting first love”

Ba tare da ta kalleshi ba fuskanta na nan yanda take ba yabo ba fallasa, duban agogon hannunta tayi kafij tace “next flight dina zai tashi in the next 10 mins, seat let’s have a chat”

Zama sukayi yana kallonta da mamaki, ganin haka ya sata cewa “ba zama nazo yi ba, i had to stop by saboda inason muyi magana.”

Attention dinshi gaba daya ya bata ya natsu sosai cikin ladabi yace “okay first love”

“Get ready by monday inason ka dawo saudi”

Cikin sauri ya dago yana kallonta, girgiza mashi kai tayi alamun yes kaji abunda na fada, 

“No but” ta katseshi don tasan abunda zai fada kenan,

Sunkuyar da kanshi kawai yayi yace “okay, i will” ya amsa ta cikin ladabi.

“You’re going back for good,” ta sake fada ba tare da ta kalli fuskanshi ba, fuskanta a hade kamar hadari babu digon murmushi ko dariya 

Gabanshi ne ya fadi, meysa first love zatace haka, ayyukanshi na nan fa? Tech Business company dinshi da yake running fah? yana son ya tambayeta dalilin hakan saidai bazai iya ba don hakan kamar jayyaya ne da ita.

Sama sama suka danyi discussion kafin time flight dinta ya gabato har lokacij ya cika kafin ya mata sallama, har cikin wajen check in ya rakata  kafin suyi sallama.

Jiki a mace ya dawo, bai tsaya ko ina ba sai tech company dinshi, wajen kamar repair shop ne da harkar kere keren abunda ya shafi karfe da motoci technically, babban elegant tech shop ne sosai mai girma ba kadan ba, yana da employers sunkai su goma kowanne yana aikinsa da bangaren da yake ma aiki, tsayawa yayi yana kallon wajen, “Autofix,”

Nan take ya fara tunanin yanda ya fara wajen, tun tasowarshi yake son harkar motoci, he’s so into automotive technology, wannan yasa yayi karatun engineering, koda ya fada ma hidaya bata musa mashi ba ta amince akan yayi abunda yake so wanda hakan ya mashi dadi sosai don a ganinshi tayi supporting abunda yake so, wanda hakan yasa yake jinta sosai aranta, 

Wajen ya kasance one of his happy place kuma its like his dream he build it da kanshi tun wajen bai zama abunda ya zama ayanxu ba, daman yana da passion din wannan.

Wannan autofix din nashi ya samu recognition a England city, don ba karamin waje bane, yana harka da manyan company’s inda suke kawo mashi ayyukansu daya shafi kere keren abubuwan fannin electronical technology.

Yana cikin top members na desiging team din hyundai,wannan yasa ya zama popular sosai achan.

Wajen ya zama popular for both maza da mata masu zuwa da motocin su, matan ma dai zuwa suke saidai su zuwansu saboda owner din wajen ne, saboda he’s resistable, babu wanda ya taba tunanin shi ba citizen kasar bane don yana da connections sosai. 

Wannan nasarorin daya samu hidaya bata sani ba kwata kwata, don bashi ne a gabanta itadai duk a ganinta wannan part din daya zaba shine daidai dashi as long as baya tunanin dawowa.

*****

Tsaye suke a wajen parking space din arrival,hidaya na daga tsaye tana receiving call while su fadwa da afiya suna daga tsaye bakin mota,cikin yan mintuna kalilan saiga mutane sun fara fitowa daga gate din international arrival, kallon gate din fadwa da afiya suka soma yi, yau ce rana ta farko da zasu sanya shi a idanunsu tun bayan tafiyar shi, saida aka gama fitowa gaba daya basuga alamun shi ba.

“ni zan koma cikin moto na nikam…” fadwa ta fada

Kasa karasa maganar dataso yi tayi inda idanunta sukayi capturing dinshi yana fitowa majestically, saurin tabo afiya fadwa tayi, 

A natse yake tafiya yana tunkaro inda suke hannunshi rike da baggage dinshi sai dayan kuma ya rike jacket dinshi, fuskanshi sai walqi takeyi don ya tara beard wanda ya qara ma fuskanshi kyau sosai, dukda yana jin wani irin fargaba hakan baisa ya sauya yanayinshi ba, gaba dayansu sakin baki sukayi banda hidaya da ta bama bangaren da yake futowa baya tana amsa waya.

fadwa ce ta kasa boye expression dinta beneath her breath tace “wowwwww”

 afiya dai tabe baki kawai tayi tana kallon ikon Allah don ya chanza gaba daya kamar bashi ba, shekara goma sha uku kenan.

TAJ kenan, the charismatic handsome young man, he’s a definition of perfection tafiya yake majestically cikin kananun kaya, fuskanshi yasha wani baqin glass daya haska fuskanshi.

waige ya soma yi kafun idanunshi su sauka kan hidaya data juya baya, dukda baiga fuskanta ba jikinshi ya bashi itace saboda kaunar da yake mata koya makance zai iya sensing intana waje.

gaba daya baima gane su fadwa ba don tun bayan tafiyar shi bai Kara ganinsu ba don basa zuwa duba shi chan england.

Yana karasowa ya rungume hidaya “first Love”

Katse wayar datakeyi tayi tare da hadiye wani mugun miyau, lokaci guda wani irin baqin ciki ya turniketa, ta dauka kusan second talatin a haka kafin ta daidaita natsuwar ta tare da sauya fuska kamar ba ita ba ta juyo inda yake fuskanta dauke da murmushi

“welcome back big baby, finally Ka dawo Zan samu peace of mind”

Murmushi yayi wanda ya fadada fuskanshi ya Kara mashi kyau ya sake kallonta yace “I’m so happy to see you,meysa kika tsaya a cikin rana? Banason kina wahalar da kanki first love”

Hannunshi ta dan saki ta kauda kanta gefe tace “dole nazo Ay na tarbeka my baby brother”

Gyaran murya ta danyi kafin ta kalli inda su fadwa ke tsaye kamar gumaka suna kallonsu, kowacce da irin abunda take ayyanawa a ranta

“Bakaga sisters dinka bane?” Hidaya ta tambayeshi tana kallon inda su afiya ke tsaye

Maido da kallonshi yayi ga inda take mashi nuni, daya bayan daya ya kallesu, yanayin fuskanshi ya dan sauya kafin ya karasa inda suke ya rungumesu ba tare da yace masu komai ba.

Fadwa ce kawai ta iya ce mashi “welcome” afiya kuwa cikin motar ta koma tana takaicin dalilin da zaisa hidaya ta tilasta sai sunzo daukan shi.

Bangaren hidaya bazaka taba iya tantance a wani irin yanayi take ciki ba saidai deep down tana jin wani irin tashin hankali da bacin rai a zuciyarta da wannan dawowar tashi.

Wannan rana ta kasance mafarin da zai sauya rayuwar shi da kaddarar shi, ranar da rayuwar shi zata sauya daga rayuwar daya saba, ranar da farkon babin rayuwarshi mai dauke da sarqaqiya zai bude.

Cigaban labari….

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 34-35

Cigaban labari…..

Bayan futar hidaya daga bedroom din fadwa ta kalli afiya daketa faman zubda hawaye, itama ranta ba karamin baci yayi ba ta soma magana ‘’ay daman saida na fada maki, kanki kamar na kifi,how could you even think about that?’’

Saurin kamo hannunta afiya tayi ‘’haba fadwa, meysa baki fada min tun wuri ba, wallahi bansan haka abun yeke ba’ na dauka duk wadannan abubuwan da ukty keyi saboda tana sonshi ne’’

‘’Ke baki da Ido ne saina fada maki? Saurin fuzge hannunta tayi daga na afiya tare da yi mata kallon kin bani mamaki kafin ta fuce daga bedroom din rai a bace itama.

Tana fita afiya tayı saurin share hawayenta, nan take kuma ta sauke wani murmushi mai wuyan fassara akan fuskanta.

Bangaren hidaya daga bedroom din afiya direct ta wuce study room dinta dake sama, idanunta yayi jaa sosai, fadin yanayinta a wannan lokacin bashi misaltuwa, tana shiga ta rufo kofar daidai nan jamid ya fito daga bedroom dinsu, kallon study room din nata yayi kafin ya kauda kanshi ya fuce daga part din nasu.

sabeeha dai tunda ta shiga dakin su bata fito ba, gaba daya ta gama shiga confusion da wannan ala’amarin dake faruwa da ita, tsoro fargaba babu wanda baya yawo a cikin ranta, har zuwa lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa, aure dai data sani, yau itace keda aure akai, kuma auren wanda baima san ina kanshi yake ba, kuma aurenda babu sanayyar iyayenta akai sannan itama an yi conering dinta, don harga allah bada saninta haka abun zai juye ba, haka ta kwana tana hawaye, ta rasa dalilin dayasa ita rayuwar tazo a haka, mey zata cema mahaifiyarta?.yanxu idan aka kamata fa a matsayin yar leqen asiri?, bama wannan ba, ayanxu dai ta tabbatar ana son ayi amfani da ita ne wajen cutarda wannan mara lafiyan, abunda ta Kasa ganewa shine meysa za a turota nan gidan, kuma maysa ka aura mata shi? da wannan tunanin barci barawo ya fusgeta

washe gari ta kama talata, shirinta ta fara yi yanda ta saba koda yaushe cikin uniform dinta, gaba daya jikinta a mace daga yanayin yanda take shirin ma, tana gamawa ta fuce daga bangarensu na yan aiki.

saman part dinshi ta wuce direct, kamar kullum saida ta fara gyaran part din cikin natsuwa kafin ta nufi dakinsa lokacin wajen karfe takwas na safe.

koda ta bude kofar dakin sanyin ac ya bugeta take taji wani irin yanayin mai wuyar fassara ya risketa, haka kawai taji wani irin sauyi a tattare da ita, kallon inda yake kwance tayi, ganin bashi kwance sannan bedside lamp dinshi a kunne ya tabbatar mata da ya tashi, a gurguje ta gyara mashi beddings din gadon kafin ta shige closet room dinshi ta debo mashi kaya riga da wanda masu laushi farare tass wanda ya saba sakawa.

tana kokarin ajiye mashi su a bakin gado taji yo ihu daga toilet din.

cikin saurin ta ajiye kayan ta nufi wajen toilet din ta soma knocking ‘’friend are you okay?’’

yana jin muryarta ya fashe da kuka, ba tare da tunanin komai ba sabeeha ta bude kofar tana mai kokarin rufe idanunta don bata san a wani yanayin zata taddashi ba, kasa rufe idanun nata tayi ganinshi jikin bangon bathroom din jikinshi har bari yake ya tamke idanunshi baima ga sabeeha ba, kallon bathroom din sabeeha ta soma yi don ganin abun da ya tsorata shi haka, idanunta ne ya sauka kan dan karamin kenkeson dake crawling a wajen, maido da dubanta tayi gareshi inda yake pointing abun,kasa dauke idanunta tayi daga kanshi, yana daure da towel a waist dinshi, take taji wani irin tausayinsa ya mamayeta, ya za ayi ace wannan katon ne ke tsoron dan wannan mininin abun, baifi ya takeshi da kafarshi ba.

hannunshi ta kamo cikin sauri ya waro idanunshi don ya tsorata sosai, ganin sabeeha ya sashi saurin rungumeta gaba dayanta ya rufe ta ruff, cikin sauri ta rufe idanunta, yauce rana ta farko data taba jinta jikin namiji kaff duniyar nan, abun yazo mata a bazata, saurin hankadashi tayi ya koma baya, kokarin dawowa ya soma yi zai rungumeta tayi saurin dakatar dashi,

‘’kaga na dauke abun bazai maka komai ba’’

kallon tiles din yayi ganin babu kyankyason yasa ya sauke wani murmushi har kumatunshi na lobawa, fuskanshi har wani walqi takeyi saboda annuri, bata san lokacin da itama ta sauke wani murmushi ba, ‘’thank you bibi’’ 

da mamaki sabeeha ke kallonshi jin sunan daya kirata dashi, ‘’waye bibi?’’

da yatsan shi yayi nuni da ita tare da dungure mata goshi, ‘’you!! you’re my bibi my hero, you save me’’

samun kanta tayi da kallon lebenshi dake furta sunan, ‘’yanxu wannan ne aka yima aure jiya? aure dai na mata da miji?, saboda me? why? what’s the reason?’’ haka ta dunga saqe saqe cikin zuciyarta, motsin data ji daga bedroom din ne yasata saurin juyawa  ta futo daga bathroom din shima ya biyo bayanta.

kallonsu jamid dake tsaye yayi, saurin gaishesa sabeeha tayi kafin ta fuce daga bedroom din, kallonta jamid yayi harta fuce kafin ya maida dubansa ga taj dake tsaye da towel rike a kugunshi don bai iya kullewa ba sosai.

excitedly ya soma magana fuskanshi dauke da murmushi ‘’good morning uncle’’

‘’morning big baby’’ jamid ya amsa shi yana kallon fuskanshi, hannunshi jamid ya kama suka zauna bakin gado 

‘’how are you today?’’ jamid ya sake tambayarshi yana mai kokarin janshi a jiki sosai

‘’i’m fine uncle, i slept well’’

kallonshi jamid ya soma yi yana wani tunani, kwata kwata babu wani improvement a tattare da rashin lafiyar taj, wannan abu yana damunshi sosai.

‘’taj’’ ya kira sunan shi 

‘’yes uncle’’

‘’zanje england zaka bini?’’

shuru taj yayi kamar mai nazarin wani abu harda sanya dan yatsa a gefen bakinshi, ‘’uncle england? ina ne england?’’

‘’bakasan england ba? achan fa ka taso har kayi karatu ka manta?’’

confusely yake kallon jamid, ganin haka yasa jiki a mace jamid yace ‘’never mind me je ka shirya’’

Jamid na zaune ya shirya fess fess abunshi, sabeeha ta shigo da breakfast dinshi da maganin shi ta ajiye ta fuce don ta basu waje, bata dade da futa ba jamid shima ya futo daga bedroom dinshi hannunshi rike da medication din taj.

Bayan futarsa da awa guda ya sake dawowa tare da barad wanda keta faman murnar zuwa wajen taj din don rabonshi daya gansa tun ranar daya futo dashi ya fadi.

a zaune suka ya tarar da taj din yana ta faman juya puzzle box dinshi,gaba daya attention dinshi na ga abun,jamid baiyi mamakin ganinshi zaune ba don yasan already wannan medication din nashi ke sashi barci, saidai ya kasa gane dalilin da zaisa ace wai the only solution to his problem shine a barshi ya dunga barci, dukda yasan he’s risking it, haka kawai yaji bayason ya barshi yasha maganin.

cikin saurin barad ya zame hannunshi daga na daddyn shi ya wuce wajen taj din, cikin murna ya soma magana ‘’uncle taj’’

da mamaki taj ke kallonshi yana pointing dinshi, ‘’you!! you!!’’ take ya kyalkyale da dariya, shima barad din dariya ya soma yi .

saurin rungume taj din barad yayi ‘’i missed you uncle taj’’

‘’i missed you too my old friend, i have a new friend now’ tunda baka zuwa wajena muna wasa’

a shagwabe barad ya kalli taj din, ‘’toh ay mama ne ta hanani zuwa’’

‘’who’s mama?’’ ya tambayeshi, jamid ne yayi saurin katse su, 

budo kofar da akayi ne yasa suka zuba ma kofar idanu, taj ne yayi saurin cewa ‘’bibi, come and see my old friend’’

saqe sabeeha tayi tana kallonsu harda taj din, don tasan by this time daman tana zuwa dubanshi ne don yawanci a daidai wannan lokacin barci yakeyi.

*****

karfe biyar daidai hidaya ta shigo gidan, hayaniyar data soma ji ne yasa ta dan tsagaita da karasawa part dinta, bangaren taj ta nufa inda take jiyo hayaniyar,budo kofar tayi daidai nan taj ya wullo pillows din da aka jera ma sitting room din, daman wasa suke yi shida barad yanda kasan sa’anni, sabeeha kuma na daga gefe a tsaye tana kallonsu tana murmushi, this is the second time dataga taj din ya futo parlorn ga kuma barad dake wasa tare dashi.

yana ganin wadda ta budo kofar yayi saurin wurgar da pillows din ya nufi inda hidaya take ya rungumeta tsam a jikinshi, barad dai tsoro ya hanashi karasowa inda suke don yana daga nesa.

sabeeha ma saida gabanta ya fadi tsabar tsoron abunda zai buyo baya, hidaya dai kasa gane meke faruwa tayi don by this time tasan barci ya kamata yayi.

‘’first love, kinga old friend dina yau ya dawo, i’m so happy, wasa ma mukeyi’’

saurin banbareshi tayi daga jikinta tana mai kallon sabeeha rai a bace tace ‘’what’s going on here,’’

ganin tana fada yasa taj cewa ‘’first love karkiyi bibi fada please i’m sorry bazan sake ba’’

ko kallon inda yake hidaya batayi ba tana mai kallon sabeeha, ‘’baki bashi medication dinshi bane?’’

‘’na bashi ma’am, an hour ago yasha’’

shuru hidaya tayi tana nazari, meke faruwa ne? to kodai yanxu medication din ya daina mashi aiki ne daman doctor yace za akai lokacin da maganin zai daina masa aiki.

saurin kauda tunanin tayi tana mai kallon barad ‘’wayace ka shugo nan’’ ta karashe cikin fada tana mai fusgo shi, duban sabeeha tayi ‘’take him back to his bedroom now!!’’

tana kaiwa nan ta fuce da barad, tana futa taj ya fashe da kuka,da kyar sabeeha ta jashi suka koma bedroom tana bashi hakuri, ‘’bibi, nayi ma first love laifi, i’m bad boy ko’’

marin fuskanshi ya soma yi yana kuka ‘’i hate my self’’

saurin rike hannunshi sabeeha tayi ta zaunar dashi a kan gadonshi kafin ta soma goge mashi hawayen dake fuskanshi ‘’no friend you’re a very good boy, kuma first love tana sonka sosai kaji, ka daina kuka idan baka son tana fushi dakai;’’

haka ta dunga lallaba shi harya hakura,

washe gari da safe haka jamid ya sake shugowa da sassafe, yana nan zaune sabeeha ta shugo da breakfast dinshi da maganinsa, tana futa jamid ya kwashe magungunan ya boyesu a aljihunsa don kwata kwata jiyan dayaga babu abunda ya faru da taj yasa shi jin bai yarda da medication dinn ba kawai bayan wannan ma har zuwa yanxu baya jin ya yarda da hidaya da wannan doctor din.

wunin ranar kuwa jamid yana tare dashi yana karantarshi tass.

Haka aka shafe sati guda jamid na dauke magungunan taj din yana boyesu ba tare da sabeeha ta sani ba don baya son hidaya tayi blaming dinta, wannan yasa da zarar ta kawo magungunan yake boye su ba tare da sanin kowa ba.

sabeeha dai ba karamin mamaki ta dunga yi ba ganin yanda ta din ya daina barcin kamar yanda ya saba, sai kawai ta fara jin qila ya soma samun sauqi ne

shiyasa ya daina barci kwata kwata bata kawo cewa dauke maganin jamid yakeyi ba.

taj dinma shi kanshi dadi yakeji sosai, ya samu sakewa, kullum yana tare da barad suna wasa, da zarar mamanshi na gaf da dawowa daga aiki kuwa zai fita daga part din gudun kartayi mashi fada, don ta hanashi zuwa wajen taj din kwata kwata.

weekends..

yau weekends kowa yana gida gaba daya, harda hidaya dasu afiya, zaune suke akan dining suna yin break fast, hidaya na hakimce akan kujerarta ta daban, gefenta kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login