Showing 84001 words to 87000 words out of 135321 words

Chapter 29 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

534

samu magaji ba yata ma zata iya gada ta’’

Wannan yasa ya dukufa akanta ya bata ilimin addini dana boko, lokacin da habiba na shekara goma churr aduniya allah ya sake azirtasu da ya mace, wannan karan santuraki bai roki allah akan zabin shi ba, yabarma allah yayi mashi zabin ko mace ko namiji mai albarka don akan habiba ya gane cewa, yara are blessings both maza da mata, albarkarsu ake nema da shiriya wanda shi yafi komai.

 

Bayan suna baby girl taci suna Hajara inda suke kiranta da hajar, habiba nason hajar sosai don koda yaushe tana tare da yar uwarta.

Tasowarsu agaban iyayensu ba da irin tarbiyar da iyayen sukayi masu gwanin ban sha’awa, ga ilimi ga wayewa.

 

Lokacin da habiba ta gama karatun secondary ta nuna wa mahaifinta son zurfafa karatunta, bai hanata ba don haka ya turata kasar waje inda ta karanci engineering kamar shi, bayan shekara bakwai ta dawo da kwalin degree dinta da masters dinta, wannan abu ba karamin dadi yayi ma mahaifin ta ba don tana da basira sosai,koda ta dawo lokacin hajar tana gab da gama secondary school dinta,acikin shekarar santuraki ya nuna son habiba ta fara aiki a company shi, sai alokacin ne mahaifiyarsu ta nuna hakan bai dace ba, abunda ya kamata shine su fara aurar da ita saita fara aikin a gidan mijinta,don duk wata diya mace mutuncinta yana gidan mijinta wannan fadakarwa da amina tayi mashi ba karamin dadi yaji ba, wannan dalilin yasa ya umarci habiba data fito da mijin aure, da farko ta nuna bata so hakan ba don ita karatu ma taso abarta ta karo, saida mamansu ta zauna da ita ta nusar da ita amfanin aure ga diya mace da kuma illolin zamanta haka babu aure.

Sanin bata da manema don bata basu dam aba dukda suna zuwa musamman lokacin da take school wannan yasa ta bama santuraki zabi akan ya zaba mata duk wanda taga ya dace.

Wannan karramawa da tayi mashi ba karamin dadi yaji ba, wannan yasa ya zauna ya mata zabe na gari wanda yasan ko bayan ranshi zai kular mashi da ya, wato dan babban amininsa wanda yake aiki a karkashinsa, shima engineering ya karanta, ta dalilin mahaifinshi ya samu aiki a company SS, tun bayan zuwanshi santuraki ya lura da hazakarshi da kamala ga wayewa, wannan yasa yay aba da halinshi kuma ya bashi yarshi abar sonshi habiba.Bayan yan watanni aka daura auren habiba da Ibrahim,

Bayan auren habiba da shekara guda hajar ta kammala nata karatun inda ta nuna son cigaban karatunta a fannin Islamic kamar mahaifiyarta, wannan abu ba karamin dadi yayi ma mahaifiyarsu da mahaifinsu ba don haka santuraki ya tura ta university of Islamic dake madina a saudi arabia inda tayi shekara biyar curr itama hade da master program dinta kafin ta dawo.

Dawowarta ta tadda abubuwan da dama na farin ciki sun faru, na farko shine yayarta habiba da yayanta biyu, Sameer suna kiranshi da santuraki sai bahijja, sai kuma cikin da take dashi na uku, sai kuma daddy da kamfanin shi yayi multiplying.

Rayuwar wannan ahalin kunshe take da tarin farin ciki da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 43-44

UPDATE!!

Shekaru sunja abubuwa da dama sun sauya,masu dadi da mara dadi, rasuwar mahaifinsu nanne wato alhaji santuraki ba karamin babban rashi bane a wajensu,musamman anne wadda tafi kusanci dashi sosai basu kadai bama harda mutanen duniya da suka sanshi da taimakon alumma, yayi contributing cigaban kasar nigeria sosai, mutanen zazzau sun shaida hakan don yayi abubuwan alkahiri sosai a mahaifar shi.

bayan rasuwar mahaifinsu duk wani nauyi daya shafi harkar ayyukan daya bari ya koma kan anne wadda ta jajirce wajen ganin cigaban kamfaninsa da alkairan da yake yima alumma da taimakon mijinta wato ibrahim.

Anne ta kasance mace mai kwazo, jajairtacci, very powerful,bata wasa da abunda ya shafi ayyukan dake gabanta shiyasa koda yaushe hankalinta na kan ayyukan daya shafi cigaban ahalin su da kamfanin su, don shi ne tattalin arzikinsu, wanda hakan ya kawo mata babban maslaha tsakaninta da ibrahim mijinta, kwata kwata bata da time din familynta ga yaya har uku donma sun taso sun girma sosai,kowanne su ya mallaki hankalinsa,sameer ya tafi karatun soja su bahijja da fadila kuma suna uni, rashin samun kulawarta a matsayin matarsa yasa ya fara sha’awar kara aure, lokacin daya fada mata yana neman aure ba karamin shiga wani hali tayi ba kuma tasan dalilinshi na hakan don ya umarci ta zabi tsakanin aikin ta na kula kamfanin mahaifinta ko kuma iyalanta, shi kanshi yasan baiyi mata adalci ba daya bata zabinnan ita kuwa batajin zata taba sakin kamfanin mahaifin nata hannun mutane, na jikinka ma zai iya komai ya cutar dakai balle kuma bare don haka ta bashi damar karo duk macen da yake so.

Bayan auren ibrahim da salamatu, anne ta shiga wani hali sosai don macece mai zafin kishi, gashi nanna bata kusa da ita balle ta tausasa ta don bata kasar ma gaba daya.

a sannu a hankali ta tattara wannan kishin nata ta ajiye a gefe guda ganin bashi da wani amfani, matar daya auro ma babu abunda zata nuna mata, kyau arziki da asali duk ta fita wannan yasa ta maida hankalinta kan ayyukanta.

bangaren ibrahim, bayan aure ya samu abunda yake nema don salamtu bata aikin komai, full time house wife, wannan ne aurenta na biyu don ta taba aure harda diya mace (laila) wadda ta taho da ita nan gidan don itama ta lashi arzikin masu arziki.

salamatu irin matan nan ne masu son abun duniya da baqin ciki ga kyashi a zuciyarta,auren ibrahim datayi tayishi ne kawai don itama da diyarta su hau sahun masu arziki dukda basu fito cikin arzikin ba saidai rufun asiri.

lokacin da salamatu ta fuskanshi yanayin gidan da arzikin gidan yana karkashin kishiyarta wato anne nan ne ta fara tunanin yanda zatayi diyarta ta auri babban dan gidan wato sameer, tsakanin yaran gidan kuwa basa jituwa kwata kwata dukda kowa part dinshi daban a gidan hakan baisa su fadila taya mahaifiyarsu kishi ba, gashi papa (ibrahim) kenan ya hada laila(agola) dasu fadila don kusan shekarunsu daya, makarantarta da komai nata ya dawo hannunshi, duk abunda zaiyi ma yayanshi yana hadawa da ita babu banbanci, anne na sane da wannan bata taba tankashi ba saidai duk abunda ya shafi yayenta bata hadawa da laila kwata kwata don batayi accepting wata agola a cikin familyn ba.

Haka suka taso bahijja ce kawai ke dan kula laila don tana da sauqin kai sosai sannan bata da hayaniya har suka dan saba, fadila ce mai zafi sosai basa shiri kwata kwata.

Bayan wasu yan shekaru sameer ya dawo, inda ya samu daukaka sosai ya zama young second lead major at the age of 29, very responsible and hondsome lokacin kuma matan gidan na gab da gama university.

tunda salamatu ta kyalla ido a kanshi ta dauki alqawarin bazata bar wannan babban kamun ba saiya auri diyarta kota halin qaqa, 

a sannu a hankali ta dunga shige mashi sosai da yake bashi da damuwa sai ya zamana yana shiri da ita tunda itama matar mahaifinshi ce, maganr so kuwa bai taba shiga tsakaninshi da laila ba don kallon qanwa yake mata kamar yanda yake kallon su bahijja da fadila.

salamatu bata yi kasa a gwiwa ba, haka ta dage saida ta shusa laila ga sameer, harya fara noticing dinta, lokaci guda kuma aka wayi gari sameer da laila na soyayya kamar ransu, yana masifar sonta sosai haka zalika itama tana sonshi kamar ranta.

Anne bata san da wannan ba kwata kwata, saida abu ya fito fili, ba karamin rikici aka samu ba tsakanin anne dashi sameer akan laila inda ta shaida ,mashi bazai taba auren yar kishiyarta ba kuma agola a gidan, amincewarta daidai yake da daukewar nunfashi ma’ana saidai bayan ranta,babu yanda baiyi ba don ganin yayi pursuing dinta abun yaci tura har saida papa ya shugo cikin alamarin, inda ya nuna mata cikar iko akan yayansa kuma auren sameer da laila ko tana so ko bata so sai anyi shi, wannan abu yayi ma anne ciwo sosai don ibrahim bai taba yi mata irin haka ba sai a wannan karan.

Abunda yafi damun anne kuwa shine yanda sameer ya dage akan laila kuma ya bijire mata, karshe dai haka ta hakura akayi auren inda aka basu part dinsu daban dake cikin babban gidan nasu, wannan yasa fadila bata shiri da laila don kwata kwata bata sonta da yayan nata. 

bangaren salamatu kuwa sai a lokacin hankalinta ya kwanta ta samu abunda take buri after all the effort, yanxu koba komai dai diyarta ta shige cikinsu kuma babu wanda ya isa ya raba auren nan idan har tana da rai.

Bayan shekara guda laila ta haifi danta na farko sufyan.

su bahijja bayan sun kammala karatunsu ta bayyanar da majeed ga iyayenta, majeed asalin dan lebanon ne,mahaifanshi haifafun kasar lebanon ne, dalilin zuwansu nigeria kuwa shine kasuwanci mahaifinsu inda suka shafe shekara biyar anan nigeria, sannan zamansu ba zaman dindindin bane don zasu iya komawa kasarsu a koda yaushe, majeed shine dansu na farko sannan yana da qanne biyu mata.

majeed da bahijja sun dauki shekara biyu suna soyayya tun tana university, ba karamin so take mashi ba shima hakan take ta bangaren shi.

Lokacin data bayyanar dashi ga papa yayi murna sosai saidai akasin haka data samu daga wajen anne, furr taqi amincewa don arranged marriage taso yi mata da dan wani babban mutun dake investing a kamfanin su, kuma sai abun yazo a daidai shima yaron yana son bahijja sosai tunda babanshi yakai mashi hotonta da proposal din auren ta.

lokaci guda bahijja ta firgice ta chanza sosai saboda anne ta hanata kusanci da majeed sannan tayi alkawarin idan har ta fada ma papa akan wannan zata iya tsine mata.

ba karamin tashin hankali majeed shima ya shiga ba son yana masifar son bahijja, daman yasan za a iya samun irin wannan misunderstanding din kuma ba kowa ne zai iya bada diyarshi ba saboda su ba mazauna nan bane zasu iya tafiya akoda yaushe, atunaninshi wannan dalilin yasa anne taqi amincewa da aurensu.

bangaren anne wannan ma yana daga cikin dalilin dayasa taqi amincewa don tayi dogon buncike akan majeed din don sanin koshi waye da asalinsa, bayan wannan ma tana da burin yayanta su zauna kusa da ita gaba daya cikin family house saidai hakan bazai samu ba koda ta amince da auren majed din da bahijjan saboda dole wata rana zai dauke bahijja su koma lebanon.

karshe dai haka papa yasan da zancen, for the second time yayi rantsuwa akan babu wanda ya isa yayi ma yayanshi tilas don haka ya tambayi bahijja inhar da gaske tana son majeed kuma zata aure shi sannan zata iya binshi koda kuwa yabar kasar nan ya koma mahaifarshi, take kuwa ta amince babu wani dogon nazari, haka ta sadaukar da kudirin mahaifiyarta akan majeed don ko ayau bata auri majeed ba bazata taba iya zaman arranged marriage ba da wanda bata so kuma tasan rayuwar ta ne zai salwanta don bazata taba son wanda za a hada ta dashi ba, haka ta amince dukda tana sane da sharadin da anne ta bata na cewa bata kuma babu ita, zata manta cewa tana da ya mai suna bahijja. 

Papa ne ya tsaya masu har akayi auren su, inda aka basu part anan cikin gidan suma don su zauna da amincewar shi majeed din, don yayi alqawarin sai ya daidaita tsakanin bahijja da anne.

a shekarar akayi auren fadila itama da dan aminiyar anne jafar, anne taji dadin wannan hadin don family jafar suna da arziki da sanayya sosai kuma suma suna da connection don haka ta amince.

bayan auren fadila da shekara ta haifi danta na farko hamad, ashekarar laila itama ta sake haihuwa inda ta haifi second born dinta abal, bahijja dai shuru babu labari, haka aka shafe shekaru har fadila ta sake samun wani cikin harta haifi diyarta kyakyawa wadda aka sanya mata suna (laila) takwarar sirikar fadila.

 That same year babban rashi ya riskesu, Allah yayi ma papa rasuwa dalilin hadarin mota, wannan mutuwa ta girgiza su sosai, bayan mutuwarshi da yan watanni bahijja  ta samu ciki itama after so many years of trying, ba karamin dadi yan uwanta sukaji ba, salamatu kuwa bayan tayima papa takaba ta tattara tabar gidan ta koma garinsu wajen danginta, koba komai dai tabar diyarta cikin arxiki, tsakanin bahijja da anne kuwa babu abunda ya sauya kwata kwata, haka ta dunga rainon cikin nan nata, ita da majeed kuwa ba karamin so suka daurama wannan unborn baby dinma,bayan wata tara a haife diyarta kyakyawa inda taci suna habiba takwarar anne kenan, suna kiranta da maya.

maya nada shekara biyu tafiyar majeed da ahalinshi ta tashi zuwa lebanon, wannan rana ta kasance rana mafi baqin ciki a rayuwar bahijja da anne don sai a ranar suka ga tsantsar tsanar datake ma majeed, haka suka bar kasar zuwa lebanon, zaman shekara guda sukayi achan majeed ya samu aiki a US inda suka tattara shida iyalinshi suka koma US.

Bayan tafiyarsu bahijja, laila ta sake haihuwa inda ta haifi mace inti wadda ayanxu take 7yrs, yanxu yayanta uku da sameer, sufyan wanda yake 25yrs ayanxu sai kuma abal dake da shekaru 23yr, sai inti last born. bayan haihuwar inti uncle sameer ya sake aure inda ya auri mubina,itama dai yar masu hannu da shuri ce, yayanta biyu itama dashi amla 5yrs sai mubin 2yrs wanda yaci sunan marigayi papa(ibrahim).

fadila ma tun haihuwar hamad wanda yake 23yrs da laila wadda take 19yr ayanxu allah bai sake bata haihuwa ba.

Wannan ne ahalin Anne da nanna………

Saudi**

saurin bude kofar motar akayi wanda ya bama wanda ke zaune damar futowa,sanye yake da riga da wando baqaqe sai wata hula kamar malafa, hannunshi rike da wata sanda sai shades glass baki daya sanya akan fuskanshi, cikin saurin mataimakinshi ya ya zagayo ya tsaya daga bayanshi kafin su shige cikin warehouse din.

wajen tsit baka jin komai sai kukan tsintsaye, gashi garin ya soma duhu,driver daya budema mutumin mota ne ya koma cikin motar ya kulle bam yana jinjina kai.

suna shiga cikin warehouse din mataimakin mutumin ya bude kofar wani daki, dakin bau babu haske kwata kwata sai dan banzan duhu, wani abu ya latsa daga waje take haske ya damaimaiye dakin.

 cikin dakin suka wuce inda mutumin ya tsaya ya sanya gloves a hannunshi tare da miqama mataimakin nashi sandarsa da yake rike da ita a hannunshi wadda ke taimaka mashi wajen takawa don yana dan dingisawa.

takowa ya soma yi harya shigo tsakiyan dakin yana mai kallon both sides of the spaces kura duk ta gama cika dakin ga wani uban zafi da dakin keyi ga wari dake tashi, mutane ne guda biyu a daure a kasa, sun jigata sosai an masu jina jina gaba dayansu ko motsawa basa iyayi tsabar wahala, muryar macen data farfado ne ya soma karade wajen ‘’dan allah ki sakeni na tafi, wallahi nayi alkawari bazaku sake ganina anan kasar ba, garin mu zan koma, dan allah karku kasheni’’

inda macen take mutumin ya nufa kai tsaye ya tsaya a gabanta ya sanya kafarshi ya shureta don a kwance take ta kasa motsawa, tsugunnawa yayi a gabanta inda ya sanya hannunshi daya ya dagota yana mai kallonta, nima dai maida dubana nayi gareta, gaba daya kamanninta ya sauya fuskarta duk an faffasa.

bakinta mutumin ya danqo babu imani ya matse fuskar ya soma magana ‘’babu wanda ya taba min aiki na barshi ya tafi da ranshi, koda kuwa aikin da yayi min anyi nasara, don bana barin abunda zai zamo min matsala nan gaba’’

bakinta na karkarwa ga jini dankare daya bushe a lebenta data kwana kusan goma bata sanya mashi ruwa ba tace ‘’oga…na roke ka kamin rai, mamana bata da lafiya, gashi inada qanne har guda hudu, wallahi basu da kowa saini achan ghana,aikin da nake yi anan ne kawai nake amfani dashi wajen taimaka masu, dan allah karka kasheni, wallahi i promise babu wanda zai san nayi maka aiki, babu wanda zai san abunda ya kaini taheel family na rokeka sir dan allah karka kashe ni’’ ta karashe tana hawaye, sai a lokacin danaji tayi maganar ghana na lura da ita da kyau, innalillahi ashe yar ghana ce, ita kuwa mai ya hadata da waennan???

wata iriyar dariya mutumin ya soma yi abun tsoro ba dadin sauraro mai sanya furgici, take jikinta ya soma tsuma, ‘’kin bani reason din da zaisa na kasheki dukda kasheki ba komai bane a wajena,bayan aikin dana turaki bakiyi min shi da kyau ba…hahahaha’’ ya sake yin wata dariya irin ta tattattun mugaye marasa imani.

mikewa yayi tsaye yana mai daga hannunshi, mataimakin nashi ne ya karaso ya miqa mashi wata yar bindiga mai silencer, yana bashi ya jaa bullet din ya saita kanta, baiyi wata wata ba ya harbeta pauu, babu imani yana kallo ta sulale jini na bin tsakiyar kanta daya harba.

ihun da akayi ne yasa ya maida dubanshi ga dayan barin, wanda aka daure ne shima ya gama furgicewa don bai farka ba sai yanxu tun bayan azabar da aka gana mashi, cikin sauri ya miqe zaune yana rokon mutumin ‘’sir dan allah kamin rai, ka fada min duk abunda kake so zanyi maka, zan kashe maka kowa just tell me what to do, but na roki abarni da raina in exchange’’

dariya mutumin ya sakeyi ‘’har kanada ikon yin yarjejeniya dani?, asking for something in exchange?,’’

‘’oga dan allah kayi hakuri, wallahi zan iyayi maka komai as a reporter ka fada min zanyi komai, zan buga jarida da manya manya shaidu wanda ina tabbatar maka zai kawo downfall din taheels,’’

wani abu mutumin ya soma yi da hakorinshi yana mai takowa inda mutumin yake ‘’kayi wasa da damarka reporter steve, ka fada min kan cewa jaridar daka buga akan taheel heir will work and zai dauka hankalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login