Showing 102001 words to 105000 words out of 135321 words

Chapter 35 - Matar Taj Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

515

mashi kaya, bata yarda kowace maid tayi hidimar data shafi taj din ita ke komai tun bayan abunda ya faru, yanxu haka ma ta wanke masa wasu abubuwan daga cikin kayansa irinsu shorts haka da fararen kayan da yake yawan sawa koda yaushe,tana saukowa da kayan tabi wajen laundry room, ashe yana hangenta daga part dinsu daman fadwa bata nan, batasan ya karaso cikin laudry room dinba sai ganinshi kawai tayi a bayanta, saurin hade rai tayi, bayan ta gaisheshi ta cigaba da abunda ya kaita, da mamaki kawai taji hannunshi kan nata,’’may i help you my lady’’ ya furta 

 bin hannun tayi da kallo kafin ta maidashi kanshi ya kanne mata idanu disgustingly, rai a bace ta zame hannunta ta fuce daga wajen.

tundaga lokacin ta fuskanci yana nemanta da sharri ne wannan yasa take kaurace mashi.

Abuja nigeria…

tunda maya ta zo gidan ya zama lively, sabo ya shiga tsakaninta da nanne sosai harda anty fadila, kullum tana gidan anty fadila, tsakanin matan uncle sameer kuwa tafi shiri da anty laila kamar uwar dakinta haka ta maidata, itama lailan na

sonta sosai saboda bahijja, bangaren hamad kuwa bata shiri dashi kwata kwata dama dama abal, tafi shiri dashi don yanada faran faran sosai, haka zalika sufyan shi bai cika shiga huruminta ba.

kullum daddy da mummy suna kiranta a waya, ayanxu mummy ta hakura da decision din daddy bayan ya zauna yayi mata bayanin dalilin da yasa ya yanke tura maya nigeria.

maganar makarantarta kuwa uncle sameer da kanshi ya nema masu university ita da laila a baze university, same course under business, kullum hamad ke kaisu ya dauko su, duk sanda za a tafi kuwa sai ansha drama, saboda duk yanda maya zatayi saitasan yanda tayi ta bata mashi rai ko ta kunna shi danma baya biye mata saboda baya son raini saidai shima idan ya tashi haka yake kunsa mata basa shiri kwata kwata.

duk cikin gidan da anty mubina ne basa shiri saboda aunty laila ta gama bata ta a wajen maya, ko yayanta ma bata wasa dasu kota jasu a jiki kwata kwata,anne kuwa ta dan rage zafin haushin iyayenta daya shafeta datake ji saidai kwata kwata bata jan mayan a jiki shiyasa tafi son nanna sosai itama.....

Matar Taj (destined with you

🩵🤍

)

   Written by 

          Queenmarh

✍️

Free page

Chapter 51

UPDATE!!

Taheel’s resident 9pm.

zaune suke suna kallon movie na avengers,gaba daya attentions dinsu yana ga screen, tsakanin taj da barad sai bet sukeyi akan wanda zaiyi surviving, sabeeha na daga cikin bedroom tana ninke kayan taj, saida ta gama tsaf ta rufe closet din nashi ta futo ta fara gyaran wajen da zai kwanta daman 10 dot suke kwanciya basa wuce hakan.

Tana sanye da hijab har kasa ta futo daga bedroom din inda ta taddasu zaune, karasowa tayi ta zaune gefen barad shi kuma taj yana daga dayan bangaren ya sanya hannunshi kan kumatunshi idanunshi kwii akan tv, duk basu lura da ita ba saida sukaji dariyarta tana kokarin katse masu attention din da suka bama tv,

cikin tsokana tayi abun don haka suka juyo suka kalleta a tare suna mai kiran sunanta  ashagwaba, ‘’bibi, aunty!!’’

‘’sorry’’ ta basu hakuri,tana mai kama kumatunta karar bude kofa da shugowar jamid yasa suka bishi da kallo gaba dayansu, saurin miqewa sabeeha tayi fusknata dauke da murmushi ta soma gaishesa suma suka gaisshesa gaba dayansu, dadin ganinsu haka yaji sosai.

pack din dake hannunshi ya miqa ma sabeeha, inda ta karba tayi mashi godiya dukda batasan menene a ciki ba.

‘’khaal yace a kawo maki, laptop ne da waya wadda zakiyi amfani dashi wajen koyon karatu, zuwa monday zaki fara online training’’

cikin murna sabeeha tayi mashi godiya sosai, ‘’aunty zan iya daukan nawa  system din tunda an saya maki sabo’’ barad ya tambayeta excitedly

‘’yes barad, thank you’’ ta amsa shi, daman da nashi take karatu da koyon yanda ake operating laptop din, shine ke koya mata, wani abun mamaki tun yana da shekara goma aka koya mashi yanda zaiyi operating system.

jinkirtawa jamid yayi yana son yi mata wata magana saidai ya kasa, chan dai ya tattara courage dinshi ya zaro wayar dake cikin aljihunshi ya miqa mata, take gabanta ya bada wani damm, babu yanda za ayi ta manta da wannan wayar da yan lekan asirin nan suka bata, ‘’naki ne ko’’ ya tambayeta

saurin sunkuyar da kanta kasa tayi tana faman zazzare idanu kamar mara gaskia, ‘’i’m so sorry, bada niyyana na bunciki kayankiba ba tare da saninki ba, i had to do it, amma inason nasan ya akayi kike ajiye da waya?’’

daburcewa tayi sai ayanxu ta gano ashe shine ya ceceta lokacin da aka so kulla mata sharri, wani iri taji a ranta, yanxu mey zata ce mashi? gashi yana tambayar yanda akayi ta samu waya bayan kowa yasan yan aiki basa rike waya a gidan.

‘’fatima,!! ya kira sunanta, saurin dagowa tayi, harga allah bata son yi mashi karya don dole ta runtse idanunta ta soma magana, ‘’daman..daman ina kiran mamana ne a boye, bansan ta yadda zanyi communicating da ita ba shiyasa na shugo da ita gidan kuma na boye ba tareda kowa ya sani ba’’

sauke ajiyar zuciya yayi tare da cewa ‘’i’m so sorry you had to go through all this’’,girgiza mashi kai kawai tayi tare dayi mashi godiya ta amshi wayar suka fita daga bangaren shida barad.

suna fita ta juya zuwa bedroom dinsu, tana shiga ta zauna a kan carpet tana mai bude package din, brand new laptop ce mai kyau sai waya,excitedly ta soma bude kwalayen, shuru tayi tana mai nazari rayuwar ta cikin watanninin nan, abunda bata taba tsammani ba suke faruwa cikin rayuwarta, gani ma take kamar she doesnt deserve all of this, mutanen da basu santa ba basu san daga ina take ba sun dauki yarda da amana sun bata,sun sauya rayuwarta gaba daya, khaal ya bata komai, gashi yanxu har karatu sukayi mata providing wanda zatayi a gida hankali kwance, sannan khaal ya kaita asibiti an mata treating wannan hakoran nata da suka zama insecurity dinta gaba daya rayuwarta.

hawaye ta soma yi tunawa da dalilin zuwanta gidan, harga allah batayi masu adalci ba kwata kwata musamman ma yanxu datayi ma jamid karya, watarana dole asirinta zai tonu matsayin yar tonan asiri da aka kawota gidan, tuna wannan kadai yana breaking zuciyarta sosai, saida tayi kuka mai isarta kafin ta lallaba ta wanke fuskanta ta futo daga bedroom din ganin wajen kusan 10 ta gifta bayan ta tattara wyar da laptop din ta ajiye.

‘’didi it’s time to sleep!’’ta kira taj bayan ta karaso parlor, baima san tana yi ba ya kura ma tv idanu kamar idanun nashi zasu fiddo waje, gashi ya hade kafafunshi ya saki baki yana kallo, hannunshi nakan remote, gyangyadi ya soma dibanshi bai sani ba ya danne remote din wanda hakan yasa ya sauya channel din ba tare da sanin shi , hannunshi nashi ma ya kasa dagashi daga kan remote din, tun daga lokacin barcin ya tafi daga idanunshi ya kafa ma screen idanu, daman tasan kiran duniya idan tayi mashi bazai amsa ta indai yana kallon tv wannan yasa ta nufi wajen socket din direct, dago da idanun da zatayi kenan kuwa idanunta ya sauka akan screen din, kanta bai gama tantance abunda ke wakana a cikin tv ba saida taji sautin  numfashi da moarn wanda ya sata zaro idanu kwal, a furgice tayi saurin kashewa dipp tare da juyowa tana mai kallon taj din, yanda take kallonshi haka yake kallonta daga sama har kasa, tashin hankali kenan, wato wani sexual adult program akeyi tsakanin mace da namiji suna making love, abun yayi nisa badan ta kashe ba da tuni anyi aika aika don har an kaiga tube tuben kaya, bangaren taj din, gaba daya ya zama confuse da abunda ya gani ayanxu, abun yafi karfin kwakwalwarshi, haka ya dunga nazarin abunda idanunshi ya gane masa, katse mashi tunanin da yakeyi tayi ‘’time for sleep’’ tana kaiwa nan ta wuce bedroom din, mikewa yayi yabi bayanta zuwa bedroom din, sai zuwa yanxu ya soma jin barci na dawo mashi.

lokacin daya karaso harta gama shimfida abun kwanciyarta a kasa daman duvet ne take shimfidawa saitayi kwanciyarta ta lulluba da bargo shi kuma yana kan gado.

tsayawa yayi a gabanta tayi saurin kauda idanunta akanshi, ‘’bibi  a cikin tv daxu naga wasu suna shan baki,kuma sun cire kaya meysa sukeyin…’’

saurin katseshi tayi ‘’kaje kayi freshen up’’ yanda ta umarceshi hakan yayi kuwa ya wuce bathroom ta bishi da kallo, taj baya taba ganin abu yayi shuru musamman abunda bai gane ba sai yayi ta tambaya,yanxu hakan ma ta tabbatar tambayar da zaiyi mata kenan tayi saurin katse shi, nazari ta soma yi, ya akayi ya sauya channel dinma?ita kanta saida ta girgiza balle kuma shi, ‘’kai wani iskaci sai turawa’’ ta furta tana mairage hasken dakin nasu.

futowa yayi daga bathroom bayan yayi brush yayi wanka ya sauya kaya zuwa na barci, wucewa kan gadon shi yayi direct ya kwanta tare da janyo duvet dinshi, juyo da kanshi yayi bakin gado wajen da sabeeha ke kwance ya kura mata idanu, ‘’bibi..bibi’’  shuru babu response wannan ya tabbatar amshi da tayi barci don haka ya turo bakinshi a shagwabe yace ‘’goodnight bibi’’ sannan shima ya rufe idanunshi.

sabeeha na jinshi tayi banza dashi don bata son ya maimaita mata maganar dazu wannan yasa tayi kamar barci ya dauketa.

karfe biyar da rabi daidai ta bude idanunta, kiran sunan allah ta farayi kafin ta miqe zaune, nauyi dataji kan cikinta yasa ta duban wajen,hannun data gani ne yasa ta razana sosai ta janye duvet din baya, take fuskan taj ta bayyana da batayi mamakin ganinshi ba don sometimes haka yake mata musamman idan yayi mafarki ya tsorata sai ya dawo kasan ya kwanta kusa da ita saidai yau abunda yafi bata mamaki shine yanda ya kanainayeta kamar wanda zai shige ciki, ya saqalo hannunshi a cikinta.

cije lebenta tayi ta fara kokarin janye hannunshi da gashi ke kwance luff ta kasa saboda nauyi gashi saima kara damke cikin nata daya dunga yi.

tashinsa ta somayi ‘’didi,…didi…wakeup’’

bude idanunshi yayi ahakali, daman lightsleeper ne bashida nauyin barci sosai, ‘’good morning bibi na’’

‘’morning ta amsa shi tana allah allah ya miqe saboda ta samu itama ta tashi, ya dauka kusan minti biyu bai tashi ba, saima kallonta daya dunga yi yana tuna mafarkin da yayi, irin abunda ya gani a tv jiya da daddare, ‘’lokacin salla yayi ka tashi muyi sallah’’ ta katse mashi tunanin nashi.

bai musa mata ba ya tashi zaune, yana zame hannunshi kuwa ta miqe yar firit da ita ta wuce bathroom din direct.

fitsari tayi, sai a lokacin ta lura da digon jinin, shap tama manta da zuwan aladarta a wannan lokacin don haka tayi wanka ta daura hijab kawai saboda kayanta sun dan baci,ta futo daga bathroom din, a zaune ta taddashi ya dafe kumatunshi ya kafa ma kofar bathroom din idanu harta futo, tundaga sama har kasa yake kallonta kamar yau ya taba ganinta har idanunshi suka sauka akan kirjinta da hijab ya lafe akai, take scene din daya kalla jiya ya dawo mashi wanda ya kasa futa daga kanshi, ganin yanda yake kallonta yasa ta kare jikinta  ‘’ka shiga kayi alwala’’

kamar yanda tace kuwa haka yabi umarninta ya mike zuwa bathroom din inda yana shiga ta sauya kaya ta zauna jiran futowarshi…..

Komawa sukayi barci sai wajen karfe goma, sabeeha ce ta fara farkawa ganin he’s fast asleep yasa ta shige bathroom ta barshi anan kasan.

A gurguje ta tube kayan jikinta ta daura towel da shower cap kapin ta shige wajen shower tare da rufo glass din.

Ruwa mai dumin gaske ta sakarma kanta, takai wajen minti ashirin kafin ta gama, ta sauya pad sannan ta nado towel a jikinta kafin ta bude shower glass din ta fito, tana fitowa tayi kicibus da taj a zaune kan wc, a razane tayi baya cikin hanzari ta koma cikin shower din, kwata kwata batayi tsammanin ganinshi ba, allah yaso ma bata futo haka ba bbu towel da tuni shikennan yaga jikinta da take masifar kunya.

, “meysa bakayi knocking ba ka shugo”

“Wiwi nakeji i cant hold it” ya bata amsa kai tsaye ko a jikinshi, “toh kayi sauri ka fita”

Bai ansata ba ya cigaba da abunda yake yana gamawa ya futa.

Saida ta tabbatar ya futa ta fito, hijab dinta dake kan rail janyo ta zumbula kafin ta fito.

Closet ta shiga ta dauka kaya kafin ta koma bathroom din ta saka kayan, lokacin data futo yana daga tsaye sai faman safa da marwa yake tsakanin dakin.

“Bibi I’m hungry” ya fada a shagwabe

Ba tare da ta kalleshi ba ta nufi wajen shinfidar da take kwanciya ta tattare su “ka shiga kayi wanka first”

“Tohm ya amsa ta kafinta ya shige bathroom din ita kuma ta fita bayan ta gyara inda suka kwanta.

Kitchen ta nufa ta dafa masu very simple meal, tana gamawa ya shugo kitchen din ya taddata anan ma sukaci breakfast din ta wanke kwanukan kafin su fito.

Daidai wajen sitting room ya tsaya yana mai dubanta yace “bibi lets have a race, na fiki muga wayafi gudu sosai jiya ma haka na wuce barad”

Dariya sabeeh tayi kafin tace” hmmm, are you sure ka fini iya gudu?”

“Yes bibi, mu gwada mu gani, idan naci zakiyi backing dina, idan ke kikaci ni zanyi backing dinki deal?”

Da mamaki take kallonshi, yanxu ya fara sauyawa sosai ba kamar da ba, daga yanayin yanda yake magana ma da wasu abubuwan hakan kuwa ba karamin dadi yake mata ba don great achievement ne, kuma duk therapy din da ake kaishi ne.

“Okay deal” ta miqa mashi hannunta, chapewa yayi kafin ya soma shiri kamar da gaske harda dan duqawa don ya fita tsayi sosai, sabeeha dai babu abunda take sai dariya don he looks so serious about it.

“On a count of 1..2..” baima kaiga cewa 3 ba ta arce, ganin haka ya sashi binta a guje, yana karasowa cikin dakin ya tsaya yana haki harda bubuga kafa cikin shagwabar daya saba yi mata yace “bibi youre a cheater, kinyi cheat”

Gwalo tayi mashi tana mai kyalkyacewa da dariya “nadai rigaka”

Cikin fushi ya wuce kan gado ya zauna harda murguda mata baki, ita ko mai zatayi banda dariya, saida tayi mai isarta kafin ta tako inda yake ta zauna a gefenshi “haba didi na, toh I’m sorry kaji? Next time bazanyi cheating ba promise”

Fuskanshi ta janyo daidai saitin tata tana mai sauke mashi murmushi “toh ka daina fushi kaji” tayi mashi irin fuskan tausayin nan, murmushi yayi mata kafin ya miqe hannunshi na cikin nata itama ta miqe, baiyi wata wata ba ya daga ta sama chak ya tallabo ass dinta ya soma jujuyata a sama yana dariya, “na shiga uku saukeni hajijiya nakeji” bai saurara mata ba haka ya dunga jujuyata yana dariya, saida ya tabbatar ta jigata kafin ya sauketa yace “nima na rama”

Yana sauketa ta soma layi kamar yar maye hakan ya sashi dariya sosai harda kama ciki, saida ta dawo daidai ta dubi fuskanshi da yaketa kyakyatawa, harta shagala, wato yana da wani irin kyau ne na musamman, at times idan tana kallon fuskanshi bata san daukewa, haka kawai kyawun shi ke burgeta.

Wunin ranar haka sukayi shi yana tsakanarta tana tsokanarshi, barad bai shigo part dinsu ba saboda school day ne.

Ranar monday ta fara online studies da taimakon jamid, shine yayi mata preparation din komai,karatu cikin sauqi har cikin gida babu wani wahala. da farko ta dansha wahala har tazo ta fara gane karatun ahankali.

ta bangaren routine dinta babu abunda ya sauya, haka zalika hidimar taj ma.

****

firgigi ya farka, yau kwana uku kenan ajere yana same mafarkin dake confusing dinshi, saukowa yayi daga kan gadonshi ya zauna gefen sabeeha, kiran sunanta ya somayi dake tana da dan nauyin barci wannan yasa batajishi ba kwata kwata, yau ko hasken dakin ma bata kashe ba saboda a gajiye ta wuni, ga mood swing daya sakata a gaba da dan cramps na ciwon mara tana shan pain killer ta kwanta, shine ma yayi dosing dinta off, ko hijab dinma yau bata sa ba haka tayi kwanciyarta da rigar barci doguwa mai dogon hannu, tunda ya zuba mata idanu ya kasa daukewa, haka ya dunga kallonta daga sama har kasan,fararen cinyoyinta tass  sun bayyana saboda yanayin kwanciyar datayi.

wani irin sabon alamari ya soma ji tun daga tsakiyan kanshi zuwa gangar jikinshi wanda ya kasa gane ko menene,da zarar ya rufe idanunshi flash din mafarkin daya dunga yi ne yake mashi gizo, sai kawai ya fashe da kuka, sama sama ta soma jin kukan nashi a kunenta wanda ya sata saurin bude idanunta ganinshi zaune a kasa.

‘’didi what’s wrong meke damunka’’ ta tambayeshi, shuru yayi ya kasa bata amsa don baima san menene ke damunshi ba, hannunta ta sanya wajen fuskanshi ta shafa donjin ko zazzabi yakeyi, babu wani zafi a jikinshi don haka ta sake tambayarshi, ‘’didi meke damunka ka fadamin mana’’

‘’nima ban sani ba, i feel so weak bibi’’ ya bata amsa yana matse kafafunshi, ta lura da wannan matse kafan da yakeyi cikin kwanakin nan batun yanxu ba saidai bata san ko me hakan ke nufi ba, ‘’menene a kafanka?’’ta tambayeshi kai tsaye, girgiza mata kai yayi tare da jan hannunta zuwa wajen, haka ta dunga binshi da idanu kamar doluwa harya sauke hannunshi wajen mararshi ‘’yana min ciwo inajin zafi’’

saurin zame hannunta tayi a wajen da mamaki take kallonshi, mey zaisashi ciwon mara shima? tambayar data dunga yima kanta kenan, ‘’sorry kaji, kayi barci zai daina, tashi ka kwanta’’

‘’no, anan zan kwanta wajenki’’ ya bata amsa, babu yanda batayi ba dashi yaqi yarda ya kwanta dan dole haka ta hakura tabarshi anan kusa da ita.

Haka yauma suka kwanta tana tashi ta ganshi kan kirjinta kamar wanda ake shayarwa, hankali kwance yake sauke nunfashi yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login