Showing 30001 words to 33000 words out of 176046 words

Chapter 11 - Sakayya 1 Hausa Novel Complete

ba daɗi da Addah Khausi bata nan”.
Murmushi Momy tayi cike da ƙaunar 'ya'yan nata da kuma yanda suke nunawa juna kulawa tace.
“Yau kuma?,Ko da yake dama haka kuke bakwa shiri sannan bakwa san rabuwa da juna”.

Fuska ya Marerece kafin yace.
“Allah yau gidan babu daɗi yau tunda gari Ya waye babu wanda yace min Haiydar kar kayi kaza, Haiydar zo in aikeka, Haiydar bakaji, Haiydar karenani, Haiydar kada fa kaci komai wurinsu Umma, Haiydar ban girme ka bane kam wai da in na saka abu bazakayi ba, Yau duk babu wanda ya faɗa min haka nayi missing ɗinta! Sosai wlh Momy Ina son Adda Khausi”.
Murmushi mai cike da shauƙi Momy tayi tare da zuba musu ido.

Raudat da shigowarta kenan ta Shagwaɓe fuska tace.
“Wallahi nima nayi kewarta Mommy yaukam tare zamu kwana ko?”.
Janyo hannunta Momy tayi tace.
“Autanah ba dole ba yau In kwana dake tunda Addah Khausar bata nan”.

Haiydar ne ya sake kallon Momy cikin yanayin kewar 'yar uwarsa yace.
“Momy dan Allah ki kira kice ta dawo munyi missing ɗin ta”.
Ramadan da Raudat suma sukayi saurin cewa.
“Please Momy ki kira”.
Kai Momy ta girgiza tace.
“Basu da network sai dai idan sunje wajen bishiyar ƙare magarka sun kira”.
Ramadan yace.
“Toh yanzu Mommy Gobe wa zai Miki shara?,da wanke-wanke da kuma gyaran falo?”.

Murmushi Momy tayi tana shafa kansa tace.
“Zanyi ƙoƙari nayi da kaina”.
Zare Ido Ramadan yayi yace.
“To wallahi Momy aɗauko Miki Addah Khausi yafi Miki gidan babu daɗi idan bata nan”.
Murmushi tayi tace.
“Toh”,Da haka hiran yazo ƙarshe Haiydar ya miƙe kana ya ɗauki Ramadan suka tafi ɗakinsu wanda zai ka fita falon Momy ƙofar nasu na jere da ƙofar falonta,
ita kuma Raudat gadon ta hau ta kwanta gefen Momyn.

Acan ɓangaren su Moddibo kuwa.
Zaune yake Atsarerren falonsa da yagaji da tsaruwa kana yana fitar da sihirtaccen ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa.
Yayin da M Jameel ke kwance akan 3sitter da waya maƙale akunnensa, Anutse Moddibo ya juya ya zuba masa Idanunsa tare tsarasa da su, still wayan yake Amsawa ɗauke kansa yayi ya cigaba da operating system ɗin sa kana ahankali ya sake maida Kallonsa kan M Jameel still wayar ne maƙale akunnensa.

Cikin ga jiyawa da wayar da yake yi Moddibo ya zuba masa idanunsa tare da motsa laɓɓansa da suka sake yin pinch kana suka tattare saboda tsananin sanyi da akeyi yace.
“Wai kai da wa kake yin wayar?”.

Gyaɗa masa kai M Jameel yayi tare da juya hannunsa alamar ya kusa gamawa.
Ganin haka yasa Moddibo maida hankalinsa kan system ɗin sa yana cigaba da duba muhimman saƙonnin da suke shigo masa.
Wayarsa dake gefen Centre table ne yayi ƙara hannu yasa ya ɗaga nan yaga sunan Abba na yawo a screen ɗin wato Abban M Jameel.
Cikin han zari yayi picking call ɗin kana yace.
“Assalamu alaikum Abba Barka da dare”.
Daga ɓangaren Abba yace.
“Barka dai Moddibo ya gida ya kuma ɗalibai?”.
“Lafiya lau Alhamdulillah Abba”.

“Masha Allah kana tare da Hassan ɗinna ka ne?”.

Murmushi Moddibo yayi wanda ke sake fitar da ainihin kyawun fuskarsa yace.
“Eh Abba muna tare waya yake tun ɗazu nayi zaton ma da kai yake yin wayar”.
Abba yace.
“Aina kira wayarsa naji Line busy shiyasa nace bari na kira ka naga dare yayi bai dawo ba za'a rufe ƙofar gida”.

Murmushi Moddibo yayi yace.
“Ayyah Abba yau kam abarshi mu kwana tare gashi naga alamun Agajiye yake bacci ma yake ji”.

Kai Abba ya gyaɗa yace.
“Toh shikenan Moddibo ayi bacci lafiya Allah ya tashe mu lafiya amma gobe da safe kuzo ina son ganin ku”.

Kai Moddibo ya gyaɗa cike da mutuntaka yace.
“Toh insha Allah Abbah”.
Kana ya katse kiran.

kallon M Jameel yayi sai kuma ya ajiye System dake kan ƙafarsa ya miƙe ya isa inda M Jameel yake yasa hannu ya cire wayar daga kunnensa ya duba screen ɗin sai yaga number ba suna saidai aƙasan Number ansa Bahrain wato ƙasan Bahrain.

Kallon M Jameel yayi yace.
“Ooo kaida Jalaludeen ne dama?”.
Kai M Jameel ya gyaɗa yace.
“Eh shi ya hana ince da kai dashi nake waya”.

Murmushi M Jameel yayi yace.
“Yayi kyau”.
Jalaludeen abokinsa ne tare sukayi karatu a Jami'atul Madina asalin Balarabe Bahrain ne...

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe yace.
“Abba ya kira yace baka koma ba har dare yayi sai nace zamu kwana tare yace gobe yana son ganinmu”.
Kai M Jameel ya gyaɗa da faɗin.
“Allah ya kaimu”.
“Ameen”.
Moddibo ya amsa tare da kallon M Jameel yace.
Bacci na keji zanje nayi wanka”.
Zare Ido M Jameel yayi yana kallon Moddibo yace.
“Wallahi inba cikin kashi na faɗa yanzu ba ba zanyi wanka ba yanda ake tsuga wannan sanyi agarin nan.

Kai Moddibo ya girgiza ba tare da yace komai ba ya wuce Bedroom.
wanka yayi da ruwa mai ɗumi, kana yayi shirin bacci.

Washe gari, da safe bayan sun dawo daga masallaci sashen Innayi suka nufa lokacin da suka shiga tana zaune kan darduma tana lazimi M Jameel ya zauna kusa da ita tare da riƙo tafin hannunta yace.
“Barka da safiya tsohuwa mai ran ƙarfe!”.

Murmushin fuskarta ta faɗaɗa tare da damƙe hannunsa dake cikin nata tace.
“Jameel Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwarku”.
Ya amsa da.
”Ameen Innayi”.
Shi kuwa Moddibo kusa da ita ya matsa ya ɗaura kansa akafaɗarta yana mai lumshe idanunsa ahankali yace.
“Barka da safiya Innayi”.
Hannunta tasa ta shafa fuskarsa tare da cewa.
“Fatan ka tashi lafiya ya ƙoƙari?”.
Ya amsa da. “Alhamdulillah” sai kuma ya miƙe tare da kallon M Jameel da still hannunsa ke cikin na Innayi yace.
“Mu je ko”.
Bai jira cewarsa ba ya fice daga sashen nata kana ya nufi nasa yana shiga kai tsaye Bedroom ya wuce ya cire naɗin Hiramin dake wuyan sa da kuma jallabiyar.
Kai ya shiga bathroom Masha Allah Komai na cikin toilet wanka ya fesa kana ya fito bakinsa ɗauke da addu'a
“Gufra naka”.Alokacin daya ziro ƙafarsa ta dama zuwa cikin Bedroom ɗin ya fito M Jameel kuwa jin ƙamshin sabulun wankan da kuma tularensa yasa ya ɗago kai sai kuma ya miƙe ya shiga toilet ɗin.
Shi kuwa Moddibo zama yayi agaban dressing mirrow ya shafa mayukan sa tare da taje yalwataccen sumarsa kana ya miƙe ya buɗe durowarsa
Masha Allah kayane aciki masu uban yawa fannin jallabiya da ban fannin yaduka da ban haka zalika fannin ƙananun kaya daban duk da cewa bai fiye amfani dasu ba yana tsaye awajen har M Jameel ya fito daga wanka bai ɗauki komai ba.

Murmushi m Jameel yayi tare da nufar jikin durowar yana cewa.
“Nasan koda zaka kwana nan ba zaka taɓa cire kayan da zamu sanya ba kai de inba jallabiya ba baka ganewa ko wani irin kaya”.
Moddibo kuwa murmushi yayi Aransa yana jinjinawa M Jameel yanda yake iya fahimtar komai nasa koda kuwa ƙwaƙa-ƙwaran motsi yayi yasan me yake nufi...

M Jameel kuwa Wani boyel Sky blue mai gidan dara-dara ya ciro musu tare da boxer da kuma singlet Fari ƙal.
Kallon Moddibo yayi tare da miƙa masa.
Murmushi Moddibo yayi tare da karɓa yana kallon kayan amma bai ce komai ba sai ya juya ya kimtsa.
Masha Allah wani irin kyau na musamman Moddibo yayi acikin kayan kalar shigar sai ta kasance tamkar kalar sararin samaniya ƙirjinsa na ƙiran jarumtaka ya bayyana acikin rigar kana yalwataccen sumar kansa ya kwanta luf yana sheƙi,Anutse ya juya wajen M Jameel dake miƙo masa takalmi da hula kalar sky blue Masha Allah m Jameel ma sosai Yayi kyau acikin kayan sai suka kasance tamkar tagwaye masu tsananin ƙaunar junansu.

Atare suka fice sashen Innayi suka nufa tun daga farfajiyar tsakar gidan Moddibo ya lumshe idanunsa yana jinjinawa tsaftar Kakar tasa har sanda suka isa ƙofanta inda sanyayyan ƙamshi turaren wuta ke tashi.
Ganinsu atare yasa ta sakar musu da murmushi atare suka shiga ɗakin suka zauna.
Ta dubesu cikin ƙaunarsu tace.
“Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku Allah yasanya farin ciki acikin rayuwarku Ubangiji ya tsareku da dukkan sharrin mai sharri”.

Cikin jin daɗin addu'ar da take musu ako yaushe suka amsa da.
“Ameen Innayi”.
Innayi kuwa miƙewa tayi ta haɗo musu tea mai zafin gaske saboda sanyin da akeyi sosai amsa sukayi.
A hankali Modibbo ya ɗan zuƙan tea ɗin ahankali har ya Ida shanyewa zuwa lokacin tuni M Jameel ya shanye nasa.
Yana ƙoƙarin ajiye Mug ɗin yaga M Jameel ya tsaresa da ido Harara Moddibo ya watsa masa shikuma saiya sakar masa da murmushi.

Kallon Innayi Moddibo yayi yace.
“Zamu je gaida Abba”.
Jinjina kai Innayi tayi tace.
“Idan kunje ku gaishe min dashi”.
Moddibo na miƙewa yace.
“Zaiji insha Allah”.
Sannan suka fice.

Suna fita suka nufi inda mota ke ajiye M Jameel ne ya buɗe gefen Driver ya shiga yayin da Moddibo ya shiga mazaunin mai zaman banza ahankali M Jameel yayiwa motar key suna isa gate ɗin Moddibo ya fita ya buɗe musu gate sannan M Jameel ya cinna hancin motar yafita saida Moddibo ya sake rufe gate ɗin kafin ya koma cikin motar M Jameel ya tayar suka bar unguwar.

Anutse M Jameel ya dubi Moddibo da idanunsa ke lumshe yace.
“Anma aikin makarantar nan zai yi kyau domin masu aikin sun san makamar aikinsu”.
Shi kuwa Moddibo kai ya gyaɗa da faɗin.
“Sosai Insha Allah”.
Tafiyar Mintuna Kaɗan sukayi suka isa gidansu M Jameel Hon yayi mai gadin ya taho da sauri ya buɗe musu tamfatsetsen gate din.

Wow Masha Allah babban gida ne wanda yake ɗauke da Sashe huɗu sai kuma BQ da kuma wajen ajiye motoci kamar takwas zuwa goma sai ɗakin mai gadi cikin gidan akwai shuke-shuke saida basu da yawa sosai bayan sunyi parking sun fito ajere suke cikin tafiyar nutsuwarsu da tazame musu jiki kai tsaye sashen mahaifin M Jameel ya nufa dasu.

Adai-dai ƙofar da zai sa dasu da falon Mahaifin M Jameel suka haɗu da Hajiya Karima kallon Jameel tayi kana ta kawar da kanta wani irin tsuke fuska tayi ganin Moddibo abayan M Jameel.
Cike da ladabi M Jameel yace.
“Ina kwana Aunty Karima”.
Fuska ta sake tace.
“Lafiya lau ɗana ya gida ya kuma ƙoƙari??”.
“Alhsmsulillah ya amsa”.
Yana mai shafa sajensa
Shi kuwa Moddibo cikin tsuke fuska alamun ba wargi ataƙaice yace.
“Ina kwana”.

Wani irin kallo ta watsa masa kafin tace.
“Kaska raɓi mai jini anzo kenan?”.
Shiru Moddibo yayi tare da kauda kansa kamar bai jitaba.
Sai ma Murmushi da yayi tare da kallon gefen dama inda Aunty Larai Amaryar Aunty Karima ke tare da ce mata.
“Yau barka dai”.yayi mgnar yana mai tsare fuskarsa da ido alamun yana nazartar ta,
Ita kuwa Aunty Larai cikin sakin fuska tace.
“A'a to Moddibo ya kuka tsaya nan ku shigo daga ciki man Jameel”.
Ta ƙare mgnar tana kallon Jameel tare da juyawa ta nufi cikin falon Daddyn Jameel din.
Cikin jin yanayin ɓacin ran da kalaman Aunty Karima suka sa mishi yace.
“Gamu nan shigowa Aunty Larai”.
Ya kare mgnar tare da
ɓata fuska cikin rashin jin daɗin abinda ta yiwa amininsa yace.
“Aunty!Aunty!!, Meyesa!!?, Meyesa!!!?”.

Cikin taune lips inta dubesa tace.
“Jameel gaskiya ne ai, amma ba zaka gane ba, ba zaka yarda ba sabida ya fika wayo.
Kawai dai ya zama dole in faɗa maka”.
Shiru M Jameel yayi tare da juyawa wajen Moddibo wanda har zuwa lokacin yake tsaye hannunsa M Jameel ya riƙe yace.
“Dan Allah kayi haƙuri inda sabo yaci kasaba da halin Aunty na roƙeƙa Kayi haƙuri mushiga daga ciki”.
Murmushi Moddibo ya sakar masa ahankali ya furta.
“Bakomai me zatayi ya dameni sam babushi tunda tana son aminina”. Yayi mgnar da iya gskyarsakan
suka shiga cikin falon.

Ita kuwa Aunty Karima tsaki taja tare da barin wajen tana maijin tsanar Moddibo.

Zaune suka samu Alh Bashir Mafindi Shahararren mai kuɗi daya sharahara aƙasa da kuma faɗin Afirca baki ɗaya mutum mai tsananin tausayin al'umma da jin ƙai.

Hannu ya buɗe musu cikin nutsuwarsu suka ƙarasa Moddibo ya nufi gefen damansa yayin da M Jameel ya nufi gefen hagunsa ya rungumesu tare da buga kafaɗar su.
Cike da so yace.
‘Yan ta gwayena Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku ina jin dadin ganinku atare kunyi kyau tamkar matasan Larabawa Allah Ubangiji ya nuna min aurenku”.
Moddibo kuwa murmushi yayi shikam sai ya zo wajen Abban Jameel ake masa maganar aure sai yaji abin banbara ƙwai duk da yasa ba duk lokacin da yazo wajen Abba saiya masa Maganar amman kullum a baƙuwa yake jin kalmar a cikin kunnuwansa.

Cike da ladabi da kuma girmamawa suka gaishesa cike da ƙaunarsu ya amsa da.
“Lafiya”.
Kana ya tambaye su ya ɗalibai?.
Suka haɗa baki wajen faɗin.
“Lafiya lau Alhamdulillih”.

Zama Abba yayi bisa kujera.
Kana su kuma suka zauna a ƙasa bisa tattausan carpet ɗin, cikin kula Abba ya ɗan sunkuyo ya kalli M Jameel kana yace.
“Yanzu kaga damuna ta kusa sauƙo za'a fara shuke-shuke to inason bana zan shuka Auduga mai yawa saboda ina son zan habaƙa Company dake Marrocco muna buƙatar Auduga mai yawa domin mun samu haɗin guwar da wani ɗan Saudia wurin sufurin Sallayoyi da zannuwan gadaje da kuma Abayoyin na mata”.

Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cewa.
“Eh Abba hakan yayi Allah ya sanya alkhairi”.
Shima Moddibo yayi Murmushi da faɗin.
“Allah yabada sa'a”.
Cikin jin dadi Abban yace.
“Ameen. Yauwa sai kuma noma shinkafa da zamuyi mai yawa da alkama, dan Company kayan masarufin dake Ɓadamaya yana buƙatar ninkin abinda yake sarrafa a shekara, domin samun haɗin guiwa da shi'ar ƙasar Niger”.
Kai suka jinjina alamun gamsuwa kana cikin kula Abban yace.
“Na sani kuma na fahimta, cewa akan su Asma'u ne ka nacewa karantarwa da kai da amininka. To Alhamdulillah na baku dama, amman ku sani suna gama secondary School, dole ku bar karantar wannan Moddibo ina buƙar taimakonku a Company's ɗin tunda Allah yayi kun karanci Business ɗin nan kafin ma ku tafi Jami'atul Madina.
Babana yanzu girma ya cinmini abubuwa sunayi min yawa dole ina bukatar tai makonku”.
Ya kare mgnar yana dafa kaɗan Jameel.
Cikin sanyi Jameel ya ɗago kansa ya kalli mahaifin nasa kana cikin sashi farin ciki yace.
“Allah ya kaimu lokacin Daddy in Sha Allah zanyi maka dukkan abinda kake so, muddin ina raye”.
Cikin jin dadi yace.
“Kaifa Moddibo baƙace komai ba?”.
Murmushi gefen baki yayi tare da cewa.
“Daddy duk inda J yake to in sha Allah ina nan”.
Cike da jin daɗin Alh Bashir
Mafindi ya shafa kansu tare da cewa.
“Allah yayi muku al'barka".
Cike da jin daɗin sukace. “Amin Ya Allah Allah ya ƙara nisan kwana da lfy”.

“Amin Ya Allah”.
Abba ya amsa tare da nuna musu dinning area da hannunsa, inda Aunty Larai ke shirya dinning ɗin tama mai murmushin jin tattaunawarsu.
Sai kuma ya kalli Moddibo kana yace.
“Bismillah kuje kuyi Breakfast”.
Moddibo kuwa kai ya girgiza a hankali yace.
“Daddy na ƙoshi”.

Kallonsa Daddy yayi cikin kulawa yace.
“Meyesa haka ne Moddibo gsky ni bana son yadda kake in kazo gidan nan kaci abinci sai kaƙi ci”.
M Jameel ne ya amshi zancen da cewa.
“Rabu dashi Daddy in baici ba sai muyi masa ɗure”.
Murmushi Daddg yayi tare da faɗin.
“Aikam".
Moddibo kuwa harara ya wurgawa M Jameel.

Adam ƙanin M Jameel yaron Aunty Karima ne yashigo ganin M Jameel yasa ya faɗaɗa Murmushin sa yace.
“Yaya Jameel Ina kwana?”.
Cikin murmushi M Jameel ya mayar masa da.
“Lafiya lai alhamdulillah Adam ya school”.
Adam kuwa kallon tsana ya watsawa Moddibo ba tare daya gaishe saba dan gani suke yana amfani da M Jameel ne wajen cin dukiyar mahaifinsu ko kaɗan M Jameel baiji daɗin abinda Adam yayi wa Moddibo ba, haka yasa ya haɗawa yaron fuska.

Acan Rugar Jauro yaya kuwa Washe gari.
Bayan Khausar sunyi Sallar asbah tare da Azkharul sabah ɗakin Goggo Nanne suka shiga ita da Dije suka gaisheta,
Ta amsa fuska asake Idanunta akan Khausar tace.
“Ya kwanar baƙunta da kuma tsoron kuliya?”.
Murmushi Khausar tayi tana wasa da yatsun hannunta har yanzu Atsorace take idan akwai abinda tafi tsoro acikin dabbobin duniya to kuliya ce da ƙadaggare.
Dije ce ta miƙe tace.
“Mun tafi gidan Hajja Nana”.
“Toh adawo lafiya".
Miƙewa sukayi suka fita ahanya Khausar ta dubi Dije cikin sanyin murya tace.
“Idan munje Kar mu daɗe tsoron gidan nake".

Kai Dije ta gyaɗa suka cigaba da tafiya bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga Hajja Nana dake hakimce akan kujeranta ta amsa Khausar kuwa kusa da ƙafafun Hajja Nana ta zauna tace.
“Ina kwana Hajja Nana”.
Ta dubeta fuska asake ta amsa tana jin ƙaunar ta aranta.
Dije ma gaisheta tayi ta amsa fuska asake.
Miƙewa Khausar tayi tace.
“Mu tafi”.
Kallonta Hajja Nana tayi tace.
“Ki zauna mutanen garin zasu zo gaisheni zan gabatar dasu awajenki”.

Khausar kuwa narai-narai da idanu tayi har cikin ranta take tsoron gidan Hajja Nana Allah ya sani tana masifar tsorob kuliya, jiki asaɓule ta zauna tare da riƙe Dije suka zauna tare.

Suna zaune Baffa Jauro yazo cike da girmamawa da kuma ladabi yace.
“Addah Hajja ina kwana”.
“Lafiya ta amsa”,tare da kallon Khausar dake takure tace.
“wannan shine ƙanina dake bina”
Murmushi Khausar tayi tare da gyaɗa kai tace.
“Baffa ina kwana”.
Dariya yayi yace.
“Lafiya Audiii ya fargaban kuliya!?”.
Baki ta ɗan tura amma batace Komai.
Can sai ga Goggo Nanne
Kusa da Khausar ta zauna tace.
“Addah Nana ina kwana”.
Ta amsa da lafiya tare da kallon Khausar tace.
“Wannan itace matar Jauro wacce kuka kwana agidanta sunanta Nanne ita ce kuma takwaran marigayi yayarki”.
Kai Khausar ta gyaɗa tana sake damƙe hannun Dije dake cikin nata.

Can sai ga Garga yazo idanun sa akan Khausar ya mata murmushi hannunta ya riƙe yace.
“Addah Nana ina kwana ya kwanan baƙuwa?”.
Hajja Nana kuwa taɓe baki tayi tace.
“Ga tanan matsoraciya saboda kuliya taƙi kwana anan".

Murmushi Garga yayi yace.
“Audii ki zama jaruma Mahaifinki fa ba rago bane babban jarumi ne”.
Murmushi tayi amma batace Komai ba.
Hajja Nanan ce tace.
“Wannan shine Garga shike bin Jauro.
Can sai ga wata mata tazo itama ta gaida Hajja Nana.

Hajja Nana ta dubeta tace.
Wannan itace Dijarro matar Garga”.
Cikin sanyin murya Khausar ta gaisheta,
Cikin sakin fuska Dijjaro ta amsa.
Ba daɗewa saiga Liman yazo sanye cikin Alkyabba kansa naɗe da hirami kusa da ƙafafun Hajja Nana ya zaune cike da ladabi da kuma dattako yace.
“Addah Hajja ina kwana”.

Ta amsa da.
“Lafiya”.Sannan ta dubi Khausar tace.
Wannan shine Aliyu Limamin garin nan Uwarmu ɗaya Ubanmu ɗaya mutum ne mai tarin Ilimin addini”.
Cike da ladabi Khausar tace.
“Ina kwana”.
“Lafiya lau ya kwanan baƙunta?”.
Ta amsa da
“Alhamdulillah”.

Bayan tafiyarsa sai ga matansa biyu Rabi da Loddo,Kai kawai Khausar ke gyaɗawa.
Ita de Khausar ta kasa sakewa,Ahaka suka riƙa zuwa duk wanda yazo Hajja Nana zata gabatar wa da Khausar shi.
Can saiga Yaya Abba yazo Hajja Nana tace.
“Wannan shine Abba ɗan ƙanina ne liman shi aka tura karatu birni yana karatun arnanci irin wanda kike yi”.

Abba kuwa ƙasa da kai yayi yana murmushi.
Ita kuwa khausar kallon Hajja Nana tayi tace.
“Wai waya ce Miki karatun Arnanci mukeyi?”.
Hannu Yaya Abba ya ɗaya mata alamar tayi shiru!.

Khausar kuwa ta wani juya masa manyan Idanunta tace.
“Taya ba karatun Arnanci mukeyi ba tace karatun Arnanci mukeyi ko ance mata acoci muke zuwa karatun?”.

Kallonta Abba yayi cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login