Showing 9001 words to 12000 words out of 176046 words

Chapter 4 - Sakayya 1 Hausa Novel Complete

kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276. muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci idan kuna ga account no da zaku tura kuɗinku ta ciki masu son kayan Ɗa'an 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,


Cikin fesa sassayyan numfashi, Modibbo ya ci gaba da faɗin.
“Kuji falalar Allahu rabbil samawati garemu, ubangiji yana sonmu yana tausayin mu, yana kuma jinkanmu."
Ya dire mgnar yana ɗan sauƙe wani numfashi dan Allah ya sani ya fara jin bakinshi ya gaji da mgna. Cikin tattausan muryarsa yaci gaba da cewa.
Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda dashi, yace:
(Ya ma'akin Allah! Shari'o'in Musulunci sunyi yawa a gareni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zanyi riƙon da shi.
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa.
(Kar harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambaton Allah.
Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
(Wanda ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yana da ladan kekkyawan aiki ɗaya, shi kuma kekkyawan aiki ɗaya yana da ladan misalin goma.
Ba ina nufin Alif lam Mim harafi bane,
A'a. Alif harafi ne, Lam harafi ne, kana shima Mim harafi ne.”.

Wani irin mayataccen kallo Samira ke bin lips ɗin Moddibo dashi, tana mai kallon dukkan yadda yake motsasu, da yadda tattausan sajensa ke zuba ƙyalli ƙawarta Ikilima Ibrahim ce ta ɗan taɓata da kafa alamun wannan wanne irin kallo ne.
Yayinda gefen damansu kuwa, wata madaidaciyar macece, Hadiza Muhammad Yahaya, wacce take cikin sabbin dalibai.
Kallon da Samira Sani keyiwa Moddibo ne ke bata mamaki.
Shi kuwa Moddibo a hankali yaci gaba da cewa.
Kuma daga Ukbatu Ibn Amir Allah ya yarda dashi yace:
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya fito alhalin muna cikin rumfa sai yace:
(Wannene daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna ba tare da yayi wani laifi ba ko yanke zumunta ba?
Mukace masa muna son haka.
Yace:
(Ɗayanku yaje Masallaci ya nemi sani, ko ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah, mabuwayi mai ɗaukana, yafi masa taguwa uku ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu da kwatankwacin adadinsu na raƙuma.)
Kunga ashe muna ɓarar da damarmakinmu riƙe da waya ba tare da mun samu mun ribaci ilimin da iyayenmu da malanmu suka bamu ba.
Kuma mai tsira da Amincin Allah yace:
(Wanda ya zauna a wani waje, bai ambaci Allah a wajenba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah, wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajenba shima zai zamanto masa abin bibiya a wajen ALLAH.
Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
(Babu wasu mutane da zasu zauna a majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, kuma basu yi salati ga annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah yaso yayi musu azaba, in yaso kuma sai ya gafarta musu.”
Jujjuya idanunsa yayi fuskarsa cike da shauƙin son Mahaikin Allah Muhammadu Rasulullah, da sahabbansa,
Wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da lumshe idanunsa, wanda yakan shiga wannan yanayi a duk lokacin da yakeyiwa ɗalibansa nuni da al'khairan dake cikin ammaton Allah da bin sunnar manzonmu abinkoyinmu abinsonmu da sahabbansa masu daraja.
Ita kuwa Khausar ƙasa tai da idanunta.
Sai kuma ta ɗan ɗago ta kalleshi jin tattausar muryarsa yaci gaba da cewa.

“Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
Babu wasu mutane da zasu tashi daga wani majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan *mushen jaki ne* kuma zai zamanto musu abin dana sani)”....
Ya ƙare mgnar da haɗe kan yatsunsa duka, kana sai ya buɗasu a tare da ware tafin hannunsa kamar ya sake abu,
alamun ya dasa babbab ɗamba, ya gama da wannan yankin.

Gaba ɗaya hankalinsu tunaninsu duk yana kansa, domin suna matuƙar jin dadin yadda wasu lokutan idan ya shiga aji yake tunasar dasu mahimman abubuwan da suka cancanci musulmi ya lizamcesu.
Yayinda wasu kuwa da sam baya shiga ajujuwansu cike da son salon sa suke sauraronsa, kasan cewar makarantar nada yalwar malamai kuma shi aiyuka sun mai yawa shisa ba dukkan class da suke dashi yake shigaba.

Shi kuwa Moddibo cikin alamun gajiya da yawan motsa lips nasa da yayi yaci gaba da cewa a gaggauce.
“Mu farka mu ribaci wannan shekarar dukanta kada muce dan wannan wata na Ramadan daya shuɗe, zamu bar wasu ayyukan ibada, mu jure mu zamo dasu ɗabi'armu a kullum domin shi ubangiji ka gafartawa bayinsa, a duk sanda yaso ya ainta wasu daga azaba zuwa rahmarsa madaumiya, mu wasar da wayoyin nan mu ruggumi Alqur'ani mai girma da tasbihai ya zama dai ita wayar nan sai time to time zamu riƙe ya ke mai karatu dake nake."
Ya faɗi hakan yana nuna gefensu Samira dake buɗe da littafi a gabansu.
Sai kuma ya ɗan gyara saƙale Lapel Microphone din a wuyar jallabiyar jikinsa dan yaji muryarsa tana ƙasa sosai alum yadan zame kaɗan, da ɗan sauri yace.

“Zaku iya duba Muslim (1/554) Abu Dawud (4/264) da waninsa duba Sahihul Jam'i, (5/342). Tirmizi duba Sahihul Tirmizi (3/140) Abu Dawud (4/264) da Ahmad (2/389) duba Sahihul Jami (5/176) Allah shine mafi sani... Abinda nace dai-dai Allah ya haɗamu a mizanin ladan abinda nai kuskure Allah ya gafartamin.”

Ya rufe mgnar da addu'a tare da juyawa ya fita.
Sukuwa gaba ɗaya numfashi suka sassauƙe, yana fitowa Malam Jamil na isowa wurin, dan shi zai shiga ya shaida musu kwanakin da aka ƙara.

Kai Modibbo ya kauda gefe, jin Aminin nashi na cewa.
“Fattanah maza yi gudu ki shiga aji kada in rigagi, shiga, dan in na rigaki nima yau gadin aji zansa kiyi mana”.
Da sauri Khausar din ta juyo tare da kallon shi cikin alamun yanai musu barkwanci tace.
“Malam ko ta window ma zan shiga”.
Murmushin yayi tare da cewa.
“Har yanzu baki girmi shiga ta window ba FATTANAH”.
Da sauri tace.
“Toh ai banyi jikiba, ka gani”.
Kawai sai ta kama jikin window alamun zata zauna ta wajen sai ta juya ta ciki.
Cikin yamutsa fuska Moddibo yace.
“Ke bar nan,”.
Ai da sauri ta diro tare, da nufar ƙofa, tana tura baki.
Shi kuwa Malam Jamil cikin tsananin son yarinyar sabida ƙwazonta da jan da kwanyarta keyi kana da ƙawancenta da ƙanwarsa Asma'u Ahmad ya bita da ido.
Rungume Moddibo yayi tare da yin mgn murya can ƙasa.
“Tuba mukeyi Moddibo ai mana tsawan a hankali ka mance baka cire Lapel Microphone ɗinba, har nima tsawar ta razanani”.
Wani irin nannauyan numfashin Moddibo ya sauƙe tare lumshe idanunsa.
Shi kuwa M Jamil murmushin yayi kana kuma ya sake shi yace.
“Lokaci na tafiya sai na fito na sallami maza kam”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da sauƙa ƙasa.

Goma dai-dai aka tashi islamiyan gaba ɗaya duk ɗaliban suka koma gida bayan M Jamil ya musu bayanin dalilin ƙarin hutun, wanda kuma suma sunga hakan.

Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi daga taron tattaunawa da malaman nasu baki ɗaya.

Bayan sunyi sallan azahar ne, kana duk suka tafi, ma'aikata sukaci gaba da aikinsu.

A gidansu Khausar kuwa.

Khausar ce kwance bisa 3 str daga ita sai yar doguwar rigar material mai taushi a jikinta, Pink collor, sai hular sanyi data sa a kanta, yayinda himilin gashinta yayi tub-tub a ciki.
Da alamun bacci take sonyi.
Cikin sanyi ta buɗe ido ta tare da juyowa ta kalli Momynta dake fitowa daga kitchen ɗinta, hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits a ciki masu sanyi, gefen ta ta zauna bisa 1 str ta ɗaura plate ɗin kan cinyarta tare kallon Khausar ɗin data miƙa mata hannu alamun ta bata.
“Tashi kije ki ɗebo Uniform ɗin ku, nasan yanzu ya bushe kizo ki goge muku kafin a kira magriba”.
Numfashi mai ɗan sanyi Khausar ɗin ta fesar tare da miƙewa zaune, ita kuwa Momy tafin sawun ɗiyar Tata take kallo cike da ganin kamannin sawunta dana ahlinta.
Hannu tasa ta ɗauki inabi guda uku. Kana ta miƙe tsaye tare da juyawa ta fita.
Ita kuwa Momy da idanu ta rakata.

Tana fita a barandar ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama ta riƙe ƙugunta.
Amina ce ta fito daga side din Gimbiya Bunayya, mahaifiyarsu kenan, uwar gidan Lamido,
Wacce daga itana sai Maman su Khausar wacce itace amaryarsa.

Wani irin kallo Amina tayiwa Khausar tare da cewa.
“Hamshaƙiya, cin abu a tsaye ba koyarwar musulunci bane”.
Fuska Khausar ɗin ta ɗan yamutsa tare da cewa.
“Ngd”. Sai kuma ta miƙawa Aminu ƙanin Amina wanda yake gefenta.
Da sauri Amina ta kwaɓe hannun yaron da bazai gaza shekara goma sha ɗaya ba tare da cewa.
“Makwaɗaicin baza, in zakaci akwai a fridge kaje a baka”.
Ido Khausar ɗin ta zuba mata, sai kuma ta sauƙe numfashi dan batayi mmkin hakanba, cikin alamun kasalan da baccin da takeji ya sakar mata, ta nufi wurin shanyan nasu, a hankali take tafiya, dan ganin shanyan nasu yana can har bayan Part ɗin Hajia Bunayya Umma.
“Wannan daga gani ma aikin Ramadan ne, shine zai zo yayi mana shanya har nan, zaice waɗan can igiyoyin tsawonsa bazai kaiba”.
Ta ƙare mgnar tana nufar can.
A hankali ta fara janye shanyan, har ta isa dai-dai window Hajia Bunayya, cikin mamaki ta ɗan tsaya jin yadda Umman ke mgn da faɗa-faɗa.
“Kada in damufa kake cewa.
Kasan kuwa irin tashin hankali da nake ciki duk sanda na buɗi idanuna na kalli Haiydar a matsayin ɗan Lamido Yariman Gembila kuwa, ko ka mance shine ɗan sa na miji babba, shin baka ganin iyakata da mulki sai dai gani sai hange tunda shine ɗa babba akan Aminu na.
Kai bakaga yadda komai zai juye min ba a gaba, ina gani sarauta zata koma ɗakin Aysha ƴaƴanta ne zasu mulki masarautarmun”.
Sai kuma tayi shiru alamun tana sauraron abin da ake cewa a ɗaya sashin.

Ita kuwa Khausar cike da tsoron halin irin na Umma, gashi dai abinda taji, amman koda zata kwana gayawa mahaifiyarsu bazata taɓa yardaba, domin Umma bata taɓa nuna kishinta a kanta, shiyasa ta ɗauki dukkan yarda ta bata.

Cikin tsananin tsoro Khausar ɗin ta zaro ido ta tare dasa tafin hannunta ta dafe ƙahon zuciyarta, jin Hajia Bunayya na cewa.
“Wallahi tallahi billahil azeem zanyi komai dan ganin bayan Aysha da yaranta, zanyi duk abinda ya kama domin in kauda Haiydar a matsayin yarima mai jiran gado, dan wlh Allah zan iya kasheshi kowama ya huta!...”.
Cikin tsananin kaɗuwa Khausar ta juya da sassarfa ta koma sade ɗin Maminta, tana isa kawai sai ta watsar da kayan bisa kujera.

Da sauri ta kamo hannun mahaifiyar tata tare da cewa.
“Momy! Momy dan Allah ki biyoni zo kiji wani abu”.
Ta ƙare mgnar a matuƙar kiɗime, wanda hakan yasa dole Hajia Aysha ta bita a baya.

Ita kuwa da sauri take jenta, har zuwa bayan window Hajia Bunayya.
Cirko-cirko suka tsaya,
Ita kam Khausar cike da firfito da ido waje take sauraron abinda Hajia Bunayya ke faɗi.

Momy kuwa wani irin...!


A hankali M Jamil yayi parking a bakin gate ɗin gidansu Moddibo juyowa yayi ya kalli Moddibo dake gefensa yana lallatsa system nasa.
“Toh wazai fita ya buɗe mana gate ne kam?”.
Ba tare da ya ɗago ya kalleshiba ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya tare buɗe tafin hannunsa alamun
Oho.
Kai M Jamil ya jujjuya tare da cewa,
“To bari ni buɗe”.
Kai ya kuma gyaɗa masa alamun.
“Toh”.
Murmushin M Jamil yayi tare da fita ya buɗe gate ɗin, kana ya dawo yaja motar suka shiga ciki.

Parking yayi kana suka fito suka nufi cikin gidan,

Kai tsaye sashin Innayin suka wuce.

Wani irin yalwataccen murmushin M Jamil yayi tare dayin saurin ya haura kan barandar zama yayi daɓas bisa tattausan carpert ɗin dake shimfiɗe a barandar.
Innayi na kwance yayinda Ummin Jamil kuwa ke gefenta tana ɓare mata banana.
Itama yalwataccen murmushin tayi tare da miƙawa Moddibo ayaban data ɓaren.
Amsa yayi tare da juyowa ya ɗan kalli M Jamil da ya zame ya kwanta bisa carpet ɗin tare da ɗaura kansa bisa cinyarta, cike da so, ƙauna, shaƙuwa, tausayawa, yace.
“Ummina kin san irin farin cikin da nakeji a raina kuwa in na ganki?”.
Murmushin kawai tayi dan ita bazata iya cewa komaiba a gaban Innayi sabida Jamil shine ɗan ta na fari, kuma su nan Gembila sashine na cikakkun Fulani.

Kawai dai abinda ta sani a baɗini tasan ta fishi farin ciki.
Shi kuwa Moddibo gefen Innayi dake kwance da alamun har yanzu nitsuwarta bai ida dawowa jikintaba, hannunta ya riƙe tare da kallon M Jamil.
“Kai dan Allah ɗagata kada ka karya mana cinyarta da katon kankan nan”.
Ya ƙare mgnar yana gutsuran banana.
Shi kuwa Jamil da sauri ya tashi zaune jin Umminshi na ture kanshi tana cewa.
“Ai kam gskyarka Moddibo”.
Tashin nasa ne, yasa ta miƙe ta nufi kitchen, trayn data shirya kulolin abincinsu ta kawo musu.
Ta ajiye a tsakiyar su,
Shi kuwa Modibbo a hankali ya kamo hannun Innayin tare da tallabota alamun so yake ya ganta a zaune.
Sai kuma duk suka kalli Innayi data buɗe kwayar idanunta jin yana tallabota.
Zaunar da ita yayi cikin kulawa yace.
“Yanzu me yake miki ciwo?”.
Cikin sanyi tace.
“Nima kaina ban saniba, kawai dai zuciyata ke a tsinke tsoro nakeji Moddibo”.
Da sauri Jamil yace.
“Toh Innayi tsoron me kuma kikeji?”.
Cikin sanyi tace.
“Tsoron kada mutuwa tai mini zuwan ba zata”.
Wani irin masifeffen tsinkewan zuciya ne ya riski Moddibo jin Jamil ya ɗan yi yar dariya tare da cewa.
“Kada ki damu Innayi ki dena jin tsoron mutuwa, domin ita wajibinmu ne ita.
Kuma tsufa ba shine hanyar mutuwaba, ba abin mamaki bane ki rayu ni nan Jamilu in mutu in barki, in bar Ummina da rashina, in bar Aminina Moddibo da rashin Aboki kamata, tabbas a al'amarin ubangiji zan mutu in barku a raye da kuma ƙunar rashina”.
Da sauri Moddibo yace.
“Yah Salam wai kai J meyasa ne wasu lokutan kalamanka a baibaisuke? Dan Allah kasan abinda zakana cewa”.
Murmushin mai sauti Jamil yayi tare da cewa.
“Zanfa mutu kam, dole zan mutu to kai dama a gani kake a haka zamu tabbata ne?”.

Da hannu Moddibo ya nuna masa Umminsa da haka kawai taji wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata.
Da sauri Jamil yasa tafin hannunsa ya sharce mata hawayen tare da cewa.
“Kada kiyimin kuka kodama na mutu kada ki damu Ummina kinga aminina Aliyu ko to shi zai zame miki madadina”.
Da sauri tayi mishi dakuwa.
Sai kuma yayi dariya mai sauti tare dace.
“Oh su Ummi ana son ɗan fari wato irin bakya son Jamilunki ya mutun nan ko”. Ya ƙare mgnar cikin tsigar wasa kamar dai kakarsa ce,
Hakanne yasasu yin murmushin ganin zata kai mishi duka ya ɗan zille yana cewa.
“Haka kawai wai kunya wai ni ɗan fari bazakice kina sonaba, toh ni kam ina sonki ina sonki ina sonki Ummina”.
Ƙeyarsa ta ɗan buge, kana ta tura musu plate ɗin dake cike da fruits sai kuma ta mimmiƙa musu fork,

Innayi kuma yar wannan hirar da sukayi yasa ta ɗan sake kaɗan, duk da har yanzu in ta rufe idanunta tana ganin abinda Allah ya nuna mata daren jiya.

Jamil ne ya kalli Innayin tare da cewa.
“Dr Jamila tazo ta dubaki ko, dan da safe kafin mu wuce makaranta na kirata tazo”.
Kai Ummi ta gyaɗa alamun eh tazo.

Frutis ɗin kawai suka ci kana suka miƙe suka nufu part ɗin Moddibo.
Suna shiga falon,
Cikin sanyi Jamil ya zauna bisa kujera tare da riƙo yatsar Moddibo manuniya, cikin wata iriyar sassayar muryar yace.
“Moddibo kasan ina jin farin ciki na musamman in naga Ummina ko?”.
Sunkuyar da kai Moddibo yayi tare da zuwa aminin nasa idanu cikin sanyi yace.
“J nasani! Na sani dan farin cikin baya ɓuya a fuskarka”.
Cikin Muryar da tafi ta ɗazu rauni ido na ciko da hawaye yace.
“Amman kuma fa farin cikina raggene, duk daɗin da nakeji in na tuna cewa Ummina ba a gidan Dadyna takeba, inajin ciwo mai yawa a raina, inajin takaicin Kasan cewar mahaifiyata bata gidan mahaifina tana can a wani gidan.
Bayan ita tasha wahalar zama dashi cikin talauci, saida yayi kuɗi dai-dai sanda zataji dadin rayuwa ya saketa, gashi yan uwanta ba masu haliba, mijin da Allah ya ƙaddara ta aura shima rayuwar ba daɗi sabida baida ƙarfi”.
A hankali Moddibo ya zauna kusa dashi cikin ƙarfafa mishi guiwa yace.
“J wanne dadine na kuɗi ya rage wanda bakayiwa Ummi ka tunafa, duk abinda kace kanaso Daddy yana baka, duk kuɗin da zaka nema zai baka, a haka har Makka ka kai Ummi yaranta ka sasu a makaranta mai kyau sanadin su kaƙi kayi aiki a ko ina kace zakayi karantarwa a makarantarsu dan ka tayata basu tarbiyya. Kana kuma yi tunda gashi yanzu sun kusa gamawa, tunda ko Asma'u nanda shekara uku dai zasu gama, secondary School, kace kuma suna gamawa zaka aurar da Asma'u kana ka ɗauki nauyin karatunta, ta na gaba tana gidan mijinta, shi kuwa Bashir na mijine kuma kace in ya gama so kake ya samu jami'atul Madina, in ya tafi can sannan kayi aure kace kuma kana aure zaka ɗauke Ummi da ita da mijinta Malam Ahmad zaka riƙe su, Jamil to meya rage na jin daɗi da baka samawa Ummi ba, ka gyara mata gidan da take, ka gyara mata ɗakinta”.
Wani murmushin mai sanyi yayi tare da cewa.
“To wai Moddibo da kake cewa haka, rainafa mallakin ubangijine a duk sanda yaga dama zai ɗaukeni daga wannan duniyar, ko ban gama cikace burukana ba, in babuni a raye wa zai maiye musu gurbina?”.
Cikin tsuke fuska Moddibo yace.
“To dama wa yake da tabbacin rayuwa, yanzu ni in dai naci zan lizanci irin tunaninka Innayi fa bata da kowa a duniya saini.
J ni zaka gayawa mutuwa? Ni Aliyu zaka gayawa mutuwa?”.
Sai kuma duk sukayi shiru suka zubawa juna ido.
Numfashi mai nauyi Moddibo ya fesar kana a hankali yace.

“J ka kalleni mana! In zame maka madubi, gwara kaifa,
kasan su Ummi kana ganin ta gafa Daddy”.
Da sauri M Jamil ya ri ƙa gyaɗa mishi kai tare da tuno maraicin aminin nasa.
Shi bai san iyayensu ba ranar da mahaifisa ya rasu, firgicin abin ne ya tadawa mahaifiyarsa naƙudansa, ta haifeshi kana itama tabi bayansa kamar yadda Innayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login