Showing 39001 words to 42000 words out of 176046 words
an saceta tana nan mu nan muke zargi”.
Cikin tsananin fushi da zuciya Baffa Umaru yace.
“Baku isa ba babu yanda za'ayi haka ya faru!”.
Babban cikinsu yace.
“Dole sai mun shiga garinku gida-gida ɗaki-ɗaki mun bincika”.
Cikin tsananin fusata Baffa Umaru yace.
“Wallahi in dai ina raye baku isa ba babu wanda ya isa yashiga garinmu yace yayi bin cike indai haka kuke so kuje kuzo da rana muyi magana”.
Babban su yace.
“Mu adaren nan muke so muyi magana”.
Baffa Umaru yace.
“Toh baku isa ba”.
Dumfaro sa sukayi da niyyar shiga Rugar gadan-gadan.
Shi kuwa baya yaja tare da jan kwari da baka yace.
“Duk wanda yake jin shi Jarumi ne kuma ya kai to ya kuskura ya shiga mana cikin Ruga yaga abinda zai faru”.
Tsayawa su kayi akuma dai-dai lokacin ne sauran mazan cikin Rugar suka fiffito mafi yawa ma sautin Baffa Umaru ne ya tashe su dan shi mutum ne mai zafin gaske musamman ma idan ransa ya ɓaci.
Acan bakin ƙofar gida kuwa sosai Khausar ta shiga mamaki sai asannan ta tabbatar da maganar Adama da tace mijinta Jarumi ne kuma Garkuwan Rugar.
Malam Liman ne yayi gyaran murya bayan isan su wajen yace.
“Tun da kunce haka yanzu ku koma da safe sai kuzo aje wajen Mai gari sai ayi magana”.
“Toh”, Babban su yace sannan suka juya suka tafi badan ransu ya soba.
Washe gari da safe bayan sunyi ta tsansu sun daddawo da hantsi Arnan garin Garinga suka zo suka haɗu aƙofar gidan Jauro.
Bayan sun gama gaisawa Jauro ya dubesu Anutse cike da kamala irin na shugaba yace.
“Mai yafaru muna sauraron ku".
Babban su yayi gyaran murya yace.
“Ƴar muce buke ce akayi kidnapping sannan muna zargin tana cikin wannan Rugar”.
Cikin danne takaicin ƙazafin da arnan ke son yi musu Jauro ya jinjina kai kana yace.
“Kun tabbatar tana cikin wannan Rugar?”.
Kai Babban su ya jinjina yace.
“Ƙwarai mun tabbatar sannan mun zo zamu shiga Umaru ya hana mu sannan Umaru shi yake sa mana Ido komai akayi bamu isa muyi magana ba sam Bama ƙaunar abinda Umaru yake mana yayi rayuwarsa muyi rayuwar mu!”.
Wani banzan kallo Baffa Umaru ya watsa musu cikin yanayin zafinsa yace.
“Ba zanyi rayuwata kuyi rayuwarku ba muddin kuna so nayi rayuwata kuyi naku to ku fita sabgarmu banga wanda ya isa ya shigo cikin Rugar mu yace zai taka mu inbar saba”.
Da sauri Jauro ya ɗaga masa hannu hakan yasa Baffa Umaru yayi shiru.
Baffa Jauro kuwa maida kallonsa garesu yayi kan yace.
“Munji mun yarda an sace muku yarinya anyi Kidnapping ɗinta”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Malam Liman yace.
“Ɗauko mana Bible agidanka”.
Kallon Yaya Abba Malam Liman yayi yace.
“Jeka ɗauko min asalin Bible na da acikin littatafai na”.
Miƙewa Yaya Abba yayi babu daɗewa ya dawo hannunsa riƙe da Bible ɗin ya mikawa Jauro.
Karɓa Jauro yayi tare da miƙawa Babban su yace.
“Gashi ku rantse da littafin ku tunda kuce ƴarku ta ɓata kuma tana garin nan”.
Ƙin amsa Babban su yayi.
Cikin sanyi Jauro yace.
“Inde ka tabbata ƴarku ta nan to ka karba ka rantse Inde ka rantse.
To mukuma zamu baku damar shiga sannan muma zamu rantse da Alkur'anin mu mai girma cewa ‘yarku bata nan amma duk da haka idan kun rantse zamu baku damar shiga cikin gida-gida ɗaki-ɗaki kuyi bin cike”.
Shi dai babban nasu kin rantse wa yayi sai wuƙi-wuƙi yakeyi da ido.
Ganin haka yasa Jauro ya kalli sauran na bayansa yace.
“To ɗaya daga cikin ku ya karɓa ya rantse”.
Still suma ƙin karɓa sukayi.
Afusace Baffa Umaru yace.
“Ba gashi ba basu da gaskiya Arnan nan neman fitina suke damu sam babu gaskiya alamarin su bayan sace-sacen dabbobi da kuke mana sai kun nemi fitina damu”.
Babban su ya juya ya kalli Baffa Umaru yace.
“Wani irin sace-sace kuma?".
Harara Baffa Umaru ya watsa masa yace.
“kana tunanin bamusan kune kuke sace mana dabbobin muba to yanzu ga Bible ka karɓa ka rantse da littafin ku cewa ƴarku ta ɓata duk alamun rashin gaskiya ya bayyana atare da ku kawai ku taru dare-dare kuzo mana da mugun nufi”.
Anutse Jauro yace.
“Umaru kayi haƙuri kaki”.
Yasan idan ransa ya ɓaci babu wanda zai iya shawo kansa.
Malam Liman ya dubesu yace.
“Tunda har baku rantse da littafin kuba kenan ƴarku bata ɓata ba in kuma ta ɓata to baku da tabbacin tana garinmu”.
Babban su yace.
“Shikenan babu matsala tunda zaku iya rantse wa da littafin ku munsan bata Rugarku yanzu magana ya ƙare.
Amma Jauro da malam Liman ku jawo Umaru kunne ya fita sabgarmu”.
Miƙewa Baffa Umaru yayi tare da nuna kansa da hannu yace.
“Ni ɗin nan ka ganni nan Babu wanda nake tsoro sai Allah daya hallicceni".
Ƙwafa Babban su yayi yace.
“Tun da haka kace shikenan amma zaka ga abinda kake tsoro”.
Da sauri Jauro ya juya ya kalli Babbansu yace.
“Mu ba mason fitina me kake nufi da zaiga abinda yake tsoro?”.
Babban su yace.
“Indai zai shiga sabgarmu to zaiga abu da yawa”.
Jauro yace.
“Toh bama son fitina tunda kuda kanku kun tabbatar da ‘Yarku bata cikin Garinmu sannan kuda kanku kunsan baku da gaskiya kun ƙi ku rantse, karku sake shigo mana Rugar mu haka ba maso idan kuma kuka sake to zamu haɗa ku da Sarkin cikin Gembila”.
Jin Jauro yace zai haɗa su da Sarkin Gembila yasa suka ce.
“To ayi hakuri ba zasu sake ba”.
Sannan suka juya suka tafi cike da baƙi ciki badan Umar daya hana su shiga ba adaren da sun samu damar kwasan dabbobi damar saboda haka suka ce ansace musu ‘yarsu.
Bayan kwana biyu Komai ya lafa ba fitina da hantsi Khausar da Dije da Ma'u sun ɗebo kayan marmari arafi suna fitowa daga cikin rafin suka hango wata mota fake agefen Rugar tasu sai kuma hango wasu mutane biyu ɗaya ya fito daga gefen dama ɗaya kuma daga gefen hagu da gudu suka shiga motar kafin su Dije su ƙara so sun figi motar.
Khausar kuwa sosai tsura fuskokin su ido kafin su shiga motar, sosai ta riƙe kamanninsu. sannan tabi motar da kallo lokaci ɗaya ta riƙe Number motar Dije da sauran 'yan matan kuwa mamaki suka shiga yi shin mai ya kawo masu motar garin sannan mai yasa da suka gansu suka gudu bayan sun san a irin wannan lokacin, duk mazan garin basa nan makiyaya sun tafi kiwo saura kuma su tafi jeji wa'anda ke rafi kuma sun tafi lambu jiki Asanyaye suka tafi.
Bayan kwana biyu da daddare Khausar na bacci, yayi da take ta takurewa wuri ɗaya sabida wani irin masifeffen sayin da ake tsula musu.
A hankali taja dogon numfashi kana ta fesar a hankali tayi lib.
Can cikin baccinta kuwa cikin wani ƙaton fili mai yalce da yashi fari ƙal-ƙal tana zaune bisa wani dutse tana fuskantar yamma kana daga bayanta kuma wani garden ne mai masifar kyau da girma babu kalan bishiya da sirran da baya ciki, wani irin ni'imtaccen iskane mai cike da ƙamshi furanni ke buso masu wata irin iska mai ɗan karen sanyi.
Gefen damanta ta juya ga mamakinta M Jameel ne zaune bisa wani dutse yana murmushi, da sauri ta juya gefen hagunta kuma, Adda Adama ce ta gani zaune bisa dutse tanata murmushi.
A can gabanta kuwa Mod....! *NO EDITING*
*Kuyi haƙuri sai yanzu na samu caji gashi ba editing. KUNSHA TYPING ERRORS*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_Page 7_
_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FREE PAGE NE YAN UWA, BA WAI FREE BOOK BANE! INA GAMA SAKIN FREE PAGE, KO KINGA an fiddashi waje na satane. Na kuma Yaseen ne doguwa. Dan haka ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa biya ki karanta*
*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*
_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace wanda bani da haufi kansa 7k ne kacal sai dai yar musilar robace., Kana masin Daɗi har Maɗigan yana da masigar kyau da tsatstsafo da ni'ima, wlh wasu in sunyi amfani dashi pan biyu sabida yadda zakiyi ta tsiyaya. 5k ne Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k ne, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan wanda wlh koda sanyin cikin mahaifane fes yake wanke shi kuma ko mai ciki zata shashi baida illa, kama budurwa ko bazawara duk zasu iya sha harma da yara. Set ɗin da 10k ne innkuma za'a sa miki komai rabi-rabi ne 5k ne, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._
🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,
Moddibo ta hango zaune a gefen gabas yana fuskantar tata, bima'ana yana kallon yamma, zaune yake akan wani dutse mai masifar sheƙi kana wasu mutane biyu na tsaye gefen hagu da damansa,
Sannan da buta gabansa bisa alama Al'wala yayi domin farin yashin daya mamaye wajen daga gabansa a jiƙe yake, kana yana mai fidda wani irin ni'imtaccen ƙamshi maisa ɗan Adam lumshe ido. Baki ɗaya haske ya mamaye ilahirin filin wajen hakan yasa itada Moddibo suna fuskantar juna yayin da M Jameel da Adda Adama matar Baffan Umaru suma ke fuskantar juna.
Kana lambu dake can bayanta kuwa yake feso musu iskar yammaci dana lambun suka haɗu waje ɗaya daga sama kuma rana ne yayi Ja yana shirin faɗuwa.
A hankali ta sauƙe numfashi mai nauyi tare da lumshe idanunta.
Da sauri ta buɗe idanun nata, jin wani irin sassayan sautin dariya mai cike da shauƙi da Moddibo yakeyi.
Cike da mamaki duk suka zuba mishi idanu.
Yayinda Adda Adama ma tuni ta fara dariya mai sauti.
Ita kuwa Khausar haka nan taji jikinta yana tsuma tare da sakewa, da sauri ta juya ta kalli M Jameel ga mamakinta shima ita yake kallo, da idonshi ya nuna mata Moddibo yana mai yin lallausan Murmushi, da sauri ta maida kallonta kan Kekkyawar fuskar Moddibo, wacce tunda take a rayuwarta dashi bata taɓa ganin yayi dariyar da har haƙoransa na gaba zasu baiyana ba.
“Fatabarakallahu fih hasanil khaliƙeen”.
Ta furga a saman lips ɗinta, lokacin da ta sauƙe ƙwayar idanunta kan fuskar Moddibo, da sauri ta kuma lumshe manyan Idanunta sabida wani irin masifeffen sheƙi da ta hango sajenshi dake kwance lip-lip yanayi,
Sautin dariyarsa da har yanzu yake ne yasata saurin buɗe idanun.
“Subahanallah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan bawa ya kuma bashi waɗan nan haƙoran”.
Ta faɗa a fili lokacin da taga ƙyellin da haƙoransa keyi har yana ɗauke mata idanunta,
Lobgoɓar da kanta tayi bisa kafaɗarta.
Wani irin sassayan numfashi ta fesar tare da tsaida idanunta a kanshi.
Shi kuwa Moddibo dariya yakeyi mai sayyan sauti wanda yake da daɗin ji, har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa yayi sama kana ya dawo ƙasa.
Yayinda ya ɗaura tafin hannunsa kan ƙirjinsa.
Cikin tsananin dariyar ya samu ya ɗan tsagaita tare da furta.
“Astagfurillah watubu ilaik”.
Sai kuma ya ɗago ya kalli M Jameel lokaci ɗaya kuma ya sake sakin dariya mai sauti yana cewa.
“Astagafitillah Wayyo cikina”.
Cikin rage girman idanunta take kallon gashin girarsa dake kwance lip.
Jameel kuwa sai Murmushi yakeyi tare da girgiza kansa.
Yayinda Adda Adama ma dariyar takeyi harda riƙe ciki.
Ita kuwa Khausar gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta daga kansa.
A haka har rana tayi mudun kuyanƙi alamun yana gab da faɗuwa.
amma kafin ya faɗi saiya rabu kashi biyu.
Yayinda Khausar kuwa ke zaune tana fuskantar yamma hakan yasata ganin abin.
Atake hankalin ta ya tashi ganin yanda ranan ya rabu kashi biyu.
Ita kuwa Adda Adama hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yau mun shiga ukun mu ku dubi yanda ranar tayi fa!”.
Tana faɗin haka duk dariya da murmushin da sukeyi ya tsaya.
Moddibo kuwa daga inda yake zaune ya ɗaga kansa sama tare da juyawa bayanshi kana a hankali yace.
“Ya Salam ya ilahi ya mujabat da'awati meke Shirin faruwa”.
Cikin tsananin gigita da tashin hankali da firgici Khausar ɗin ta saki kuka mai cike da rauni tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un, hasbunallahiwani'imanwakil, mun shiga uku”.
Sai kuma ta juyo ta kalli Moddibo da ya gyara zamanshi kana a hankali yace.
“Babu abinda zai faru wanda Allah bai sani ba, Insha Allah Ubangiji zai mana maganin duk kan abinda yayi tsanani”.
M Jameel kuwa kasa furta komai yayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunsa.
ita kuwa Khausar ganin M Jameel na Hawaye kawai sai itama tashiga yin kuka amma ba mai sauti ba.
Cikin wani irin yanayin da bazai misaltuba Moddibo ya dubesa kafin yace.
“Haba J. Kamar ba namiji ba addu'a ya kamata muyi duk kan tsanani yana tare da sauƙi”.
Still dai M Jameel baice komai ba.
Shi kuwa Moddibo cikin sanyin jiki ya fuskanci Khausar cikin wata iriyar murya yace.
“Khausar tausayi na kike ji ne?”.
Cikin kwaranyar hawaye ta gyaɗa mishi kai tare da sakin raunataccen kuka mai cushe numfashi, lokaci ɗaya numfashin ta ya fara cushewa yana ɗauke wa, cikin yanayi wahalar neman numfashi taga Moddibo ya...!
Dai-dai lokacin kuwa ta farka daga baccin da takeyi ciki razana tare da kaɗuwa ta dafe kanta da takeji yana jujjuyawa.
Kana duk da sanyi da ake tsulawa a garin wani irin zufane ke tsastsafo mata ta ko ina.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya, ta juya gefen hagunta ta karanta A'uziyya ƙafa uku kana ta canza hannun kwanciyar ta zuwa dama.
Sai dai sam baccin yaƙi zuwa mata, sai ta kama karatun Alqur'ani cikin sassayan sauti,
Cikin ikon Allah ta samu bacci ya kuma yin awon gaba da ita.
Baki ɗaya Wunin wannan ranan akasalance tayi koda abinci ta kasa ci haka zalika koda yawan surutu sai ta rage sosai mafarkin ya tsaya mata arai da zaran ta tuna irin mafarkin da tayi sai taji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske.
Da daddare cikin ikon Allah data karanta Alkur'ani mai girma tare da bin haddarta da Malam Liman ya bata sai taji sauƙin abin aranta duk da kuwa bawai ta daina jin tsinkewar zuciyar bane amma ya ragu sosai.
Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Khausar suna zaune a farfajiya gidan Hajja Nana su uku ita Yaya Abba da kuma Dije suna hira jefi-jefi take sanya musu baki aciki daga ƙarshe ma ta miƙe tace zata je ta kwanta sai Dije ma ta miƙe ganin haka yasa Yaya Abba ya musu rakiya har gida.
Washe gari:Da safe still haka Khausar ta tashi bata da wani ku zari koda abinci ne ta kasa ci iyakacinta tasha Tea ko ruwan kunu sannan ta kasa faɗawa kowa irin mafarkin da tayi domin jikinta ya mutu sosai da mafarkin.
Da daddare ba kinta ɗauke da Sallama tashiga gidan Hajja Nana.
Asaman laɓɓa Hajja Nana ta amsa mata Sallamar tana binta da harara dan tunda taƙi markaɗa mata wake take jin haushi ta.
Ita kuwa khausar bata masan Hajja Nana nayi ba ta nemi waje ta zauna tare da kallon Hajja Nana tace.
“Yunwa nakeji ki bani abinci zanci”.
ta faɗa tana kallon ƙorenta dake jere guda goma sha Uku.
Harara Hajja Nana ta wurga mata tace.
“Gashi ki ɗauka ki ci”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da Matsawa jikin ƙoren tashiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa saboda taga gidan Malam Liman anyanka kaji cikin Sa'a kuwa tana buɗe ɗayan taga Jan miyar dage-dage da kuma tuƙeƙƙen tuwon shinkafa.
Ta gyara zamanta tare da wanke hannunta ta fara cin tuwon cikin Mintuna kaɗan ta cinye tass sannan ta kuma janyo wani Ƙoren dan sosai take jin yunwa sannan bata wasa da cikinta dan ita dai ko ciwo bai cika hanata cin abinciba karo na forko kenan a rayuwarta da abu ya tsaya mata a rai