Showing 72001 words to 75000 words out of 176046 words
har kina goyon bayan sa akan ni kin zaɓe sa kin barni? Yoh shine mugu mana ni ta gari”.
Ware idanu Asma'u tayi tare da langwaɓar da kai tana dariya tace.
“Haba ƙawar arziƙi matsayinki yafi haka, dan Allah kada ki sake faɗan hakan aise kisa ayimina dariya”.
Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.
“Kinsan gwara in gane matsayina ai tun wurima,
idan kinfi ƙaunar Moddibo insan matsayina”.
Dariya mai sauti Asma'u tayi da faɗin.
“Maida wuƙar ranki shi daɗe Fattanah”.
Murmushi Khausar tayi tare da kishingiɗa akan gadon.
Acan falo kuwa bayan Moddibo da M Jameel sun sake gaisawa da Ummi ta miƙe tashiga kichen ba daɗewa ta fito hannunta riƙe da babban tray dake ɗauke da Warmers ta ajiye musu.
Murmushi Moddibo yayi yace.
“Sannu da gajiya Ummi”.
Murmushi tayi tace.
“Yawwa Babana”.
M Jameel kuwa miƙewa yayi yashiga kichen ya dauko musu Plate da cups guda biyu kana ya dawo ya zauna.
Kulan ya buɗe, da sauri ya gyara zamansa jin wani ƙamshi mai daɗin ya ratsa hancinsu.
M Jameel ya lumshe ido tare da zuba musu akan Plate.
Moddibo ya matso tare da tsirawa Pride rice ɗin da yaji vegetables da naman kaza amsar spoon ɗin da M Jameel ke miƙa masa yayi, cikin fesar da numfashi Moddibo ya ɗibi abincin ya kai bakinsa, lokaci ɗaya yaji daɗi ya mamaye masa baki, kallon Ummi yayi tare da faɗin.
“Ummi wannan girkin yayi daɗi”.
murmushi tayi tare da tsiyaya musu tea mai ɗumi.
Bayan sun gama ci.
M Jameel ya goge bakinsa da tissue kana yace.
“Ummi ɗazun ina zakije dama?”.
Tana matsar da Flaks ɗin tea tace.
“Wallahi Maman Khausar zanje dubawa, bata da lafiya shekaran jiya a asibiti suka kwana jiya ne aka sallame su da safe”.
Girgiza kai yayu kana yace.
“Ayyah Subhanallah Allah yabata lafiya Allah yasa zakkan jikine”.
Amin Ummu tace.
Yayinda shi kuwa Moddibo Aransa yace. “Uhhhm yarinyar kamar aljana ita da mahaifiyar ta babu lafiya har ankwantar da ita a asibiti jiya-jiya aka sallame su, amma yau har ta gararo yawo, har tana rawa agidan mutane kamar wacce aka yiwa bushara da Aljanna, ita kuwa wannan daɗin me takeji”. sai kuma ya taɓe baki takaicin halayyar yarinya yasa bece musu komai amaganar ba.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.
“Toh Ummi mu zamu tafi”.
Ummi ta juya ta kallesa da murmushi afuskarta tace.
“Da wuri haka Babana?”.
M Jameel ne yace.
“Ai dama a gaggauce muka zo Ummi, dan kwana biyun nan naga ya maida hankalinsa akan rubutun da yake inagama ya kusan gamawa”.
Ummi kuwa kallonta ta mayar kan Moddibo kana tace.
“Masha Allah Ubangiji Allah ya taimaka, ya kuma baku sa'a ka kusa gama wa kenan?”.
Cike da nitsuwa Moddibo ya amsa da.
“Ameen”,Kana yace.
“Eh Ummi na kusa gamawa, amma waɗan da na tura ƙasar Ɓadamaya ma tukunna wanda na turawa, Sheykh Jabeer ya duba min su har yau basu dawo ba, to inaso kawai na haɗa wa'annan ma dake wancan bugun Hafs ne wannan kuma Warash ne”.
Yai da mgnar tare sauƙe numfashi kana ya cigaba da cewa.
Warash ne nake rubuta wa to inaso idan nagama rubuta wannan ɗin na tura masa, wala Allah ya tuna mishi da duba wancan ɗin.
Nasani abubuwa ne suka masa yawa da yake ya wanci yakin arewacin nan duk wanda ya rubuta Kur'ani shi ya ake turawa sai ya duba yagani toh zanyi ƙoƙari na gama rubuta wannan ɗin sai ahaɗa akai gaba ɗaya ko zan samu ya haɗa min su lokaci ɗaya idan ya duba ingancin su”.
Jinjina kai Ummu tayi cike da yabawa jajurcewarsa da kuma ƙoƙarin sa tace.
“Masha Allah Allah yatemaka Allah ya bada sa'a abu yayi kyau Allah yabar mana irinku Moddibo Allah yayi jagora”.
Moddibo kuwa cikin jin daɗin addu'ar ta yace.
“Ameen Ummi Allah ya amsa Nagode”.
Miƙewa M Jameel yayi idanunsa akan Ummin sa yace.
“Ummi zamu tafi”.
Tana ƙoƙarin kwashe Plate da sukayi amfani dashi tace.
“Toh Nagode Allah ya muku albarka”.
Suka haɗa baki wajen faɗin.
“Ameen”.
kana suka fice.
Bayan sun ɗauki hanya M Jameel ya dubi Moddibo wanda shike Driving ɗin yanzu yace.
“Ni ka sauƙe ni agida”.
Moddibo da still hankalin sa ke kan Driving yace.
“Ba zamu tafi tare ba?”.
Girgiza kai M Jameel yayi kana yace.
“A'a nasan rubuta zaka je kayi sannan Abba ya kirani akan batun yana so naje Ɓadamaye batun Company sa akwai sabbin Injina da aka kawo, za'a saka kaga na daɗe ban jeba, amma wannan karon ko naje baze wuce kwana biyu zanyi in dawo ba”.
Moddibo kuwa jinjina kai yayi kana yace.
“Toh yaushene tafiyar?”.
Kai M Jameel ya Girgiza tare da faɗin.
“Toh dai ban sani ba tukun”.
Moddibo dake ƙoƙarin shan kwana yace.
“Yawwa zanyi ƙoƙari inga na gama rubutunan idan zaka tafi sai ka tafi min dashi”.
Shi kuwa M Jameel Kai ya gyaɗa cike da gamsuwa da maganarsa yace.
“Toh shikenan hakan ma yayi Allah yatemaka”.
Moddibo ya amsa da.
“Ameen”,tare da parking motar bayan ya isa ƙofar gidan su M Jameel.
Sauƙa M Jameel yayi tare da yi masa sai anjima, kai Moddibo ya gyaɗa kana yaja motar ya tafi.
Yana isa gida bayan yayi Parking motarsa ya wuce Bedroom ɗinsa kasancewar yana da alwala yasa ya ɗauko abubuwan buƙatar sa na rubun Alkur'ani da yakeyu kana yaciigaba da rubutu, saida aka kira sallar La'asar sannan ya tashi yaje masallaci ya gabatar da sallan la'asar, bayan ya dawo kuma, yazo ya cigaba da rubutun, yana yi yana karantar Suratul Kahfi kasancewar yammacin jumma'a ne, sai misalin ƙarfe biyar kafin ya ajiye Kur'ani.
Acan ɓangaren Innayi kuwa zaune take akan kujera ’yar tsugunno acikin kichen tana juya miyar zogala wanda yaji namar Rago da kuma wadataccen man Shanu da wake yana tashin ƙamshi bayan ta sauƙe miyar ta ɗaura Ruwan shayi daya ji na'ana, kaninfari da kuma ɗanyan citta yana tafasowa yana ƙamashi mai daɗin shaka.
Flaks guda biyu ta ɗauka ta juye sannan ta ɗauki ɗaya ta nufi sashen Moddibo dashi.
Acan gidansu Asma'u kuwa bayan tafiyar Moddibo da M Jameel Khausar ta miƙe tare da fitowa falon Idanunta akan Ummi tace.
“Toh Ummi mu tafi ba dama kince gidan mu zaki jeba”.
Jinjina kai Ummi tayi tace.
“Eh Khausar inaso naje na duba jikin Mommyn ki”.
Ba tare data zauna ba tace.
“Toh Ummi mu tafi”.
Kai Ummi ta jinjina kana ta miƙe suka fita su ukun Bashir ƙanin Asma'u ne kaɗai suka bari agida Ummi da kanta take Driving Khausar da Asma'u na baya suna hira.
Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa Kallonsu Boka Kar'uzu yayi cikin wata razananniyar tsawa yace.
“Wannan maganin ya riga daya ɓaci, ta lalata komai yanzu sai anyi aikin dai-dai-ta fuskarta ma tukunna kafin azo ayi aikin jawo hankalinsa, yaran nan biyu da kuka gani kuke magana akansu yarane dasu na tsaye da sunan Allah da riƙo da Ibada, musamman ma Moddibo da kuke magana akansa kwata-kwata baya rabuwa da alwala ajikinsa ka masa zaiyi wuya”.
Cikin tashin hankali Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da duk tagama shiga ruɗu.
Boka Kar'uzu kuwa cigaba yayi da cewa.
“Yanzu sai munyi aikin wata uku kafin fuskarta ya dawo dai-dai sannan sai tabar Sallah na tsawon watanni shida kafin mu samu mu fara aiki shiko aikin za'ayi na tsawon watanni shida kafin ta fara nuna masa muradanta”.
Kana ya maida kallonsa ga Hajiya Lami data zabga uban tagumin tana kallon sa cikin Muryansa Mara daɗin Amo yace.
“Kema naki hakanne sai tayi wannan watannin”.
Dafe ƙirji Hajiya Lami tayi tare da zare Ido kana tace.
“Har Watanni shida shida Boka kafin wannan lokacin fa har sun kusa gama Ss 2 ma zasu tafi 3 awannan lokacin daka ɗiba mana”.
Cikin tsawa da hargagi yace.
“Dole sai anbi wannan ƙa'ida idan ba haka ba babu abinda zaku samu ya tafi dai-dai!”.
Ta gumi Hajiya Lami ta rafka kana tace.
“Shikenan Babu damuwa Indai burinmu zai cika tunda ai makarantar basu gama ba zamu bi ahankali”.
Ya yamutse fuska tare da watsa musu wani kallo da jajayen Idanunsa cikin wata murya mara daɗin Amo yace.
“Ƙa'idah ne yanzu zata je tayi ta aiki da wannan maganin na tsawon watanni ukku fuskarta zai koma dai-dai a Idanunsa sannan bayan wannan kuma tsawon watanni kar kuyi sallah daga nan kuma zan fara haɗa magani na tsawon watanni shida kafin su tun kare su daga magana”.
Murmushin Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zamanta tana fuskantar Boka Kar'uzu da kyau tace.
“Toh shikenan ba matsala.
Amma fa ciki ya zube aiki yayi kyau!”.
Wani irin mahaukaciyar dariya mai matuƙar razanarwa Boka Kar'uzu ya saki da faɗin.
“Ai dama dole aiki zaiyi kyau idan kun bishi da ƙa'ida wannan ma ku kuka je kuka ɓatashi!”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Godiya muke Boka ana gaba zamu kiyaye”.
Kai ta gyaɗa kana yace.
“Toh ya batun aikin toshe mahaifar!?”.
Kai Hajiya Bunayya ta Girgiza tare da faɗin.
“Boka muga ma da batun aikin Amina tukunna, kaga ga yayar ta ma tana zaune ba tayi aure ba, sannan ga itama Aminan ta girma shiru, amma ita kace rabonta ne yayi nisa abin ya ɗaure mana kai mun rasa yanda zamuyi har wajen ƙan wata na tura ta Aƙasar Khautal ko zata samu rabonta acan amma acan ɗin ma shiru kuma kaga ta dade da gama karatu amma har yau Auren bai samu ba zamu jona mata wani makarantar ta fara zuwa jami'a kawai, tunda itama kanta Amina dan wasa da karatun take da tayi shekaru biyu da gamawa amman sai aikin maimaita aji gashi har shegiyar yarinyar nan ta kusan cimmata”.
Kai Boka Kar'uzu ya ɗago daga bugun ƙasar da yake tare da cewa.
“Babu matsala ita Aseeya rabonta yana nan tafe”.
Cike da jin daɗi Hajiya Bunayya tace.
“Godiya muke Boka Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye Hatsabibi Uban Hatsabibai!”.
Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya kece dashi cikin jin daɗin kirarin da ta masa yace.
“Aikin ki zai tabbata ƙaramar la'ananniya Aljani ɗan ƙundalu mai ido Atsakiyar kai zai cika miki burinki ku fita da ƙafar hagu ta baya!”.
Miƙewa sukayi suka fice kamar yanda ya faɗa ransu fesss suna tsalle da kafar hagu kamar kutaren agwagi...
Acan ɓangaren su Ummi kuwa bayan sun isa gidan su Khausar sun gama gaisawa da Mommy da kuma Hajiya Ruƙayya da har zuwa lokacin suke tare.
Mommy tana murmushin tace.
“Ummi ya fama rigimar Khausar, ɗazun nan tace zata je ta duba ki ashe kina hanya”.
Dariya Ummi tayi tace.
“Ai lalle dai kam Hajiya Aysha babu ruwan Khausar ai”.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Kina dai karate ta Amma Khausar ba dai rigima ba?".
Aunty Ruƙayya tayi Dariya kana tace.
“Ai Khausar bata da rigima ita dai baza'ayi gulma agaban Idanunta bane, sannan ba za'a cakake ta ta haƙura ba, kunga kuwa ai da gaskiyar ta”.
Dariya Ummi tayi tace.
“Aikam de lalle da gaskiyar ta”.
Ita kuwa Mommy Dariya tayi kana suka cigaba da hira.
Washe gari Asabar suka koma makaranta Khausar kuwa cikin tsoro da fargaban abinda Moddibo zai mata ta zuciyarta ya riƙa bugawa da ƙarfi lokacin da yashigo raba musu questions pepar tayi zaton zai mata hukunci sai taga baima kalli inda take ba.
Shikuwa Moddibo kawai ya fita sabgarta ne ganin alamar bata da cikikakkiyar nutsuwa in ya biyata zata zarar dashi.
Akwana atashi haka al'amura suka cigaba da tafiya komai yana wakana Moddibo ya kammala rubutun Kur'aninsa ya bawa M Jameel ya tafi wa da Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa na Adamawa.
Satin M Jameel biyu ya dawo tare da shedawa Moddibo ya karɓa harma ya fara dubuwa Insha Allah nan kusa zai turo masa.
Karatun su Khausar na tafiya komai na tafiya dai-dai yanda ake buƙata Anyi gasar musabaƙa jihar Taraba Makarantarsu Khausar Al'ansar Academic school_ shine yazo na farko Khausar ce tazo na ɗaya a haddar Izu arba'in yayin da Asma'u tazo na biyu Aishatu Abdullahi tazo na uku ,A haddar Izu biyar Raudat ce tazo na ɗaya kyaututtuka masu yawa suka samu kana suka dawo cike da nasarori.
Yanzu karatu na tafiya akwana atashi babu wuya wasa gaske yanzu Khausar suna Ss2
thirth term suna shirye shiryen fara Exam gashi kuma Ramadan ya kawo kai yayin da ake ta shirye shiryen shiga Ramadan tuni Gwamnatin Jaha ta rarraba malamai zuwa inda ko wanne zaiyi Tafseer kamar yanda aka saba Moddibo da M Jameel antura su Babban Masallacin juma'a dake ƙofar sarki Gembu anan zasuyi Tafseer ɗin su na Ramadan.
Lokaci natafiya karatun su Khausar na sake tafiya yanda ake buƙata tsakanin Amina da Khausar babu wani jituwa hasalima gaba ce domin har gobe M Jameel na sake nuna kulawa ta musamman akan Khausar yayinda Moddibo kuwa kwata-kwata baya lura da al'amuran Khausar hasalima idan tayi laifi zai yanke mata hukunci fiye dana kowa wannan dalili yasa basa shiri kana babu wata jituwa atsakaninsu.
Alhamdulillah ayaune Khausar suka rubuta exam na ƙarshe kuma da Geography suka rufe.
Taro Moddibo yasa aka haɗa kamar yanda aka saba a kowani ƙarshen hutu ko baki ɗaya Malaman sun haɗu awajen zamansu haka ma ɗalibai Khausar da Asma'u na zaune awaje ɗaya.
Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya nufo wajen as usual cikin shigar sa kaman ko yaushe sanye yake cikin Jallabiya fari kansa naɗe da hirami idanunsa sanye da ɗan siririn farin glass daya ƙawata kyawun fuskarsa yalwataccen sajensa zuwa gemunsa ya kwanta luf-luf yana sheƙi.
Cikin tsantsar nutsuwa da sanin darajar kansa ya gyara zaman microphone ɗin tare da hura iska kaɗan kana yayi gyaran murya yace.
_“Bismillahir Rahmanir Rahim, Innalhamdulillah nahmaduhu wanasta'inuhu wanastaghfiru wa'nazubillahi min shururi anfusna wamin sayyi ati a'amalina, man yahdillahu fala mudillahlah waman yudlil fala hadiyala, Wa'ash hadu Allah ilahalillahu, Wa'ash hadu anna Muhammadu Abduhu wa Rasulullah (S.A.W)”._
Sai kuma ya ɗan lumshe idanunsa tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.
“Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala mai kowa mai komai, da yakawo mu wannan lokaci da muke shirin karɓan hutu saboda gabatowan wannan wata mai falala, haƙiƙa watan Ramadan wata ne mai falala da rahma wanda duk kan musulmi yake da burin ganinsa.
Baki ɗaya wajen shiru yayi kowa ya maida nutsuwarsa zuwa garesa yayin da Samira kejin aduk lokacin data mallakesa babu macen da takaita sa'a a faɗin wannan duniya tamu ta bani adam.
Malam Arɗo kuwa Aransa yake jin Moddibo ne Garkuwa kuma ginshiƙin makarantarsa.
Moddibo kuwa cikin yanayin sanyin Muryar sa mai cike da nutsuwa ya cigaba da cewa.
“An abu Huraira ta radiyallahu anhu,
_Manƙama Ramada Imanan Wahtisaban gufra lahu mata ƙaddama min zambi muttafaƙun Alaik”_
Ma'ana ankarbo daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda, yana cewa Duk wanda watan Ramadana ya kama yana mai Imani da kyautatawa ana kankare masa zunubansa da suka gabata”.
Ya sauƙe sanyayyar Ajiyar zuciya mai sanyi kana ya cigaba cewa.
“Wannan kaɗai zai iya nuna maka muhimmanci da kuma darajar wannan wata hakika wannan watar ba wata bane na wasa watane daya kamata mu tsaya mu miƙa lamuranmu ga Ubangiji Mabuwayi gagara Misali, sannan mukasance masu yawan Karatun Alkur'ani, Istigfari, hailala da kuma tasbihi, ba sai na tsawaita ba ko naja duk abinda zance kun sani”.
Sai kuma ya maida kallonsa ga sauran Malaman yace.
“Koda akwai mai magana?”.
Duk suka girgiza kai alamar babu Moddibo kuwa M Jameel ya miƙawa microphone ɗin kana ya koma ya zauna shi kuwa M Jameel bayanai ya ƙara akan na Moddibo kana ya sanar dasu Bayan Sallah da sati ɗaya zasu dawo.
Yana gama Maganar ya juya tare da kallon Khausar da ita adai-dai lokacin Idanunta na kasansa cikin Sanyayyar Murya yace.
“Lelewal zoki rufe mana da addu'a!”.
Anutse Khausar ta gyaɗa kai tare da miƙewa.
Shikuwa Moddibo kallon mamaki yabin M Jameel dashi amma baice komai ba.
Amina kuwa jitayi tamkar zuciyarta zai buga saboda baƙin ciki da kishi.
Ita kuwa Khausar cike da tsoron Modibbo dake sa ta nemo nutsuwa ta amshi microphone ɗin cikin zazzaƙan Muryanta tayi addu'a kana aka tashi kowa ya watse dalibai nata murnan hutu kowa ya koma gidansu cike da farin ciki.
Da daddare Khausar na zaune akan 1sitter hannunta riƙe da wayar Mommy yayin da Mommy kekan 3sitter ta miƙe ƙafafunta Hannunta riƙe da kofin tea.
Anutse Mommy ta ɗago kanta tare da sauƙe Idanunta dake kan Khausar Wacce baki ɗaya hankalinta ke kan wayar da take dannawa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Khausar tunda an baku hutu ko dai za kije Jauro Yaya kuyi azumi tare".
Da sauri Khausar ta ajiye wayarta tare dasa hannu ta dafe ƙirjinta tace.
“Nashiga Ukuna! Dan Allah dan darajar Annabi Mommy Kar kiyi Wannan maganar, kibar tsohuwar nan tunda dai bata ne maba”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan yanzu azumi saura sati amma nasan zaiyi wuya acikin satin nan idan bata neme kiba”.
Marerece fuska Khausar tayi kana tace.
“Allah yasa karma ta nemeni duk da garin yamin daɗi Mommy amma inaso in tayaki aiki”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Toh shikenan ba matsala hakan ma Allah ya zaɓa Mana abinda yafi zama alkhairi”.
Acan ɓangaren su Hajiya Lami kuwa zaune take afalon Hajiya Bunayya tare da Samira Sani da kuma Amina.
Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Yanzu dai saura mana watanni biyu mu gama cika Umarnin Boka Kar'uzu na watanni shida daya ɗiba mana kada muyi Sallah, kafin na ƙarshe da zamuyi muje mu karɓi maganin su zo suyi aiki dashi”.
Murmushi Hajiya Lami tayi tare da jinjina kai tace.
“Eh haka ne bayan Sallah da sati Uku zamu gama”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Gashi kuma azumi ya gabato amma acikin wannan azumin ma ace ba zamuyi sallah ba kuma watan falala da ibada!?”.
Wani kallo Hajiya Lami tayi mata kana tace.
“Idan ke zakiyi sallah ki ɓata aikin da kikayi to kinyi na wancan watannin shida da kika samo fuskar ’yar ki ya dawo dai-dai a idanunsa, sannan yanzu wata ɗaya da rabi daya rage ne zaki ɓata ba zaki iya jira ba. Agaskiya nikam zan cika ƙa'idata domin in samu cikar burin ‘yata”.
Samira kuwa zama ta gyara tana fuskantar Hajiya Bunayya da kyau tace.
“Agaskiya Ummah kar muyi wasa da wannan damar da muka samu idan yaso idan muka gama sai mu rama bashin sallah dake kan mu!”.
Ita kuwa Amina Kallon mahaifiyarta tayi tare da ƙanƙance Idanu kana tace.
“Yanzu ke Ummah wasa zakiyi da wannan damar da muka sha wahala tsawon watanni muna yi!?”.
Zare ido Hajiya Bunayya tayi tare da nuna kanta da yatsa tace.
“Ina waya faɗa miki ko an faɗa miki daɗi nake ji ga yayarki azaune gaki kuma kema azaune”.
Ta ida maganar dai-dai lokacin da Asiya ta fito daga Bedroom bayan ta gama sauraron duk abinda suke faɗa zama tayi akan 1 sitter dake fuskantar Hajiya Bunayya cikin sanyin murya tace.
“Gaskiya Ummah!, Gaskiya Ummah!! Kada neman duniya yasa mu rasa ƙiyama tare da rahamar Ubangiji, Ummah sallah da arayuwar duniya itace farkon abinda