Showing 111001 words to 114000 words out of 176046 words

Chapter 38 - Sakayya 1 Hausa Novel Complete

ciwon ciki”.
Dafe kunci M Jameel Yayi yana saurarensa.
Murmushi Jalaludeen Yayi kana ya cigaba da cewa.
“Tun haɗuwar mu na farko kafin ku fahimci wanene ni kafin ku fahimci komai akaina, kana tun kafin afahimci wanene ni asan komai akaina na bashi abinda yasha wanda ya karyar masa da ƙarfin sha'awarsa har yake ji kamar baya buƙatar mace acikin rayuwarsa”.
M Jameel ya gyara zamansa tare da cewa.
“Ikon Allah”.

Jalaludeen kuwa cikin yanayin su na can yaci gaba da cewa.
“Toh ajiya akwai abinda yafaru ko dai mace tashiga rayuwarsa ko dai akwai macen data kama jikinsa wannan dalili yasa gaba ɗaya takarya alƙadarin abinda ke jikinsa!”.
Ajiyar zuciya M Jameel ya saki kana yace.
“Toh fa”.
Murmushi Jalaludeen yayi tare da faɗin.
“Kai kuma kwaɗayin ka ne ya kaika dana bashi maganin yana cikin sha kawai ka amshi kofin kasha shiyasa kuka kasance atare haka amman ai kai naka ba kamar nashi bane ”.

Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Amma dai gaskiya Jalaludeen baka da mutunci”.
Dariya Jalaludeen yayi kana yace.
“Nifa bance komai ba gaba ɗaya abinku lafiya lau yake kawai dai sha'awar ce na kwantar”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“Toh yanzu shi kuma wannan ya za'ayi dashi dan yanzu wallahi ya tashi ya tafi ɗaki kamar zaiyi kuka”.
Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.
“Kukan ma yakeyi yanzu”.
Ware ido M Jameel Yayi kana yace.
“Lallai dai kam maza sun gamu da aiki kenan”.
Jinjina kai Jalaludeen yayi tare da cewa.
“Gaskiya yanayin daya ke ciki ne awahale yake haka ya wuni jiya still haka ya kwana gashi kuma yau ma ya wuni haka”.
Cike da tausayawa M Jameel yace.
“Toh yanzu ya za'ayi ?”.
Girgiza kai Jalaludeen yayi tare da cewa.
“Gaskiya ban sani ba dan bani da yanda zan mishi kawai abune daya zo masa babu yanda za'ayi haka zaita rayuwa mafita ɗaya ne kawai yayi ƙoƙari yayi aure”.

Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da cewa.
“Ok zamu yi ƙoƙari muga mai ya dace tunda gashi dama duk abinda ya dace mun gama”.
Jinjina kai Jalaludeen yayi kana yace.
“Masha Allah amma yanzu ka samu ruwan ɗumi kasa masa laimun tsami yaji kana ka sanya zuma yaji sai ka bashi yasha zai ɗan ji sauƙi”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan ba matsala mun gode”.
Sallama sukayi tare da katse kira.
Miƙewa M Jameel Yayi yashiga cikin kichen dake falon ya buɗe Flaks dake ɗauke da ruwan tea ya zuba a Cup lemun tsami ya duba yaga babu rufe Cup ɗin yayi ya nufi cikin gadin ɗin gidan ya tsunko guda biyar sannan ya dawo ya wanke tare da matse su duka acikin shayin kana ya buɗe kofin roban zuma yasa.
Fita yayi a kichen ɗin ya nufi Bedroom din Moddibo yayi Knowking ƙofar.

Dai-dai lokacin da Moddibo ya cire kayan jikinsa ka ya zura Jallabiya kasancewar boxers ya takure masa jiki har yana jin mallakinsa na yimasa ciwo saboda yanda ya takuresa ya hanasa miƙewa cikin gajiyawa ya mike ya cire boxes ɗin tare da cewa.
“Bari naga iya inda zaka tsaya uban ƴan zalamammu”.
Yayi maganar yana kallon jikin nasa daya miƙe ya tsaya acikin Jallabiyar.
Muryar M Jameel yaji yana cewa.
“A.J ka buɗe min ƙofar mana in baka magani”.
Daga ciki Moddibo ya buɗe masa ƙofar.
Kallonsa M Jameel Yayi sai kuma ya kalli yanda ya ɗaga rigar kawar da kai gefe yayi yana jin dariya na neman kufce masa.
Kofin dake riƙe ahannunsu ya miƙa masa.
Cikin Sanyayyar muryarsa yace.
“J Me wannan?”.
M Jameel ya Kalli kofin kana yace.
“Kasha mana zaka ji sauƙin abinda ke damunka na fahimci meke damunka A.J”.

Moddibo bai sake cewa komai ba ya amshi Cup ɗin ya koma bakin gado ya zauna tare da kafa kansa ya shanye tass kana ya ajiye kofin, cikin ikon Allah lokaci ɗaya yaji zufa ya fara sauƙa masa Atake yafara jin abinda ke damunsa na sauƙa kaɗan-kaɗan amma still jikinai ɗin na nan amiƙe ahankali yaji lips ɗin sa ya daina rawan zamewa yayi ya kwanta akan gadon yana sakin ajiyar zuciya akai-akai.

Acan gidansu Khausar kuwa zaune suke afalon Mommy suna cikin hira ka jiyo sallama.
Cikin sauri Haiydar ya ɗago kansa tare da cewa.
“Laaaaah....!


*Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki yar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group na ɗin da zanke posting. Ko kinga littafin SAKAYYAH a waje na satane*





*By*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[24/07, 6:14 AM] Halimatu A/rahman Sadeeya: Spjnyh. Miƙewa Haiydar yayi kana ya nufi ƙofar falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Oyoyo Uncle Naseer”.
Khausar dake zaune kan 1sitter sanye cikin riga da baƙin wando Pencil da riga pinch color mai gajeren hannu gaban rigar an rubuta Never Give Up manyan boobs ɗin ta sun cika gaban rigar yayin da bajejjen ƙugunta ya baje acikin wandon, kanta sanye da hular Net baƙi gashinta ya zubo ta gefen wuya, a hankali ta juyo ta kallesa tare da faɗaɗa fara'ar dake saman fuskarta kana tace.
“Laaa Uncle Naseer”.
Shi kuwa Naseer ido ya zuba mata yana sakar mata da wani irin shu'umin murmushi yayin da yashiga bin ilahirin jikinta da kallo wani irin kallon Up and Down yake mata yana jin komai nata na kars burgesa soyayyar ta na kuma ninkuwa a ransa.
Cikin wani irin salo kana still Idanunsa na kanta ya wani lumshe ido afili ya furta.
“Masha Allah Matata ta girma”.
Mommy dake zaune kan 3sitter tayi murmushi tare da cewa.
“Masha Allah Naseer mutanen India kwanan nan mukayi magana da Aunty Jameela kece min ka kusa dawowa Ashe-ashe dawowa yazo ma”.
Murmushi yayi kana cikin yanayin zumuɗinsa yace.
“Aidai kam suma Surprised ɗin su nayi babu wanda yasan dawowana akwanan nan kawai sai ganina sukayi”.

Cike da kulawa Mommy tace.
“Masha Allah sannu da zuwa ka iso”.
Raudat da Ramadan dake zaune suka mike tare da zuwa suka riƙe hannunsa,hannun Raudat ya riƙe tare da ɗagata sama kana yace.
“Iyeee Baby Raudat Masha Allah an girma anyi kyau. Amma dai duk da haka Matas tayi miki wayau ta fiki kyau”.
Murmushi Mommy dake zaune tayi kana tace.
“Haka dai kace”.
Ware ido yayi kana idanunsa akan Khausar yace.
“Allah kuwa Mommy dubi fa Khausi na tafita kyau”.

Khausar kuwa lallausan tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta.
Sai kuma ta miƙe ta nufi kichen ta ɗauko drinks da Snacks sai kayan Friut tafi to masa dashi.
Har zuwa lokacin batayi magana ba sai dai da zaran sun haɗa ido zata sakar masa da ɗan guntun murmushi kamar yanda shima yake sakar mata.
Haiydar kuwa da sauri ya saki hannun Naseer kana ya nufi sashen Hajiya Bunayya yana faɗin.
“Ummah,Ummah ga Uncle Naseer kizo ku gaisa".
Miƙewa Ummah tayi fuskarta ɗauke da murmushi Amina ma miƙewa tayi tana murmushi tabiyo bayansu.

Cike da farin ciki Amina tace.
“Uncle Naseer mutanen India”.
Washe baki Naseer yayi domin shi mutum ne mai fara'a da son nuna shi wani ne, kana ga fafa da iyayi baya ga haka yana da budeɗɗen ido da son holewa.
Ita kuwa Hajiya Bunayya kallonsa takeyi da murmushi afuskarta tace.
“Naseer sai ganinka mukayi babu sanarwar anyi karatu angama ka dawo Nigeria kenan?”.
Sha fa sumar kansa yayi yana shan Fruit da Khausar ta kawo masa yace.
“Wallahi kuwa Ummah nazo ganin Matata ce muyi aure in ɗauke ta mutafi.
Amma Ziyara nazo yi muku zan koma da matata, dan bazan iya zaman Nigeria ba”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Ayyah Naseer ai nan ma muna da waja-je masu kyau kodai India sunfi mu Weather mai kyau ne?”.
Girgiza Kai yayi tare da cewa.
“No Mommy bawai Weather mai daɗi ba kawai dai can ɗin zan samu aiki ne sannan gaskiya ni yanzu bazan iya rayuwar Nigeria ba”.
Ya ida maganar yana ya mutse fuska cike da Iyayi.
Murmushin da bai wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Aikam dai kam yayi kyau Allah ya taimaka bari na koma ina aiki”.
Ta ida maganar tare da miƙewa dan Allah ya sani ya ƙona mata rai da batun ya aure Khausar su koma India.
Amina kuwa siririn tsaki taja cike da jin haushin yanda Naseer ke Shish-shigewa Khausar ta miƙe tabi bayan Hajiya Bunayya suka fice.

Bayan fitarsu Mommy ta miƙe tashiga Kichen Haiydar ma miƙewa yayi tare da ɗaukar Ramadan da Raudat suka fita danmai yi musu lesson yazo.
Falon ya rage daga Khausar sai Naseer, Ahankali Khausar ta miƙe da niyyan barin falon cikin sauri Naseer yace.
“Ohh My dear Wife Why are you going?”.
Murmushi Khausar tayi aranta tace Ohh Uncle Naseer sam bazai canza ba, wannan kalma ya riƙe ta tun yarinta alokacin batasan ma'anarsa ba amma yanzu da zaran ya faɗa kunya take ji wai matarsa ko kunya faɗa agaban su Mommy baya ji.
Anutse ta dawo ta zauna a inda ta tashi, cikin tsareta da Ido yace.
“Tunda baki gaisheni ba bari in gaishe ki”.
Cikin sauri tayi ƙasa da kanta kana tace.
“A'a Uncle Naseer ina yini ya karatu fatan ka dawo Lafiya?”.
Sumar kansa ya shafa kana yace.
“Karatu Alhamdulillah ya naki karatun??”.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Alhamdulillah Uncle Naseer nan da kwana goma zamu gama Secondary school Insha Allah”.
Washe baki yayi yana binta da wani irin kallon yace.
“A'a Masha Allah Abu yayi kyau kenan abu zai tafi dai-dai yanda aka tsara”.
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Ɗago kansa yayi tare da miƙewa ya koma kusa da ita.
Cikin wata narkakkiyar murya ya kalleta tare da cewa.
“Khausar ina fatan baki manta da maganar mu bako?”.
Murmushi tayi still ba tace komai ba sai ƙasa da tayi da kanta tana cigaba da wasa da yatsun hannunta”.
Shi kuwa Naseer sake narkar da muryarsa yayi tare da faɗin.
“My Khausi kinsan dai ina sonki, ke tawa ce inaji Ajikina Ubangiji ya halicce ki ne domin ni kaɗai kinsan ina matuƙar ƙaunarki ina burin ki kasance matata ke ta dabance ina miki sahihiyar ƙauna bani da burin daya wuce mu zamto ma'aurata in mori ni'imar da Allah ya halitta miki”.
Batare data ɗago kanta ba tace.
“Uhm”.
Shi kuwa wani narkar da fuska yayi tare da lanƙwasar da harshe kana yace.
“Meyesa ne komai nace sai kice Uhm?. Yanzu ke kanki bakya jin kina so kiyi Aure ne? aike kanki kin girma kin kai matakin da akan kanki zaki buƙaci na miji atare dake musamman ma na miji irina wanda zai iya gamsar dake tare da biya Miki duk kan buƙatunki ko ba haka bane?”.

Lokaci ɗaya Khausar ta kwaɓe fuska cikin yanayin rashin jin daɗi da kuma rashin tsammanin abinda ya faɗa ta ɗago kanta tare da Kallonsa sai kuma ta kawar da kanta gefe fuska a tsuke.
Shiko sake narkar da murya yayi tare da tsira mata Idanu kana yace.
“Shifa rayuwar nan baya tafiya dai-dai dole sai ansamu dai-dai-to atsakanin halittar Namiji da mace, rayuwar nan bata da wani daɗi idan har babu mace akusa da namiji, haka itama mace rayuwar bata mata daɗi idan har babu Namiji akusa da ita, musamman idan anfara tafiya irin matakin shekarun kin nan daga Sha tara, Ashirin, Ashirin da ɗaya,Asirin da biyar, Talatin,har zuwa talatin da biyar dole tana buƙatar Namiji”.
Ya sake narkar da murya yana binta da wani shu'umin kallo yace.
“Muyi Aurenmu Khausar zaki ci gaba da karatunki a India sai kije kiyi karatunki acan”.

Ƙasa ta sake yi da kanta kana cikin yanayin ɓacin rai ta ɗago batare data yarda sun haɗa ido ba tace.
“Ni bana sha'awar zuwa India nafiso in zauna an ƙasata kusa da Mommy na bana buƙatar duk wani abu da zai nesanta ni da ita da kuma ƙasata domin duk abinda India take dashi ai muma muna da shi harma fiye da nasun”.
Cikin sauri ya sake Matsawa kusa da ita tare da sanya hannunsa zai kamata.
Da mugun sauri ta kauce ranta babu daɗi ta kallesa kana tace.
“Ya haka Uncle Naseer mai yasa zaka kama min hannu?”.
Ido ya lumshe yana jin sautin muryarta na ratsa shi sai kuma ya buɗesu akanta tare da cewa.
“Ohh My God wai Khausar har yanzu baki waye bane? me haka kamar ba ƴar zamani ba!? Dan na taɓa ki ai bawani abu bane kada ki manta tun kina ƙarama ko su Abba sun sani ke mallaki nace idan Ubangiji ya nufa”.

Fuska ta sake ɗaurewa kana cikin sauri tace.
“Toh kabari sai Ubangijin ya nufa kasamu. Shaidu sai inzama mallakin naka”.
Ta ida magarta tare da miƙewa tabar wajen.
Binta yayi da kallo bajejjen ƙugunta wanda duk takun da tayi sai sun motsa tamkar da gangan take juyasu.
Dai-dai lokacin kuma Mommy ta fito daga kichen yana ganin ta ya miƙe tare da cewa.
“Mommy bari in isa wajen Yafendo Dadu”.
Shi ɗin ɗan ƙanwar Gimbiya Dadu ce,
Ya ida maganar tare da ficewa kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga falon.

Gimbiya Dadu dake zaune tana shan Fruit ta Washe baki kana tace.
“Nasiru lallai mutanen India masha Allah sannu da zuwa”.
Zama yayi daga gefenta yana murmushi kana yace.
“Yafendo fatan mun sameku lafiya?”.
Cike da farin ciki tace.
“Lafiya lau Nasiru ina ƴar Uwata ƴar Autanmu”.
Zamansa ya gyara tare da cewa.
“Tana lafiya tace in gaisheki”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Ayyah Ina Amsawa”.

Gyaran murya yayi tare da fuskantar Gimbiya Dadu kana yace.
“Yafendo na gama karatuna yanzu na dawo sannan na dawo da burin yin Aure. Ya maganar mu da khausar tana nan dai ko?”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Gimbiya Dadu ta sauke tare da lumshe Idanunta kana ta saki wani shu'umin murmushi tare da kallonsa kana tace.
“Sosai ma kuwa maganar ku tana nan mai zai hanata da izinin Ubangiji maganar ku tana nan baka da matar data wuce Khausar yau ɗin nan zan yiwa Abbansu maganar”.
Cike da farin ciki ya saki sanyayyar ajiyar zuciya kana yace.
“Kai Alhamdulillah Yafendo na naji daɗi”.
Murmushi kawai tayi shi kuwa miƙewa yayi bayan sun sake taɓa hira ya tafi.

Bayan kwana uku.
Ahankali Khausar ta sauƙa daga motar dake kaisu makaranta hannun riƙe da Raudat ta nufi ajinsu ta kaita kana ta dawo tashiga ajinsu Lokacin har an fara raba booklet kallonta Malam Isma'il dake raba Booklet ɗin yayi kana yace.
“Lelewal mai yasa kike son zuwa letti ne Exam ɗin ma baza ki fito da wuri ba?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da cewa.
“Ayyah Malam ayimin afuwa”.
Harara Samira Sani dake bayan ta ta watsa mata cike da tsanar ta Asma'u dake gefen ta ta girgiza kai domin ita dai ta rasa me. Khausar ta tsare musu suka tsaneta.
Khausar kuwa zama tayi Malam Isma'il ya bata Booklet da kuma Quatons peper Na Arabic da zasuyi yau ma kamar kullum tun kafin a gama rabawa Khausar tashiga answering Questions ɗin cikin mintunan da baza su gaza ashirin ba ta kammala.

Acan office ɗin Moddibo kuwa zaune yake ya jingina bayansa da jikin kujera yayin da ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya akan deks ɗin Idanunsa na lumshe.
Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da jan dogon tsaki.
Domin da zaran ya rufe idanunsa babu abinda yake gani sai moment da suka kasance da yarinyar cike da damuwa ya sauƙe numfashi kana aƙasan ransa yace.
“Na godewa Allah da yasa karatun yaran nan yazo ƙarshe kana naji daɗi da cewa sun gama Exam ɗina, bazan sake shiga ajinsu ba”.
Da sauri ya runtse Idanunsa haka nan yake jin kunyar kansa da kansa ya rasa ta yanda zai fassara al'amarin yasan tun farko yarinyar bata da kunya bare kuma wannan abu ya faru shin taya zai iya haɗa ido da ita?.

Anan sashin su kuwa.
Atare Khausar da Asma'u suka fito daga Area class ɗinsu har zasu wuce suka hango M Jameel tsaye.
Abakin Office ɗin su Moddibo.
M Jameel ne tsaye ya jingina bayansa da jikin ƙofar yayin da Amina ke tsaye gefensa cikin iyayi da yauƙi ta kashe murya tare da cewa.
“Malam sai gobe idan Allah ya kaimu zan dawo ko Principal ya dawo na amshi result ɗina”.
Anutse M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.
“Ok Allah ya kaimu ki gaida gida”.
Sake karya murya tayi cikin tsaresa da ido tace.
“Toh gida zaiji Malam kaima ka gaida gida”.
Jinjina kai yayi batare daya sake kallonta ba yace.
“Gida zaiji”,Juyawa tayi tabar wajen.
Dai-dai lokacin da Asma'u da Khausar suka iso a tare Kallonsa Khausar tayi tare da cewa.
“Barka da rana Yah Jameel”.
Murmushi ya sakar mata kana yace.
“Yawwa Khausi bar ka dai yanzu kam an zama manyan ƴan mata ankusa agama Secondary school a huta a shiga babin girma ko?”.
Jinjina kai tayi cikin jin daɗi ta kalli Asma'u kana tace
“Ai lallai dai kam bari kawai Yah Jameel jinmu nake tamkar ansaki tsuntsuwa daga sheƙarta.
Wani irin daɗi mukeji mun kusa mu rabu da rayuwar bauta rayuwar duka cin zali, kaɗe ɗan kwali, harara, tsawa, hantara,”.
Kallon ta M Jameel Yayi tare da juya idanunsa zuwa office ɗin ya mata alamar Moddibo na ciki.
Cikin sauri ta sanya hannunta ta rufe bakinta tare da barin wajen bayanta Asma'u tabi tana ƙyalƙyala dariya tare da cewa.
“Khausar ga Moddibo na miki magana wai kije”.
Dariya M Jameel yayi ganin
Cikin sassarfa Khausar ta fice daga wajen batare data yadda ta juya ba.

Moddibo kuwa na zaune a office duk Maganar da sukayi akunnensa da zaran sautin muryanta ya ratsa kunnensa zaiji tsikar jikinsa ya tashi tamkar ana stikaresa da allura hakan yasa ya runtse Idanunsa da ƙarfi kana yayi shiru.
Allah ne kaɗai yasan yana yin da yake ciki.

Khausar kuwa na fita wajen motarsu ta nufa ta samu duk su Amina su shiga ita kadai ake jira tana zama Driver yaja suka tafi.
Asma'u kuwa na fita ita da Bashir mai Napep ɗin su ya iso ya ɗauke su suka tafi.

Washe gari da yamma bayan Khausar sun dawo makaranta misalin ƙarfe Uku ta fito cikin wata Bugaggiyar shadda milk color anyi masa ɗinkin dogon riga da kuma zubi da akayi sa da Coffee zare fuskarta ɗauke da light Make-up yayin da tayi ɗaurin Aysha Buhari ta zuba jelar gashinta ta gefen dama dake fitar da sanyayyan ƙamshi kana ta yafa milk colour gyale akafaɗarta Hannunta riƙe da jaka Coffee haka ma takalmin Half cover coffee color jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Balila da kuma Sedection.
Kai tsaye Bedroom din Mommy ta nufa bakinta ɗauke da sallama tashiga ganin Mommy Bata ciki yasa ta fito tare da nufar kichen.

Tsaye ta samu Mommy tana yanka albasa.
Mommy na ganinta tace.
“Har kin gama shiryawa?”
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh Mommy na gama shiryawa”.
Jinjina kai Mommy tayi tana cigaba da yanka albarsar tace.
“Idan kinje ki Gaishe da Ummin Asma'u”.
Kai ta gyaɗa tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login