Showing 42001 words to 45000 words out of 176046 words
har ya hanata cin abinci na kwana biyu son ta Tara yunwar shiyasa.
ta cinye ƙore biyun tas dan dama tuwon ba wani mai yawa ake samata ba tunda akwai yawan kanukan.
Hajja Nana kuwa juyawa tayi da mamaki ta kalleta kafin tace.
“Yanzu har kin cinye tuwon nan”.
Kai Khausar ta gyaɗa mata tace.
“Na cinye mana kuma yanzu ma ƙarawa zanyi dan yunwa nakeji rabo na da abinci tun shekaran jiya da daddare fa sai dai in ta Shan abu mai ruwa-ruwa”.
Taɓe baki Hajja Nana ta kuma yi tace.
“Toh bubbuga rumbu ga shican ki ƙara ki cinye duka ma in Kinga dama”.
Ta Faɗa tare da tura mata wani akoshin.
Ɗauka Khausar tayi kamar wasa ta cinye dake abincin ba wani da yawa ake sawa aƙoron ba dake sun san cewa ƙorenta da yawa mafi yawan lokuta ma loma ɗaɗɗaya takeyi ako wani ƙoren idan tayi loma sha uku ya wadatar mata a dai cikin tsohuwa ta kuma tsinci nama ta cinye to shiyasa ba'asa mai yawa.
Ita kuwa Hajja Nana ganin yanda Khausar ke cin abinci yasa tayi zaton gatse take mata ta harareta da faɗin.
“Mutum kamar jaki wannan ci haka ki cinye wannan ƙoren ki cinye wancan”.
Ta ida maganar tare da sake tura mata wani ƙoren.
Ita kuwa khausar ta ƙoshi amma saboda ta ƙular da ita yasa ta janyo ta buɗe naman kan abincin ta cinye sannan ta gutsiri kamar loma biyar ta zuba akwanan dake empty.
Wani kwanon Hajja Nana ta kuma tura mata still ta cinye naman ta kuma gutsura ta zuba a sauran kwanon.
Hajja Nana ta dube ta cikin tsareta da ido tace.
“Wai har yanzu baki ƙoshi ba?”.
Khausar cikin yamutsa fuska ta gyaɗa kai kana tace.
“Eyyy ban ƙoshi ba”.
Wani akoshin Hajja Nana ta sake tura mata, Khausar kuwa laluma ta cigaba dayi idan taji da nama ta cinye ta gutsits-tsira tuwon ta bari.
Ita kuwa Hajja Nana kamar wacce akace ta leƙa taga aika-aikan da Khausar keyi da tuwon ta miƙe cikin fushi tace.
“Shegiyar yarinya gantalelliya ni kike nunawa barikanci, 'yar banza kinje kin zauna gidan Mayu kema kin koma kamar Mayya, sai cin nama kamar kura, wato ma duk naman kike lalubewa dan mayta ai dai na sani in dai ba cikin zanine da keba ai yaci ki ƙoshi”.
Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da riƙe ƙugunta tace.
“Naci ɗin idan ni Mayya ce kinsan inda na samu maita, tunda nazo saboda shegen maƙo ko zabuwa ɗaya kin kasa yanka min gaki da Zabbi kamar zasu kashe ki ga shanu kuma aina Babana ne”.
Salati Hajja Nana tayi tare da fashewa da kuka.
Kasancewar duk dare aƙofar gidan ta suke zama yasa Baffa Umaru daya ji sautin kukan ta ya miƙe kasancewar Allah ya bashi kunne komai ƙanƙantar sautin abu ya kan iya ji.
Ganin Hajja Nana na kuka yasa Baffa Umaru nufarta tare da cewa.
“Addah Nana Meya faru?”.
Nuna Khausar tayi da hannu kana tace.
“Wannan ‘yar Usmanu har zata min gori wai gadon Ubanta na riƙe kaji shegiyar gantalalla yarinya dan ma Allah yayi dan ke macece!”
Ƙasa da murya Baffa Umaru yayi yace.
“Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri kinsan yarinta ke damunta idan ta girma ba zatayi ba”.
Ya ida maganar tare da jan hannun Khausar suka fice waje.
Bayan sun fita ya juya ya kalleta yace.
“Haba Khausar kidena ki koyi yanda zaki zauna da manya kinga Addah Nana tsufa ya kamata tana buƙatar rarrashi da lallami, kinga duniyar nan ba matabbata bace idan yau kaine gobe ba kai bane ita rayuwar nan bata da tabbas, ki koyi magana mai daɗi ke idan Mahaifinki ina ita fa ɗan ta ne data haifa acikinta kuma ɗan ta mafi soyuwa agareta kada ki sake haka kinji Khausar am”.
Ta gyaɗa masa kai da faɗin.
“Toh shikenan Insha Allah bazan sake ba”.
Ya shafa kanta yana murmushi yace.
“Allah ya miki albarka kizo muje gidana mu kwana zansa ayanka miki Zabbi kici tun da mun gama cin abinci".
Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi tace.
“Toh”.
Ya riƙe Hannunta suka tafi suna tafiya suna hira har suka isa gidan bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Adda Adama ta fito daga ɗaki tare da amsa musu sallamar.
Kallon Adama Baffa Umaru yayi yace.
“Akwai nama ne?”
Adama tace.
“Eh akwai Zabbin da aka yanka da yamma yanzu nake ƙarasa dahuwarsu”.
Yace.
“Toh shikenan ki ƙara sa gyarasu ki kawo ma wannan Kuran Birnin taci”.
Dariya Khausar tayi tana zama akan taburman da Adama ta shimfiɗa musu, shi kuma Baffa Umaru ya zauna daga gefenta yayin da Adama taje taci gaba da aikinta kasancewar farin wata ya haska ilahirin garin.
Anutse Baffa Umaru ya kira sunanta da faɗin.
“Khausar”.
Ta ɗago kanta tana kallon fuskarsa acikin farin watan kafin tace.
“Na'am”.
Idanunsa kanta yace.
“Kinsan kamannin Babanki?”.
Kai ta girgiza masa tare da faɗin.
“A'a bansan kamanninsa ba”.
A sanyaye yace.
“Amma kin san akwai Baffanki ai yayan Babanki Hammadu Ɓadamaya ko?”.
Tace.
“Eh amma Ɓadamaya yake ko?”.
Yace da ita.
“Eh yana can Ɓadamaya dashi da Iyalansa da kuma ahalinsa gaba ɗaya.
Insha Allah wataran Zakije shida Babanki Uwa ɗaya Uba ɗaya".
Kai ta jinjina da faɗin.
“Eh Mommy na tafaɗa min cewa inada Baffa yana can Ɓadamaya dashi da matarsa da kuma ‘Ya‘yansa”.
Murmushi yayi yace.
“Toh idan kinje zaki ga mai kamannin Mahaifinki sak da sakin sunan sa Aliyu shine yake kama da Mahaifinki ya gaji Babanki komai da komai kuma shine aka aurawa yayarki Nenne”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Toh yaushe zanje in gansa?”
Yace.
“Kinga kamannin Mahaifinki kamar balarabe kinga ba yabon kai ba mutanen Rugar mu duka kyawawa ne amma kyawun mahaifin ki ya fita da ban farin Mutum ne kyakkyawa ga kuma gashin kansa mai tsawo da sheƙi wannan gashin naki ma shi kika ɗauka”.
Idanunta ta lumshe cike da kewar mahaifinta sai kuma ta buɗe su tace.
“Aikam nasan gashin sa na ɗauka ba Mamansa ba da kai agwagwiye".
Murmushinsa ya faɗaɗa da faɗin.
“Ina Addar tawa kike yiwa ba'a itama tsufa ce yasa gashinta kaɗewa”.
Murmushi tayi tace.
“Ai lalle kam”.
Sai kuma ta dai-dai-ta nutsuwarta tace.
“Ku kuma dama nan ne asalin Rugarku?”.
Kai ya gyaɗa mata yace.
“Eh asali nan ne Rugar mu iyaye da kakanni”.
Tace.
“Toh Meyesa ita Hajja Nana ta dawo nan kuma ina ne asalin garinsu Babanmu?”
Murmushi yayi yace.
“Asalin garinsu Babanki yana da nisa lokacin da Addarmu tayi aure ta daɗe kafin tazo ta samu haihuwa to data haifi na farko sai Allah ya sake kawo wasu akan lokaci ta haifi yara uku sai Allah yayiwa kakanki daya haifi Babanki rasuwa,sai ta nemi zata dawo to data nemi zata dawo sai sukace tabarmu su yaran ita kuma tana son yaran sosai sai tace Inde akan dukiya ne tabar musu duka subarta ta taho da ‘Ya‘yanta”.
Zama Khausar ta gyara tana sauransa da kyau.
Shi ko a hankali ya cigaba da cewa.
“Dake dangin Mahaifinki mutane ne masu karamci sai sukace su ba dukiyar su suke buƙatar ba kawai dai suna so suriƙa ganin ɗan uwansu ne sannan ita macece kada subar mata nauyi amma tunda tana son Zama da ‘ya’yanta baza su hanata ba sai suka bata duka gadon Mahaifinki da kuma na Baffanki da ƙannensa mata biyu hadda mai sunanki.
A ranar da tashigo Rugar nan tashigo da aƙalla shanu sun kai ɗari biyu sannan harda raƙuma da tumakai duk gadon sune aka ɗauka aka basu suka dawo”.
Sassayan ajiyar zuciya ta saki tana jinjinawa lamarin.
Baffa Umaru ya cigaba da cewa.
“Toh tun daga lokacin ne zamanta ya dawo nan daga baya Allah yayiwa mahaifan mu rasuwa da gida huɗu ne kacal anan mahaifinmu su suka fara kafata da duk nan dajine mahaifinmu ne ya sare bayan rasuwar mahaifinmu da kuma mahaifiyarmu,
itace ta zame mana Uwa da uba tun muna yara itace ta renemu nida Mahaifinki mun taso tare atare mukayi wasan ƙasa ta raine mu tare ta zame mana kamar uwa Shiyasa mu awajen mu Adda Nana ba ya bace kaɗai uwa ace a garemu”.
Ita kuwa khausar Ajiyar zuciya ta kuma saki tare da faɗin.
“Ikon Allah Allah mai iko Mabuwayi Gagara misali”.
Murmushi Baffa Umaru yayi yace.
“Kin gane ko mu Addah Nana Uwace agaremu ba Ya ba sannan maganarta Umarni ne awajenmu muda ‘Ya’yanmu babu mai saɓa mata har jikokin mu kinga keda kika zo kina wannan abin sai akaga lallai ta samu karan tsaye”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Lallai dai kam,to amma ina ne asalin su Babanmu?”.
Murmushi yayi yace.
Gobe zan faɗa Miki Idan Allah yakaimu rai da Lafiya zan ƙara sa baki labarin insha Allahu”.
“Toh Allah ya kaimu goben lafiya”. Cewar Khausar
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Naji ma Addah Nana na cewa kafin ki koma Abbah zai kaiki Ɓadamaya kije kiga Baffanki da ‘Ya‘yansa”.
“Toh ina kuma ance da nisa?”.
Khausar ta tambaya
“Eh danisa amma ai tafiyar wuni ɗaya ce zaku isa”.
Ya bata amsa.
Miƙe sawunta tayi bisa taburmar tare da cewa.
“Toh shikenan ba matsala, Insha Allahu zamuje, nima ingansa sannan kodan inga mai kama da Babana”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Sannan kuma kafin ku tafi zakuje kiga Addarki ‘yar Baffanki da yake Ɓadamaya tana nan Rugar Fulani dake ma ƙobtanmu Adda Ikki aikin santa?”.
Murmushi tayi tare da gyaɗa masa kai tace.
“Eh na santa ai itakam tana zuwa har gidanmu ta dubani duk dangin Babana ma ita nafi sani”.
Yace.
“Toh shikenan Zakije wajenta kiyi kwana biyu”.
Tace.
“Tun kwanaki nake cewa Hajja Nana zanje in dubata, tace min ba yanzu ba, wai in bari ingama sanin mutanen garin nan”.
Adama dake sauraron hiransu ta miƙe hannunta riƙe da kwanan da ta gama gashin Zabbin dake ta tashin ƙamshi sannan ta haɗo musu da madara mai ɗumi.
Akan tabarmu ta ajiye musu su duka ukun atare sukaci.
Gyatsa mai sanyi Khausar kana tace.
“Kai gaskiya naci naji daɗi Nagode”.
Bayan sun kammala ne Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.
Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru ya miƙe zaune, tare da kasa kunnensa sosai wanda hakan ya kasance ɗabi'arsa ne,
domin shine Garkuwar Rugar tasu, jin motsin tashin sa yasa Adama miƙewa ita ma ta zauna, kusa dashi tana faɗin.
“Lafiya”.
Ajiyar zuciya ya saki da faɗin.
“Naji tsayuwar mota daga can nesa sannan naga haske yashigo har cikin garin nan kamar da akwai wani abu ko dai munyi baƙi ko kuma wani abu!".
Ahankali tace.
“Toh yanzu fita zakayi kenan?”.
“Dole in fita ai Adama idan ban fita ba ‘yan uwana zan bari wani abu yazo ya ritsa da mune ai bazan bari ba dole in fita inga ko menene”.
Ya faɗa a hankali.
Ita kuwa Adama riƙe hannunsa tayi fuskarta na bayyanar da tashin hankali tace.
“Nikam ina tsoro wallahi”.
Da sauri yace.
“Kada ki damu Insha Allah babu abinda zai faru wanda Ubangijin bai sani ba”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Kai rashin network ɗin garin nan yana damun mu wallahi, kaga da akwai network tunda yawanci kowa yana da waya zaka kik kira su awaya kowa ya fito kaga idan yaso sai sufito ku haɗu Atsakiyar garin amma Ni ina tsoron fitarka kai kaɗai”.
Suna cikin Maganar ne sukaji antura ƙofar gidansu anshigo Murfin ya fadi ƙasa Kifff kasancewar ba wani Murfin kirki bane gadon kara ne da gwafa aka haɗa.
Cikin han zari ya mike ya tsaya.
Itama miƙewa tayi da saurin ta riƙe hannunsa tace.
“Fita zakayi dan Allah kada ka fita ka tsaya dan Allah kar ka fita”.
Ya juya ya fuskanceta yace.
“Ya kike so inyi idan ban fita ba kina jifa anshigo gidan nan”.
Yana ida maganar ya fin cike hannunta dake cikin nasa ya fita.
Cikin sauri ta shari gabansa ta fito ya zama na itace agaba shi yana bayanta.
Suna fitowa idanunsu ya sauƙa akan mutanen uku dake sanye cikin baƙaƙen kaya hannunsu riƙe da bindigi da kuma toch ligh mai masifar haske.
Arazane Adama tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Ƙaran buɗe ƙofa da kuma sautin Muryan Adama ne ya fito da Khausar daga ɗaki wacce farkawanta babu daɗewa tana fitowa sukayi saurin kashe mata ido da hasken toch ligh dinsu ita da Adama.
Cikin daga Murya suka ce da Adama
“Ki matsa agabansa kada jini ya taɓa ki ki matsa kada mu illataki!”.
Aruɗe tace.
“In matsa agabansa!?Bazan matsa ba, ku suwaye ne? sannan me kuke nema? me kuka zo yimana acikin daren nan?”.
Ɗaya daga cikin sune yace.
“Kashe sa muka zo yi!”..
Cikin tsananin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n hasbunallahiwani'imanwakil.
dan Allah kada ku kashesa,me yayi muku zaku kashe sa?,Meyesa?”.
Ɗaya daga cikinsu ba wanda yayi magana da farko ba yace.
“Saboda yana hanamu rawan gaban hantsi zamu kashe sa muga takan tsiya bashi yace taurin kai ba”.
Baffa Umaru kuwa murmushi yayi mai cike da Jarumtaka da kuma rashin tsoro yace.
“Ni zaku kashe?,To idan kunga na mutu kwana nane ya ƙare,Kuma Ubangiji shi ya ɗauki raina.
Amma ku baku isa ba babu mai rayawa babu mai kashewa sai ubangiji.
Dan haka raina baya hannunku kuma ajalina baya hannunku idan kunga na mutu ma kada kusa aranku ku kuka kashe ni!”.
Ya ida maganar tare da zabura zai shiga ɗaki dan ɗauko kwari da bakasan.
Ita kuma Adam da saurin riƙesa dai-dai lokacin da suka harbesa akafaɗarsa na dama.
Ƙaran harbin ne ya tashi gaba ɗaya ilahirin mutanen garin Aɓangaren Hajja Nana kuwa tana tashi daga bacci sanadiyyar ƙaran harbin ta dafe kanta da faɗin.
“Wayyo Umaru na Allah ka kare mana Umaru” domin shine mutum na farko daya faɗo mata arai cikin rawan jiki ta miƙe tare da ɗaukar zaninta ta ɗaura kana ta ɗauki mayani ta yana.
Aɓangaren Baffa Jauro yana miƙewa yace.
“Umaru”.
Ya kira sunan sa cikin daga murya.
Baki ɗaya ‘Yan uwansu da sauran jama'a babu wanda ya faɗo masu arai sai Baffa Umaru ko wannensu daya farka zai ce.
“Wayyo! Umarunmu”.
Shi kuwa Umaru juyawan da zai yi sai suka samu damar sake harbinsa ahaƙarƙarinsa na hagu.
Cikin ƙarfin hali da ɗaga sautin Muryar sa yace.
“La'ilah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi(S.A.W) Adda Nana ki yafemin yau kam zasu kashe ni ki yafemin kece madadin Uwa awajena duk abinda nayi ki yafemin yau kam sun kasheni sun kashe ni,Yaya Jauro, Yaya Sadu, Yaya, GarGa, Yaya Liman, Yaya Garba,Yaya Sale yau kam sun kasheni sun cire muku ɗaya cikin goma kun zama ku tara!”.
Adama kuwa Aruɗe ta riƙesa jikinta na kyarma taja numfashi amma ta gagara sakewa.
Ita kuwa Khausar numfashin taja amma ta gagara sakewa saboda tsananin ruɗu da tashin hankali da tashiga kamar zata shiɗe!.
Ihun da kiran sunan da yake yasa suka janye toch ligh ɗin su dake fuskar Khausar da Adama suka mai dashi sama wannan dalili ya bawa Khausar damar kallon fuskokinsu da kyau amma baki ɗaya jikinta ya sandare bata da wani kataɓus ɗin motsawa.
Su kuwa ƙirjinsa suka saita suka sake harbinsa akwai wani ƙaton tukunya agefen ya ratsa ya ɓula.
Shi kuwa Baffa Umaru ƙirjinsa ya dafe da faɗin.
“Laila Ha'illalhu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)” Shikenan rai yayi halinsa.
Su kuwa mutanen garin baki ɗaya gidan Baffa Umaru suka nufo ko wannensu na rataye da kwari da bakansa sukuwa jin hayaniyar mutanen yasa suka ɓulla ta bayan gidansa suka fice tare da zuwa inda suka bar motarsu suka shiga.
Shi kuwa Baffa Umaru ta cikin tukunyar gefensa ya faɗa jini nata ɓulɓula.
Hajja Nana ce farkon shigowa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa tana isa tsakiyar gidan,
Ƙofar dakinsa ta nufa, tana isa inda yake ta janyo gawar ta rungume tana kuka tare da faɗin.
“Umaru! Umaru!! Umaru!!! Yau kuma mai zan gani gawar Umaru zan riƙe ahannuna kamar yanda na riƙe gawar Usmanuna!”.Cikin kuka sosai take maganar.
Su Baffa Jauro da sauran mutanen ne suka shigo sudai Allah Allah suke su ƙarasa cikin gidan suga abinda ya faru dashi sam basu yi tunanin bin bayan mutanen ba.
Ita kuwa khausar hanyar da suka bi suka fita take nuna musu da yatsa ta kasa furta komai bare kuma ta taɓuka wani abun Yaya Abba ne da ya shigo yace.
“Yayane Khausar!?”.
Cikin matsananci kuka da tashin hankali tace.
“Yaya Abba sun gudu sun kashe shi sun gudu sunbi ta nan na gansu sunbi tanan!”.
Azabure Matasan suka bi wajen ina tuni sun shiga motarsu sun gudu sukuma su Baffa Jauro, Baffa, Sadu da sauran rungume gawar ƙaninsu sukayi suna kuka.
Hajja Nana kuwa tattaɓa jikinsa tayi, Sadik yace.
“Baba mu ɗaukesa mu kaisa asibiti”.
Sake rungume gawarsa Hajja Nana tayi tace.
“Saddiƙu wani asibiti zamu kaisa bayan sun kashe sa baya numfashi bashi da rai!?”.
Jauro ne ya karɓesa ya duba shima ya rungumesa ganin ya rasu Baki ɗayan su akan Gawarsa suka kwana.
Ita kuwa khausar gaba ɗaya ta rikice ta duburburce bata taɓa gani ankashe mutum agaban ta ba sai lokacin tayi kuka har ta godewa Allah manyan Idanunta sunyi luhu-luhu dasu ba abinda ke faɗo mata arai kamar yanda sukayi hira dashi.
Washe gari akaje aka kira
Ƴan sanda acikin gari suka je sukayi bin cike tare da rubuce-rubucen su na banza da wofi sannan akayi masa sallah aka kaisa gidan sa na gaskiya.
Kana akazo aka zauna zaman makoki, Addar Khausar Ikki da zata je wajenta a Rugar Fulani ce tazo da taji labarin rasuwar Baffa Umaru tana zuwa kai tsaye gidan Baffan Umaru ta nufa duk ‘yan uwan suna can suna karɓan gaisuwa.
Khausar na ganinta ta tashi da gudu ta Rungumeta tana kuka tace.
“Addah Ikki agaba na agabana fa suka kashe shi sun harbesa sun kashe sa ya rasu har lahira!”.
Addah Ikki tace.
Kiyi shiru Khausar duk mai rai mamacine addu'ar mu yake buƙata”.
Kai Khausar ta gyaɗa amma ta gaza tsaida kukan ta Ganin haka yasa Addah Ikki taja hannunta suka fita zuwa gidan Hajja Nana.
Suna Shiga Khausar ta tsaya cikin Muryanta daya dishe da kuka tace.
“Ni ina tsoro bazan shiga ɗakinta ba akwai kuliya”.
Addah Ikki tace to kitsaya na koreta sannan tashiga ɗakin ta fito da kuliyar tasa awani ɗaki ta rufe.
Sai asannan Khausar ta yarda tashiga ɗakin bayan sun zauna Addah Ikki ta zauna ta riƙa yi mata nasiyya tare da kwantar mata da hankali.
Yaya Abba ne ya ɗauki wayarsa ya tafi Bishiyar ƙare zancenka ya kira duk dangi na nesa ya riƙa sanar da su har ya kira Baffa Hammadu na Ɓadamaya ya sanar masa.
Shima washe gari Baffa Hammadu ya ɗauko iyalansa baki ɗaya suka taho da yammaci gab maghariba motocinsi su guda biyu ajere suka shigo Rugar kai tsaye ƙofar Hajja Nana suka nufa sukayi parking motocinsu.
Ita kuwa Khausar na cikin ɗakin Hajja Nana manne da jikin Addarta Ikki suka jiyo Sallama,
Addah Ikki ce ta miƙe da faɗin.
“Laaa Umma na sannan sai Baffanta yashigo daga bayansa kuma wani kyakkyawan matsakaici mutun ne fari ƙal kamar balarabe yayin da Yaya Abba ke biye dasu abaya.
Durƙusawa Khausar tayi tare da fashewa da kuka kalaman Baffa Umaru ne kawai keyi mata suwwa akunne.
Rarrashinta Addah Ikki ta shiga yi tana bata haƙuri da kyar ta tsaida kukan tace.
“Addah Jiya da daddare