Showing 90001 words to 93000 words out of 176046 words
Haidar Mommy ta ƙwalawa kira bayan yazo tace ya ɗauki kular sashen Gimbiya Dadu ya kaimata dan Mommy tunda ta lura da Khausar batason zuwa yasa ta rage aikanta sashen shi kuwa Haiydar daga sashen Gimbiya Dadu ya wuce sashen Hajiya Bunayya.
Hajiya Bunayya dake zaune akan kujera ta faɗaɗa fara'ar fuskarta ganin Haiydar ta tsira masa idanu kana tace.
“Babana kaine dama yanzu nake niyyan zuwa in yi maka albishir”.
Murmushi Haidar yayi tare da zama kana yace.
“Daga sashen Gimbiya Dadu nake nace bari nazo na gaishe ki”.
Murmushi tayi masu cike da Ma'anoni tayi kana tace.
“Insha Allah bayan sallah mashin ɗinka zai zo kaga dama tun shekara biyu baya naso saya maka Abbanka yace saika ƙara girma kuma kaga yanzu aika girma”.
Jinjina kai Haidar yayi cike da tsananin farin ciki mara mistuwa ya gyara zamansa kana yace.
“Nagode Ummah Allah yarabaki da sharrin maƙiya”.
Murmushin gefen baki tayi kana tace.
“Bana son godiyar nan Babana”.
Cike da farin ciki ya miƙe ya nufi sashen su fuskarsa ɗauke da murmushi ya shiga falon zaune ya samu Mommy da Khausar.
Kallonsa Mommy tayi kana tace.
“Ina ka tsaya?”.
Zama yayi daga gefen Khausar still.
Fuskarsa da murmushi da yakasa ɓoyewa ya numfasa tare da cewa.
“Mommy Machine ɗina ya Kusa isowa fa, kinga tun shekara biyu baya Umma taso siya min shine Abba ya hanata yace saina ƙara girma ai yanzu kam dai na sake girma bazai hana ba ta saya min Machine sabo mai kyau bayan sallah zai iso”.
Khausar kuwa tunda ya fara magana ta tsira masa idanu saida ya kai aya ta sauƙe ajiyar zuciya mai zafi tare da furzar da iska daga bakinta kana babu walwala afuskarta ta kawar da kanta gefe tare da cewa.
“Kai kuma farin ciki kake ko?”.
Juyawa Haiydar yayi tare da kallon ta kana yace.
“Sosai ma kuwa kema kamata yayi kije kiyi mata godiya”.
Harara Khausar ta ɓalla masa.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Rabu da ita ai ni zanje.
A yanzu kam aika girma yanda kake da tsawon ƙafan nan”.
Murmushi yayi tare da kallon Khausar kana yace.
“Sosai ma Mommy ai yanzu na girma yanzu fa shekara kusan sha shida nake nema gashi mai shekara sha takwas ɗinma na fita koda yake sha bakwai ne da yan watanni ne ko gareta”.
Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“Ai lallai dai kam kama cika sha shida kam Allah yasa kafara hawa asa'a.
Ubangiji ya tsareka da sharrin ƙarfe.
Allah yatsare gabanka da bayanka!.
Ubangiji ya makantar da idanun makiyan ka akanka!.
Allah ya tsare ku ga duk kan abinda zai cutar da rayuwar ku! Allah ya muku katangan ƙarfe da dukkan abin da zai zama sharri acikin rayuwarku!”.
Cike da jin daɗin Addu'ar ta Haiydar yayi Murmushi tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Mommy na”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da kallon Mommy kana tace.
“Ameen ya Allah Mommy tunda kinyi addu'a magana ta ƙare baza'a ji tsoron komai ba babu bakin uwa akansu duk kan mai sharri zaiyi ya gama babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji”.
Murmushi Haiydar yayi tare da kallon Khausar kana yace.
“Aikam Addah Khausy babu bakin uwa akaina duk kan wani mai mugun nufi zai ƙare akansa”.
Murmushi Mommy tayi cike da ƙaunar ƴaƴan nata,
kallon ta ta mayar kansu tare da cewa.
“Ku tashi kuje kuyi bacci dan mu samu mu farka da wuri mu kaiwa Ubangiji bukatun mu”.
Miƙewa sukayi tare da yiwa juyawa sai da safe kana kowa ya wuce ɗakinsa ya kwantar.
Misalin ƙarfe ɗaya na dare Mommy ta farka kallon Lamiɗo daya miƙe yashiga toilet tayi sai kuma ta miƙe ahankali ta tafi side ɗinta.
ɗakin Khausar tashiga tare da kunna haske.
Idanunta suka sauƙa akan Khausar dake sharan bacci ƙara sawa tayi tare da bubbuga ƙafarta kana tace.
“Khausar ki tashi kiyi nafilla”.
Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta cikin Muryan bacci ta kalli Mommy kana ta yunƙura ta zaune bakinta ɗauke da addu'a tace.
“Toh Mommy”,Sannan ta Sauƙa ta shiga toilet.
Juyawa Mommy tayi ta koma ɗakin Lamiɗo lokacin data shiga har ya fara Sallah kai tsaye toilet ta shiga ta ɗaura Al'wala bayan tayi ta fito tare da shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah cikin nutsuwa ta keyi bayan tayi sujja tayi Subhana Rabbiyal a'ala³ kana ɗaura da du'inta.
“Ya Allah kayuwa ƴata zaɓin alkhairi,Ya Allah kashirya Khausar kasata ahanya madaidaiciya Ya hayyu ya ƙayyum ka tsare mata imaninta, Ya Allah ka kare min Haiydar ɗina ya Allah katsaresa daga sharrin mai sharri ya Allah ka kare min ita ya Allah kabawa Ramadan da Raudat ilimi mai albarka da yayunsu dama dukkan ƴaƴan musulmai. Ya Allah katsare min ƴaƴana daga sharrin,Mutum, aljan da kuma ƙarfe, ya Allah katse min imanina Allah ka tsaremin zuciyoyinsu, ka tsaresu da sharrin hassada, ƙeta, munafurci, da ƙyashi ya Allah ka kare min mijina kabiya masa buƙatunsa na Alkhairi dama ɗauka cin al'ummar musulmai.
Bayan ta idar da nafillah ta ɗauki Alkur'ani ta shiga Muraja'a.
Khausar kuwa ƙarfe biyu da rabi bacci ya riƙa fisgarta akan Sallaya ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi yayi nasarar ɗauke ta.
Can cikin baccinta ta fara wani mafarki mai cike da al'ajabi ganinta tayi.
Gata nan tsaye a wani ƙaton fili.
Baki ɗaya ilahirin filin ashare yake kuma , yashine malale a wurin iya ganinka sai wani irin haske mai masifar ƙyalli da ɗauke idon da ya cika wajen baki ɗaya, ahankali ta ɗaga kanta ta fuskanci gabas, da sauri ta rumtse idanunta gani wata ya fito ta gabar juyawa tayi taga yamma da sauri Still nan ya fito ta yamman sake juyawa kudu tayi still ta nan ma ya fito ahankali ta sake juyawa arewa, wani irin masifeffen karkarwa jikinta ya farayi, ganin tanan ma watan yafito duk kusurwa huɗu wata ya fito sai asannan ta lura da haskensa ne yake ɗauke mata ido.
Ahankali taga wani kyakkyawan.
Yaro fari ƙal agabanta yayinda gashin kansa ke kwance lib-lib, daga bayansa ta hango wani kyakkyawan mutum sai dai fuskarsa na kallon gefe hannunsa na kan yaron yana shafawa cikin wata.
Sanyayyar murya yake kallon yaron kana yace da ita.
“Wannan shine jininmu mahaɗinmu, wannan shine sanadin haɗayyarmu bugun zuƙatanmuuuhh”.
Ya ƙarasa jan kalmar cikin wata iriyar ƙasalalliyar murya mai cike da shauƙi.
Ita kuwa ƙoƙari take taga fuskar mutumin sai dai ta kasa sai iya fuskan kyankyawan yaron take iya kallo.
Dai-dai lokacin kuma ta buɗe Idanunta jin Muryan Mommy nacewa.
“Khausar, Khausar ki tashi zaki makara fa ƙarfe huɗu tayi bakiyi Sahur ba anjima kaɗan zaki fara ce mana kin fara jin wahalar azumi”, Ta faɗa tana buga ƙafarta da saurin Khausar ta tashi zaune tare da sakin ajiyar zuciya kana tace.
“Innslillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin Astagfirullah wa'atubu ilaik”.
Sai kuma tayi addu'a ta shafa.
Mommy dake tsaye har yanzu kuwa sake taɓata tayu tare da cewa.
“Khausar kada ki koma bacci fa kitaso”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Mommy na tashi bazan koma ba”.
Juyawa Mommy tayi ta fice ita kuma Khausar toilet ta shiga.
Brush tayi kana ta fito kai tsaye falon ta nufa.
Samu tayi Mommy ta haɗa mata ɗumamen tuwon jiya da Tea mai kauri ahankali ta zauna tare da kai tuwon bakinta da ƙyar ta haɗiye baki ɗaya jikinta yayi mugun sanyi da mafarkin da tayi.
Mommy dake zaune a kujeran falon ta juya ta kalleta ganin bata cin tuwon yasa ta girgiza kai tare da cewa.
“Kici abinci fa Khausar kin sanki sarai da cin abinci anjima kaɗan zaki fara cewa yunwa kike ji”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da iskar bakinta kallon Mommy tayi kana cikin sanyin murya ta lumshe Idanunta tare da cewa.
“Mommy wallahi tuwon ne nakeji kamar ba zai shiga ba babu wani abu ne?”.
Kai Mommy data tsira mata Idanu ta gyaɗa kana tace.
“Kije kichen akwai indomie dana ɗaura wa Haiydar shima yace ba zai ci tuwo ba to amma ke kam nasan indomie ba wani riƙe Miki ciki yake yi ba”.
Lumshe Idanunta tayi kana ta buɗe su akan Mommy ahankali ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Bari in cisa yau ɗin kam amma Mommy da kifi ne koda nama”.
Tayi tambayar ne domin bata fiye son kifi ba.
Kawar da kai gefe Mommy tayi kana tace.
“Da kifi ne idan zaki ci kici idan kuma baza kici ba ki bari”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jan siririn tsaki kana tace.
“Bari dai inci, tuwon ne naji kamar bazai ciwu ba shi ɗin ma miyar aida kifi”.
Mommy dai Bata sake cewa komai ba ahankali Khausar ta miƙe tashiga kichen ta ɗauki Plate ta ɗibi yanda zai isheta kana ta fito ta zauna tare da Bismillah ta fara ci bayan ta gama ta ɗauki tea da Mommy ta haɗa mata da bread taci.
Haiydar ne ya shigo da Sallama idanunsa akan Plate da Khausar ta gama cin indomie.
Kallonsa Mommy tayi kana tace.
“Jeka ɗebo indomie yayi sannan ka taho min da tuwo”.
“Toh",Ya amsa kana ya wuce kichen ɗin ya juye indomie sannan ya zubawa Mommy tuwon ya fito.
Khausar dai na zaune tana lumshe Idanunta tare da tuna irin mafarkin da tayi wanda ya tuno mata wanda tayi shekaru biyu baya a Jauro Yayah.
Ahankali ta saki ajiyar zuciya tare da juyawa ta kalli Haiydar da yagama Sahur ɗin ta gyara zamanta tare da cewa.
“Haiydar nikam yanzu wani surah kake?”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ke ɗin wace surah kike?”.
Zama ta gyara tare da cewa.
“Hmmm aini nayi nisa ina Maryam kaga insha Allah zan samu sauƙa biyu”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Toh ni ina Yasin Insha Allah zan samu sauƙa uku insha Allah duk azumi goma zanyi sauƙa ɗaya”.
Murmushi Mommy dake duba wani littafin addini tayi kana tace.
“Masha Allah yayi kyau Khausar ya akayi kika tsaya wasa ya wuce ki”.
Langwaɓar da kai tayi kana tace.
“Mommy kinga ai shi baya taya ki yin aiki nice ke tayaki aiki kinga shi duk lokacin daya keso zaiyi karatu.
Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“Eh haka ne da wannan dan wannan amma dai ki dage kema”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan Mommy zan dage insha Allah amma Mommy ke izu nawa kikayi”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Insha Allah nima zan samu uku kaman na Haiydar”.
Ware Ido Khausar tayi tare da tura madedecin bakinta kana tace.
“Insha Allah nima zan dage duk azumi goma sai nayi sauƙa”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da faɗin.
“Aikam da kin kyauta amma sai kin rage baccin safe”.
Jinjina kai Khausar tayi kana tace.
“Insha Allah zan rage”.
Jin kiran assalatu yasa suka miƙe Haiydar ya tafi masallaci Mommy da Khausar suka shiga ɗaki suka ɗaura alwala kana suka gabatar da sallah bayan sun idar Khausar ta zauna tayi Azkharul sabah tana gamawa ta mike ta dawo falo ta gyara tare da sharewa kana ta fita zuwa kofar sashen nasu ta gama share ko ina sannan ta wuce Bedroom ta kwanta kasancewar akwai mai yi musu wanke-wanke tun kafin su shiga Sallah ta zo ta kwashe kayan ta wanke.
Ahankali azumi ya cigaba da tafiya kwanaki suna tafiya lokaci yana ja cikin ikon Allah har angama goman farko goma na marmari inji hausawa ko?. Har an shiga goma na biyu, goma na wuya ko? Yau an kai azumi na goma sha biyu.
Yayin da Aɓangaren Moddibo da M Jameel sunyi nisa acikin tafsirin Suratul Nisa sun fassara har zuwa ayoyi na tamanin da tara zasu tashi akan aya na Casa'in
Da daddare Misalin ƙarfe tara M Jameel da Moddibo ne zaune acikin masallaci gaban ko wannensu ɗauke da system da kuma roban Swan water mai sanyi Moddibo na cikin shigarsa as Usual kamar ko yaushe Jallabiya Neavy blue kansa ɗaure da Hirami M Jameel kuwa sanye yake cikin gezner blue da babbar riga.
Cike da nutsuwa M Jameel Yayi gyaran murya tare da hura Microphone ɗin kana yace.
Ya buɗe da addu'a kamar ko yaushe.
Lokaci guda masallacin ya kaure da kabbara tamkar zasu tsaga masallacin saboda yanayin zafin jinjinsa da kwarjininsa cike da sakin fuska.
Ya cigaba da cewa.
“Anma ba'ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”.
Atare suka hada baki wajen cewa.
“Wa'alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.
A hankali ya numfasa tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya kana ya dubi ɗumbin jama'ar dake zaune acikin masallacin cikin tsantsar nutsuwa ya juyo da system ɗin gabansa kana yace.
“Acigaba da tafsirin Alkur'ani mai girma Amasallacin. Juma'a dake ƙofar gidan Mai martaba Sarki Gembulan Lamido Bashiru zamu cigaba da tafsirin Alkur'ani mai girma acikin Suratul Nisa'i zamu tashi a aya ta cassa'in”.
Sai kuma ya juya ya Kalli Moddibo kana yace.
“Aramma Bismillah”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa kana ya ɗan jingina bayansa da jikin kujeran cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da nutsuwa da zaƙi yayi basmala kaya ya fara karanta ayoyin kamar haka;
_“(90)Illallazina Yasiluna Ilaƙaumim Bayna Kum wa Bayna hum misaƙun Auja,Ukum hasirat suduruhu an yuƙatalalukum.Walau sha Allahu lasallaɗhum Alaikum falaƙatalukum.Fa'in'itazalukum falam yuƙatilukum Wa'alƙau Ilaikumussalama fama ja'alallahu lakum Alaihim Sabila”._
Moddibo ya ida kai Ayar yana mai lumshe idanunsa akuma take tsikar jikinsa suka tashi yayi saurin buɗe idanunsa tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana ya cigaba da furta Aya ta gaba kamar haka.
_“(91)Satajidunah Akharina Yuriduna Anyamanukum Wayamanu Ƙaumahum kullamaraduu Ilalfitnatin Urkisu fiha.Fa'in lam ya'atazilukum Wayulƙau Ilaikumussalama Wayakfuru Aydiyahum Fahuzuhum Waƙtuluhum haysu saƙiftumuhum.Wa Ula'ikum ja'alnalakum Alaihim sulɗanammubina”._
Wani irin numfashi M Jameel ya saki tare da rintse idanunsa kana jikinsa ya ɗauki tsuma yana mai jin fassarar Ayar na yawo Atsakiyar kansa Atake kuma zuciyarsa ta cigaba da bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.
Yayinda gaba ɗaya al'ummar dake cikin masallacin dama wajensa sit kakeji kamar ba mai numfashi sabida tsananin yadda sautin karatun ke ratsa musu zuƙata da ƙoƙwale.
Shi kuwa Moddibo ya kai minti ɗaya kafin ya saki gauron numfashi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi sabida sanin ma'anar ayoyin da zai kawo a gaba, cikin wani irin raunin tare da tsoron Allahu wahidun ƙahhar, gaba ɗaya muryarsa ta sake rauni cikin dakiya ya cigaba da Karanta Ayar Kamar haka.
_“(92)Wama kana limu'uminun An yaƙtula Mu'uminan Illakhaɗa'a.Waman ƙatala Mu'uminan khaɗa'a fatahriru Raƙbatatin Mu'uminatin wadiyyatun Musallamatu Ila'ahlihee Illah An yassaddaƙun.Fa'in kana min ƙaumin Aduwwillakum Wahuwa Mu'uminun Fatahriru Raƙbatin Mu'uminatan.Wa'in kana min ƙaumim baynakum wa baynahum miysaƙun Fadiyyatun Musallamatun Ila Ahlihi watahriru raƙbatin mu'uminatin.Famallam yajidu fasiyamu shahraini mutatabi'ayni taubatan Minallah.Wakanallahu Aliman hakima”._
Wani irin nutsuwa cikin masallacin yayi musamman ma wa'anda suka san fassarar ayoyin wa'anda basu san fassarar ba kuwa mu'ujiza ta Kur'ani ta dinga ratsasu tare da Sanyayyar sautin Muryar mai karatun.
Moddibo kuwa idanunsa ya lumshe sakamakon wasu zafafan hawaye masu ɗumi da suka cika cikin ƙarfi ya furzar da iska mai zafin gaske Tabbas kashe ran mumini baƙaramin tashin hankali bane amma baki ɗaya awannan zamanin an maida rai ba abakin komai ba.
Ya gyara zamansa tare da cigaba da karantar Ayar kamar haka.
_“(93)Waman yaƙtul mu'uminan Muta'ammidan Fajaza's'uhu Jahannama! halidan fiha wagadiballahu Alaihi wala'anahu! wa'aaddalahu Azaban! Azeeymah!!!!!”_.
Awannan lokacin hawaye ne suka ciko idanun Moddibo jin irin tsananin azaban da Ubangiji ya tana darwa duk wanda ya kashe ran mumini batare da wani hakkiba.
Walahabahu la'anar Ubangiji kana fajaza'ahun jahannamu khaleedan fiha, fa ubangiji yace kana aka ɗaura da Azaban Azeeymah!!!, Duk wannan tanadinefa da Ubangiji yayiwa mai kashen ran mumini da gangan.
Wani irin rawa jikin Moddibo keyi tamkar wanda aka konawa wuta a jikinsa cikin tsananin sheshsheƙan kukan da yake son dannewa ne ya bu ɗe baki a hankali dan kawo aya ta 94 sai kuma ya juyo cikin tsananin rauni ya kalli M Jameel da gaba ɗaya j....
*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*
_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._
🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,
*By*
*GARKUWAN MARUBUTA*
[19/07, 8:57 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_page 16_