Showing 69001 words to 72000 words out of 176046 words
dake fuskanta ya gushe cikin ɗaure fuska cikin kakkausan Murya tace.
“Khausar!, Khausar!!, Khausar!!!, Ki cigaba Nagode da abinda kike min Khausar, duk irin tarbiyyan da nake baki fatali kike dashi ko, kina ɗaukar rashin yarda kina ɗaurawa mutane ki sani Manzon Allah (S.A.W) Yace.
:Azzana zambu walau kana haƙƙun”.
Khausar kuwa ƙasa da kai tayi hawaye masu zafi suka cika Idanunta shin sai yaushe mahaifiyarta zata amince da gaskiyar da take so ta sani akan Hajiya Bunayya basa ƙaunarta cutar da ita suke sonyi.
Cikin sanyi murya tare da rauni gami da ban haƙuri tace.
“Shikenan Mommy kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki”.
Mommy bata tanka taba ta juya ta gyara kwanciyar, ta itama Khausar juyawa tayi ta kwanta zuciyarta babu daɗi.
Washe gari Alhamis Da safe Dr ya shiga ya basu sallama dan jikinta yayi sauƙi Sosai Lamiɗo da kansa yaje ya maido su gida.
Suna dawowa Hajiya Bunayya ta shigo hannunta riƙe da babban Warmers da tayi Perpesoup ɗin Kaji ta shigo dashi.
Zama tayi akan 2sitter tace.
“Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.
Mommy tayi yar dariya tare da faɗin.
“Jiki yayi sauƙi Yaya sai faman hidima kike dani kamar wacce tayi haihuwar farko?”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi da faɗin.
“Ai mai ɓari yafi son akula dashi fiye da mai haihuwa”.
Khausar dake tsaye duk takaici ya gama cikita gashi babu dama ta faɗawa mahaifiyarta gaskiya sai ta hau kanta da faɗa bayan da ta iya daga ƙarshe ma Saboda takaici kawai sai ta koma Bedroom ɗin ta ta fara karatu.
Wunin ranan haka Hajiya Bunayya ta yini tare da Mommy ta cigaba da kulawa da ita.
Washe gari juma'a dai-dai lokacin da maza suka tafi Juma'a dai-dai lokacin da kowa ya tafi Sallar juma'a Akuma lokacin ne Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka tafi gidan Boka Kar'uzu.
Khausar da Mommy ne zaune suna hira sosai jikin Mommy yayi ƙarfi abinka da mai juriya ga kuma kulawa da take samu.
Sallamar Aunty Ruƙayya ya katse musu hirar da suke.
Khausar ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kana tace.
“Aunty Ruƙayya sannu da zuwa ina Affan?”.
Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tana zama tace.
“Affan yana lafiya bacci ma yake ya mai jikin”.
Khausar tace.
“Jiki da sauƙi”.
Aunty Ruƙayya tace.
“Masha Allah Ubangiji ya ƙara sauki”.
Cikin sakin fuska Mommy ta gyara zaman hular dake kanta tace.
“Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa ya gajiyarki?”.
“Hajiya Ruƙayya tayi murmushi da faɗin.
“Babu gajiya ya jikin naki?”.
“Jiki yayi sauƙi ya yara?”.
Alhamdulillah ta bata amsa.
Khausar kuwa miƙewa tayi cikin neman izinin tace.
“Ayyah Mommy zanje gidan su Asma'u?”.
Ido Mommy ta zuma mata, na tsawon second bakwai tana kallonta kana tace.
“Toh yayi kyau”.
Khausar kuwa juyawa tayi ta shiga Bedroom Dogon rigar dake jikinta ta cire tare da ɗaura towel tashiga toilet,
shawer ta ɓude ta sakarwa kanta ruwan ɗumi,
ta ɗauki kusan minti shabiyar kafin ta fito ɗaure da towel da tsawon sa bai wuce gwiwar taba yayin da ƙarami ke kanta tana tsane ruwan kanta.
Stool ta janyo ta zaune tare da goge ruwan jikinta ta ɗauki Vassiline lotion ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafe sai kuma Kajol ta zizara a idanunta mascara ta ɗauka ta taje gashin Idonta da sukayi tsayi tamkar tasa Eyelashes golb mai sheƙi ta ɗauka ta shafa asaman pinch lips ɗin ta sai yayi kamar jan baki ta shafa kallon fuskarta tayi a mirrow sosai tayi kyau.
Miƙewa tayi ta nufi jikin durowar ta buɗe uban kayan dake ciki ta zubawa ido ahankali Idanunta suka sauka akan wani Less Coffee da aka masa adon cycle da rastin Milk colour ta janyo ta sanya Masha Allah Sosai ɗinkin less ɗin ya mata kyau tare da fitar da shape din jikinta skirt ɗin ya zaune ɗass ajikinta tare da fitar mata da tsarerrenn ƙugunta haka ma rigar ta zauna ɗass ajikinta ɗan kwalin ta ɗauka tayi ɗauri mai kyau sai kuma ta ɗauki glaye medium size milk color kana ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi.
Falon ta fita tun kan ta isa Aunty Ruƙayya ta ɗago kanta tare da tsira mata Idanunta jin ƙamshin daya ratsa hancinta ta saki murmushi kana tace.
“Iyeee Masha Allah Khausar irin wannan kyau sai kace preety ta ƙasar India”.
Hannu Khausar ta sanya ta rufe fuskarta tana dariya sai kuma ta buɗe tace.
“Kai Aunty Ruƙayya Ina Zan samu koda rabin kyawunta ne?”.
Ware ido Aunty Ruƙayya tayi kana tace.
“Allah kuna kama dan da zakije India ma cewa za'ayi ke ƙanwarta ce, har rawan kanki ma irin natane a Film ɗin Chori-Chori Cubke-Cubke ne”.
Mommy Kam murmushi take musu batare da tace komai ba.
Khausar kuwa Murmushin jin daɗi tayi tare da tsugunnawa ta ɗauki wayar Mommy tace.
“Mommy zan tafi da wayarki".
Kai kawai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta ɗauƙi wayar tare da faɗin.
“Na tafi”.
ta ida maganar tana gyara zaman Handbag din Hannunta tare da ciro earpiece aciki
Suka haɗa baki wajen faɗin.
“Adawo lafiya".
Kai ta jinjina tare da ficewa,
Abokin gate ta haɗu da Haiydar riƙe da MP ɗin sa, cikin sauri tace.
“Yauwa Haiydar dan Allah aramin MP ɗinka”.
Cike da mamaki ya zuba mata ido tare da cewa.
“Yau kuma to ke kuma da ba jin kiɗa ya dameki ba, me zakiyi dashi?”.
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Wallahi yau dai shauƙi nakeji zanje wurin Asma'u mu ɗan rausaya”.
Murmushi yayi yana mamakin wai yau Khausar ce da cewa zata sha ƙiɗa, kawai miƙa mata yayi. Tare da cewa.
“Kuma kikasa gyale ko?”.
Cikin daɗi tace.
“Ngd kai rabani kullum mutum liƙe da hijabi kamar maitakaba” na mgnar tana fita ta tari adaidaita sahu ta shiga.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan an idar da Sallah juma'a ya kalli M Jameel dake Driving yace.
“J yakamaya muje mu gaida Ummi kafin mu koma gida!”.
Kai ya Jinjina kana yace.
“Dama abinda nake son faɗa kenan ka rigani”.
Gyara zama Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraron ƙira'ar dake tashi amotar kana ya shafa sajensa yace.
“Muje toh”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da juya akalar motar zuwa unguwar su Ummi.
Suna cikin tafiya wayar M Jameel ya hau ruri yana duba screen ɗin wayar yaga Bahrain ba suna sai Number Dariya M Jameel yayi still hankalinsa nakan Driving din yace.
“Jalaludden! Wallahi Jalaludeen!! nayi mana abinda ransa keso”.
Moddibo da Idanunsa ke lumshe yayi ɗan guntun Murmushi ba tare daya buɗe idanun ba yace.
“Toh ka ɗaga mana kar ya yanke”.
Picking M Jameel yayi tare da Sallama.
Amsawa Jalaludeen yayi da faɗin.
“Idan kun isa ku gaishe da Ummi”.
M Jameel yayi Murmushi kana yace.
“Kana biye da mu ne?”.
“A'a bana biye daku na dai rigaku zuwa na gaisheta”.
Cewar Jalaluddeen
Dariya M Jameel yayi sai kuma ya zare ido yace.
“Wallahi Jalaludeen kada ka razana mana tsohuwa!”.
Murmushi Jalaludeen yayi yace.
“A'a bazata ra zanata ba sannan ba zata tsorata ba ai mun taɓa zuwa tare daku baku dai sani bane kuma na bayyana mata ta ganni”.
“Wallahi Jalaludeen ka kiyaye mufa”.
Dariya Jalaludeen yayi kana yace.
“Tare dai mukayi sallama jumma'a a sahu daya.
Yanzu kuma Na dai hango ku ahanya zakuje yanzu ina katakon nan?”.
Da sauri M Jameel yace.
“Wani katakon?”.
Cike da tsokana Jalaludeen yace.
“Katakon dake gefenka”.
Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Moddibo yace.
“A.J ɗin nawa ne katako?”.
“Eh inba katako ba shi menene? ka faɗa masa cewa akwai furen dake ƙoƙarin tsiro a jikinsa tun daga ƙasa har ya isa zuciya ya gab da kanshi tuni ma ya ratsa zuciyarsa amma bai sani ba”.
Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Moddibo da still Idanunsa ke lumshe kamar mai bacci kana yace.
“Wai yace in faɗa maka akwai furen da zai fito tsakiyar kanka yama ratsa zuciyarka”.
Sai asannan Moddibo ya buɗe idanunsa ya kalli M Jameel tare da faɗin.
“Ka ganni karabu dani da kalaman Jalaludeen, shiya sani can yaje yata faman maganganunsa da baza ka gane kansu ba bare gindinsu ya riƙa yi mana maganar damu mutane zamu gane ba sai wanda sai sune masu ganewa ba”.
Dariya Jalaludeen yayi yace.
“Zaka gane ne ai lokaci ne yana zuwa”.
Dariya M Jameel yayi tare da hong aƙofar gidan Ummi ganin shiru ba'a buɗe masu bane yasa, M Jameel fitowa ya buɗe, kana ya dawo yaja motar still kafaɗarsa saƙale da wayar
Jalaludeen ne yace.
“Ku gaishe da Ummi idan kun shiga”.
Sannan ya katse wayar kana shi kuma ya kutsa kai cikin gidan.
Dai-dai lokacin da a dai-dai-ta ya ajiye Khausar kudinsa ta basa tare da buɗe ƙaramin ƙofar dake maƙale da gate ɗin tashiga,
Batama lura da babban gete ɗin dake ɗan buɗe ba,
ganin mota a fake a harabar gidan yasa ta isa wajen kasancewar glass ɗin tink-tenk ne yasa bata fahimci da mutane aciki ba rawar kanta kuma ya hanata fahimtar alamun yanzu motar ta tsaya.
Jikin gefen mai zaman banza ta nufi tare da kallon fuskarta ajikin mirrow sai kuma ta juya manyan Idanunta kalaman Aunty Ruƙayya suka dawo mata kunne tana kama da Preety matsa pinch lips ɗin ta tayi tare da lasa kadan sai kuma ta juya manyan Idanunta.
M Jameel kuwa dake mazaunin Driver murmushi ya saki domin ya tabbata bata san da mutane aciki ba.
Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa zaune suke gaban boka Kar'uzu cikin tsananin ɓacin rai da fushi Boka Kar'uzu ya buga musu wata razananniyar tsawa cikin sautin muryarsa mara daɗin sauti
bayan ya gama sauraron Hajiya Bunayya yace.
“Ai seda na faɗa muku aduk lokacin data fara aiki da maganin kada tayi alwala da sallah na tsawon wata ɗaya amma saboda taurin kai kuka bari tayi alwala tayi sallah shiyasa yake kallon fuskar ta kamar na ƙonennen Biri”.
Atsorace Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da itama ɗin Iran take kallo.
Sun kasa hafimtar sharrin boka na wasa da hankali da ƙarya sun kasa tuna sam bai faɗa musu hakanba a lokacin, su kasa aminta mgnar boka dubune babu gsky ko ɗaya sai yaudara da taɓewa.
Acan ɓangaren su Moddibo kuwa sake kallon madubi Khausar tayi tare dasa hannu ta gyara man lips ɗin ta sai kuma danna MP ɗin cikin Sa'a kuwa sautin waƙar BUGA ya fara tashi.
A hankali ta gyara tsayuwar ta, tare da fara jujjuya ƙugunta a hankali tana mai rausaya jikinta.
Zuwa tsakiyar waƙar kam fa da abu ya jiƙa, sai ga mayafinta bisa kafaɗarta gefe ɗaya, sosai take jujjuya mazaunenta tare da motsa dukkan jikinta, tana mai kallon kanta a madubi.
Sai kuma ta kalli Glass ɗin tare da ɗaura bakinta akai ta saki zazzafan kiss muahhhh.
Shi kuwa Moddibo dake zaune idanu ya zuba mata tare da manna kumatunsa adai-dai glass ɗin sai kuma hakan yasa lips ɗinta sauƙa kan....!
FREE page sun kusa ƙarewa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ki biya 1k dinki ya isheki
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_Page 12_
_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Littafin SAKAYYAH na kuɗine wannan Free page ne ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 saura shafi huɗune kacal ana biyar na gama Free page*
Da sauri Modibbo ya rintse idanunsa, tare da shafa sajensa domin, badan glass dake tsakani ba da akan tattausan sajensa sumbatar zata sauƙa.
Shi kuwa M Jameel cikin sauri ya lumshe idanunsa tare da gyara zamansa yana fuskantar ta da kyau.
Ita kuwa Khausar hannu tasa tare da gyara zaman ɗaurin ɗan kwalinta, sai kuma ta canza Baitin da take ji zuwa.
Waƙar Lamba tana marming tamkar zabia kai kace itace ta raira waƙar, bin baitukan takeyi tana jujjuya manyan idanunta, tana mai girgiza jikinta zuwa ƙugunta.
lumshe manyan Idanunta kumayi tare da fitar da sautin zazzaƙar muryanta a fili ta tace.
“Kai zan yiwa kalamaina.
Kai zan baiwa muƙamai na. Ungo makullaina ka riƙe.
Ta ida bautin tare da nuna saitin fuskar Moddibo da yar yatsarta ma nuniya.
Wani irin shu'umin murmushi M Jameel ya sake tare da sa hannunsa ya riƙon hannun Moddibo da ya yunƙura zai ɓalle karfin motar.
Ita kuwa Khausar, cikin azama taci gaba da bin waƙar cike da zazzafan shauƙi tace.
“Ni ban furta da wasa ba, samari dukka basu kai ba, kana nan banganin kowa da ido, dan basu isheni kalloba”.
Tayi mgnar bisa alamu daga ainihin cikin ranta take bin waƙar, M Jameel kam murmushi yakeyi cike da shauƙi.
Modibbo kuwa ya cika yayi fam dan har ransa yakeji yarinyar ta tarainashi gani yake kai tsaye ma dashi takeyi, gashi kuwa M Jameel ya riƙe masa hannunsa ƙam-ƙam.
Ita kuwa Khausar mazari uwar rawa, ƙugunta da ƙirjinta take motsawa a slowly tana mai ci gaba da cewa.
“Kai zaka zauna adamana, kuma ka bani gurin kwana, wannan shine fassarar mafarkin da nake kullum cikin baccina”.
Wani irin yar-yar Moddibo yaji tsikar jikinsa na tashi domin suna jinta ras kasan cewar Glass ɗin bayan motar a suna ƙasa kaɗan.
Ita kuwa Khausar
ida baitin tayi tana mai nuna Moddibo dake kwance jikin kujeran Idanunsa alumshe da yatsan hannunta tana murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau.
Shi kuwa Moddibo Cikin fushi ya fuzge hannunsa daga riƙon da M Jameel yayi masa tare da sanya tattauaan tafin hannunsa da niyyan buɗe motar.
Shi kuwa M Jameel cikin sauri ya riƙe tafukan hannunsa da ƙarfi tare da girgiza masa kai alamar ya bari suga iya gudun ruwanta.
Ƙwafa Moddibo yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran ya cigaba da kallonta.
Ita kuwa rawanta ta cigaba dayi tana Girgiza jikinta ganin abin nata ba mai ƙare wa bane yasa Moddibo buɗe motar cike da tsananin fusata.
Kamar walƙiya ko wanda ya diro daga sama haka taga Moddibo a gabanta,
Cikin tsoro, mamaki, da kiɗima kalli fuskarsa cikin zare ido ta tayi ƙasa da kanta,
domin bata tsammaci da mutum aciki ba.
Shikuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya fito daga motar tare da tsaida idanunsa akanta yana mai ƙara tsananta suƙe fuskarta da ya ƙara razanata.
Ita kuwa cikin tsananin ruɗu da tashin hankali mara misaltuwa ta ɗaura hannunta akai.
tare da zubewa akan gwiwoyinta tana mai girgiza kanta gaba ɗaya ta gaza cewa komai.
M Jameel kuwa gefen Driver ya buɗe tare da fitowa yana dariya mai sassayan sauti,
dai-dai lokacin da Ummi da Asma'u suka fito daga cikin gidan zuwa harabar gidan.
Idanu Ummi ne suka sauƙa akan Moddibo da M Jameel kafin kuma ta maida ganinta kan Khausar dake durƙushe ta kama kai da hannunta duka biyu,
cike da mamaki asaman fuskarta Ummu tace.
“A'a ikon Allah Khausar lafiya ya dai haka!?”.
Kasa cewa komai Khausar tayi, still hannunta na kanta haka zalika ta kasa ɗago kanta banda bugawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta keyi da ƙarfi.
Ganin Ummi da tambayar da take yiwa Khausar yasa Moddibo basarwa kamar baisan da ruwan ɗigon Khausar dake tsugunne gabansa ba,
cike da nutsuwa da kuma takun ƙasaita ya janye ƙafarsa da ya ɗaga da niyar zaiyi wasan ƙollo da Khausar ɗin yana mai maida fushinsa ya haɗiye ya juya ya nufi gaban Ummi.
Murmushi Ummi tayi Idanunta akan Moddibo tace.
“Sannun ku da zuwa Babana, dama yanzu nake shirin zuwa unguwa zanje duba jikin Maman Khausar”.
Ta ida mgnar ta maida kallonta kan Khausar da har zuwa yanzu take durƙushe sai dib dab dib dab da sautin zuciyarta ke badawa, cikin kula tace.
“A'a Khausar yaushe kika zo? ya jikin Mommyn ki?”
Ita dai Khausar bata ɗago ba bare kuma ta motsa, gani take aduk lokacin da tayi kuskuren ɗaga kanta Moddibo zai iya kifeta da azabebben marinsan nan mai sa mutum ganin taurari masu wutsiya.
Cikin kula Ummi ta juya ta kalli Moddibo dake tsaye hannunsa na acikin aljihu murmushi tayi kana tace.
“Allah yayi zaku zo ku sameni, kuzo mushiga daga ciki”.
Kai suka jinjina tare da wuceta, ita kuwa Ummi juyawa tayi zuwa gaban Khausar ɗan tsugunna tayi tare da riƙo hannun Khausar tace.
“Duk cikin gaishe da Malama ne har haka Khausar? to taso mu tafi”.
Sai asannan Khausar ta ɗago kanta tare da sakin wani nan-nauyan ajiyar zuciya, ganin Moddibo bai nan cikin mutuwar jiki tabi Ummi falon.
Suna shiga Khausar tayi saurin janye hannunta daga cikin na Ummi, kana ta kama na Asma'u suka nufi Bedroom ɗinta”.
Suna shiga Bedroom ɗin Khausar ta janye hannunta daga na Asma'u ta zauna agefen gadon Idanunta cike da ruwan hawaye ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Asma'u nashiga ukuna!nikam yau naga ta kaina, Allah yana jarabtana ta hanyar haɗani da Moddibo a bauɗaɗɗen yanayi,
zuwa na kenan naji wata waƙa tamin daɗi na tsaya ina bi uwa zabiya.
Kuma kin sanima fa ni ban fiye jin waƙa ba, sannan bai dameni ba amma kawai ɗazu naji wata waƙa MP din Haiydar Wai ita Buga da Lamba kuma wallahi nasan Haiydar ne ya haxa min da bai bani aron MP ɗinsa ba ai da banjita ba bare inji yamin daɗi, kawai na kama rawa tamkar yar gala,
ashe Moddibo na kallona nikam bansan irin hukuncin da zai minba gobe amakaranta, ƙilan ma ya sake sakani kaɗe ɗan kwali nikam nashiga Ukuna! Laifi kan laifi gashi gyale na yafa ga uban turaren dana zumbuɗa ga rawa dajin waƙa Wayyo ni Batula Faɗimatuzzahara naga ta kaina!”.
Ta gumi Asma'u tayi tare da kallon, Khausar da tayi narai-narai da ido kana tace.
“Ke kam dai Khausar kamar saɓani Allah yake haɗaki dashi”.
Narai-narai tayi da ido tare da dafe kuncinta da hannun biyu kana tace.
“Mummunan saɓani ma kuwa, na sharri ma ya Allah kashiga tsakanin na gari da mugu, Allah kara bani dashi ya Allah kada ka bashi ikon zalunta na, tun da dai arashin sani nayi kuma babu wanda yafi ƙarfin kuskure ai seya min uzuri ko?”.
Janye mata tagumin Asma'u tayi tana dariya tace.
“Kece Khausar wani zubin sai ahankali, kawai daga zuwa saiki hau rawa kamar mazari da anyi magana ki wani ce Allah yashiga tsakanin na gari da mugu sannan da kike maganar uzuri a'a ba'asi za amiki ba uzuri ba kuma waye mugun waye na garin”.
Sheƙeƙe Khausar ta ɗago kai tare da tsirawa Asma'u Idanu kana tace.
“Nifa na lura dake tun ba yanzu ba, kinfi ƙaunar Moddibo dani wato