Showing 3001 words to 6000 words out of 176046 words
jawo ya ɗaura, kana ya zare na ƙasan, matseshi yayi tare da shanyasa.
Sannan ya fito yana mai tsane tattausan sumar kansa da ƙaramin towel ɗin.
Gaban dreesin meeror'nsa ya tsaya, ya fara kimtsawa, cikin yanayin nitsuwarsa da rashin yin abu da gaggawa...
Bayan ya gamane ya fito fes yana baza ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa, sai wani irin kyalli sajensa keyi, yayinda jajayen lips ɗinsa suke wani irin sheƙi tamkar dai irin yadda lips ɗin jarirai yake sheƙi in sun ɗan laso lips ɗin.
Wata tattausar jallabiya blue color mai ɗan karen taushi da kyau ne, a jikinsa, tayi cib-cib da ɗan madaidaicin jikinsa, sai kuma fararen takalma half cover masu taushi da ya zira tattausan sawayensa da suke farare ƙal, yayinda dun-duniyar sawun nasa ke sarari.
Farin hirami ya naɗa a kansa, irin naɗin nan na zamani wanda matasan larabawa keyi,
Sai wayarshi daya zira a ajihun gaban jallabiyar tasa, wani irin sassayan ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa yake zubawa,
Taku yakeyi cike da kamala, yayinda hannunsa na dama ke riƙe da jakar system nasa.
Cikin yanayinsa na nitsuwa ya ƙara so bakin kitchen ɗin.
Siraran Idanunsa ya ɗan jujjuya ya kalli tsakiyar gidan baki ɗaya, sai ya kuma ɗan leƙa cikin kitchen din, nan ma babu alamun Innayi.
Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya nufi ɗakin nata, ganin takalmanta a bakin ƙofar.
“Assalamu alaikum”. Yayi sallama cikin wata iriyar sassayar muryar mai cike da haiba nitsuwa da kamala.
Sai kuma yayi saurin shigowa cikin ɗakin.
Ganin Innayi na kwance bisa sallaya babu ko pillown ga kuma karkarwa da jikinta keyi.
A hankali ya rusuna tare da takwara ƙafarsa ta dama ya zauna kanta ta hagu kuma ya tsaidata, cikin kulawa da tarin so tausayi, ya motsa lips ɗinshi a hankali yace.
“Yah Salam.
Innayi! Innayi!! Innayi!!!”. Ya kirata sau uku, ganin bata amsa bane, yasashi manna tafin hannunsa kan goshinta, wanda hakan ne yasata buɗe kwayar idanunta da sukayi ja.
Sai kuma ta medasu ta rufesu, sai ga wasu hawayen masu zafi sun kwaranyo mata.
Jiki na rawa tasa hannunta, ta kamo hannunsa, murya a raunace tace.
“Aliyu”. Da sauri ya zuba mata idanun tare da tsareta dasu, domin zai iya cewa, wannan shine karo na biyu a rayuwarsa da yaji ta kirasa da asalin sunansa na yanka.
A hankali yace.
“Na'am Innayi meke damunki? Meyasa baki kirani kin gaya min baki da lfy ba? Tashi mu tafi asibiti”.
Ya ƙare mgnar yana mai tallabota ya zaunar da ita.
Wani dogon numfashi Innayin taja cikin rawan murya tace.
“Aliyu ka zauna, kaji abinda zan gaya maka”.
cikin yanayin kulawa a sanyaye yace.
“A'a muje asibiti tukuna, sai mun dawo”.
Cikin ɗan ɗaga murya tace.
“Aliyu ka bari kaji abinda baka saniba.
Bana son in mutu in barka a nahiyar maraici, bana son in mutu da abinda ni kaɗaice na sani kuma nakeda dama da ikon sanar da kai, idan na mutu a haka ban sanar da kai abinda ke bibiye da muba, nayi maka cuta mafi muni a rayuwarka.
Aliyu ka bari in sanar da kai abinda Allah ya nuna min a daren jiya”.
A hankali ya fesar da nannauyan numfashi, sai kuma ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin, jiyo Muryar Amininsa mafi ɗan uwa, wato M Jamil yanayin sallama, a hankali yace.
“Wa alaikassalam J”.
Ya ƙira Aminin nasa da sunan da duk duniya shi kadai ke kiransa da hakan,
Ido ya zubawa M Jamil ɗin a hankali tare dayi masa alamun ya shigo da kwayar idanunsa,
Cikin yanayin sauƙin kai sakin fuska faram-faram Jamil ya sako kansa cikin ɗakin yana mai cewa.
“Iya innare yau me kika dafa mana ne, dan tun jiya da na dawo ƙasar nan banci komai ba, nace sai abincinki zanci ko na Ummina”.
Sai kuma yayi shiru tare da matsowa kusa da ita...
Cikin Masarautar Gembilan kuwa.
Wata Kekkyawar matace yar duma-duma mai kyan shiga da haiba, ke zaune bisa kujera, yayinda System ke gabanta bisa ɗan madaidaicin stool yayinda fuskarta ke manne da wani ɗan farin glass siriri.
Da alamu typing takeyi.
Kai ta ɗan jinjina tare da juyowa ta kalli dinning area inda hayaniyar yaranta ke tashi.
Kai ta ɗan jinjina tare da kallon wata yar narkekkiyar matashiya da bazata wuce 14 year's ba.
Ido ta zuba mata ganin ta nufota da sauri.
Hannunta ɗaya.
Riƙe da school bag da takalmin sinika da kuma ɗan madaidacin hijabin Uniform ɗin ta.
Da sauri ta rusuna gaban Matar tare da juya mata baya tana cewa.
“Ayya Momy tubke min kaina, nayi-nayi yaƙi sai na ƙulleshi sai ya sule”.
Kwaffa tayi tare da cewa.
“To wai ke kam Khausar yaushe ne zaki iya, tubke gashin kanki”.
Ta ƙare mgnar tana tattaro suman Khausar din yana mai zamewa,
Sai kuma ta ɗago kanta ta kalli Ɗan matashin yaron da yanzu ya fito cikin Uniform ɗinsa. Wanda yake iri ɗaya dana jikin wacce aka kira da Khausar.
Da alamun ya gama shirinsa tsab.
Cikin tsuke fuska ya watsawa Khausar din harara tare da cewa.
“Gsky ni zan tafi Ramadan Raudat zomu tafi, kullum ita ke jaza mana yin letting muje aita zanemu kamar bayi.
Ni wlh da zan samu a rabamun hanya da ita inaso, muna shiga school kamar wasu shaidanu zakaji an fara cewa.
FATTANAH kuka biyewa ko, duk sai an gama shiga aji kafin ku iso.”
Cikin yanayin tsiwa da son girma ta miƙe tsaye tana ɗaure ɗan kwalinta harara ta watsa mishi tare da cewa.
“Wallahi ka shiga hankalinka dani Haydar in baka dena cemin FATTANAH ba zan fasa maka baki”.
Dogon tsaki yaja tare da juyawa ya nufi ƙofar falon, yana gyara zaman net ɗin sa. Tare da cewa.
“Sai ki gayawa wanda yasa miki sunan, ko kuma ki nitsu ki dena rashin kunya da rawan kai”.
Cikin ɗan ɗaga murya Momyn nasu tace.
“Gsky Babana bana son wannan sunan da aka liƙawa Mamana sam bafana son sunan”.
Da sauri yace.
“Toh Momy ai ita ta jawa kanta fitinenneyar ce ta gasken gaske, in dai kinji faɗa to da ita a ciki, in kuma babu ita to zakiji ance ai gulma akayi ta maidawa maishi, wai ita ba'a gulma da ita, itafa tana iya zuwa zuwa ta samu ana faɗa ta shiga tayi kane-kane sai an gama tace wai me dalilin faɗan”.
Ya ƙare mgnar yana fita.
Ita kuwa Khausar zama tayi gefen Momynsu tana sa takalmanta da ɗan sassarfa domin yau din ranace ta musamman a wurinta tana cike da ɗokin zuwa makaranta kasancewar yau suka dawo hutu, kuma hutune na canjaza aji da JSS zata tafi SS 1 wanda takega matakin samun encinta ne kenan zata taka, tunda yanzu zata koma aji da matan aure, a islamiyar safe, sai kuma na bokone tacan anan ne babu enci sai randa ta gama sa takalmin ta saka, tana sakin yelwataccen murmushi.
Yayinda Ramadan da Raudat suke tsaye gefenta.
Hannu tasa ta kama hannun Raudat tare da cewa.
“Mu tafi”.
Da sauri ta juyo ta kalli Momyn nasu tare da kwaɓe fuska jin tana cewa.
“Ku biya sashin Gimbiya Dadu ku gaidata, bata da lfy”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Momy zamuyi letti muje wannan mai sunan baban naki ya samu damar sawa a azabtar dani”.
Ta ƙare mgnar cikin son zillewa zuwa sashin Gimbiya Duda, ita kuwa Momy tsuke fuska tayi tare da cewa.
“Ku biya ku gaisheta da jiki nace ko”.
Cikin bin umarnin mahaifiyar tata badon tasowa tace.
“Toh Momy”.
Daga nan ta kada kan ƙannen nata Duk suka fito.
Sai kuma tayi sauri ta juyo tare da cewa.
“Momy mun tafi”.
Murmushi tayi sanin manufar ta yasa cikin lumshe idanu tace.
“Allah ya kaiku lfy ya baku Sa'a Allah yasa ki shiga SS 1 da ƙafar dama, Allah ya shirya min ku”.
Cike da jin daɗi tace.
“Amin Ya Allah”.
Kana suka fita.
Suna fitowa suka samu duk sauran yaran gidanma sun fito.
Kamar haɗin baki kab ɗin su sashin Gimbiya Dadu suka nufa.
Kai tsaye suka wuce har bedroom ɗin ta domin bata falon.
Su Asiya ce, a gaba ita da sauran ƙannenta, sai kuma su Khausar din.
Zaune suka sameta bisa tsakiyar gadon mulkinta, mai martaba Lamido Gembilan yana zaune ƙasa bisa carpet, yana haɗa mata tea,
Cikin tarin biyayya, da sauri suka rusuna baki ɗayansu, kusa haɗa baki sukayi wurin cewa.
(“Allah saine Abba, noi nɓanɗu Dadu?) Allah ya faranta maka Abba ya jikin Dadu?”.
Cikin son ahlin nasa ya jinjina masu kai tare da cewa.
(“Yettore Allah nwodi dama) an godewa Allah da sauƙi”.
“Allah ntokkin dama”.
Suka faɗa a tare, cikin tankwashe sawunsa yace.
“Allah jabu”.
Amin suka faɗi baki ɗayansu,
Yayinda Khausar kuma taketa jan hijabinta, tana mai sunkuyar da kanta ƙasa,
Allah ya sani bata ƙaunar abinda zai kawo ta gaban Gimbiya Dadu,
Domin jikinta da nitsuwarta duk rasasu takeyi, sabida wani irin mayataccen kallo mai bada tsoro da tsohuwar ke Binta dashi.
Kamar koda yaushe kuma hakane, duk da bata da lafiya, amman wani irin masifeffen kallo ta tsare Khausar ɗin dashi har bata jin gaisuwar da jikokin nata keyi mata,
Cikin taɓe baki Asiya tace.
“Dadu wannan wanne irin kallo ne? muna gaidaki kinyi shiru?”.
Jin hakanne yasa Khausar ɗan ɗago kanta,
Ai kuwa ido cikin ido sukayi da Dadu.
Da sauri ta motsa lips ɗin ta a hankali tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un”.
Sabida wani irin tashi da tsikar jikinta ya farayi, yam-yam.
Ita kuwa Dadu har lau bata cire idanunta a kantaba,
Haydar ne ya ɗan miƙa tsaye tare da kamo hannun Ramadan da Raudat yace.
“Dadu Allah ya sauwaƙa, zamu tafi school kada muyi letti Raudat muje”.
Abin mamaki har lau Dadu batama san anayi mata mgna ba, bare ta amsa musu, gaba ɗaya nitsuwarta da kallonta yana kan Khausar....!
Lamido kuwa ido ya zubawa maifiyar tasa, cike da mamakin lamarinta, ya zama ana kallon kalo, ita tana kallon Khausar data kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi shi kuwa yana kallonta.
Asiya kuwa itama miƙeqa tayi tare da kaɗa kan ƙannenta tayi gaba Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta ɗan miƙa tare da cewa,
“Uhum”. ta fice
Ya zama daga Dadu sai Lamido sai Khausar.
Cikin wani irin yanayi da Khausar din keji ta kuma kallon Dadu, wacce zuwa yanzu ta saki laɓen bakinta na ƙasa, wani irin yawu mai cike da mayataccen kwaɗayi ne ya tsinko mata, har yana ɗan sauƙowa kan lips ɗin ta.
Cikin sauri Khausar ta miƙe jin Lamido yana cewa.
“Mamana tashi ku tafi”.
Ai kafin ma ya rufe bakinsa, tuni ta fita tana mai cewa.
“Toh Abba”.
Ita kuwa Dadu wani nannauyan numfashin ta sauƙe tare da juyowa takalli ɗan nata, dake miƙa mata cup ɗin tea.
Cikin diriricewa tace.
“A'a bana buƙatar abin zaƙi, a kawo min abu mai yaji-yaji”.
Cike da biyayya yace.
“Toh”.
Kana ya miƙe ya fita.
Tuni su Khausar kuwa sun shiga school bos ɗinsu,
Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta kalli Ramadan dake cewa.
“Kalli fa 8:13 na tabbatar yauma zamu zanu”.
Cikin sanyi tace.
“Mu dai Allah ya rufa mana asiri daga SS 2 akwai matan aure da yawa a ciki, so ba batun duka a side ɗin mu.
Kuma ma duk bama saɓa doka cikin nitsuwa da tarbiyyar mu muke, ko nayi litting nasan za'ayi min uzuri.
Cike da jin daɗi, Khausar tace.
“Nima dai Allah ya yaye min masifa da cin zalin su Moddibo tunda yau dai zan tafi Ss 1 ɗin, da ba duka ba zagi, wlh inci karena babu babbaka”.
Taɓe baki Haydar yayi tare da cewa.
“Mu gefen maza, babu manya, duk yarane, manyan da dare suke zuwa, shiyasa babu roggomi”.
Asiya ce ta kalli Khausar cikin yanayin son yarinyar tare da cewa.
“Ai wlh ke dai in baki nitsuwa ba ko jami'a kikaje in dai Moddibo na cikin malamanku, na tabbatar zai san matakin da zai ɗauka a kanki.
Sannan ma da kike batun kin tafi Ss1 akwai matan aure, kin mance cewa, na safene, na islami.
Akwai na rana zuwa biyar bokone, kuma kuna tare da moddibo.”
Kwaffa tayi tare da cewa.
“Kai na shiga ukuna wlh”..
Anan gefen su Modibbo ku, fir innayi taki aje asibitin. Su kuna su kasa fahimtar ta, gani suke zafin zazzaɓin maleria ne yake son sata surutai shiyasa suke hanata mgn sukayi ta mata addu'o'i hardai ta ɗan fara samun nitsuwa har bacci ya ɗan sureta.
Gani ta ɗan rumtsane yasa suka tafi wurin Ummin M Jameel suka ɗauko Ummin dan tazo ta ɗan kula da ita.
Suna isa bakin gate, ba tare da sun shigaba, Ummin ta kalli M Jamil da yayi saurin fitowa bayan yayi parking marfin motar ya buɗe, mata cikin tsananin son mahaifiyar tasa, yace.
“Bismillah Ummi fito ki shiga wurin Innayinki, domin mu dai yau mun gaza gane kanta, da alamun Ita dai dare ɗaya gigin tsufa ya sauƙo mata”.
Ɗan buge ƙeyarsa tayi tare da ciwa.
“Tsufa kan zai cimma taka uwar mafa, kawai dai inaga zafin zazzaɓine kusan wasu lokutan yanasa yara surutai, to ita kuma girma yazo dole in ciwon yayi zafi zatayi kamar na yara”.
Juyowa tayi ta kalli Moddibo daya jingina kansa jikin kujerar gaban motar gefen mai zaman banza,
Cikin sanyin murya yace.
“Uhmmmm Ummi waifa cewa tai taga taurari suna sauƙowa ƙasa har kamar zasu taɓa rufin side nan, anya kuwa Ummi wannan zazzaɓi ne?”.
Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa cikin alamun nazari yace.
“Ina tsoron kada fa matsalar ƙwaƙwalwa ce, nayi nayi muje asibiti kuma taƙi.”
Ya dire mgn tare haɗa kan yatsun hannunsa.
Jamil ne yaci gaba da cewa.
“Saida fa Moddibo yayi ta mata tofi kafin muka samu tayi bacci har muka fito ɗin.”
Cikin kulawa Ummi tace.
“In sha Allah babu komai, bari in shiga, ku kuje”.
To Jamil yace kana ya shiga mota, ita kuma tayi cikin gidan.
A hankali ya miƙa dalleliyar motarsa ƙirar BMW kan shimfiɗeɗen titin,
Yana tafiyar hawainiya, murmushin yayi ganin kallon da Moddibo yake masa.
“Sanin yau za'a dawo makaranta ne, yasa nayi ƙoƙarin dawowa baro Marrocco, duk da akwai ayyukan da ban gama dasu a company'nba,”.
Cewar M Jamil shi kuwa Moddibo kai ya jinjina alamun yana jinsa, shi kuwa M Jamil gudu ya ɗan ƙara tare da ci gaba da mgn dan yasan ba lallai ne Moddibo ya amsa mishi da bakiba, inda sabo ya saba, kuma shi yasan cewa body language al'adane ko ɗabi'a koma yace halittar Moddibo ne.
Juyowa yayi ya kalleshi tare da cewa.
“Na zaƙu muje makarantar nan, dan nasan zaiyi kyau sosai a tsarin gyarashi da akayi”.
Cikin ɗan ƙwaɓe fuska yace.
“In an gama gyaran ba”.
Da sauri M Jamil yace.
“Kamar yaya za'a gama mana”.
Juyowa yayi ya ɗan kalli M Jamil ta gefen ido kana a takaice yace.
“Toh ba'a gaman ba”.
Cikin sauri M Jamil yace.
“A.S da gaske ba'a gama ba?”.
A.S shine sunan da yake kiran Moddibo dashi kuma su biyu kaɗai suka san ma'anar sai kuma abokan karatunsu.
Shi kuwa Modibbo littafin dake gaban motar ya ɗauka tare da buɗe wa kana yace.
“Dama tun lokacin da za'a bada hutun na faɗa bazai isa a gama gyaran school ɗin ba, musamman da ya zama an ƙara yawan class, kana ga gina hall din da akace za'ayi, kuma dole aikin bazaiyi guduba sabida Ramadan, tun lokacin nace a ƙara kwanakin hutun, sabida samun isasshen lokacin, wannan Ba fulatanin yaƙi”.
Murmushin M Jamil yayi tare da cewa.
“Toh kai meyasa baka ƙara hutunba, ai da sai ka sanar”.
Juyowa yayi ya kalleshi bayan hannunsa yasa ya shafa tattausan sajensa tare da cewa.
“Uhmmmm”.
Ya san me wannan Uhmmm ɗin take nufi, kai ya jinjina tare da cewa, “Mu dai yan kallone,".
Da sauri yace.
“Nima haka, dan na gaji ko yaushe sai ya kwaɓa abu yazo yana cemin ina mafita”.
Dai-dai lokacin aka buɗe musu gate din makarantar, Ya Salam.
Wani irin tsarine da zubi makarantar yake dashi, tsari mai burgewa, yayinda shima makarantar Moddibo ya ƙawatata da tsirrai na kyautata muhalli.
Tabbas gyara kam da saura ba'a gama shi ba.
Domin daga woje dai kam an kammala komai amman daga ciki, duk cikin ajujuwan a hargitse yake.
M Jamil nayin parking, wani kekkyawan dattijo bafulatani ya nufo matar tasu da sauri, bisa alamu dai shine shugaban makarantar domin duk malaman na miƙa gaisuwar garesa cikin mutuntawa.
“Moddibo! Moddibo!! Moddibo!!!.”
Jamil ne ya fito yana murmushin tare da cewa.
“Allah rene,”.
Da sauri yace.
“Ina Moddibo”.
Cikin motar Jamil ya nuna masa, da sauri ya sunkuyo,
Yayinda shi kuwa Moddibo meda bayansa yayi ya jingina tare da lumshe idanunsa, murmushi Dattijon yayi tare da cewa.
“Ga ɗalibai duk sun dawo makaranta ta cika maƙil ga sabbin ɗauka, kuma aiki baifi rabi ba, ya zamuyi?”.
Cikin taɓe baki yace.
“Allahu a'lamu!”.
Jamil ne ya juyo ya kalli Malam Ahmad da Malam Habibullah da suma fitowar su kenan daga can cikin makarantar.
Shi kuwa Malam Arɗo Umaru mamallakin makarantar kuma .
Kai ya ɗan dafe tare da cewa.
“Dan Allah ka fito Moddibo kasan bayanin da zakayi musu, kana ka kara musu kwanakin hutun, tsawon lokacin da kakega za'a iya gama gyaran”.
Yadda ya dire mgnar da karya wuyane yasa Moddibo fitowa.
Murmushin sauran malaman sukayi, domin sosai tsufa ya fara cimma Mala Arɗo, zuwa yanzu ya kamata ragamar makarantar ya zama a hannun yara, domin badon Allah yasa Moddibo ke tsara komai na jadawalin abubuwan ciki da wajen makarantar ba, da tuni ta durƙushe, to amman sabida shi da sauran haziƙan malamai da suke da tsananin kula da tarbiyyar yara da sukeyi yasa har yau makarantar bata da na biyu a faɗin birnin Gembila.
Kusan a tare suka rakaya cikin makarantar.
Yayinda hayanin ɗalibai manya da yara maza da mata, ke tashi.
Juyowa yayi ya kalli Jamil tare da cewa.
“J kaje masallaci kayi mgn duk mu su haɗu a tsohon halla ɗin mu na sama.”.
To Jamil yace yana tunanin to me zaice musu,
Masallacin ya wuce tare da yin sanarwan.
Nan take kuwa, duk ɗaliban suka haura sama, suka shiga cikin babban hall ɗin nasu wanda yake ƙato sai dai duk da haka yanzu ya musu ƙaramin,.
A gafen mazama suma duk sun haɗu a halla nasu.
Shi kuwa Moddibo office nasa ya wuce.
Jim kaɗan ya fito, da Lapel Microphone a hannunsa yana saƙalasa a wuyan tattausan jallabiyar jikinsa Malam Ahmad ne ya matso kusa dashi tare da cewa.
“Zamu jirane ko an ƙara mana hutu”.
Ɗan murmushin gefen baki yayi tare da cewa.
“Hutu kuwa sosai ma har na tsawon mako uku za'a ƙara”.
Cike da murmushi yace.
“Mu tafi kenan”.
Kai ya gyaɗa masa tare da cewa.
“Suma duk yanzu zan kaɗa kansu ko wacce tai gida sai dai muma muna da zama na musamman”.
Ai kuwa jin haka yasa duk malam suka zauna jiran.
Shi kuwa ya haura saman yana mgn da M Jamil a waya.
“Su maza basu da hayaniya, kawai J ka ɗanyi musu nasiha, kana kace sai bayan mako uku zasu dawo kafin nan an gama gyara,
Sai dai masu zuwa hadda suci gaba da zuwa."
Cike da gamsuwa M Jamil yace to.
Kana sukayi sallama.
Dai-dai lokacin kuma su Khausar suka shiga cikin makarantar,
Da in ka gani kace a ƙasashen ƙetarene, domin makaranta ce mai zaman kanta, mai cike da haziƙan malamai, duk