Showing 129001 words to 132000 words out of 176046 words

Chapter 44 - Sakayya 1 Hausa Novel Complete

da abinda kikayi min, kuma ki sani wlh ban yafeba*

Isrnett. Gaban motar ne ya bugi Ramadan, kamar gilmawar walƙiya ya faɗi agefen kwaltan.
Akuma dai-dai lokacin motar Moddibo da M Jameel ya tsaya awajen cikin sauri M Jameel ya buɗe motar tare da fita yana cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”. kana ya nufi inda Ramadan ke kwance.
Moddibo kuwa kansa ya dafe tare da rintse idanunsa.
Akuma dai-dai lokacin Malam Isa,Malam Ahmad da malam Sa'id suka ƙara so Kasancewar lokacin ne Malamai suka fara zuwa wasu ma ko Parking basuyi ba.
Motar daya bige Ramadan kuwa ko tsayawa bai yiba ya ɗiba aguje.
Aminu kuwa cikin tsoro da tashin hankali ya juya tare da kallon Ramadan dake kwance yayin da M Jameel ke tsugunne kansa zuwa lokacin tuni Ramadan ya suma ɗagosa M Jameel yayi tare da ɗan buga kuncinsa yana cewa.
“Ramadan! Ramadan!!”.
Amma ko motsa wa baiyi ba alamar babu nunfashi atare dashi.
Cikin sauri Malam Arɗo ya fito daga cikin makaranta kasancewar ɗaya daga cikin Malaman yashiga ya sanar masa an samu hatsari awaje.
Moddibo kuwa cikin sauri yayi wa motar key tare da ƙoƙarin bin bayansu ganin basu da niyyar tsayawa yana ƙoƙarin gilmawa M Jameel ya ɗaga masa hannu tare da faɗin.
“A.J ka tsaya mu ɗauke sa mu kaisa asibiti”.
Jin haka yasa Moddibo fasa bin bayan motar kana ya tsirawa bayan motar Ido ya tsaida ganinsa kan number burki ya taka.
M Jameel kuwa cikin sauri ya ɗauko Ramadan ya sanya shi cikin motar ya tada suka nufi asibiti, Malam Arɗo kuma motar Malam Isa suka shiga tare da kallon sauran Malaman dake tsaye kana yace.
“Malam Isma'il ku shiga ciki”.
Kana Malam Isa yaja motar suka tafi.

Haiydar kuwa har zuwa yanzu ya kasa buɗe Idanunsa saboda tsananin tsoro da tashin hankali ji yake yana buɗe idanunsa zai ga ƙwaƙwalwar Ramadan abaje akan kwalta hakan yasa ya runtse Idanunsa kana ya sanya hannunsa duka biyu ya dafe kansa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Raudat kuwa kuka take tamkar ranta zai fita yayin da take yarfe hannunta tare da bubbuga ƙafarta tana cewa.
“Wayyo Ramadan ina za ku kaisa Meyesa mesa Wayyo Ramadan ɗina!”.
Malam Isma'il ne ya ƙara so kusa da Haiydar tare da riƙe hannunsa ganin yanda jikinsa ke rawa kana yace.
“Haiydar buɗe idon ka”.
Girgiza kai Haiydar yayi still cikin Muryan kuka yace.
“A'a tsoro nakeji in buɗe ido na inga ƙwaƙwalwan Ramadan akan kwalta”.
Girgiza kai Malam Isma'il yayi tare da cewa.
“Babu komai babu abinda ya sameshi beji ciwo ba motar ce ta bigesa ya koma gefe amma bata bi ta kansa ba!”.

A hankali ya buɗe Idanunsa da sauri kuma ya sake ware su ganin babu kowa sannan Ramadan ma baya nan cikin rawan murya ya kalli malam Isma'il tare da cewa.
“Ina Ramadan ɗin?”.
Kallon titin Malam Isma'il yayi tare da faɗin.
“Malam Jameel da Moddibo sun tafi kaishi asibiti sannan Malam Arɗo yabi bayansu yanzu kutafi cikin makaranta ka kwantar da hankalinka kaji?”.

Girgiza kai Haiydar yayi yace.
“Ya za'ayi kace in kwantar da hankalina kansa yafashe ko?
ya karye ko? Ko dai ya mutu ne?.
Cikin sa ya fashe ko? Kan kare sa akayi akwalta ko!?”.
Duk alokaci ɗaya ya jero masa tambayar.

Girgiza kai Malam Isma'il yayi kana yace.
“Wallahi babu abinda ya sameshi kawai dai tsoro ne idan mutum bai taɓa accident ba dole tsoro zai sa ya suma kaje kashiga cikin makarantar maza kushiga ciki”.
Dai-dai lokacin kuma ɗalibai suka fara zuwa cikin rarrashi Malam Isma'il yace.
“Ku shiga ciki”.
Raudat kuwa kuka ta riƙa yi tana yarfe hannu tsugunna wa Malam Isma'il yayi ya ɗauketa suka shiga cikin makarantar kana ya shiga bawa Haiydar ƙarfin guiwa.

Acan ɓangaren su M Jameel kuwa suna isa Hospital ɗin aka karɓi Ramadan tare da kaisa Emergency Room.
Atake aka fara bashi temakon Gaggawa kasancewar akwai ƙwararrun Likitoci cikin ikon Allah beji wani rauni ba sai karaya daya samu aƙafarsa na hagu.
Cikin mintunan da baza su gaza talatin ba ya farfaɗo tare da fashewa da kuka kana ya buɗe Idanunsa tare da cewa.
“Wayyo ƙafata Addah Khausi Ƙafata, Wayyo Addah Khausi Ƙafata”.
Ahankali Moddibo dake gefensa ya matsa tare da riƙe hannunsa kana yace.
“Sorry Ramadan kayi haƙuri kayi shiru kaji”.
Cikin kuka sosai Ramadan ya kallesa tare da cewa.
“Mommy na Malam akaini wajen Addah Khausi.
Ina Addah Khausi na Ƙafata ciwo yake min zafi?”.
Ya ida maganar yana jujjuya kai yayin da gaba ɗaya zufa ya wanke masa ilahirin jikinsa Musamman saman goshin sa amma babu hawaye a Idanunsa yayinda ƙafansa ya sake kamar roba ya langwaɓe.
Cike da rarrashi da kuma tausayawa Moddibo yace.
“Kayi haƙuri zai daina insha Allah”.
M Jameel kuwa magunguna da abubuwan da za'ayi ɗauri Dr ya rubuta masa kana ya ya fice tsaye ya samu malam Arɗo maƙale da waya akunnen da alama da Lamiɗo yake magana.

Cikin yanayin jimami ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.
“Wallahi kuwa akwai yaron wajenka da mota ta ɗan kuskuresa yanzu haka ma muna asibiti”.
M Jameel ne ya gyara tsayuwar sa tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya lumshe idanunsa.
Cikin sauri Malam Arɗo yace.
“A'a ka kwantar da hankalin ka Mai Martaba baiji wani ciwo ba.
Dan Allah dan Annabi ka kwantar da hankalin ka”.
Ganin Malam Arɗo ya katse kiran yasa M Jameel cewa.
“Malam wai batun ɗauri ne ƙafarsa ta karye to yanzu ance za'a yi masa ɗauri”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi kana suka fita da M Jameel.

A can Gidan Lamiɗo kuwa tun bayan tafiyarsu Ramadan Makaranta Mommy ta kasa miƙewa taje ta gyara ɗakin mijin nata.
Duk da kuwa cewa itace da girki baki ɗaya jikinta Asanyaye yake bata da wani kuzarin kirki yayin da Khausar ke kwance gefenta har zuwa lokacin hannunta na dafe da maranta.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta yunƙura da niyyar miƙewa dai-dai lokacin Lamiɗo ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

Yana shiga idanunsa akan Mommy tare da cewa.
“Aysha!, Aysha”.
Cikin sanyin murya da mutuwar jiki Mommy tace.
“Na'am”.
Sai da yayi ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa tare da cewa.
“Zo muje ki rakani?”.
Kallon Mamaki Mommy tayi masa tare da faɗin.
“Ina zamu je?”.
ƙasa yayi da kansa kana yace.
“Ke kam zoki rakani wani waje mana”.

Atake zuciyarta ya tsinke ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi kana tace.
“Rakiya kuma ina kuma zamuje. Mai Martaba ka faɗa min?”.
Ta ƙara sa maganar tare da kallon ƙwayar idanunsa da take iya hango tsantsar tashin hankali da damuwa.
Cikin rawan murya tace.
“Meyesa mu Ramadan”.
Jin abinda tace yasa Khausar dake kwance tayi saurin miƙewa Atake Idanunta suka cika da ruwan hawaye lokaci ɗaya tsoro ya rufeta!.

Cikin dakiya Lamiɗo yace.
“Babu Abinda Ya samu Ramadan ke kam zoki rakani”.
Cikin yanayin sadaukar wa Mommy ta kallesa kana tace.
“Dan Allah ka faɗa min Meya samu Ramadan ɗina!”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Kizo mu tafi mana”.
Miƙewa Khausar tayi cikin rawan murya dan tuni hawaye suka wanke mata fuska kana tace.
“Dan Allah Abba inzo mu tafi”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh”.
Cikin sauri ta sanya dogon hijabinta dake fitar da sanyayyan ƙamshin ta fita, shima Lamiɗo fita yayi sashen Hajiya Bunayya ya nufa yana kirata kasancewar shi kansa be san waya samu hatsari acikin ƴaƴan nasa ba Haiydar, Aminu, ko Ramadan.

Mota suka shiga Khausar na gaba Lamiɗo Gimbiya Bunayya da Mommy suna baya.
Lokaci ɗaya hankalin Mommy ya sake tashi ganin sun nufi hanyar asibiti cikin tsanananin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n dan Allah Mai Martaba ka faɗa min me yasamu Ramadan ɗina?”.
Girgiza kai yayi tare da kallonta kana yace.
“Nima kaina ban sani ba Aysha babu yanda muka iya da hukuncin Ubangiji”.
Hajiya Bunayya kuwa ƙasa tayi da kanta cikin tsananin farin ciki da jin daɗi ta saki murmushi aranta tace Alhamdulillah burina ya cika in. Allah ya yarda yau ankawar min da Haiydar da Ramadan na huta dole inƙara musu kuɗi me tsoka yanda zasuji farin ciki na kawar min da ƴaƴa biyu maza ɗin nan shikenan Mai martaba bashida wani ɗa Namiji sai Aminu dole Aminuna shi zai gaji sarauta.

Ahankali ta ɗago kanta Idanunta cike taf da ruwan hawaye ta kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n. Mai martaba mai yafaru?”.
Cikin yanayin damuwa yace.
“Ni kaina ban sani ba ance min dai ɗana Namiji ne amma ban sani ba Aminu ne...”.
Aruɗe Hajiya Bunayya tasa hannu ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ɗaya-ɗayan nawa”.
A hankali ya fesar da iska daga bakinsa kana yace.
“Kuma ban sani ba ko Haiydar, ko Ramadan ne ban sani ba sai mun shiga”.
Mommy kuwa lumshe Idanunta tayi tare da faɗin.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan min ha”_.
Suna isa suka fito bayan Driver Yayi parking Malam Arɗo na ganin Lamiɗo yayi saurin miƙewa tare da isa inda suke kana yace.
“Sannunku da zuwa Mai Martaba”.
Khausar kuwa tun da suka fito take kuka baki ɗaya jikinta ya gama bata Ramadan ne kuma ya rasune.

Batare da Lamiɗo ya amsa Barka da zuwan da yake masa ba yace.
“Acikin ƴaƴana waye ne yasamu hatsarin?”.
Malam Arɗo ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Ƙaramin ne”.
Ƙasa daure wa Khausar tayi kuka ta fashe dashi tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Mommy Ramadan ne,
sai da yace kada yaje makaranta yau kawai abarshi kada yaje kamar yasan me zai faru dashi na nace dole na muka turashi”.
Mommy kuwa kasa daure wa tayi hawaye masu zafi suka shiga zubo mata.

Dai dai lokacin M Jameel ya dawo daga sayo magungunan a Pharmacy dake cikin Hospital ɗin.
Kallon Malam Arɗo Lamiɗo yayi kana yace.
“Ku kaimu ciki”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare dayi musu Jagora kasancewar Mai matarba ne da iyalansa yasa aka barsu suka shiga.

Suna Shiga idanun Khausar ya sauƙa akan Moddibo dake Rungumeta da Ramadan yana lallashinsa.
Ramadan na kallonta ya fashe da sabon kuka tare da cewa.
“Adda Khausi ƙafata Addah Khausi zoki riƙe min ƙafata”.
Kallonsa ya mayar kan Mommy tare da cewa.
“Mommy ancire min ƙafata ko? Bana jinta a jikina”.
Sai kuma ya kalli Lamiɗo daya zuba masa Idanu cikin matsanancin kuka yace.
“Abbah Ƙafata, Ƙafata”.
Kallonsa ya mayar kan Hajiya Bunayya ya langwaɓar da kai amma baice komai ba.

Hajiya Bunayya kuwa kallon Moddibo tayi jikinta na tsuma tace.
“Ina Haiydar kadde shi yana mutuware?, Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ido Moddibo ya zuba mata tare da tsaida idanunsa acikin nata abinda ba ɗabi'arsa bace ba kuma al'adarsa bace haɗa ido da mutum amma haka nan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akan matar yana kuma nazartan ta.
Cikin yanayin ɓacin rai M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.
“Haba Hajiya wannan wani irin kalma ne ya za ayi kice yana mutuware?”.
Hannu tasa tare da share hawayen fuskarta kana tace.
“To ina yake? Ina Haiydar Allah sarki babban ɗan mu wanda zai gaji Mahaifinsa a sarauta Wayyo Haiydar”.

Malam Arɗo da shigowarsa kenan ya kalleta tare da cewa.
“Haiydar na nan lafiya yana makaranta yana karatu kana suna cikin kulawa!”.
Da sauri Ta haɗiye wani abu mai masifar ɗaci tare da cewa.
“Toh Ina Aminuna?”.
Cike da kulawa malam Arɗo yace.
“Shima yana cikin ƙoshin lafiya wannan ne kaɗai Accident ɗin ya faru dashi”.
Lokaci ɗaya wani masifaffen ɓacin rai da baƙin ciki ya mamaye zuciyarta cikin ranta tace Haiydar bai mutu ba sannan shima wannan karayane ka ɗai?”.
Tsaban zancen zuci dake cinta saida kalmar Karaye ne kaɗai ya fito fili.

Atare Khausar da Moddibo suka kalleta jin abinda tace wannan ɗin ma Karaye ne kaɗai Moddibo ya maimaita kalmar Aransa.
Khausar kuwa kwallon ta tayi tare da tsareta da ido tana sake maimaita kalmar aranta.
Malam Arɗo ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Mai Martaba karaya yasamu dama akan za'a yi masa ɗauri ne saboda Andu basa gaba ɗaya baiji wani ciwo ba Karayane da Allah ya ƙadarta toh insha Allah yanzu za'a yi masa ɗauri”.

Jinjina Kai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Mun gode Allah ya saka da alkhairi”.
Cike da damuwa Malam Arɗo yace.
“Dan Allah kayi haƙuri akasani ne, tsautsayi aka samu wanda baya wuce ranan sa mai motar kamar da gayya yayi ko tsayawa bai yiba ya gudu baki ɗaya abin yazo da akasani ne bamu taɓa samun irin wannan akasin abakin makarantar ba”.
Girgiza kai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Bakomai Malam Arɗo ai babu yanda muka iya da ƙaddara ko agadon Mahaifiyarsa yake idan Allah ya ƙadarta zai karye dole ya karye Waman Ƙadarallahu Haƙƙa ƙadrihi”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da cewa.
“Haka ne kam”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Amma bana son ɗaurin asibiti zamu koma dashi gida ayi masa na Gargajiya”.
Jingina kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Toh shikenan Babu matsala”.
M Jameel ya Kalli Ramadan cike da tausayawa kana yace.
“Toh Mai Martaba Allah ya ƙara sauƙi”.
Kana ya miƙa masa ledan maganin daya sayo yace.
“Gashi magunguna ne na rage zugi da zafin ciwo koda ɗaurin gidan za'ayi masa za ayi amfani dasu”.
Karɓa Lamiɗo yayi tare da faɗin.
“Toh angode”.
Kana ya sanya hannu acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kiran number Malam Bala mai ɗauri.
Katse wayar yayi bayan sun gama mga, juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya da Mommy kana yace.
“Mutafi to”.
Sai kuma ya juya ya kalli Khausar dake kuka hadda sheshsheƙa yace.
“Haba Addah Khausi kiyi haƙuri mana ai sai ki ƙara tayar masa da hankali shi yana kuka yana kiran ki sannan kema kina kuka ki bashi ƙarfin gwiwa mana”.

Kai ta gyaɗa tare da Matsawa kusa dashi still Moddibo na riƙe dashi bakin gadon ta ƙara sa Moddibo kuwa saurin lumshe idanunsa yayi.
Ita ko Khausar cikin kuka ta kalli Ramadan tare da cewa.
“Kayi haƙuri Ramadan da mun sani da baka je makarantar nan ba tun jiya kake cewa baza kaje ba kana ta roƙon Mommy kada kaje”.
Kallonta ta mayar kan Mommy tare da faɗin.
“Dan Allah Mommy duk sanda yaron nan ya sake cewa ba zaije makaranta ba kada abarshi yaje tun jiya yake ta roƙo yau ɗaya abarshi ya huta kamar yasan abinda zai faru dashi”.
Kasa cewa komai Mommy tayi ɗan ita kaɗai tasan yanda zuciyar ta ke mata.

Khausar kuwa ahankali ta tsugunna akan Ramadan ganin yanda goshinsa ke tsats-tsafo da zufa ta ɗago lallausan tafin hannunta tare da mannawa agoshin sa ta yarfe masa zufan.
Ahankali Moddibo ya tsirawa tafin hannunta Idanu cikin wani irin yanayi sannu Ahankali tsikar jikinsa ya fara tashi lumshe idanunsa yayi kana ya tuna lokacin da Amafarki ta sanya Lallausan tafin hannunta tana shafa Sajensa, ɗan juya hannunta ya buɗe Idanunsa da suka sauya launi tare da kallon hannunta yanda take shafa goshin Ramadan ɗin cikin nutsuwa yasa yaji wani abu mai masifar ƙarfi ya tsirga masa tun daga kan yatsan ƙafansa har zuwa ƙwaƙwalwar kansa lokaci ɗaya... ɗin sa ya harba da ƙarfin gaske cikin sauri ya cije lips ɗin sa tare da lumshe idanunsa yana kiran Sunan Allah Aransa.

M Jameel ya juya ya Kalli Moddibo da Idanunsa ke lumshe kana yace.
“Mu tafi ko?”.
Kai ya gyaɗa tare da yunƙurawa ya ɗauki Ramadan dake ta faman kuka Khausar ta kauce gefe tana sakin ajiyar zuciya.

Anutse Moddibo ya juya ya fita kana suma suka fice daga ɗakin zuwa harabar asibitin yana isa jikin motar ya samu har Lamiɗo yashiga gaba kana Mommy tashiga baya cikin sauri Hajiya Bunayya tace.
“Kawo shi nan in riƙe shi”.
Banza Moddibo yayi tamkar baiji me tace ba haka nan zuciyarsa ke raya masa Mommy ce mahaifiyarsu saboda kammani kana ga yanda Khausar ke kiran sunan Mommy akai-akai haka ma Ramadan yasa ya fahimci itace Mahaifiyarsu.
Buɗe bayan motar yayi tare da kallon Mommy da hankalinta ke tashe ahankali ya ɗago Ramadan tare da ɗaura mata shi akan cinyarta.

Cikin sanyayyar muryarsa mai cike da kamala nutsuwa da ladabi da kuma ƙwarjini yace.
“Mommy dan Allah kada ki tada hankalin ki. Insha Allah zai samu lafiya ki cigaba dayi masa addu'a”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Nagode Allah ya saka maka da alkhairi Ubangiji ya Albarkanci rayuwar ka nagode”.
Kansa a ƙasa ya amsa da.
“Ameen Allah ya sawwaƙa”.
Sannan ya rufe musu mota.
Driver yaja suka tafi kana Moddibo da M Jameel suka shiga motarsu suka tafi.
Sannan Malam Arɗo da Malam Isa suka shiga mota suka tafi.

Ahankali Moddibo ke Driving yayin daya tsirawa titin Idanu,M Jameel dake gefe ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Kai Allah ya gyara wannan al'amarin Ubangiji Allah ya ƙara tsarewa ya kare gaba!”.
Anutse M Jameel ya juya ya kalli Moddibo jin bai amsa addu'ar tasa ba cike da kulawa yace.
“Ya dai? A.J meyafaru ne kayi shiru? Ina ta magana ba reply?”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai zafi da kallon M Jameel kamar wanda aka fisgo maganar daga bakinsa yace.
“Wannan Accident ɗin shiryeyyene!”.
Zare ido M Jameel Yayi tare da cewa.
“Kamar ya shiryeyyene?”.
Ƙaramin tsaki Moddibo yaja kana yace.
“Akwai abinda ban gamsu dashi ba amma babu komai insha Allah zamuyi bin cike saboda na ɗauki number Motar Allah dai yabawa yaron nan Lafiya”.
Sauƙe numfashi yayi tare da fesar da iska daga bakinsa kana yace.
“Kaga yanda mahaifiyarsa tashiga tashin hankali amma matar nan da suka zo da ita hmmmm”.
Sai kuma yayi shiru tare da faɗin.
_“Astagfirullah Wa'atubu Ilaik ³_”.
A hankali ya numfasa tare da cewa.
_“Azzanna zambu walau kana haƙƙun,_
Allah kagafar ta min Allah kaya femin munana zato dana yi mata”.
Kallon M Jameel Yayi kana yace.
“J bangamsu da yanayinta ba”.
Jinjina kai M Jameel yayi tare da cewa.
“Sosai ma nima na lura da wani yanayi atare da ita amma dai Astagfirullah Allah mun tuba”.
Har suka shiga makarantar ba wanda ya sake magana Moddibo na Parking ya fita.

Acan gidan Lamiɗo kuwa bayan sun isa Lamiɗo ya riko Ramadan aka kafadarsa Already mai ɗaurin yazo kai tsaye sashen sa ya nufa dashi cikin sauri Mommy ta tsaya daga gefensa cikin raunin murya tace.
“Mai Martaba akaishi wurina kawai aje amasa acan”.
Kallon ta Lamiɗo yayi kana yace.
“Aysha aje amasa awaje na kawai ni yakamata inyi jinyarsa tunda yaro na miji ne”.
Girgiza kai tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Zaka bar uzurorin kane ai ƙaramine zan iya yi masa komai yanzu da Haiydar ne zaka iya cewa zai fi ƙarfin indinga ɗaga sa ko kuma yi masa wani abu”.
ta faɗa Idanunta na zubar da hawaye
Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“In dai har kina so in Samu ƙarfin gwiwa kidena zubar da hawaye kin san Banason ganin hawayen ki”.
Khausar kuwa tuni ta bar wajen.
Bayan sun shiga falon Mommy Malam Bala ya ɗaura ƙafar cikin tsanananin azaba Ramadan ke kuka saboda zafi da raɗaɗi daya ke ji miƙewa Mommy tayi tashiga Bedroom ɗin tana hawaye cike da tausayinsa Khausar ma miƙewa tayi ta shige Bedroom ɗin ta yana sheshsheƙa ba zata iya juran Kallonsa cikin ciwo ba Lamiɗo kuwa riƙe sa yana rarrashin sa bayan angama ɗaurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login