Showing 153001 words to 156000 words out of 176046 words

Chapter 52 - Sakayya 1 Hausa Novel Complete

kai Ummi tayi kana tace.
“Toh ya zamuyi idan an faɗa zai zama matsala zasu kashesa tunda sunce basu yarda afaɗa wa hukuma ba shiyasa dole muyi hakuri”.
Jinjina kai Khausar tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Toh shikenan Ummi Insha Allah zamu cigaba da yiwa Yah Jameel Addu'o'i Allah ya bayyana shi”.
Jingina kai Ummu tayi tare da cewa.
“Yawwa shine abinda ya dace Allah yabamu Sa'a”.

Wunin wannan ranan haka Khausar tayi ta rarrashin Asma'u da Ummi kana tana sake basu ƙwarin gwiwa kan cewa da izinin Ubangiji M Jameel zai dawo bayan Sallar sala'sar ta koma gida tana isa gida daga bakin.
Barandarsu ta jiyo sautin kukan Ramadan cikin sauri ta cire takalminta tare da shiga falon bakinta ɗauke da Sallama.
Cike da damuwa ta sauƙe Idanunta akan Ramadan daya kifa kansa kan cinyar Mommy cikin rauni da raɗaɗin ciwo yake jujjuya kansa akan cinyar Mommy kana yana cewa.
“Mommy Kaina ciwo!,Mommy Kaina zai fashe!”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe Cike da damuwa tace.
“Subhanallah Ramadan yau tun safe kake ta cemin kanka na ciwo to meke faruwa ne na baka magani kasha abanza ko dai in kira Abbanka ne akai ka asibiti?”.
Cikin tsanananin ciwo ya Girgiza mata kai yayi kana cikin Muryan kuka yace.
“Mommy ni dai Banason allura aƙara min magani kar kaina ya fashe”.
Khausar kuwa cikin sauri ta cire hijabinta kana ta ƙara sa kusa dashi tare da ɗaura tafin hannunta akan goshinsa lokaci ɗaya zafi ya ratsa tafin hannunta har ƙananan jijiyoyin kansa sun tashi suna harbawa cikin sauri ta kalli idanunsa gani tayi sun kaɗa suyi jawur dasu kana yanayin su ya koma kamar ajuye.

Saurin kallon Mommy dake jera masa sannu tayi kana tace.
“Subhanallah gaskiya Mommy akaishi Asibiti”.
Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Ramadan dake ta juyi kana ta kalli Khausar dake cikin damuwa ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Nima nace aikai shi asibiti amma yace baya Son allura da zaran nace akaisa saiya sa kuka”.
Girgiza kai Khausar tayi kana ta sake shafa goshinsa da yayi masifar zafi cike da damuwa tace.
“Mommy yaushe za'a biye masa jifa yanda kansa yayi zafi kamar wuta”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Bari akwai maganin da Abbanku yace zai sayo masa yanzu bari idan ya kawo za'a bashi idan Allah yasa ya samu sauƙi shikenan idan kuma abin be lafa ba dole sai mutafi asibitin”.
Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.
“Toh shikenan Allah ya bashi lafiya Allah kuma ya dawo da Abba lafiya”.
Mommy na shafa kan Ramadan tace.
“Ameen”.

Acan ɓangaren Abban Jameel kuwa ahankali ya miƙe tare da kallon wayarsa kana ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da nufar toilet domin ya watsa ruwa baki daya baya jin daɗin jikinsa bakinsa ɗauke da addu'a ya shiga toilet din kana ya fara wanka.
Hajiya Karima dake zaune afalon kasancewar itace da girki tayi saurin kallon wayar Abba dake ruri miƙewa tayi tare da isa kan 3sitter ganin number babu suna yasa tayi saurin picking tare da kaiwa kunnenta tace.
“Assalamu Alaikum”.
Ba tare da mutumin ya amsa Sallamar taba yace.
“Ina Mahaifin Jameelu?”.
Da sauri ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa.
“Me kuke so ku faɗa min nice mahaifiyarsa”.
Cike da gadara Mutumin yayi gyaran murya kana yace.
“Dashi muke son magana, muna son muji shin kuɗin mu sun haɗu ne?.
Zamu faɗa masa inda za'a ajiye kuɗin sannan kuma da inda za'a zo akarɓi Jameel”.
Hajiya Karima kuwa cikin ƙasa da murya tace.
“Haba bayin Allah kuji tsoron Allah mana.
Yanzu fisabilillah ina zamu samu Million ɗari da hamsin wannan aiba rayuwa bane duk da cewa Mahaifinsa mai kuɗi ne ina zai samu wannan uban kuɗin acikin ƙaramin lokaci kawai dai ku temaka ku rage idan ku akayi wa haka ya zakuji? Gwara dai ana rage mugunta”.
Dai-dai lokacin da Abba ya fito daga wankan batare daya gama ba jin alamar muryan Hajiya Karima na magana ƙasa².
Yana fitowa ya Fisge wayar ahannunta tare da mannawa akunnensa dai-dai lokacin da mutumin ke magana cikin tsanananin fushi da gadara yace.
“Ok haka ma kuka ce. Wato wasa da mu ku keyi kun maida mu bamusan abinda muke ba, toh Insha Allah daga yau har gaban Abadan baza mu sake kiran kuba. Alhj Bashir ya maka kyau duk irin halarcin da gargaɗin da muka maka baka jiba har kuna sake neman ragi”.

Cikin tsanananin kaɗuwa, ruɗu, da tashin hankali. Abba ya girgiza kai kana cikin raunin murya yace.
“Dan Allah da m...”.
Kafin ya ƙarasa yaji ɗit-ɗit-ɗit alamar sun kashe kiran.
Cikin wani irin yanayi ya zauna tare da sake kiran layin yaji akashe Aruɗe ya shiga fito da sauran numbers din su yana kira amma baki ɗaya Switch off.
Kansa ya dafe da hannunsa na dama yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da wayar.
Cikin wani irin fushi ya miƙe tare da kallon Hajiya Karima dake tsaye azabure ya ɗaga hannunsa tare da kife ta da mari kana ya sake watsa mata wani gigitaccen marin da saida taga gilmawar taurari cikin wani irin fushi ya cigaba da yarfa mata maruka gefen hagunta da damanta.
Muryarsa na rawa yace.
“Karima na saki acikin wannan maganar tunda aka fara. Meyesa zaki ɗauka min waya. Karima kin cuceni. Wallahi Karima duk wani abinda ya faru da Jameelu kece sanadi kece kika ja ke kika cutar min da rayuwar ɗana”.
Da sauri ya dafe ƙirjinsa dake wani irin zafi kana ya ɗago ya kalleta da idanunsa da suka sauya launi zuwa tsantsar tashin hankali kana yace.
“Karima haka nayi dake kina gani ɗazu akan idonki na dawo daga Taraba naje na karamo kuɗi na sake karɓan bashin banki 50 millons yanzu ruwan kuɗi ahannuna Million Ɗari da arba'in da biyar ne Million biyar ne kaɗai ya rage kuma nasan da izinin Ubangiji ba zasu gagara ba zan nemosu amman shine zaki nema min ragi”.
Hajiya Karima kuwa kuncinta ta dafe tare da sun kuyar da kanta ƙasa tana mai cike da taraddadi.

Cikin rauni da fusata Abba ya cigaba da cewa.
“Saboda bake kika haifi min Jameelu ba shine zaki salwantar da rayuwarsa, yanzu da ɗan da kika haifa a cikin kine zaki masa irin wannan abin? Karima kin cutar da rayuwata cuta mafi muni, muddin wani mummunan abu ya faru da Jameelu na bazan taɓa yafe miki ba”.
Cikin zubda hawaye Hajiya Karima tace.
“Haba Alhj wallahi ni ba haka nake nufi ba, kafahimceni tunda naga wancan karon ma da aka nemi ragin ai sun rage shiyasa nace barin ne mamaka sauƙi”.
Dai-dai lokacin Moddibo ya shigo falon idanunsa suka sauƙa akan Abba da jikinsa ke rawa idanunsa sunyi Jawur tamkar zai tsats-tsafo da hawayen jini yayin da numfashinsa ke seizing.

Cikin sauri Moddibo ya ƙara sa tare da riƙe Abba kana ya zaunar dashi akan kujera cikin sanyin murya yace.
“Abba mai ya faru?”.
Kasa cewa komai Abba yayi baki ɗaya baya cikin hayyacinsa numfashinsa sai kai koma yake cikin rauni da ficewar hayyaci yace.
“Karima kin cuceni Meyesa zaki min haka. Meyesa zaki ƙuntata min ta wannan hanyar!?”.
Cikin sauri Hajiya Turai ta shigo ganin halin da Abba ke ciki yasa kai tsaye ta wuce Bedroom ɗinsa tare da ɗauko masa magani kana ta kira Dr Muktar ya ɗagawa tace.
“Dan Allah Dr maza kazo jikin Alhj ya tashi gaba ɗaya ma numfashinsa sama yake yi”.
Da Ok Dr ya Amsa kana ta katse kiran tare da fitowa da magani ta ɓare tare da miƙa masa.
Cikin azabebben rawan da jikinsa keyi ya ture hannunta tare da cewa.
“Ba zan shaba Karima kin cuceni kin cutar da rayuwata, kin datse min farin cikina. Meyesa haka Karima duk abinda ya samu Jameelu Karima kece sanadi idan wani abu ya samu Jameelu Karima kece sanadi!”.

Ganin alamar baya cikin nutsuwarsa yasa Moddibo cewa.
“Dan Allah Abba ka kwantar da hankalin ka”.
Girgiza kai Abba keyi yana cewa.
“Karima kin cuceni kin cutar da rayuwata kin katse min farin cikina”.
Zama Moddibo yayi kana cikin sanyin murya ya shiga Furta.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin la haula Wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim”_.
Ahankali Abbah yafara bin bakinsa yana karato adduo'in tun yani yi Aransa har yafara afili.

Hajiya Turai kuwa number Dr Muktar ta sake Kira yana ɗagawa tace.
“Dr kayi sauri dan Allah ina katsaya har yanzu baka zoba kuma na faɗa maka jikin Alhj ya tashi gashi mun basa magani yaƙi sha”.
Cikin sauri Dr Muktar yace.
“Gani nan na fito dama yanzu zan wuce asibiti amma yanzu na kusa gidanku ma ina ƙara so wa”.
Cike da damuwa tace.
“Toh shikenan sai kazo dan Allah kayi sauri”.
Ta ida maganar tare da katse kiran kana ta juya ta fice.
Moddibo kuwa ciki sanyi ya riƙe hannun Abba tare da cewa.
“Abba dan Allah kayi haƙuri ka cigaba da Addu'a”.
Kai Abba ya gyaɗa kana ya cigaba da maimaita adduo'in but still ɓarin da jikinsa keyi bai dai naba saima ƙaruwa da yake.
Dai-dai lokacin da Dr Muktar yayi hong mai gadi ya buɗe masa kana cikin sauri ya fito daga motar hannunsa riƙe da fest aid box Hajiya Turai dake Safa da marwa a coumpund ɗin ta masa jagora zuwa ɗakin suna shiga Dr Muktar ya zauna kan 1sitter kana ya buɗe Aidbox ɗin sa tare da gwada Bp Abba.
Cikin sauri ya kalli Abba tare da cewa.
“Subhanallah jinin Alhj ya hau sosai na faɗa muku ku daina kawo duk wani abu da kuka san zai ɓata masa rai, ko kuma tayar masa da hankali”.
Ya faɗa tare da ciro sirinji kana yace.
“Alhj bari nayi maka allura baki ɗaya damuwa yayi masa yawa”.
Ajiye sirinji Dr Muktar yayi kana ya balli magunguna ya miƙa masa tare da cewa.
“Alhj gashi kasha”.
Girgiza kai Abba yayi cike da rauni yace.
“A'a bazan shaba”.
Asanyaye Dr Muktar yace.
“Ayyah Alhj dan Allah kasha mana”.
Girgiza kai Abba yayi tare da cewa.
“A'a bazan shaba menene amfanin rayuwata matuƙar dai bazan iya temakon Jameelu na ba.
Meye riban cigaba da rayuwata matukar Jameelu na baya tare dani?”.

Cikin sauri Moddibo ya Girgiza kai tare da cewa.
“Subhanallah Abba kada kace haka kada zafin damuwa yasa mu kaucewa lissafin hankali da na Musulunci Abba kayi addu'a dan Allah ka karɓi maganin kasha Abba. shin yakakeso nayi idan har kaima ka faɗi ciwo ya kwantar da kai”.
Cikin tausayawa ya kalli Abba idanunsa cike da ruwan hawaye kana yace.
“Abba na tabbatar ko da J na nan bazai yi farin ciki da haka ba Abba dan Allah kayi haƙuri kasha maganinka, ganinka cikin dauriya shike bani ƙarfin gwiwa Abba bazan so ganin wani mugun abu yasa Meka ba. Idan har wani abu ya sameka Abba ya zanyi da rayuwata!?”.
Ya ida Maganar tare da miƙawa Abba maganin karɓa Abba yayi tare da kaiwa bakinsa ya haɗiye miƙewa Dr Muktar yayi kana yace.
“Alhj bari a maka Allura”.
Kai Abba ya gyaɗa kana Dr Muktar ya masa bayan ya masa ya juya ya fice.
Sannu Ahankali Abba ya fara maida numfashi kana ya jingina bayansa da jikin kujera ahankali numfashinsa ya fara dai-dai-ta Atake zufa ya shiga tsats-tsafo masa agabaki ɗaya ilahirin jikinsa.
Moddibo kuwa ganin haka yasa ya miƙe ahankali tare da ɗaukan remote ɗin AC ya kunna kana ya dawo ya zauna agefensa.

Matsawa kusa da Abba Hajiya Turai tayi kana ta ɗauki hankief ta shiga goge masa zufa,
cikin sanyin murya tace.
“Sannu Alhj Ubangiji ya sawwaƙa maka, ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu Jameelu sai al'khairi”.
Kallonta yayi amma baice komai ba.
Moddibo ma ahankali ya dawo kusa dashi ya zauna kana cikin sanyin murya yace.
“Abba ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu J Abba yanzu fa abinda ya kawoni da mukayi waya kace ansamu kudin kwata kwata Abba yanzu fa Million biyar ne ya rage akan kuɗin da muke nema ai abu yazo ƙarshe insha Allah babu abinda zai samu J,
Kuma ma kafin inzo nayi waya da Ummi tace akwai wasu gwala-gwalai guda biyu gobe zata kaisu Taraba, da akan yau zata kaisuma to dare yayi, ta kuma cemin in sha Allah zasu iya kai two million.
Kajifa alamomin nasara Abba meye zai tayar maka da hankali!?”.

Ahankali Abba ya ɗago jajayen Idanunsa tare da kallon Moddibo kana ya kalli Hajiya Turai sai kuma ya maida kallonsa kan Hajiya Karima dake tsaye cikin rauni ya nuna ta da yatsa kana yace.
“Karima ce nashiga wanka suka kira.
Karima ta ɗauka wai tana musu maganan ragin kuɗin nace ta nema min ragi ne?
Tabarni mana Jameelu ba ɗana bane ai zan fashi ɗana amma Meyesa Karima zata min haka!?”.
Moddibo kuwa cikin wani azabebben tsinkewar zuciya ya riƙe kansa tare da cewa.
“Innalilahi wa'inna ilahi rajiu'n.
kika nemi ragin kuɗi kuma Aunty Karima amma gaskiya baki kyauta mana ba”.
Cikin tsananin tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar yaci gaba da cewa.
“Amma gaskiya baki kyauta manaba, ai wannan mugunta ne an saki ne ko kuma annemi wani temako awajenki fisabilillahi? wallahi kin cutar damu wannan shine cuta mafi muni da kika mana bayan kinji gargaɗin da sukayi”.
Ya ƙarashe mgnar cikin raunin murya yana jin zuciyarsa na wani irin zafi da karaya.

Cikin sauri Hajiya Turai ta kalli Hajiya Karima tare da Girgiza kai cike da takaicin halayyar ta tace.
“Idan har ba tayi haka ba ai bata cika Yadukko ba, ai dama baka sanin mai sonka da gaskiya sai kashiga wani hali, wasu kuma burinsu su samu hanyar da zasu musguna wa rayuwarka suke nema”.
Kallon Hajiya Turai Hajiya Karima tayi kana ta kalli Abba da Moddibo cikin Muryan kuka tace.
“Agaskiya ni anyi min bahaguwar fahimta nima Ina son Jameelu tamkar ɗa yake awajena fa, ke Hajiya Turai da kike wannan maganar nida ke waya fara zama da Jameelu ne?”.
Banza Hajiya Turai tayi da ita tana jin wani irin takaicin abinda ta aikata aranta.
Sannu Ahankali bacci ya fara fisgar Abba saboda magani da Alluran da aka masa nan take Bacci ya ɗauke sa kwanciya Moddibo ya gyara masa akan kujeran kana ya miƙe tare da ɗaukar key ɗin motarsa zuciyarsa cike da rauni damuwa da tashin hankali duk sun bayyana afuskarsa.
Yana fita yashiga motarsa tare da yimasa key yayin da hawaye suka cika kwarmin Idanunsa Driving yake yana sake try numbers din da suke kira kasancewar duk lokacin da suka kira saiya yi copy amma baki ɗaya Swich off.
Ahankali ya fito da Number M Jameel kana Yayi dearling cikin ikon Allah yaji wayar tashiga tana ringing lokaci ɗaya ya shiga cikin matsanancin farin ciki afili ya furta.
“Yau kuma wayar J tana shiga”.
Cikin sauri ya juya akalar motarsa zuwa gidan Ummi kana ya Parking awaje tare da buɗe gate ya shiga coumpund ɗin yana cewa.
“Ummi! Ummi!! Ummi!!!”.
Ummi dake tsaye Atsakiyar falo tayi saurin fitowa tare da cewa.
“Na'am Babana me yafaru?”.
Cike da walwala yace.
“Ummi wayar J ɗina yana shiga yau”.
Cike da farin ciki Ummi ta ware ido kana tace.
“Wayar Jameelu yana shiga?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa still da murmushi afuskarsa ya gyaɗa mata kai kana yace.
“Wallahi yana shiga Ummi bari ma kiji”.
Ya faɗa tare da dearling number M Jameel aikuwa ya shiga ya fara ɗut-ɗut-dut cikin Sauri ya samata akunne da sauri Asma'u da Bashir dake Bedroom suka fito jiyo sautin su Ummi cikin farin ciki.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Bari in Kira nima".
Ta ida maganar tare da dearling number kasancewar wayar na hannunta still ya shiga yana ringing.

Cikin sanyi ta juya ta kalli Moddibo tare da cewa.
“Babana to ya baya ɗauka kuma?”.
Cikin wani masifaffen tsinkewar zuciya da tsoro Moddibo ya kalleta cikin ƙoƙarin ɓoye tsoronsa yayi Murmushi tare da cewa.
“A'a Ummi Insha Allah tunda har wayarsa tana shiga zai ɗaga mu cigaba da kira da izinin Ubangiji zai ɗaga Agaskiya Ummi yau naji sanyi”.
Murmushi Ummi haram Asma'u, da Bashir.

“Har naji hankali na ya dan kwanta wayar J ɗina ya shiga, kinga farko kafin mu rasa shi kiran wayarsa muka fara rasawa Ummi, yanzu kuma Insha Allah mun samu kiran wayarsa shi zamu ƙara samu next da izinin Ubangiji”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Ameen”.
Cikin jin sanyi Asma'u tayi murmushi kana tace.
“Alhamdulillah wayar Yah Jameel ya shiga gaskiya munyi farin ciki”.
Malam Ahmad daya fito daga wanka ya fito coumpund ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.
“Alhamdulillah Asma'u maza kawo musu abinci suci tunda mun samu wayar Jameelu ya shiga maza kawo musu abinci”.
Moddibo kuwa kallon Malam Ahmad yayi kana yace.
“Nikam ma Malam baki ɗaya cikina ya cushe baki ɗaya farin ciki ya cika min cikana”.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“Nima cikina ya cika baki ɗaya farin ciki nake ji”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.
“Dan Allah ku zauna kuci abinci wayarsa muka fara rasawa yanzu kuma wayarsa muka faru samu insha Allah shi ma zamu sameshi nan kusa ”.
Dai-dai lokacin Asma'u tazo ta ajiye musu abincin.
Tun ɓatan M Jameel sai yau Ummi da Moddibo sukaci abinci mai nauyi acikinsu duk da ba dayawa suka ciba.
Miƙewa Moddibo yayi kana yace.
“Ummi bari naje in faɗawa Innayi ta tayamu farin ciki”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.
“Aikam dai gwara kaje”.
Ficewa yayi tare da tafiya Driving yake Cike da farin ciki har ya isa gida yana zuwa ya shiga sashen Innayi.
Innayi dake ki shimfiɗe ta miƙe kana tace.
“Alhamdulillah Moddibo naga kana cikin farin ciki da alama akwai labari mai daɗi?”.
Kai ya gyaɗa still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Innayi wayar J ɗina ya shiga yau”.
Kai Innayi ta gyaɗa tare da cewa.
“Alhamdulillah gaskiya munyi farin ciki. Allah ya bayyanar mana dashi”.
Ameen ya amsa tare da wucewa sashen sa cike da farin ciki yana shiga ɗaki ya kira layin Malam Arɗo.
Malam Arɗo na dagawa yace.
“Malam Alhamdulillah yau wayar J ɗina yashiga a cigaba da taya mu da addu'a a masallacai da makarantu”.
Cike da farin ciki malam Arɗo yace.
“Masha Allah da izinin Ubangiji zai fito Insha Allah zamu cigaba da addu'a”.

Awannan daren haka Moddibo Ummi, Asma'u Bashir malam Ahmad da Innayi suka kwana cike da farin cikin shigar wayar M Jameel.

Yayin da Aɓangaren Abba ya kwana cikin taraddadi da tashin hankali koda ya farka tsakiyar dare kuka yayi ta yi yayin da Hajiya Karima ke kuka tana basa haƙuri kana tana cewa bada niyya tayi ba.

Aɓangaren gidan Lamiɗo ma haka Khausar da Mommy suka kwana azaune da Ramadan da kansa ke masifar ciwo da zaran an bashi maganin da Lamiɗo ya kawo yasha ciwon zai ɗan lafa jimawa kaɗan kuma zai sake tashi tsakiyar dare ya farka ya riƙa kuka dole Ummi ta kira Abba ya kawo masa magani cikin ikon Allah yana sha ciwon kan ya lafa.

Washe gari; Moddibo, Malam Arɗo, Ummi Innayi duk wani makusancin M Jameel na cikin farin ciki kana duk wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login