Showing 114001 words to 117000 words out of 176046 words
da gyara rikon Handbag din ta kana tace.
“Insha Allah zata ji Mommy”.
Dai-dai nan suka jiyo Sallamar Naseer afalo, cikin sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ɓata fuska lokaci ɗaya ta nemi fara'ar dake fuskanta ta rasa.
Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.
“Ya dai haka daga jin muryan sa kin wani tsuke fuska sai kace wanda yazo miki da wani mugun abu”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Babu komai Mommy”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da fita tana cewa.
“A'a wa nakeji kamar Naseer mutan India”.
Yana zaune kan kujera ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh Mommy nine”.
Dai-dai lokacin da Khausar ta fito miƙewa yayi idanunsa akanta yace.
“Wooow Masha Allah”.
Sam ya mance da Mommy dake tsaye a wurin.
Gaba ɗaya imaninsa ya tafi gareta cike da zalama ya nufi Khausar tamkar zai rungumeta yana faɗin.
“Wowww my dear Wife you look so georoures, Fantastic, beautiful you look so Pretty”.
Khausar kuwa ganin yanda yake matsota zai Rungumeta yasa taja baya da sauri tare da cewa.
“Nagode.
Mommy kuwa kallon ikon Allah take ganin yanda baki ɗaya hankalinsa ya tafi kan Khausar da alama ya mance da tana wajen.
Gyaran murya tayi tare da cewa.
“A'a Naseer ka zauna mana akawo maka abin taɓawa mana”.
Girgiza kai yayi da faɗin.
“A'a Mommy Nagode”.
Itako Khausar ɓata fuska tayi babu walwala atare da ita tace.
“Mommy na tafi".
Cikin sauri ya mike tare da bin bayanta kana yace.
“My dear Wife Ina Zakije?”.
Ataƙaice tace.
“Unguwa”,
Cikin yanayin zumuɗinsa yace.
“Bari in sauƙe ki”.
Mommy kuwa ita kanta rawan kansa ya bata tsoro ganin yanda yake nuna zalamarsa afili kamar kura yaga ɗanyen Nama!”.
Da sauri Mommy ta kallesa tare da cewa.
“A'a Naseer ka bari basai ka kaita ba ai zata shiga Napep”.
Zare ido yayi tare da cewa.
“A'a Mommy na isa kamar ni ace Matata tashiga Napep no, impossible kamar Matar Naseer Ibrahim ɗancanji amma ace Matata na hawa Napep Ina bai yiba bai yiba”.
Ita kuwa Mommy aranta tace Ohhh wannan yaro dai Allah yamasa kurari bawai basu da arziƙinba mahaifinsa nadashi amman kurarinsa yafi kuɗin nasu yawa bashi da aiki sai cika baki.
Khausar kuwa tuni ta fice cike da takaicin zumuɗinsa.
Da sauri yabi bayanta yana cewa.
“My dear Wife ki tsaya mana let me drop you”.
Banza Khausar tayi masa tayi ficewar ta.
Kashe murya yayi tare da cewa.
“Dan Allah ki tsaya mai yasa kike yin haka?”.
Ba tare data juya ba kana cikin ɗaure fuska tace.
“A'a Uncle Naseer ka bari kawai zanje da kaina gidansu Asma'u nefa Napep ma zan shiga”.
Murmushi yayi kana yace.
“Yawwa muje kinga nima sai ingaishe da Umminta kinga dama na daɗe banga Asma'u ba yau ya kamata mu gaisa”.
Khausar kam sake ɗaure fuska tayi tare da cewa.
“Yaya Naseer Allah da kabari kada in saka wahala nasan baza ka rasa abinyi ba”.
Langwaɓar da kai yayi tare da marairaice fuska kana ya karyar da murya tare da cewa.
“Please My dear Wife allow me to escort you kinsan dai Ina ƙaunarki sannan ina son kasancewa da ke banaso kidinga nesanta kanki daga gareni”.
Siririn tsaki taja aranta kana tayi gaba abinta domin har ga Allah zalamarsa na bata tsoro.
Shi kuwa da sauri ya nufi Parking space tare da ɗaukar motarsa yazo ta gefenta tare da buɗe mata kana ya karyar da murya tare da cewa.
“Please Wife to be kishigo mana”.
Dai dai lokacin da gate man ya buɗewa Lamiɗo da Gimbiya Dadu suka shigo bisa duk kan alamu daga asibiti suke anje duba lafiyar Idonta dan bayan ta fito hannunta na riƙe da ledan magunguna da kuma tambarin asibiti.
Gimbiya Dadu kuwa tun da ta sauƙa daga mota Idanunta nakan Khausar ta wani kafeta da Ido tare da sake laɓenta na ƙasa.
Khausar kuwa cikin rawan jiki da tsinkewar zuciya tayi saurin koma wa bayan Naseer zuciyarta na bugawa da mugun ƙarfi cike da tsoro take karanta duk wata addu'a da tazo bakinta.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“A'a Nasiru ya dai ina zakuje kaida Mutuniyar taka?”.
Cikin yanayin zumuɗinsa da rawan kai ya shafa ƙeyarsa tare da cewa.
“Abbah zan kaita gidansu Asma'u ne dan banaso ta hau Napep”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Yayi kyau Allah ya kiyaye hanya, Khausar sai kun dawo”.
Kasa cewa komai Khausar tayi still tana tsaye bayan Naseer zuciyarta na cigaba da tsinkewa ganin har zuwa lokacin Gimbiya Dadu na Binta da ido burinta su haɗa Ido.
Gyaran Murya Lamiɗo yayi kana yace.
“Khausar shiga mota ku tafi”.
Cikin sauri tace.
“Toh Abba”.
Kana ta fito daga bayan Naseer tashiga gaban motar.
Kallon Gimbiya Dadu Naseer yayi kana yace.
“Yafendo sai mun dawo”.
Ya ida maganar tare da buɗe mazaunin Driver ya shiga kana yaja motar suka fice ahankali ya dai-dai ta hancin motarsa suka hau kwalta.
Sai asannan ya juya ya kalli Khausar da fuskarta babu annuri kona misƙala zarratin zaman blutooth dake kunnensa ya gyara ajiyar zuciya ya saki yana bin ilahirin jikinta da kallo hannunsa ya kai tare da ranƙwafawa kanta zai riƙe yalwataccen sumar dake gefen wuyanta zai shinshina.
Cikin sauri Khausar ta kauce tare da watsa masa wani kallo.
Tsuke fuska yayi tare da marairaice murya kana yace.
“Haba My Wife mai yasa zaki min haka kibari mana in sinsina gashinki naji wannan Sanyayyar ƙamshin da yake fita”.
Sake tsuke fuska Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta kana tace.
“A'a nidai Yaya Naseer ka bari bana so”.
Langwaɓar da kai yayi kana cikin wata murya mai ɗauke da zallan shauƙi da sha'awa yace.
“Toh na bari ai yanda kike so haka za ayi hope dai kina sona?”.
Ƙasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta amma ba tace komai”.
Sake narkar da muryarsa mai ɗauke da zallan sha'awa kana yace.
“Dan Allah kice kina ƙaunata ko zanji daɗi kinsan na daɗe ina dakon soyayyarki azuciyata, Khausar kece rayuwata bazan iya rayuwa idan babu keba kece muradin raina, kece fitilar dake haskaka rayuwata ina miki sahihiyar ƙauna wanda bana yiwa kaina”.
Lumshe idanunsa yayi tare da kallon fuskarta zuwa ƙirjinta kana yace.
“Kece wacce zuciyata keda burin kasancewa da ita, kece farin cikina muddin ban mallakeki amatsayin matata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba, My Khausi saboda ke nadawo Nigeria ba dan keba wlh bazan dawo ba.
Duk yawan kyakkyawawan matan dake India babu wacce ta burgeni ta kuma kwanta min arai sai ke duk kyawunsu kallon maza nake musu!”.
Ita dai Khausar batace komai ba sai wasa da take da yatsun hannunta.
Naseer kuwa karyar da murya yayi tare da lashe lips ɗin sa kana yana binta da wani shu'umin kallo ya lumshe Idanunsa tare da cewa.
“Khausar inada burin mallakar ki ke kaɗai ce zaki iya sarrafani, akan shimfiɗata sannan ke kaɗai ce zaki iya bani farin ciki akan shimfiɗa ta”.
Lokaci ɗaya Khausar ta sake haɗe fuska cike da takaici tarasa Meyesa Naseer yake mata wasu irin maganganu marasa kan gado.
Al'amarin Naseer yafi kama da irin mayaudaran mazan nan na zamani.
Shirune ya ratsa motar har suka isa ƙofar gidansu Ummi yayi Parking daga waje, Ahankali Khausar ta ziro ƙafanta da suka sha jan lalle.
Dai-dai lokacin Asma'u ta iso.
Ganin Khausar yasa ta faɗaɗa fara'ar fuskarta kana tace.
“A'a Khausisi, Lelewal tawa”.
Murmushi Khausar ta sakar mata tare da gyara zaman gyalenta kana tace.
“A'a ina kika je?”.
Asma'u na gyara wuyan hijabinta ta kalli Khausar tare da cewa.
“Wallahi kitso naje”.
Jinjina kai Khausar tayi kana tace.
“A lallai dai kam”.
Juyawa tayi ɓangaren da Naseer ke tsaye ya zuba mata ido ɗauke kanta daga garesa tayi kana ta mayar da kanta kan Asma'u tare da cewa.
“Asmeey ga Uncle Naseer”.
Sai alokacin Asma'u ta ganesa da murmushi afuskarta tace.
“Laa Uncle Naseer Mutanen India fatan kazo lafiya. Khausar tace min kadawo toh Allah yatemaka”.
Kai ya jinjina cike da Iyayi kana yace.
“Wallahi na dawo amma fa saboda My Khausi nazo, ana ɗaura mana aure kuma zan ɗauki abata mukoma can”.
Murmushi Asma'u tayi tare da kallon Khausar da ta tsuke fuska kana tace.
“Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi”.
Da sauri ya amsa da.
“Ameen”.
Khausar kuwa hannun Asma'u ta riƙe zasu shiga gida.
Da sauri yace.
“Ya dai haka My Khausar ba zaki tsaya mu ɗanyi hira ba?”.
Ataƙaice ta girgiza masa kai tare da cewa.
“A'a”.
Shafa kansa yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Toh ƙarfe nawa zaki koma gida sai inzo in ɗauke ki”.
Babu walwala atare da ita tace.
“A'a ba sai kazo ba Uncle Naseer zan koma”.
Wani irin zare ido yayi tare da girgiza kai kana yace.
“A'a My Khausi kar ki min haka.
Ni dai ki faɗa min ƙarfe nawa zanzo ɗaukarki”.
Ƙaramin tsaki taja aranta tare da cewa wannan mutumin ya fiye naci afili kuma juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.
“Toh ka dawo ƙarfe shida na Yamma”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan My Wife sai nazo”.
Ya ida maganar tare da shigewa motarsa yaja.
Bayan sun shiga cikin gida Khausar ta juya tare da kallon Asma'u kana tace.
“Ya dai naga kamar Ummi bata nan?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh Ummi ta tafi gidan Innayi. Ni kaɗai ce sai Bashir dana bari yana mana gadin gidan shiyasa ma ana gama min kitson na dawo.
Jinjina kai Khausar tayi kana tace.
“Ayyah yayi kyau”.
Kai tsaye Bedroom din Asmau suka shiga fridge Asma'u ta buɗe ta kawo mata drinks da Fruit.
Kallon Friut ɗin Khausar tayi tare da zabga ta gumi.
Zama Asma'u tayi daga gefenta cike da kulawa tace.
“Ya dai Khausar tunanin me kike?”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare cire gyalenta ta ajiye kana ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Ni wallahi lamarin Uncle Naseer ya fara damuna”.
Asma'u na ninke hijabin data cire ta kalli Khausar tare da faɗin.
“Mai yafaru?”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tashiga zayyanewa Asma'u abubuwan daya yima tun daga zuwansa har yanzu daya kawota kana ta ɗaura da cewa.
“Asma'u Uncle Naseer yana bani tsoro abubuwan da yake gwada min sun fi kama dana mayaudara idan yana wani abun tamkar yana da wani nufi akaina, sannan yana yawan nuna zalamarsa akaina, ya rinƙa wani abu kamar maye!”.
Dariya Asma'u tayi tare da cewa.
“Wataƙil tsanananin son da yake miki ne kike ganin kamar haka, kinga tun kina ƙarama kamar da wasa ya fara ce Miki matarsa har gashi girma yazo wataƙil tsananin soyayya ne sannan kinga ya zauna a ƙasar da al'adun mu ba ɗaya dana suba kinga ƙasashen India wannan sai ahankali runguma da sumbata basu ɗauke shi abakin komai ba may be shiyasa kike ganin yake miki haka kuma kinga ai ya riƙa dole zaiso mace”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi kana tace.
“Anya kuwa Asma'u abin nasa is too hight ɗazun fa agaban Mommy saura kaɗan ya rungumeni saida na kauce”.
Dafe kunci Asma'u tayi tare da kallon Khausar da fuskarta ke ɗauke da alamun damuwa kana tace.
“Toh tunda har haka ne ki kiyaye al'amarin sa”.
Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tace.
“Zan kiyaye insha Allah amma gaskiya ya fara bani tsoro baki ɗaya al'amarin sa azalamance yake”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Amma duk da haka yana sonki”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana ta buɗe Idanunta dake lumshe tace.
“Na sani Uncle Naseer na ƙaunata, amma kuma wani lokaci soyayyar tafi kama da Sha'awa”.
Girgiza kai Asma'u tayi tare da cewa.
“No Khausar kada ki fassara shi da haka, sannan kinga yanzu lokaci yayi da zaki bawa Uncle Naseer dama kinga dama ga Maganar da Hajja Nana tazo da ita cewa kina gama Secondary school za ayi batun Aurenki kinga yanzu munzo gangara koma ince mungama kawai”.
Shiru Khausar tayi tare da lumshe Idanunta tana jin wani iri azuciyar ta.
Asma'u ta cigaba da cewa.
“Sannan kin gani tayi miki maganar Yayanki Aliyu idan har baki amince da Naseer ba kika fitar dashi amatsayin wanda kike soba dole Yaya Aliyu za'a liƙa miki, kuma kinga Yaya Naseer tunda ansan Asalin sa sannan ansan komai nasa, kuma ke kanki kinsan yana masifar sonki”.
Ƙaramin tsaki Khausar taja tare da kallon Asma'u kana tace.
“Kayya Asma'u Asalin nasa har wani kyau gareshi!?
Mahaifiyarsa fa ƙanwar Gimbiya Dadu ce Uwar su ɗaya ubansa ɗaya, kuma duk ɗabi'u da hallayar Gimbiya Dadu babu wanda mahaifiyarsa ta bari, sannan kuma shine ɗan Auta wajenta Ni Wallahi tsoron su na nake ji wallahi nama fi tsoron mahaifiyarsan”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta cigaba da cewa.
“Amma shi Uncle Naseer bashi da matsala Saboda zuciya nason mai kyautata mata, shi kuma tun ina ƙara ma yake nunawa kowa cewa. Ni ta da bance ni ta musamman ce awajensa, na ɗaukesa ne tamkar wani sashina amma banjin Uncle Naseer awani mataki na daban sannan batun Yaya Aliyu kuwa gaskiya saidai Hajja Nana tayi duk abinda zatayi, amma ni bazan Aure shiba babu ta yanda zanyi na aureshi”.
A hankali ta furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta kalli Asma'u da itama ita take kallo.
Idanunta ta lumshe cikin sanyi murya tace.
“Ni inaji azuciya ta ina da muradin da nake da ita na, musamman da nake buƙata inada muradin da nake so Asma'u ina da wani abun da nake so, wanda ni kaina bansan menene ba.
Amma Uncle Naseer ba irin Nature da nakeso ajikin namiji yake dashi ba dama yanada ilimi Addini kamar Yah Jameel ne to da ya tsarkaka, dama ace ɗabu'unsa irin na Yah Jameel ne da ya cikemib ko wanne gurbi”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe kana tace.
“Allah ko?”.
Tayi mgnar a fili yayinda zuciyarta ke saƙa wasu zantukan, ita kuwa Khausar kai kawai ta gyaɗa mata.
Cikin sauƙe numfashin Asma'u tace.
“Allah ya mana zaɓi mafi alkhairi dai”.
Cikin lumshe ida Khausar tace.
“Amin”.
Hira suka cigaba dayi, ƙarfe biyar dai-dai Khausar ta miƙe tare da ɗaukan gyalenta ta yafa kana ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Asma'u Ni zan tafi”.
Saurin Kallonta Asma'u tayi tare da cewa.
“Toh ba kince sai ƙarfe shida zaki tafi ba?,Kuma ina Uncle Naseer zai zo ya ɗauke ki!?”.
Baki Khausar ta taɓe kana tace.
“Guduwa zanyi kafin yazo ɗin dai, ai shiyasa nace masa shida kinga yanzu biyar zan tafi”.
Murmushi Asma'u tayi tare da cewa.
“Toh idan yazo fa?”.
Ka faɗa Khausar ta ɗage tare da taɓe baki kana tace.
“Sai kice masa na tafi”.
Ta ida maganar tana ficewa da sauri.
Asma'u tabi bayanta dan yi mata rakiya.
Misalin ƙarfe shida saura kwata Naseer yayi Parking aƙofar gidansu Asma'u tare da danna Hong.
Asma'u dake sauraran zuwansa ta sanya hijabi ta fita zaune ta samesa acikin mota kana tace.
“Bata daɗe da tafiya da taga iska ya taso”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Nagode”.
Kana ya figi motarsa yabar layin kai tsaye gidansu Khausar ya nufa lokacin daya isa ankira maghariba direct masallaci ya wuce ya gabatar da sallah kana ya wuce gidan kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya shiga.
Shigarsa ba daɗewa Haiydar ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama kana ya gaishesu tare da ajiye kulan abincin Gimbiya Dadu.
Har ya juya zai fita.
Naseer ya kallesa tare da cewa.
“Please Haiydar kace da Khausi tazo zamuyi hira”.
Kai Haiydar ya gyaɗa kana yace.
“Toh Uncle Naseer sannan ya fita”.
Kai tsaye masallaci ya wuce sai Misalin takwas saura kwata ya koma sashen su bakinsa ɗauke da Sallama.
Khausar dake zaune kan 1sitter sanye cikin Neavy blue riga da wando na bacci mai santsi wanda ya sauƙa har ƙasa rigar kuma mai hannun Spaghetti ne kanta sanye da hular Net jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen ta yayin da hannunta ke riƙe da wayar Mommy tana latsawa.
Da sauri Haiydar ya kalleta tare da cewa.
“Addah Khausar na manta ban faɗa miki ba, ɗazu kafin na wuce Masallaci Uncle Naseer yace. In faɗa miki kije ki same shi a sashen Gimbiya Dadu yana son ganinki”.
Nanda nan Khausar ta canza fuska tare da cewa.
“A falon Gimbiya Dadu kuma!?”.
Harara Mommy ta watsa mata kana tace.
“Toh cin yeki Gimbiya Dadu za tayi ko kuma me Ni nalura wani shan ƙamshi kike yiwa Naseer fa, idan kinsan bakya sonshi ki fito fili ki faɗa, sannan ki fito da wanda kike so, tun kafin kakar ki tazo ta buwayemu da batun Aurenki.
Kinga dama ta ajiye target ne kina gama Secondary school magana ya ƙare za azo ayi miki aure”.
Ajiyar zuciya ta sauƙa kana ta cigaba da cewa.
“Idan kuma kinƙi baki da hujjar da zaki ƙi Auren Aliyu, dole kibi zaɓin ta dan haka ma gwara ki tsaida zuciyarki kisan me kike ciki don in duniya duk zasu taru babu mahluƙin da zai hana batun wai kin gama secondary School za'ayi miki aure, tunda har Hajja Nana ta rantse, dan haka gwara kawai ma ki tsaida zuciyarki, ki fidda mijin da zai iya barinki kici gaba koda kinyi aure, kuma da fidda wanda kike sone, zamu samu hujjar nuna mata kinada wanda kike son”.
A hankali Khausar ta janye idonta daga kallon Mommy kana tace.
“To amma ni gaskiya ba zanje.
Falon Gimbiya Dadu ba”.
Ɓata fuska Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.
“Maza ki wuce kije idan ita kura ce to ta cinye ki”.
Miƙewa Khausar tayi badan ranta yaso ba sai dan ganin yanda Mommy ta ɓata rai yasa ta ɗauki hijabinta dake fitar da ƙamshi sanya kana ta fice.
Acan ɓangaren su Moddibo kuwa zaune suke aɗakin Innayi shi da M Jameel bayan sun kammala cin abinci Anutse ya miƙe tare da kallon Innayi da suke magana da M Jameel ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Innayi saida safe”.
Kallon sa M Jameel da mamaki afuskarsa yace.
“Zaka je ka kwanta fa kace?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Eh”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ok nima zan tafi gida”.
Ahankali Moddibo ya buɗe Idanunsa dake lunshe kana yace.
“Mu kwana anan mana tunda har ƙarfe takwas tayi”.
Girgiza kai M Jameel yayi tare da miƙewa kana yace.
“A'a ina so Inje gida”.
Kallon yanayin fuskarsa Moddibo yayi tare da cewa.
“Dan Allah mu kwana mana”.
Ataƙaice M Jameel yace.
“A'a tafiya zanyi”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke tare da cewa.
“Toh shikenan ni zanje in kwanta”.
Ya Ida maganar tare da ficewa.
Da kallo Innayi da M Jameel suka bisa har ya ɓacewa Kallonsu.
Moddibo kuwa yana shiga falonsa yayi saurin yarfe hannunsa tare da jan tsaki tare da jan numfashi kamar wanda yaci yaji lokaci ɗaya lips ɗin sa suka kama rawa cikin yanayin damuwa ya dafe kansa tare da cewa.
“Ya salam³,Wannan wani irin al'amari ne meke mai wuyar ɗauka haka?”.
Cikin mutuwar jiki ya wuce kichen tare da ɗaukan Cup ya ɗauraye ya zuba ruwan Tea kana ya yanka lemun tsami ya matse sannan ya zuba zuma ya kafa kansa ya shanye tass, ajiye Cup ɗin yayi ya fita zuwa Bedroom ɗin sa yana shiga ya kwanta ko minti ɗaya baiyi da kwanciya ba yayi saurin miƙewa ya zauna cikin sauri ya sake komawa ya kwanta tare dayin ruf da ciki cikin wani irin yanayi yasanya hannunsa duka biyu ya danne mararsa saboda wani masifaffen