Showing 165001 words to 168000 words out of 176046 words
da haƙuri ya mike ya fita.
Bayan angama shirya Ramadan an masa wanka an suturtasa yanda addinin Musulunci ya tsara aka kaisa gidansa na gaskiya.
Bayan andawo Lamiɗo da ƴan Uwansa da kuma Abokan arziƙi aka zauna zaman Makoki.
Wunin wannan ranan haka Mommy da Khausar suka yini cikin alhini da jimamin rashin Ramadan Hajiya Bunayya kuwa sosai tayi farin ciki sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci mutuwar ta shigeta domin ayanda take nunawa tafi Mommy damuwa wani abin ma Mommy ke tausarta tana bata haƙuri.
Washe gari Khausar ce zaune a ƙasa Mommy na Kan kujera gabansu Kuma kayan Breakfast ne.
Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Khausar tare da cewa.
“Khausar ki matso kici abinci”.
Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Mommy da kumburarrun Idanunta kana cikin sanyin murya tace.
“Mommy ba najin yunwa”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.
“Khausar ki matso kici abinci bana son haka zamuyi fushi da abinda Ubangiji ya jarabcemu da shine Allah daya halicci Ramadan yafimu son sa shi ya bamu Ramadan kuma shi ya ɗauke mana shi!”.
Wasu hawaye masu masifar zafi ne suka zubowa Khausar akuncinta cikin matsanancin kuka tace.
“Mommy shikenan!, Shikenan Ramadan ya tafi baza mu sake Kallonsa ba shikenan mun ransa shi har abada. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kallonta Mommy tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye Akuma dai-dai lokacin wayarta ya ɗauki ruri.
Kallon screen ɗin wayar tayi nan taga sunan Hajja Nana na yawo.
Cike da ladabi tayi Picking tare da kaiwa kunnenta tace.
“Hajja ina yini?”.
Daga ɗaya ɓangaren Hajja Nana tace.
“Lafiya lau ina Khausar!?”.
Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Khausar da hawaye ke zuba a Idanunta kana tace.
“Gata nan”,
“Toh ki bata wayar”, cewar Hajja Nana ta.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da miƙawa Khausar wayar.
Amsa Khausar tayi cikin Muryan kuka tayi sallama.
Cike da kulawa Hajja Nana tace.
“Ke kuma lafiya ya naji muryanki haka kukan me kike!?”.
Cikin sheshsheƙan kuka Khausar tace.
“Hajja Nana Ramadan ɗin mune ya rasu”.
Hajja Nana kuwa cikin sauri tace.
“Innalillahi Wa'inna Ilahi rajiu'n Ayyah Allah sarki Ubangiji Allah ya jiƙansa da rahma Allah yasa maicetone ai bamu da labari bamu sani ba bawa Mommy naki”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa Mommy wayar.
Jin Mommy ta amshi wayar yasa Hajja Nana cewa.
“Wai ashe Ramadan ya rasu!?”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Eh Wlh”.
Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauke tare da cewa.
“Ikon Allah Meye sameshi haka?”.
Numfashi Mommy ta fesar tare da gyara zaman ta kana tace.
“Wallahi ciwon kai ne mako ɗaya”.
Cikin sanyin murya da tausayawa Hajja Nana tace.
“Allah sarki Allah ya gafarta masa Ubangiji yasa maicetone! Dama yanzu Malam Liman zai shigo Gembulan Insha Allah zan biyo shi muzo”.
Jinjina kai Mommy tayi cikin sanyin murya tace.
“Toh Allah ya kawo ku Lafiya mungode sosai”.
Bayan Mommy ta kashe wayar ta kalli Khausar data zubawa kayan Breakfast Ido Cike da tausayawa ta shiga lallashinta.
Acan gidan Ummi kuwa Moddibo ne zaune afalon ya tsurawa waje ɗaya Idanu yayin da Ummi kanta ke ƙasa hawaye zira-zira baki ɗayan sun zurfafa acikin tunanin da suke Asma'u ta fito daga kitchen cikin mutuwar jiki ta tsugunna kusa da Ummi kana cikin sanyin murya tace.
“Ummi”.
Ahankali Ummi ta ɗago Idanunta dake zubar da hawaye kana cikin sanyin murya tace.
“Na'am”.
Lumshe idanu Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ummi yanzun nan mukayi waya da Khausar tace in gaisheki”.
Kai Ummi ta gyaɗa cikin sanyin murya tace.
“Ina Amsawa”.
Asma'u kuwa cikin raunin murya tace.
“Ummi wai Ramadan ya rasu fa”.
Cikin sauri Ummi ta ɗago kanta dake ƙasa ta kalli Asma'u shima Moddibo cikin sauri ya kalli Asma'u zuciyarsa na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe cikin raunin murya tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yaushe ya rasu!?”.
Gyara zama Asma'u tayi cikin sanyin murya tace.
“Shekaran jiya fa take cemin randa tazo bayan ta koma ciwon kan ya fara mishi, sunyi ta sintirin asibiti a banza, tace shekaran jiya kuma haka aka kwana dashi haka jiya da Asbah ma ya tashi dashi washe gari da safe bayan sallar Asbah ya rasu sai bayan Azahar akayi jana'izar sa!”.
Girgiza kai Ummi tayi tare da fesar da numfashi kana tace.
“Allah sarki rayuwa Ayyah Aysha ta ɗanɗani Mutuwa mai zafi da raɗaɗi mutuwar ɗa akwai ciwo Allah ya masa rahma Allah yasa maicetone”.
Cikin sanyin murya Asma'u tace.
“Ameen Ummi”.
Jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.
“Insha Allahu zanyi ƙoƙari muje”.
Moddibo kuwa ahankali ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya kalli Ummi tare da cewa.
“Allah yajiƙan sa da rahma, shine yaron da Mota ya buge ko?”.
Kai Asma'u ta gyada tere da cewa.
“Eh shine”.
Cije lip ɗinsa na ƙasa yayi tare da cewa.
“Allah sarki kwanansa na gaba alokacin Allah ya gafarta masa”.
Cikin sanyi murya Ummi tace.
“Ameen”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.
“Ummi bari in tashi Inje wajen Abba naji ya ake ciki muji daga Jiya zuwa yau ko sun kira”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan”.
Cikin sanyin jiki ya miƙe tare da ficewa kai tsaye gidan Abba ya nufa.
Bayan ya isa gidan ya shiga falon Abba nan ya samu Dr Muktar zaune zama gefen Abba yayi bayan sun gaisa Moddibo ya sauƙe numfashi kana cikin sanyin murya yace.
“Abba har yanzu basu kira ba”.
Kai Abba ya gyaɗa masa tare da rintse Idanunsa kana yace.
“Basu kira ba Aliyu bansan me mutanen nan suke nufi da muba”.
Tagumi Moddibo da Abba sukayi duk sunyi jugum-jugum dasu.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana Hajja Nana da Malam Liman suka iso gidan Lamiɗo bayan sun gama gaishe-gaishe suka zauna har aka Idar da La'asar Lamiɗo ya shigo tare da kallon Hajja Nana kana yace.
“Hajia ki fito malam Liman yana jiranki”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh gani nan fitowa”.
Kallonta ta mayar kan Mommy dake jan Carbi kana tace.
“Yanzu kam ba abinda zance miki, ta'aziyya muka zo miki amma Insha Allah kwanan nan zan dawo kan batun Khausar”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.
“Toh shikenan Nagode Hajja Nana Allah ya saka da alkhairi”.
Miƙewa Khausar tayi tare da bin bayan Hajja Nana jikinta sanye da dogon hijabi har ƙasa yayin da hannunta ke riƙe da wayarta Idanunta sunyi luhu-luhu dasu suna fita coumpund ɗin taga Malam Liman acikin mota amazaunin Driver.
Wara kumburarrun Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Iyeee lallema tsohon nan ashe ka iya mota?”.
Murmushi malam Liman yayi tare da gyada mata kai kana yace.
“Eyyy sosai ma kuwa dama lokacin da kikaje ai mota ta talalace ne shiyasa ankaita wajen gyara to wata aka sake siya min”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ashe kunji daɗi ƙauyenku akwai mota”.
Jinjina kai yayi da murmushi afuskarsa yace.
“Hadda ke ai acikin ƙauyen ya zaki cire kanki?”.
murmushi tayi cikin yanayin sanyin tace.
“ai Lallai dai kam to Allah ya tsare muku hanya”.
Ta faɗa tare da komawa cikin falon Ummi.
Kallon Hajja Nana Malam Liman yayi bayan ya dai-dai-ta motar akan kwalta yace.
“Addah Nana za muje gidan Malam Arɗo wannan ɗaliban nawa”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh ba matsala muje mana”.
Jinina kai Malam Liman.
bayan sun isa gidan malam Arɗo yayi Parking tare da isa falon baƙinsa wanda ke harabar gidan bakinsu ɗauke da Sallama.
Daga ciki malam Arɗo wanda ke zaune tare da Moddibo ya amsa tare da basu Izinin shiga.
Bayan angama gaishe-gaishe Malam Arɗo yace.
“Lafiya Malam Liman yau ziyarar yamma”.
Cikin jimami Malam Liman yace.
“Wallahi ɗan gidan Mai martaba Lamiɗo ne ya rasu shine muka zo Ta'aziyya”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi tare da faɗin.
“Bashakka hakane ai yaron ɗalibin mune, wallahi ni lokacin da akayi jana'izar nasa banji ba amma Insha Allah zanje ta'aziyya da izinin Ubangiji”.
Kai Malam Liman ya gyaɗa tare da gyara zamansa kana yace.
“Wallahi kuwa rasuwa abin tausayi wai ciwo dare ɗaya ya tsananta”.
Girgiza kai Malam Arɗo yayi da alamun damuwa atare dashi yace.
“Ayyah haka fa kwanaki mota ta bigeshi abakin Makarantar mu fa. Yaron ya samu karaya wannan bugewan ba wanda yayi tunanin zai warke Allah sarki ashe ajalin nakusa”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.
“Haka fa rayuwar take ciwon Ajali lokacin ɗaya zai shige mutum sai dai kaji ance babu shi saidai fatan Allah yasa mu cika da Imani”.
Baki daya suka amsa da Ameen banda Moddibo daya zubawa ƙasan ɗakin Idanu da alama ya zurfafa acikin tunanin da yake.
Ahankali Malam Liman ya juya tare da kallon Moddibo kana ya maida kallonsa kan Malam Arɗo tare da cewa.
“A'a Malam Arɗo wannan jikan namu dashi kaje kwanakin baya ko?”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da kallon Moddibo da har zuwa lokacin kansa ke ƙasa yace.
“Eh jika nane kuma Malamine Amakaranta na”.
Murmushi Malam Liman yayi tare da faɗin.
“Ayyah Masha Allah Yayi kyau amma lafiya na ganshi haka baki ɗaya ya canza ko bada shine ku kaje Jauro yaya kwana kiba”.
Cikin sanyi malam Arɗo ya gyaɗa kai kana yace.
“Eh da shine mukaje”.
Cike da mamaki Malam Liman yace.
“Amma lafiya kuwa?”.
Numfashi Malam Arɗo ya fesar tare da Girgiza kai kana yace.
“Ina kuwa lafiya wannan zamani da Allah ya kawo ku. Malam Liman kai dai Ubangiji ya rufa mana asiri”.
Anutse Malam Liman ya gyara Alkyabbar dake jikinsa kana yace.
“Amin ya Allah".
Kana ya ɗaura da cewa.
“Amman Meke faruwa?”.
Gyara zama Malam Arɗo yayi tare da fuskantar Malam Liman cikin sanyin murya yace.
“Akwai wani Amininsa Yaron Alhj Bashir mai Dala Jameelu da aka sace baki ɗaya abin ya fitar mana hayyaci mun rasa wani irin tunani zamuyi ma acikin wannan al'amari”.
Cikin sauri Malam Liman yace.
“Sunhanallah”.
Cike da damuwa Malam Arɗo ya gyara zama tare da zayyane musu duk abinda ke tafiya yanda aka sacesa da kuma yanda akanemi kuɗin fansa kana da yanda suka daina jin labarinsa kwata kwata.
Girgiza kai Malam Liman yayi kana yace.
“Subhanallah”.
Ya faɗa tare da maida kallonsa kan Moddibo wanda shima adai-dai lokacin ya ɗago Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur baki ɗaya fuskarsa tayi fayau ya rame.
Cike da tausayawa Malam Liman yace.
“Amma yanzu baku da labarin sa!?”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana cikin raunin murya yace.
“A'a bamu da labarinsa yau kusan kwana goma sha biyu kenan bamu da labarinsa, sannan wayarsa bata shiga suma kuma sun daina kiran mu abinda yafi komai tayar mana da hankali kenan, bamusan Inda J yake ba”.
Malam Liman kuwa Anutse ya fesar da nunfashi cike da tausayinsa kana ya gyara zamansa tare da cewa.
“Bakomai Insha Allah za muyi addu'a da izinin Ubangiji duk inda yake a faɗin duniyar nan Ubangiji zai bayyana shi”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da Gyara zamansa Malam Liman ya cigaba da cewa.
“Da Iznin Ubangiji Allah zaiyi dalilin da za'a ganshi zan baka addu'a'o'in idan har zaku jure kuyita yi da kai da mahaifiyarsa da kuma Mahaifinsa, to za ayi nasara kuma nima zan tayaku”.
Cikin sauri Moddibo ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Munaso Malam ai addu'a'u Saiful mu'uminun ce ita addu'a itace makamin bawa dama ita muke tayi ai”.
Kai Malam Liman ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan zan baka adduo'i Insha Allah da izinin Ubangiji Allah zai bayyana shi, aduk inda yake afaɗin duniyar nan sai dai walau ko araye ko amace amma Ubangiji zai bayyana shi insha Allah za'a ga walallanilansa”.
Cikin sanyi Moddibo yace.
“Mun gode Malam”.
Cike da nutsuwa da kamala Malam Liman ya fara bashi Adduo'i Moddibo kuwa cikin sauri ya ɗauki jotter da biro ya fara rubutawa wasu da yawa daga cikin Adduo'in Moddibo ya sansu wasu kuma baisan suba sabida shi ilimi kogine faɗi gareshi. sosai ya riƙa faɗa masa adduo'in Moddibo kuwa yana rubuta adduo'in yana bitar su yasan da izinin Ubangiji idan ya zauna na awa biyu yayi research ɗinsu zai haddace su.
Bayan Malam Liman ya gama bawa Moddibo adduo'in Hajja Nana ta saki ajiyar zuciya kana tace.
“Toh Ubangiji Allah ya karesa Allah ya bayyana sa aduk inda yake”.
Cikin sanyi murya suka amsa da Ameen.
Kallon Malam Liman Hajja Nana tayi tare da faɗin.
“Ai wannan Jikanmu ne ka tuna ƙawata Innare?”.
Kai Malam Liman ya gyaɗa mata tare da cewa.
“jikanta ne?”.
Jinjina kai Hajja Nana tayi tace.
“Eh shine”.
Murmushi Malam Liman yayi tare da faɗin.
“A Masha Allah Yayi kyau”.
Ita kuwa maida kallonta kan Moddibo tayi wanda gaba ɗaya ya zubawa takardan adduo'in ido kana tace.
“Idan ka koma ka gaishe min da ita yau kam bazan samu zuwa ba yanzu ma munyi yamma”.
Kai ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.
“Toh mun gode Allah ya saka da al'khairi Insha Allah zataji”.
Miƙewa Hajja Nana da Malam Liman sukayi tare da yi musu Sallama suka tafi Moddibo kuwa yana fita daga gidan Malam Arɗo kai tsaye gidan Abba ya wuce Bayan sun gaisa Abba yayi shiru tare da tsirawa waje ɗaya ido gabansa da magunguna da alamar bai daɗe da gama shaba.
Ahankali Abba ya maida kallonsa kan Moddibo da yaga yayi mugun rama ya sake zama wani so silent duk da dama can bamai yawan magana bane amma yanzu shirun yayi yawa.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da faɗin.
“Aliyu kaga yanda ka koma kuwa ka dawo kamar wanda yayi shekara yana jinya”.
Kallon Abba Moddibo yayi tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo kana ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da cewa.
“Abba”.
Still Idanun Abba na kansa yace.
“Na'am”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.
“Insha Allah Abba inaji Ajikina J ɗina ya kusa bayyana”.
Numfashi Abba ya fesar tare da sakin murmushi na alamar jin daɗi kana yace.
“Allah yasa haka Aliyu”.
Ahankali Moddibo ya amsa da Ameen kana yace.
“Abba ya zun nan akwai wani malami da muka haɗu dashi agidan malam Arɗo ko Malam Arɗo da kansa wajensa yake zuwa ɗaukan darasi ya bani adduo'i masu tarin yawa”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa tare da cije Lip ɗin sa na ƙasa kana yace.
“Adduo'in da nake ji ajikina insha Allah Ubangiji zai amsa mana, gashi ya bani adduo'i da dama yace mu riƙa yi dani da kai da Ummi. Insha Allah duk inda J yake afaɗin duniya Allah zai bayyana mana shi za muji labarinsa aduk inda yake”.
Murmushi Abba yayi tare da faɗin.
“Mungode ƙwarai Allah yasa adace”.
“Ameen yace kana yaci gaba da cewa.
“Kyansa ma mu ƙara harda Azumi amma dama Ni tuntuni ina Azumin Abba kaima ka gwadayi.
In Sha Allah ni zan shiga itiƙafi na tsawon kwanaki uku Insha Allah”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan Moddibo Allah ya temaka”
Nan Moddibo ya bawa Abba adduo'in kana ya tafi kai tsaye gidan Ummi ya nufa itama ya bata Adduo'in cikin sanyin murya tace.
“Toh Babana Insha Allah zanyi”.
Kai ya gyaɗa kana ya fice kai tsaye gida ya nufa yana isa sashen Innayi ya wuce sannan ya mata bayanin duk abinda ya faru tare da bata Adduo'in da Malam Liman ya bayar kana ya faɗa mata saƙon gaisuwar da ƙawarta ta bata.
Kana ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Toh zan shiga 'itiƙafi a ɗaki”.
Jinjina kai Innayi tayi da faɗin.
“Toh me dame kake bukata?”.
Girgiza kai yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Bana buƙatar komai Akwai Friuts a Fridge sannan akwai kayan tea kuma azumi zanyi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh Allah yatemaka Allah ya bada sa'a.
Ameen ya amsa tare da nufar Bedroom ɗinsa.
Yana shiga yaja ƙofa ya rufe tare da nufar toilet ya ɗaura alawala yana fitowa ya zauna bisa salla ya fuskanci gabas.
Ya fara rera karatun Al'ƙur'ani sai karfi ɗaya ya fara jero Adduo'i yanayi yana kuka.
Sai ƙarfe uku ya kwanta ƙarfe huɗu dai-dai ya farka yasha tea da fruits Washe gari ya tashi da Uzumi haka ya yini da azumi yaita Adduo'i da karatun Alkur'ani idan dare yayi haka zaita nafilfili sai karfe uku zai kwanta ƙarfe huɗu zai tashi yayi Sahur haka ya cigaba da rayuwa har tsawon kwanaki uku aɗaki yana fadawa Ubangiji bukatarsa Aɓangaren Abba ma haka ya ɗauki tsawon kwanaki uku yana bautar Ubangiji haka Ummi ma baki ɗaya ta miƙawa Ubangiji lamuranta.
Yau ya kama kwana na huɗu kenan ahankali Moddibo ya fito daga falonsa tare da tsayawa abakin farandar.
Innayi dake tsaye ta zuba masa ido lokaci ɗaya taji hawaye na zubo mata ganin yanda yayi wani masifar ramewa idanunsa sunyi luhu-luhu dasu yayinda sajensa ya cika fuskarsa kasancewar gashi mai santsi da laushi yasa sai sheƙi yake fuskarsa nan tayi fayau sai sheƙi take alamun a ɗan kumbure take sabida yawan kuka da rashin isasshen bacci.
Lumshe Idanu Innayi tayi hawaye masu zafi suka zubo ganin kamar daga jinya ya tashi.
Moddibo kuwa ahankali ya ɗaga kai ya kalleta jin yandata tsaresa da ido.
Cikin rawan murya tace.
“Moddibo kaga yanda ka dawo kuwa?”.
Murmushi mai ciwo yayi tare da Girgiza kansa cikin sanyin murya yace.
“Innayi bari na tafi wajen Ummi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh baka tsaya kaci abinci ba”.
Girgiza kai yayi kana yace.
“A'a Innayi na ƙoshi”.
Kallonsa Innayi tayi Idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Dan Allah Moddibo ka tsaya kaci wani abu dubi yanda ka dawo fa”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh shikenan Innayi ki bani tea”.
Cikin sauri ta hado masa tea ta kawo masa karɓa yayi yasha bayan yasha ya fita kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga falon.
Ummi na ganinsa tayi saurin miƙewa tare da fashewa da kuka mai cike da rauni.
Moddibo kuwa cikin sauri ya ƙarasa kusa da ita tare da riƙe tafin hannunta kana cikin raunin murya yace.
“Ummi meyafaru Ummi kuka kuma?”.
Cikin zubda hawaye ta kallesa tare da cewa.
“Babana abubuwan sun haɗu sunyi min yawa acikin kwanaki Ukun nan Ba Jameelu na sannan kai ɗinma da nake gani inji sanyi na daina ganinka. Babana kaga yanda kadawo fa”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Ummi Insha Allahu in Allah ya yarda hawayen mu ya kusa daina zuba inaji Ajikina J yana kusa damu”.
Numfashi ta fesar tare da cewa.
“Allah yasa hakan Babana dubi yanda ka dawo fa kamar wanda aka sallamo daga asibiti kana tafiya Iska na ɗibarka”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Asma'u data zabga tagumi tana binsu da kallo baki ɗaya itama ta rame ta sake zama shiru.
Cikin sanyin murya tace.
“Asma'u kawo masa abinci yaci”.
Kai ya Girgiza Asanyaye yace.
“Ummi bana jin yunwa”.
Cikin sauri da sanyi Ummi tace.
“Zafa kaci abinci matuƙar kana son hankalina ya kwanta to kaci abinci Babana”.
Cikin sanyi yace.
“Toh Ummi”.
Ahankali Asma'u ta fito hannunta riƙe da Plate ɗin dambun shinkafa dayaji Vegetables ya na fidda ƙamshi da soyayyan naman kaza akai da kwalin exotic.
Agabansa ta ajiye masa kallon Ummi yayi ganin yanda ta tsare da ido tana zuba masa, ahankali ya fara cin abinci duk da yana jin cikinsa ya cushe yaci ya kai rabi kana yasha lemon Kaɗan.
Ture Plate din yayi kana yace.
“Ummi bari Inje gidan Abba”.
Kai ta gyaɗa da fadin. “Adawo lafiya”.
Moddibo na fita kai tsaye gidan Abba ya nufa yana isa ya shiga falon bakinsa ɗauke da Sallama Atare Abba da Malam Arɗo dake zaune suka amsa masa cikin sanyi Moddibo ya nufi gefen Abba ya