Showing 102001 words to 105000 words out of 176046 words
can dajin nasu mana”.
Ta ida maganar tare da shiga motar taja murfin ta rufe da ƙarfi.
Sai kuma ta sauƙe glass ɗin motar tare da cewa “Haiydar, Ramadan, da Raudat ku shigo motar tunda ku dai ta Ubanmu ne”.
Cikin takaici Haiydar ya girgiza kai alamar a'a su tafi.
Ita kuwa Khausar ciki takaici ta ɗaga Raudat da Ramadan ta sakasu cikin motar tare da nunawa Haiydar ƙofar motar alamun ya shiga.
Murya a cushe yace.
“Toh kefa Adda Khausy”.
Cikin danne fushinta tace.
“Kada ka damu zan shiga Napep”.
Zai yi mgn tayi tayi saurin cewa.
“Dan Allah kada kace komai shiga kuje”.
Ta ƙare mgnar tana turashi ciki, dole ya shiga. Ita kuwa Amina tsaki taja tare da cewa.
“Dole su kam shiga ke kuma sai kije can kishiga naki na Uban”.
Kallon Habu tayi kana tace.
“Haba kaja motar mu tafi”.
Da mamaki Habu drive ya kalleta kana yace.
“Haba Amina taya zamu tafi mu barta anan dubi hadarin daya taso sannan babu kowa a haraban makarantar ya za'ayi mutafi ne”.
Harara ta galla masa kana tace.
“Mu tafi kuma wallahi idan ka ƙi na rantse da Allah saina sa Ummah tasa akoreka”.
Ahankali Haiydar ya juya ya kalli Amina wanda tun da suka fara magana bai sa baki ba yace.
“Haba Addah Amina Meyesa haka Fisabilillah ai koma menene bai kamata ki hanata shiga mota ba dubi hadari fa kuma kin san yadda take tsoron yanayin ruwan sama”.
Harara ta watsa masa kana tace.
“Rufe min baki an hanata ɗin rufe min baki ɗan Iskan yaro zaka nuna min ƴan Ubanci kenan ruwan ya cinyata, ta mutuma kawai kowa ya huta”.
Da ɓacin rai Afuskarsa ya kalleta kana yace.
“Ni dai bazan nuna miki ƴan Ubanci ba, saboda bamu tashi da shiba, kuma wallahi idan na koma gida na faɗawa Ummah ma ke kanki kinsan sai tayi miki faɗa”.
Dogon tsaki taja tare da cewa.
“Kayi sauri kada ƙuda ya rigaka”.
Jin haka yasa Haiydar yin shiru sai kuma ya kalli Amina tare da cewa. “Matsa min In ɗauki jakata bazan iya tafiya in barta anan ba”.
Girgiza kai Khausar tayi kana tace.
“A'a Haidar kada ka ɗauka ka shiga dasu Ramadan ku tafi nima yanzu zan biyo bayanku”.
Amina kuwa kallon Habu Driver tayi kana tace.
“Mu tafi”.
Jin haka yasa Khausar jan marfin motar tare da rufewa kana tace.
“Pless dan Allah Haiydar zauna ku tafi, in Sha Allah babu abinda zai sameni”.
Dole ya zauba ba don ya soba,
Shi kuwa Habu ba yanda ya iya haka yaja motar ya tafi.
*Yar uwa littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, in dai kin ganshi a waje to na satane, a Groups ɗina na sakayya ne ɗai ya halatta, 1k ne biya ki karanta cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ban yafe ba a karanta min littafi ba'a biya ba in kin tura kuɗin ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*
Khausar kuwa shiru tayi tare da bin motar da kallo har ya fice aharabar makarantar, ahankali ta juya ta kalli cikin makantar babu ɗalibi ko ɗaya duk sun watse haka zalika ma Malamai duk sun watse shiru tayi sai kuma ta ɗaga kanta sama ganin yanda hadari ya taso ga iska dake kaɗawa da ƙarfi.
Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki haka ta fara jan ƙafanta har ta fice acikin Makarantar tsayawa tayi abakin titin koda zata samu Napep amma takai minti biyar babu abin hawan da yazo ya gifta sakamakon hadari daya taso sosai a garin yasa dukkan ababe hawa tsagaita zirga-zirga tana nan tsaye har aka fara ɗan yayyafi hakan yasa ta fara tafiya ahankali a gefen titin.
Ba tayi nisa da makarantar ba taji an buɗe gate ɗin makarantar da ɗan sauri ta juya, akan motar Moddibo Idanunta suka sauƙa da sauri ta kawar da kanta gefe kana ta cigaba da tafiya.
Acikin mota kuwa Moddibo ne da M Jameel yayin da Moddibo ke Driving M Jameel na gefen me zaman banza.
Kallo ɗaya Moddibo yayiwa bayanta ya ganeta, baki ya taɓe Aransa yace yau kuma wannan wani sabon rashin kunya tayi musu suka sauƙeta, sai kuma ya ɗage kafarɗarsa alamun ita ta jiyo.
M Jameel kuwa sam bai ganeta ba saida suka gifta wajenta sannan yaga fuskarta.
Da mamaki ya furta.
“A'a Lelewal”.
Cikin sauri ya ɗaura hannunsa kan Moddibo tare da cewa.
“A.J tsaya Please dubi duk ɗalibai sun watse amma sai ita kaɗai mai ya tsayar da ita anan kuma ga hadari baƙiƙƙirin dubi fa yanda garin yayi duhu ko Babba hadarin na bashi tsoro yakeyi!”.
Juyawa Moddibo yayi tare da Kallonsa cikin yanayin nutsuwarsa yace.
“To ina ruwanka da ita!?”.
Wara Ido M Jameel yayi kana yace.
“Ban gane ina ruwana da ita ba? ɗalibarmu cefa! sannan kullum a mota ake kawo su sannan zuwa ake aɗauke su, kana mun ganta ba'a tafi da ita ba sannan ka duba ita kaɗai ce a layin nan dubi fa yanda layin babu kowa”.
Kallon gefen Ido Moddibo yayi masa kana ya taɓe baki.
Da sauri M Jameel ya cigaba da cewa.
“Haba A.J ya za'ayi kace haka?”.
Moddibo kuwa juya idanunsa yayi kana yace.
“Toh Meye haɗin mu da ita? kasan Meye Uzurin daya tsayar da ita?
Sannan kasan Meye dalilin tsayuwarta! Wata ƙil ma wani bishiyoyin anguwar takeson hawa”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“Ai koma mene sai mu tsaya mu tambayeta ko?”.
Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“Nifa bazan tsaya ba”.
Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Dan Allah A.J da darajar Annabi Muhammad (S.A.W) mu taimaki yarinyar nan.
Yanzu idan Asma'u ce zaka iya barin ta awajen nan ne?”.
Da sauri Moddibo ya kallesa kana yace.
“Asma'u kuma mai ma zai tsayar da ita anan mai zai haɗa ta faɗa da wasu har tayi musu rashin kunya su sauƙeta amota, ai Asma'u baza ta kasance haka bama!”.
Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.
“Amma kayi tunani ƴa mace ce ita ko addininmu ya koyar mana da kula dasu da kuma kula da al'amuran daya shafesu A.J bai kamata ba na roƙe ka dan Allah ba danni ba kuma badan ita ba dan Allah da kuma darajar Manzon mu kayi haƙuri ka tsaya! In ma bazaka ɗauketa ba, ni ka sauƙin bazan iya tafiya in bar Khausy cikin wannan yanayin A.J bazan iya barin ta ananba”.
Ya ƙarashe mgnar cikin wata iriyar raunatacciyar murya mai fito da sirrin dake binne cikin zuciyarsa.
Hannu Moddibo ya sanya tare da dafe goshinsa alamar ya gaji da damuwar M Jameel ahankali yasanya lallausan tafin hannunsa ya shafa sajensa ba tare da yace komai ba ya taka burki ya tsaya.
Yana mai kallon yadda M Jameel ya sauƙe numfashi.
Ganin ya tsaya ya sanya M Jameel sakin murmushi tare da buɗe motar ya fita cikin sassarfa da ɗan gudu ya nufi inda Khausar take dan sun ɗanyi mata nisa kana ga yayyafin da aka fara da ƙarfi da kuma rugugi alamar ana gaba da kecewa da ruwa mai ƙarfi.
Moddibo kuwa da kallo yabi M Jameel ta mirror motarsa.
Aransa yace Ohhh J ji yanda yake gudu kamar wani yaro ko ya gani a wannan ƴar nan har yake jinta cikin zuciyarsa.
Khausar kuwa tana ganin M Jameel ta saki nannauyan Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Yaya Jameel”.
Cike da kulawa ya kalleta tare da cewa.
“Lelewal mai yafaru yana ganki anan ke kaɗai, bayan baki ɗaya student's sun watse”.
Ahankali ta kallesa sai kuma tayi saurin lumshe Idanunta tare da cewa.
“Wallahi Yaya Jameel Amina ce ta hanani shiga motarsu yau kam masifa take ji dashi”.
Girgiza kai yayi tare da faɗin.
“Subhanallah gaskiya bata kyauta ba, maza zo ki shigo mota mutafi”.
“Toh”,tace tare da bin bayansa cikin sassarfa yayinda ko wanne gaɓa na jikinta ke motsawa.
Ɗan guntun tsaki Modibbo yaja, tare da kauda kansa daga kan madubin, ganin yadda suka wani jero da J ɗinsa.
Suna isa wajen motar M Jameel ya buɗe mata bayan gefen da Modibbo yake tashiga, sannan shi kuma ya zagaya ya shiga a hankali Khausar ta ɗaga kanta tare da kallon gaban motar ai kuwa idanunta suka sauƙa akan Moddibo da batasan yana cikin motar Ba gashi ta zauna asaitin bayansa.
A kuma dai-dai lokaci ruwa ya kece tamkar da bakin ƙorya, key Moddibo yayi wa motar tare da figarta a dan guje suka fara tafiya.
Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.
“A.J kasan zamu biya ta gida ka sauƙe ni tun safe Abba ke kirana wai Inje Yana son magana dani muje ka sauƙe ni”.
Kallon sa Moddibo yayi tare da cewa.
“Baza ka bari sai anjima ba?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“A'a muje dan Allah ka sauƙe ni saboda bansan me yake sona dashi ba yanata ne mana tun tuntuni”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh naji”.
Yayi mgnar tare da haharan M Jameel ɗin,
Sannan ya cigaba da Driving ɗin sa.
Shi kuwa M Jameel murmushin yayi tare da ɗan mishi alamun zunɗe.
*Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, daga gobe in dai kinga littafin SAKAYYAH a wani wuri to na satane, yar uwa ki biya 1k ne kacal ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin kowa a kanki littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa kada ki karanta in baki biyaba 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*
Khausar dake zaune abayan motar kuwa ƙanƙame jikinta tayi saboda yanda ɗumin motar ke ratsata sam cikin motar babu sanyi da yawa ba kamar waje da iska ke kaɗawa ba.
Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyara Questions peper dake hannunta ta sake rungumesu aƙirji sai kuma ta gyara zaman wuyan hijabinta wanda har tattausan gashin gaban goshinta mai sansti ya bayyana.
Baki ɗaya cikin motar a wadace yake da wani irin ni'imtaccen sanyayyan ƙamshi mai daɗin shaƙa yakeyi, Ahankali Khausar ta maida kallon kan bayan Moddibo da take fuskanta sanye yake cikin ɗanyen Boyel fari ƙal yasha guga sosai yayin da kansa ke sanye da hula zanna bukar wadataccen sumar ƙeyansa ya kwanto lib-lib gwanin kyau sai sheƙi da ƙyalli yake zubawa.
Ƙeyar tasa ta zubawa ido sai kuma ta gallawa ƙeyar tasa harara tare da murguɗa masa baki.
Tana ɗago Idanunta suka sauƙa akan Idanun Moddibo ta madubin jikin motar yana kallonta cikin mugun sauri tayi ƙasa da kanta zuciyar ta na mai bugawa da ƙarfin tsiya.
Moddibo kuwa Ƙoffa yayi tare da haɗa harshensa da hoƙorinsa ya fitar da wani sauti kana yace.
“Hmmmm!”.
Kallon sa M Jameel da Idanunsa ke lumshe yayi kana cike da kulawa yace.
“Ya dai A.J?”.
Shiru Moddibo ya masa tare da watsa masa Harara!.
Ware Ido M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Ya dai kake ta harare-harare acikin mota!”.
Ƙin tanka masa Moddibo yayi ya cigaba da Driving ɗinsa tare da ƙara tsuke fuska.
Khausar kuwa shiru tayi sai kuma ta sake ɗago kanta ahankali ta kalli madubin ganin ya kawar da kansa gefe yasa ta sake liƙawa ƙeyansa harara tamkar idanunta zasu manne bisa ƙeyar tasa, kana ta ɗago hannunta na dama ta ɗan haɗe kan yatsun tare da buɗe su ta watsa masa alamar Jarabebbe! Mayatacce!! Masifeffe!!! Fitinenne!!!! sai kuma ta sake watsa masa Harara tare da kai hannunta ƙeyarsa kamar zata kai masa ronƙwashi.
A kuma dai-dai lokacin ya ɗago ya kalleta ta madubin.
Azabure taja baya tare da jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa.
Cikin fushi Moddibo ya watsa mata mugun kallo tare da cewa.
“Anh zan karyaki wallahi kakkarya ki zanyi in watsar dake atiti inyi tafiyata, ƴar rashin kunya fitsararriya”.
Ita dai Khausar rumtse Idanunta tayi da masifan ƙarfi tare da sake rungume question peper ta aƙirji gam-gam.
M Jameel kuwa daya ta kure jikinsa waje ɗaya idanunsa alumshe saboda sanyi da ake yayi saurin buɗe idanunsa yayi tare da kallon Moddibo dake Driving tamkar bashi yayi maganar ba cikin tsaresa da Ido yace.
“Ha'a wai mai yake faruwa a motar nan ne kake abubuwa iri-iri daga Harara, Ƙoffa, tsaki, tsuke fuska, yanzu kuma sai cewa zaka kakkarya!,To waima wa zaka karya ne kam?”.
Cikin fushi Moddibo ya juya ya kallesa kana yace.
“Ai duk wanda zan karya ya sani!
Karya yarinyar nan zanyi fitsararriyar banza mara kunya idan kina sake kuskuren kallon min ƙeyata saina gutsitsi-tsiraki na ƙwaƙule miki manyan mayatattun idonun ki masu kama da na yan maye na jefar! A titi ko na samu salama”.
Lokaci ɗaya tsoro ya dirarwa Khausar jin wai zai Kakkarya ta ya ƙwaƙule mata ido cike da tsoro ta kuma ƙara rumtse Idanunta tare da ta kure jikinta ajikin kujera ita kanta batasan dalilin da yasa yake mata haka ba ita dai tasan da zata samu dama itama karyashin zatayi ta kuna tsitstsige gemunshi.
Akuma dai-dai lokacin suka isa ƙofar gidan su M Jameel Moddibo yayi Parking.
Ɓude Murfin motar M Jameel yayi tare da fita duk da ruwan da ake tsugawa bai hana sa saka kansa ta cikin glass ɗin side da Khausar take ba, cikin ƙasa da murya yace.
“Lelewal be careful don't Misbehaving kinga bana nan yaseen kika mishi ba dai-dai a titi zai wurgaki ya tafiyarsa”.
Kai ta gyaɗa masa cike da alamun tsoro sai taji kamar ta fita ta bisa.
Shikuwa M Jameel kallon Moddibo yayi tare da cewa.
“Toh Allah ya tsare Allah ya kaiku lafiya A.J Amana ce, dan amana A.J ka kularmin da ita”.
Daga haka ya juya da gudu ya nufi cikin gida zuwa lokacin duk ya jiƙe saboda yanda ruwan ke sauƙa da ƙarfi.
Acikin motar kuwa lumshe idanu Moddibo yayi ba tare da yaja motar ba.
Khausar kam ƙasa da kanta tayi aranta tace wannan dai akwai bahagon mutum, fisabilillah yana kallon yanda ake tsuga ruwa kamar da bakin ƙwarya amma yaja ya tsaya jifa yanda ruwan ke sauƙa.
*Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan na gama Free page, 1k ne kuɗin samun damar karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, biya ki karanta cikin Aminci*
Sun kai kusan minti biyar ahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai ba banda sautin ƙaran ruwa babu abinda ke sauƙa ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Khausar ta ɗago Idanunta ta kalli madubin cikin motar,
idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna.
Harara ya watsa mata kana cikin wata razananniyar murya da shi kansa bai san yana da ita ba yace.
“Uban me kike abayan mota koni.
Driver kine harda wani hakimcewar ki abaya a dole kega Sarauniya kin samu Driver!
Kifita idona fa, nifa ba J bane zan karya kifa”.
Cikin sauri ta buɗe bayan motar ta fita aranta tace Gwanda inyi yanda yake so dan yanda yake kiran zai karya nin nan inda yazo da tsautsayi sai yajawa Mommy asarata, gaban motar ta buɗe ta shiga amma duk da haka saida ta ɗan jiƙe sabida ruwan da ya fara ƙarfi, tana zama yaja motar suka tafi.
Akuma dai-dai lokacin ruwan ya sake kecewa da ƙarfin gaske tamkar da bakin ƙwarya ake tsuga ruwan.
Khausar kam lumshe Idanunta tayi aranta tace ya Allah ka kaimu gida lafiya ka rabani da wannan bawa naka lafiya,
domin akwai rata tsakaninsu da gida sosai ahankali ta buɗe Idanunta ta kalli titin da yayi shiru babu hayaniyar sai ƙugin motarsu da kuma yanda tayun ke fesar da Iska da ruwan kan kwalta fuuuu kana har zuwa yanzu garin ɓakiƙƙirin yake duk da kuwa yadda ake sheƙa ruwan alamar har yanzu ruwan bashi da niyyar ɗauke wa.
Suna cikin tafiya akayi wani irin walƙiya mai haske.
Da sauri Khausar ta rumtse idonta tare da furta.
“Bismillahi”.
A lokacin guda kuma ta sake buɗesu da sauri sabida
jin wani irin rugugi da akayi mai bada sautin rududuuu-duuuuhhh kana ga walƙiya daya haska da wani irin sauri Khausar ta rungume jikinta waje ɗaya aranta tace.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakil Subhanal Lazi yusabbihul ra'adu bi handihi wal Mala'ikatu min hiyfatin”._
Cikin tsananin tsoro tayi addu'ar domin arayuwarta babu abinda take masifar tsoro a damuna kamar tsawa da walƙiya sam bata yarda ta haɗa ido da walƙiya da zaran taga za'a yi walƙiya zata rufe Idanunta ta sunkuyar da kanta.
Shi kuwa Moddibo tafiya ya cigaba dayi yayin da titin yayi shiru babu hayaniyar komai sai bishiyoyi dake rangaji ruwa na sauƙa akansu Sanyayyar iska mai cike da Ni'imah na kaɗasu baki ɗaya shaguna dake gefen titin arufe suke baki daya garin babu hayaniya sai jefi-jefi suke hango Mutane.
Suna cikin tafiyar aka sake wani walƙiya mai masifar haske ja, alamun yanzu za'a ƙara kecewa da ruwa.
Atsorace cikin ɗaga sautin murya tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ta ida addu'ar tare da kife kanta akan gwiwarta yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa A ɗan juya kai Moddibo yayi kalleta, domin shi kansa zuciyarsa ta harba sabida walƙiyar saida ta ɗauke masa ido saboda yanda walƙiyar tazo da haske mai ƙarfin gaske sosai yaji tsoron walƙiyar amma sai yayi addu'a aransa kana yana cigaba da tafiya bai tsaya ba.
Bayan walƙiyar ba daɗewa aka saki wata tsawa mai sautin rututuuuu alokaci ɗaya zuciyarsu ta buga domin ji sukayi tamkar ƙasa zai tsage.
Atake wani matsananci tsoro ya sake lulluɓe Khausar yayin da jikinta yashiga rawa tamkar mazari kanta ta kife acinyarta zuciyarta na cigaba da bugawa da masifan ƙarfi kana har zuwa lokacin kanta na sunkuye akan ƙafafunta tun daga wannan rugugin.
Yayinda gaba ɗaya mazauna garin Gembu Mebila suke cike da taraddadi sabida bisa dukkan alamu yau da tsawa da rugugin ruwan yake sauƙa.
Acikin haka ne aka sake walƙiya mai masifar haske irin walkiyar nan mai zuwa tamkar an watsa dogon bulala koko tafiyar maciji,
Da masifar haske da tarsatsi yazo tamkar an watsa bulala Sharrrrrr sai kuma a take aka saki wata iriyar tsawa mai masifar ƙarfi yabi yo bayansa wanda ke fitar da sautin felelelelelelelen da masifar karaji da gigita dukkan bani adam
Cikin wani irin tsananin tsoro da gigita Khausar ta saki ƙara mai masifar sauti tare da furta. _“Hasbunallahu wani'imal wakil. Subhanal Lazi yusabbihul ra'adu bi hamdihi wal Mala'ikatu min hiyfatihi”._
Atake aka sake sakin wani walƙiyar haɗe da wata iriyar firgitacciyar tsawa mai masifar kara mai razana dan adam dasa hanjin mutum kaɗawa.
Cikin tsananin tsoro da masifar gigita ta dari ta ɗago kanta a kiɗime ta afkawa jikin Moddibo yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa shi kansa Moddibo wani irin tsoro ne ya kamasa saboda hasken walƙiyar saida ya tsaga glass ɗin gaban motarsa tare da bada sautin ƙarararassss!!!.
Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta kanainayeshi, bashida wani kataɓus ɗin motsa wa, sabida yadda ta kife kanta afaffaɗan ƙirjinsa