Showing 90001 words to 93000 words out of 262297 words
for him, baya so ya sake letting dina down. Daga karshe dai na gaya masa cewa nan da about a month zamu koma Nigeria kuma muna zuwa aure za'a yi min da Munir, whom I despise, dan haka zabi ya rage nasa, is either ya zauna a America ya cigaba da playing bad boy role dinsa ni kuma a aura min munir ko kuma ya dawo yayi facing daddy ya karbi aurena. Ina fadin haka na katse wayar, ko minti daya ba'a yi ba ya kira, na katse kiran na kashe wayar gaba daya. Na san na kunna masa wuta. Dole ya dawo cikin sense dinsa yasan abinyi.
Ranar da yamma naje na samu mommy a dakin daddy tana gyara masa kaya. Na zauna a kusa da ita nace "Mommy wannan da kuke zance ke da yaya Walid rannan, sunansa Abbakar, dan garin Abuja ne, he is an architecture, iyayensa manyan mutane ne sosai a garin abuja. Ina son kiyi wa daddy maganar sa dan cikin satin nan na keso zaizo England ya gaishe da ku" mommy ta kalleni fuskarta kamar gonar auduga tace "kai Alhamdulillah, he is your final choice kenan ko?" Na gyada kai tace "Allah ya kawo shi lafiya" nace "Amin" har na mike sai kuma tace "Moon, kash, kinga har naso in manta, daddynku gobe zai yi tafiya, president ne ya tura shi wani summit a South Korea kuma zasu dan jima a can, dan yace ma maybe sai dai mu hadu a Nigeria tunda mu zamu tafi da wuri kinsan maganar bikin Nuraddeen ya tashi" na danyi jim ina jin babu dadi, dan da karfi na nazo so nake ayi wacce za'a yi a cikin satin nan a gama. Nace "OK, shikenan sa hadu da daddy a Nigeria, in yazo kawai sai ya gaishe ki ke" mommy tayi dariya, na tsaya ina kallonta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, tace "Moon kenan, ina kika taba ganin saurayi yazo ya gaishe da uwa?" Sai da ta fada sannan nima nayi dariyar abin, tace "kawai kice masa yayi zamansa a Nigeria za muzo mu same shi" nace "ai baya Nigeria yana America, dama munyi dashi ne zai biyo ta England sannan ya karasa Nigeria" mommy tace "babu wani abu ai, yazo kawai ku gaisa, in yaso sa hadu da daddyn ku a Nigeria" daga haka na koma part din mu ina lissafin ba haka naso ba ni kam. Amma Allah yasa jinkirin ya zamar mana alkhairi. Dan nasan ba karamin takaici zan sha ba a wajen bikin nuraddeen, a lokacin kowa zai san na gama makaranta.
Sai da daddare na kunna wayata. Messages ne suka fara rige rigen shigowa waya ta, nace a raina 'waya gaya maka barno gabas take ne da, dan kaga ina wani lallabaka shine zakake daga min kai. Na fara karantawa "shine kika kashe wayar ko?" "Please karki kuma mentioning wani munir or else.... I don't even know what I will do" "OK, i will come, pick me up in the airport tomorrow morning" nayi murmushi a raina nace 'na gano lagonka ai yanzu, kishi.
Amina ce ta shigo tanata kumbure2, nace "ke kuma ke da wa kike bata rai" tace "wai Nigeria zamu tafi bikin Nuraddeen, ni wallahi banson zuwa, ina zuwa gida yanzu zancen aure za'a fara yi min, duk an bi an saka min ido a gida kamar ni nafi kowa girma" dariya nayi sosai nace "that makes the two of us, at least ke ba'ayi miki mijin bama, ni yana nan an ajiye min dan haka bani da bakin cewa ai mijin ne bai zo ba" ta zauna a kusa dani tace "yanzu muyi shawara, ki lallaba mana mommy ta bar mu anan, sai mu zauna a gidan Hafsat su suyi tafiyarsu" na harare ta nace "you are joking, right? Mommy n ce zata tafi ta barmu a gidan Hafsat? Ai in mafarki kike ma yanzu ki farka" ta sake bata rai "to ni yanzu ya zanyi, ni ba samari nake yi ba kema kin sani, kuma ni gaskiya bana son a yi min auren family wallahi, ni nafi son in samu miji na da kaina wanda nake so shima kuma yake sona" murmushi nayi jin ta ambaci kalmar so, tace "this is not a laughing matter oo, ke ma fa ba son munir kike ba na sani" nace mata "wai waye yake maganar wani munir ne dan Allah? Akwai wanda zai zo kasar nan gobe, shine wanda zan aura, zan hada ku ku gaisa" tace "kina nufin baffa zai bari? Duk wannan zaman jiran naki da munir yayi?" Nace "matsalarsa ce kuma wannan, babu wanda ya matsa masa yace lallai sai ya jira, ni dai abinda na sani shine baffa yace in na gama karatu ban sami miji ba za'a hada ni da munir, to na samu, babu sauran maganar munir kuma".
Sai da nazo kwanciya bacci sannan na kira sultan, bugu daya ya dauka nace "na dauka kayi fushi ai" yayi ajjiyar zuciya yace "ni na isa? Bayan kinsa yau na wuni da waya a hannuna saboda ina tsoron kar in ajiye ki kira ban gani ba" daga nan na bashi labarin cewa ba zai samu ganin daddy ba sai nan da kamar 3-4 weeks a Abuja. Muka gama plan din zuwansa gobe, ban ankara ba kawai sai gani nayi har karfe biyun dare tayi muna ta hira ba tare da lura da time ba.
Washegari ya kira ni ya gaya min sun taso. Sai a lokacin naji gaba na yana faduwa, can I really face sultan? A wayar ma da yaya ballantana ido da ido. This is going to be very awkward. Nayi wa kaina alkawarin na daina munafuntar iyayena dan haka na tafi gurin mommy nace mata "Mommy Abdallah yau zai zo, kuma yace yana so inje in dauko shi a airport" tace "to shikenan ai babu wani abu, sai ki dauki driver ya kaiki. Allah ya sa albarka a ciki" nace "Ameen, nagode mommy" wannan shine abinda muka yi lacking da a relationship din mu, albarkar iyaye, ko da yaushe in iyayenka suna saka maka albarka to ba zaka taba tabewa ba. Na rasa inyi kwalliya ne ko kar inyi? Wanne kayan zan saka? Karshe dai na gayawa Amina nace dan Allah tazo ta rakani, ina ganin kamar in tare muke kunya ta sata yi sauki. Amina ce ta matsamin wai lallai sai nayi kwalliya, wai ai ba haka ake zuwa taryan saurayi ba, ita ta dauka wani sabon saurayi ne, bata san Sultan babu abinda bai sani nawa ba. 😂. Sai da na nemi Hijab din da yafi kowanne girma a cikin hijabai na sannan na saka. Tsaki Amina tayi tace "wallahi baki isa ba, koni da na girma a 'yalleman ba zan saka wannan hijab din inje gurin saurayi ba" ta dauko min gyale nima nace bata isa ba, a karshe dai wani hijab din na dauko wanda bai kai wancan girma ba na saka. Muka yiwa mommy sallama muka tafi. Karfe 12 jirgin su ya sauka. Ni dai tunda naji announcement na sunkuyar da kaina kasa. Can naji Amina tace "gashi nan ya taho" ban dago kaina ba nace mata "ya akayi kika san shine?" Tace "ko yadda yake kallonki ma ai dole a gane. Kai amma fa ya hadu, a ina kika samo shi? Dan Allah ki samo min irinsa nima". Sallamarsa ce ta hana ni karasa kai mata dukan da nayi niyya, ai babu shiri na juya baya na, ga mamaki na sai naji yana dariya, Amina ma ta biye masa suka yi tayi, yace "chafdi, kice akwai rigima kenan" Amina tace "ba karama ba kuwa, kaga kuma yadda ta zauna take ta koda min kai? Wai kyakykyawa, ga ilimi da hankali, shine ta dauko ni wai lallai sai nazo na ganka" dukan da nayi niyar yi mata dazu shina karasa yi mata yanzu, ta matsa daga kusa dani tana dariya, shi kuma ya matso har sai da naji dumin numfashinsa a jikina "please ki juyo mana in ga fuskarki, you have no idea how much I have missed you" ya ga bani da niyyar juyowa sai ya zagayo, ai muna hada ido nayi sauri na rufe fuskata da hannayena, nima kuma zuciya ta tana son ganin tasa fuskar daurewa kawai nake yi. Wayyo ni kam naga ta kaina. Dariya suke yi min sosai shida Amina. Lallai namiji bashi da kunya, wato shi ko a jikinsa ko? Da sauri nayi gaba na tafi gurin motoci, ina zuwa na shiga na zauna. Anan na samu damar kallonsa kafin su karaso, ya rame, ya tara gashi a fuskarsa but he still looks more handsome to me than duk mutanen da suke gurin. Suna tafiya shida Amina tana ta zuba masa zance, Allah ne kadai yasan yawan karerayin da take shirga masa. Suna karasowa ga mamaki na sai naga ya bude wa Amina gaba shi kuma ya shigo baya kusa dani. Ai kuwa na dunkule a guri daya kamar zan shige cikin kujerar, yana shigowa ya kalleni ya kyalkyale da dariya yace "Amina juyo kiga 'yar kauyen 'yalleman" tana juyowa tace "a'a wannan ai kauyancin ta ya wuce nan, maybe daga wata rugar da bamu sani ba ta taho" ni dai ina jin su bance komai ba. Can Sultan yace "kinsan Allah, ko ki ware daga wannan nannadewar da kikayi kamar macijiya ko kuma..... " sai kuma yayi shiru, na leko ta cikin hijab dina nace masa "ko kuma me?" Ya dauke kansa yace "zaki sani ne duk ranar da na kamaki" what? Me wannan mutumin yake nufi? Driver ne ya katse min tunani na yana tambayar ina zai kaimu. Nayi sauri nace masa "take us to the nearest saloon" Sultan ya kalleni yace "mai zakiyi a saloon kuma?" Nace "not me, you. You really need a haircut" yayi sauki ya shafa fuskarsa yace "damn" it is my turn to laugh now, dan haka nima na rama dariyar da yayi min, ya harare ni yace "how do I look?" Nace "terrible". Wani hadadden barbing saloon yayi wa driver kwatance, muka je ya shiga ciki ya bar mu a waje, nan Amina ta zagayo baya ta fara min barin hakora, "gaskiya gayen nan ya hadu, dan Allah dan ina ne?" Nace mata "Abuja" tace "gaskiya ni kam har yafi min kyau akan Zayed din Hafsat" nace "laa, wannan maganar kamar a kunnen Hafsat dan sai na gaya mata" yana fitowa naga ya koma sak Sultan dina, da murmushi a fuskarsa ya shigo yace "to yanzu fa?" Nace "like the Sultan I know" daga nan gidan Takawa inda Sultan yake sauka muka je, kiri2 yaki fita daga motar wai bai gama gani na ba. Sai da nace masa ina gayyatarsa dinner yau da daddare a gida sannan ya sauka. Muka tafi Amina tana ta santin sa, ni kuwa bata san haushi take bani ba. Dama saurin da muke dan mu samu muyi sallama da Daddy ne, muna zuwa kuwa muka tarar ana fito da kayansa, nan muka sake komawa airport muka rakashi, sai da ya bimu daya bayan daya yayi hugging din mu sannan ya tafi.
Muna komawa gida na gayawa mommy Abbakar zai zo dinner da daddare, nan ta fara yi min mitar ban iya girki ba "idan da ace kinyi spending koda quarter of time din da kika yi spending kina karatu a kitchen, da yanzu kin zama chef. Amma ke ba zaki yi girki ba. To yanzu ni kike so inyi masa abincin? Go to the kitchen jare, a haka zaki koya ai" na bata fuska nace "mommy idan kuma abincin bai yi dadi ba fa?" Tace "matsalarki ce kuma wannan" na kara shagwabe fuska "please mommy" tace "zan yi masa amma ba dan ke ba, dan shi" a raina nace "oho dai". Ana magrib Sultan yazo, wa yaga gandoki, anan masjid din embassy yayi sallah sannan ya kira woni. Yaya Walid tare suka tafi da Daddy, yaya Habeeb kuwa tun last week yana Nigeria, sune abokan nuraddeen ana ta shirin biki, dan haka a palon su na sauki Sultan, wata kyalliyar amina ta kuma zama tayi min tana yi tana cewa "irin wadannan samarin in baka kwalliya yanzu sai wata ta kwace maka shi" ni kuwa jinta nake yi kawai dan nasan mai kwatar sultan a hannuna sai ta shirya, kuma sultan ba kwalliya ta yake so ba, ni yake so. Already mommy ta aika an shirya wa Sultan dining din palon, dan haka ina shiryawa kawai can na wuce. Ina shiga palon na hangoshi dare2 akan dining yana serving kansa a raina nace 'oh Sultan da abinci, at least dai ai ka bari azo ayi maka bismillah ko' ina shiga ya dago yana kallona yace "bismillah, zo muci abinci" shi ko kwalliyar da Amina ta zauna ta tsara min ma bai gani ba, shi ta cikinsa yake yi. Na zauna a kan kujerar da take facing dinsa na rafka tagumi ina kallonsa yana lodawa cikinsa abinci, no wonder yake so energetic, lallai akwai aiki a gabana. Sai da cikin sa ya fara cika sannan ya dago yana kallona, sai kuma ya dan saki baki yace "menene wannan a saman idonki?" Nace "it's called an eye shadow" yace "menene amfaninsa?" Nace "kwalliya" ya saki baki yana kallona, yace "Amina ce tayi miki ko?" Na gyada kai nace "I look terrible, right" yayi dariya yace "no my love, you look beautiful, with or without make up, you are always beautiful" nace "thank you" suddenly na jefe shi da tambayar da take raina tun sanda muka dauko shi daga airport. "Sultan, me yasa kake shan giya" lemon da yake bakinsa ya fesar kan dining din saboda kwarewar da yayi, wanda yake hannunsa kuma ya zame ya zube a kasa, ya dago dara daran idansa yana kallona da mamaki, sam bai san na san da wannan side din nasa ba.
Episode Forty Nine : Ya Habeeb
"What?" Ya tambaya da mamaki, ban maimaita tambayata ba sai ruwa dana zuba a cup na mika masa, bai karba ba, na ajiye a gabansa. Ya sake tambayata "me kika ce?" Na kalle shi cikin ido nace "cewa nayi me yasa kake shan giya" ya bata rai sosai yace "who told you that?" Nayi shiru ban kalle shi ba, can yace "damn it, it's Steve, isn't it?" Nace "tun kafin muyi magana da Steve na sani" ruwan dana ajiye masa ya dauka ya shanye sannan ya mike ya bar dining area din ya koma cikin palon, nima na mike na bi bayansa, na zauna kujerar kusa dashi. Jin bashi da niyyar yin magana yasa na sake cewa "baka ce komai ba fa?" Ya juyo yana facing dina ya wani bata rai yace "can we please just drop this? I really don't want to talk about it now" nima na bata rai nace "why not? Sai bayan anyi bikin mu tukunna zamuyi maganar? Look Sultan da ace zan rabu dakai saboda kana shan giya da tuni na rabu da kai, amma ba wai hakan yana nufin nayi na'am da dabi'ar ba, ina dai saka ran cewa zaka daina. Nayi maka maganar ne yanzu saboda naga har mun fara maganar zuwanka gurin daddy dan haka ya kamata duk wani personal issues din mu muyi solving" na dan yi shiru ina studying dinsa, he looks really disturbed, ya saka duk kan hannayensa a cikin gashin sa, na cigaba "nasan kusan 70% na troubles dinka with the police are related to your drinking habit, saboda fadar annabi ne cewa ita giya itace shugabar dukkan alkaba'i, zata iya saka mutum yayi sata, zina, har ma kisan kai. Sultan zanyi tolerating komai akan ka amma banda drunk husband, what if one day ka dawo a buge kayi min duka?" Da sauri ya kalloni yace "I will never hurt you" nace "you can't be sure, duk sanda kasha u will lost control of yourself, maybe ma ba zaka gane koni wacece ba" alamun bacin raine karara a fuskarsa yace "please ki daina wannan maganar mana, wai what has come over you ne today? Ke fa baki san komai akan maganar nan ba kuma banyi niyyar ki sani ba har abada, yadda kika dauki abin sam ba haka yake ba. Amma na miki alkawarin one day zamuyi maganar but not today. You have no idea what I was going through kafin in hadu dake, and you also have no idea how much I have changed bayan na hadu dake" nace "na yarda, i don't understand and I may never understand. Ni yanzu dai please so nake kayi min alkawari guda daya. Promise me that you will never touch alcohol again" ya jingina da jikin kujerar ya zubo min idanuwansa, a hankali yace "I will do anything for you" na girgiza kaina nace "and that's where you are wrong a duk changes din da kake kokarin yi tunda muka hadu, you are trying to change for me, what I want is for you to change for YOU. Ka gyara ba dan ni ba sai dan kanka, dan ka gyara tsakaninka da ubangijin ka. Idan Allah ya duba niyyar ka yaga cewa dan shi kake komarin gyara rayuwarka sai ya taimaka maka, amma idan ya ga cewa danni kake kokarin gyarawa sai ya barka dani ko kuma ma ya hana ka ni din gaba daya" sai yanzu naga tension din fuskarsa ya ragu, a hankali ya fara murmushi idonsa a cikin nawa yace "thank you for loving me so much. I love you too. Na miki alkawarin one day zamu zauna zan baki labari akan my drinking habit, yadda na fara da struggles din da nayi akai" na lumshe idona inajin tausayinsa a raina, oh dear sultan, what other dark secret are you hiding?" Ya sake langwabar da kai gefe yace "please mu bar maganar nan haka, OK? Dan Allah kiyi min murmushi in ga dimples dinki mana" na rufe fuskata da hannayena ina jin kunyar kallon da yake min. Daga nan muka bar maganar muka koma plans na rayuwar mu, dan yanzu gaba dayan mu munyi shirin taryan koma menene zai faru. Sultan ya