Showing 228001 words to 231000 words out of 262297 words

Chapter 77 - Maimoon Hausa Novel Complete

suka fi saka idonsu akan spouse din mata akan maza. Dalili na biyu shi zayed kusan rabin rayiwarsa a England yayi ta, dan haka sanda ya tashi aure in banda wadanda suka je nema mishi auren babu wanda zai ce yasan matar sa, bayan anyi auren ma a England din suka zauna bai kawo ta nan ba har sai da ta haihu, zayed is older and stronger than I was, dan haka babu wanda zai kalli matarsa yace wani abu a kanta, dalili na uku kuma the most important shine, tsakanin aure na dana zayed shekara talatin, three full decades, abubuwa da yawa sun chanza, duk yawancin masu akida ta tribalism a family din mu babu su yanzu sai kalilan, suma kuma sunyi sanyi sosai" na fahimci bayanan ta, na kara tambayar ta daya abinda yake zuciya ta, nace "to yanzu ummee idan Takawa ya dawo kina ganin ba zai samu matsala ba kenan?" Tayi shiru kamar bata jini ba, sai naji babu dadi a raina, I shouldn't have asked that, sometimes surutu na yana sakawa in wuce limit dina, nace "am sorry ummee I shouldn't have asked that" tace "Sadiq ba zai zo ba ai, da ace zai zo da tare zasu zo da sultan, tunda kika ga basu zo tare ba to ba zai zo ba". Ban kuma tambayar ta komai ba, sultan ma kuma tunda muka fara maganar baice komai ba. Washegari muka cigaba da zagayawa gida jen 'yan'uwan ummee, kuma Alhamdulillah muna samun karbuwa a gurin su, duk da few of them ne suka san da zaman sultan a duniya. Rannan mukayi waya da Mommy, tace min " Ibrahim fa yazo neman auren Amina a gurin Daddy" da murna ta nace "laaa, amma shine Amina ko ta kirani ta gaya min?" Mommy tace "ai Amina ta tayar da rigima, tace ita yanzu bata son shi" nace "me ya faru?" Tace "wa ya sani ne, taki gaya min komai, shi yasa na kira ki ko zaki tambayar mana ita, kinga yaron nan sai faman zirga zirga yake amma ko fita gurinsa taki yadda tayi ballantana suyi magana, kuma naga daddyn ku sosai yana son hada wannan auren" nace "insha Allah Mommy zanyi mata magana, ko menene ma zamu sani". Ina kiran Amina ce min tayi "babu wani abu da zaki gaya min in chanza mind dina fa" nace "kin san ma maganar da zanyi miki kenan?" Tace "ai kowa maganar da yake min kenan, tunda ni ce mai auren nasa kuma nace na fasa banayi ba shi kenan ba sai a kyale ni" nace "OK munji mun kyale ki kin fasa auren sa, to amma ko zamu iya sanin dalili?" Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "he doesn't love me. Duk abinda yake fada a baki ne kawai amma vai kai zuci ba" nace "ya zaki ce haka Amina? Wani abin yayi miki daya nuna miki cewa baya sonki?" Ta fara kuka tace "har yanzu Moon ke yake so, yana kulani ne kawai saboda muna kama dake, bana son in aureshi muyi ta samun matsala akan hakan" nan ta bani labarin abinda ya faru tsakanin su kwanan baya, nace "amma Amina tunda kika ga ya dawo ai ina ganin ya kamata ki saurare shi, ballantana kuma da maganar aure ya dawo, meaning he is serious this time around. Bansan menene a zuciyar Ibrahim ba amma nasan yayi nadamar abinda yayi wa matarsa ta farko, kuma yayi mata hakan ne saboda baya sonta, bana jin zai kuma making the same mistake a kanki, idan da baya sonki da gaske da ba zai ce zai aure ki ba" na jima ina bata shawarwari, da gaske Amina tana son Ibrahim dan haka na san zata sauko ne ta sake bashi second chance.
Bayan munyi waya da Amina sai nayi deciding inkira Amira in ji ita ma ya take ciki, na kira ta ta dauka da murnarta, tace "Moon naje gidanki aka ce ba kya kasar ma, ina kuka tafi haka babu ko sallama?" Nace "munje saudi gurin ummeen sultan" tace "dama 'yar can ce?" Nace maka kawai "eh" munjima muna hira sannan tace "kanin ki yazo gurina rannan" da sauri nace "and?" Tace "I don't know Moon, sam banji wani abu a raina akansa ba. Amir ma yazo yana gayamin maganar aurensa, he said if am interested in him, bayan auren nasa we will talk. Moon nayi addu'ah nayi istikhara amma banji komai a raina game da Abbas ba, I tot I had something for amir amma tunda yayi min maganar aurensa naji na hakura" nace "yanzu me zakiyi Amira?" Tace "Moon alhakinku ne yake ta bina har yanzu, shi dama alhaki ai kuikuyo ne, me shi yake bi, happiness dinku dana katse muku shi ya saka zanyi spending the rest of my life in sadness" nace "ba haka bane Amira, shi ubangiji ai mai gafara ne, yana yafiya kuma yana son bayinsa masu nadama da neman gafara, sai dai laifin da kika yi ba ubangiji kika yiwa ba, mu kika yiwa, dan haka ubangiji ba zai yafe miki ba har sai mu mun yafe miki. Ni na yafe miki ba tun yau ba, amma abin tambayar shine, kin nemi gafarar Ibrahim? Shi kika fi cutarwa, shine yafi kowa shan wahala kuma har yanzu bai huta ba, shawara ta gareki shine, ki je ki nemi Ibrahim ki roke shi gafara, na tabbatar zai yafe miki, in kuma ya yafe miki, na tabbatar zaki ga chanji sosai a rayuwar ki, saboda hakkin wani baya taba barin mutum yaci gaba a rayuwa".
2 hrs ·

Episode Ninety One : His Mother's Son 2
Tace "to ni yanzu moon ta ina zan same shi?" Nace "How will I know ni da bana kasar ma" tace "Moon tsoronsa nakeji, tunda ya gane gaskiya bamu hadu ba, bansan wacce irin karba zai yi min ba" na danyi tunani a raina, tabbas Ibrahim yana jin haushin Amira sosai, dan haka ba lallai ne yasaurare ta ba in taje wajansa, Allah ma yasa karya faffalla mata mari. Sai kuma wata shawara ta fado min arai na, nace "abinda za'ayi Amira, kije gidan mu gurin Amina, ni zan kira ta in yi mata bayanin abinda nake so tayi, zata hada ki da Ibrahim kuyi magana, duk abinda ake ciki kuma sai muyi waya" ina gama yawa da amira na sake kiran Amina, ta dauka tace "what again?" Nace "ke dalla can ba maganar shi zanyi miki ba" sai nayi mata bayanin duk yadda mukayi da Amira, nace "yanzu taimako nake nema a gurinki, so nake ki hada su ta roke shi gafara, kema dan Allah sai ki tayata rokonshi" tace "kuma kika ce min ba maganarsa zakiyi min ba" nayi dariya nace "amma ai ba maganarsa dake nayi miki ba, maganar abinda ya faru tsakaninsa da amira nayi miki" ta danyi tsaki tace "ba lallai ne fa ya yafe matan ba, tunda har yanzu bai manta ki ba ba lallai ya yafewa wadda ta raba ku ba" nace "in kika hada su ne zaki tabbatar cewa ya manta dani yanzu, nayi miki alkawarin zaki sha mamaki, bazan miki alkawarin zai manta dani completely ba tunda nima ban manta dashi completely ba amma babu zancan soyayya, an wuce gurin, sai mutunta juna. Duk kanin mu, ni da ke, Ibrahim da Amira, duk mutane ne mu, muna making wrong decisions a rayuwar mu, muna sabawa Allah ma kansa ballantana mutum, amma in muka nemi gafarar Allah sai ya yafe mana, ya sake bamu chance saboda yana son mu chanza mu zama mutanen kirki, ti me yasa mu mutane ba zamu ke yafe wa junan mu ba? Me yasa zamu ke riko a ranmu bayan munsan cewa muma muna so in mun yiwa wani laifi ya yafe mana. Please Amina kiyi kokari kiga Ibrahim ya yafe wa Amira kema sai ki yafe masa ki sake bashi chance" ina kallon sultan ya shigo dakin da takardu a hannunsa ya tsaya yana kallona, Amina tace "shikenan, zanyi magana da Amirar in gani, I will see what I can do" muka ajiyar wayar. Sultan har yanzu yana tsaye yana kallona, am sure yaji ambaton sunan Ibrahim da nayi a waya, na tsaya ina jiran inga reaction dinsa, ya karaso inda nake yace "miss problem solver, kina nan amma kina solving problems din wadanda suke thousands miles away" naji dadi da ya fahimce ni, ya zauna a gefe na ya miko min takardun hannunsa yace "Ummee tayi miki maganar nan?" Na karbi takardun ina dubawa, da sauri na mike zaune sosai ina kara dubawa, na girgiza masa kai nace "bata yi min maganar ba, ta dai ce saboda kai ta fara kasuwancin ta, amma bata gaya min cewa sunan ka ne akan komai ba" dukkan takardun abinda Ummee ta mallaka ne, hatta takardun wannan gidan, da bank account dinta, da takardun dukkan contracts din data karba na shigo da kaya, duk sunan sultan ne a jiki. Na ajiye takardun ina kallonsa, yace "how do I tell her ni bana son kudinta?" Na girgiza kaina nace "mahaifiyar kace sultan, duk abinda ta baka ba faduwa tayi ba kuma kaima in ka karba ba faduwa kayi ba, karbar da zaka yi a ganina shine nuna godiyar ka gareta, inka mayar mata ka nuna mata baka so ba zata ji dadi ba, ka karba amma sai kace mata ka barta a matsayin care taker ta dukiyar taka, ta cigaba da kula da ita kamar yadda takeyi da" yace "to wannan uban cash din kuma da yake banki ya zanyi dashi?" Nace "kudi ne fa, you can do anything with it" ya jawo ni kan cinyarsa yace "ke a shawarar ki me kike ganin ya dace inyi dasu?" Na gyara kwanciyata a kan cinyarsa na danyi tunani kadan sannan nace "why not ka sake gina wata orphanage din, kuma ka bunkasa wacce kake da ita already, kace kana son gina musu makaranta da daukan malamai. Kaga idan kayi haka daga kai har ummee zaku samu lada har karshen rayuwar ku", yana murmushi yace "har ke da kika kawo shawarar" na mayar masa da murmushin nace "yes, har ni dana kawo shawarar". Washegari Ummee ta kaini gidan su zayed na wuni a can Umm zayed me kirki sosai gata wayayyiya, da sister dinsa zahra, na sake sosai dasu muna ta hira da zahra ina vata labarin England, wai tana son zuwa tayi karatu amma an hana ta a gida, muma cikin hira tace "amma kinfi sister dinki kirki, ita bata yiwa mutane magana" nayi dariya nace "ba haka bane ba, Hafsat tana da kirki sosai, kawai dai banbancin halayya ne a tsakanin mu, ni ina da surutu da saurin sabo da mutane ita kuma bata kula mutane sosai, amma in kika saba da ita zaki fahimci tana da kirki sosai. Abinda zakiyi ki lallaba a barki ki je England gurinsu ki dan kwana biyu, zakiyi mamakin kirkin Hafsat" sai magrib sultan yazo ya dauke ni muka koma gida. A hanya yake ce min "yaushe zamu koma Nigeria ne, Takawa yana ta waya wai ya kamata in taho haka nan" nima nayi missing gida sosai, amma nace masa "akwai rigima da ummee kenan" yace "sosai kuwa, dan yadda take ta plans dinta tunani take yi munzo garin nan kenan, ta manta ina aiki a can, besides Takawa ba zai taba barina in dawo nan da zama ba" a raina nace wasa kenan, dan nashi namiji guda daya kamar rai, his only heir, sultan yace "abinda za'ayi yanzu in munje gida, naga kunfi shiri da ita, ki tayar mata da maganar komawar mu Nigeria mu gani abinda zata ce, sai muyi mata bayanin ai ana ta nemana a office din mu sannan kema asibitin da kikayi booking zaki yi antenatal suna nemanki, mu ce mata amma zamu ke zuwa from time to time" na yarda da shawarar sultan dan haka muna dinner na fara maganar, dama sai da na gama jero adduoi sannan na fara magana, tunda na fara ta ajiye spoon din hannunta tana kallona, na duburburce na kasa karasawa, na kalli sultan amma sam yaki dago kansa ya kalleni, tace "yaushe kuka hada wannan plan din? A hanya ko kuma dazu a daki? You are not going anywhere. Me zakayi da aikin a can din? In aikin yi kake so sai ka nema anan ai. Ke kuma wanne antenatal zaki yi wanda ba zaki iya yi anan ba? You are a doctor, kinsan duk abinda kike ji kinsan kuma drugs din da zaki sha, ki rubuta masa sai ya siyo miki, sai menene kuma ake yi a antenatal din? Akwai kanin zayed shima doctor ne anan, ki shirya gobe sai muje ayi miki scanning" na kalli sultan na ga har yanzu baya kallona, nace a raina, wato zura ni kayi dama ka barni ni kadai ko? Ai kuwa muna komawa part din mu na fara sauke masa kwandon bala'i, "shine dazu kaki yin magana ko" yace "dama nasan ba zata yarda ba, I just want to confirm" nace "shine kayi using dina kayi confirmation din ko? I tot we are suppose to be a team" yace "we are a team. Yanzu ni bansan me zance wa Takawa ba idan ya sake kira, dazu daya kira cewa yayi da yasan zamu dade da kema ba zai barki ki taho ba ballantana har in biyo ki. Yanzu me zance masa?" Nace "oho, ni dai ba zaka sake yin using dina ba ehe, kawai dan ace ni ce marar kunya" ya jani muka zauna yana langwabar da kai, "hava love, ba using dinki nayi ba, kin san ina jin kunyar ummee ba zan iya yi mata musu ba shi yasa nayi shiru. Ina son komawa Nigeria amma kuma bana son inyi hurting ummee" na danyi tunani sai kuma nayi murmushi nace "then tell Takawa the truth, ka gaya masa ummee tace ba zamu dawo ba anan zamu cigaba da rayuwa har illa masha Allah" ya dan yi shiru sai kuma ya fara dariya, yace "that means war" nace "then let them have the war, mu sai mu zama 'yan kallo" ya manna min kiss yace "that's why I love you more every day".
Washe gari muka je scanning. Dani da Sultan da Ummee. Private clinic ne na Ahmad kanin zayed, kusan sa'an sultan ne dan haka muna zuwa suka kama hira, yana da fara'ar sosai da wasa kamar zayed. Tare muka shiga dakin scanning din gaba daya, ya fara min tambayoyi ina amsawa yana tsokana ta, ummee tayi masa bayanin cewa nima doctor ce, yace "shi kenan ma kinga abin yazo da sauki, duk bayanan da zan miki kin sani, sai dai kawai mu duba muga lafiyar babyn shikenan" nace "doctor we don't want to know the sex of the baby" da sauri sultan yace "when did we decide on that?" na harare shi, ummee tayi dariya, nace "kullum yana cewa mace ce ni kuma ina cewa namiji ne, so I tot mu barshi kawai in an haihu magani" sultan yace "no, ban yarda ba, dan kinsan ke zaki yi loosing shi yasa kika ce haka" Ahmad yace "ai ya danganta da kwanciyar babyn, idan babyn ya kwanta yadda zamuga sex din shi kenan in kuma ba haka ba sai mu bari daga baya mu sake dubawa" ni dai na bata rai, dan nasan in aka ga macece sultan in ya saka ni a gaba da tsokana har sai nayi kuka. Ummee taga na bata rai tace "abinda za'a yi, in kaga sex din kar ka fada musu, ni zaka fada wa, ni zanyi deciding me za'ayi dashi" sultan ya fara kunkunin ummee tafi sona a kansa. Doctor Ahmad har da juya screen din dan kar in gani, sam bai daga min riga ta ba, ta cikin rigar ya saka handle din ya kama jujjuya shi akan cikin yana yiwa ummee da sultan bayanin komai, sultan sai washe baki yake yi. Sun fi minti talatin suna kallo, sultan wai bai gaji da gani ba, sai da doctor yace "kai da za'a haifa maka a baka a hannunka ba sai kayi ta kalla ba?" Ya rubuta result ya bamu, ya rubuta wani ya bawa ummee. Alhamdulillah komai normal yake tafiya. Daga nan muka koma gida. Washegari doctor Ahmad ya kira sultan wai yana son muje gidan sa mu wuni a can, yana son ya hada ni da matar sa. Matarsa mai kirki sosai, Firdausi, zamuyi kusan sa'anni ni da ita, sai dai ita har tayi 'ya'ya biyu, Amra da Afra, su sultan suka fita suka barmu tare, tare muka hada lunch tana ta yaba methods of cooking dina, bata san cewa da zero nake ba daga baya na koya, muna gama shirya table su sultan suka dawo muka yi lunch tare, nace da doctor Ahmad, "da fatan dai baka gaya masa ba" yace "ai nayi wa ummee alkawari, duk wanda yake so ya sani sai dai ya tambaye ta" nan muka zauna hira akan banbancin al'adun mu da nasu, da yadda zamani yake chanza both al'adun mu da nasu. Ummee ce ta kira ni a waya tace mu dawo gida haka nan, na duba agogo naga 4:30, nayi mamaki cewa da tayi mu dawo da wuri bayan hira tana dadi, Ahmad yace bara su biyo mu kawai dama sun jima basu je gidan ummee sun gaishe ta ba. Muna yin packing na lura da motoci da yawa a gidan, ni dai ina mamaki na kalli sultan ya daga min kafada alamar shima bai sani ba, a palon farko muka ga al rataye balloons pink and blue, a kofar shiga palo na biyu an yi decoration an rubuta 'Welcome to the Gender Reveal Party' mamaki ne ya kamamu, dama Ummee party ta shirya mana? Muna shiga kuwa aka dau tafi da sowa, da 'yan'uwan sultan nan kusan duk wanda yake gari yazo, na kalli Ahmad naga yana mana dariya, wato dashi aka hada baki shi yasa ya gayyace mu gidan sa. Ni dai ba zan iya cewa ga abinda ya faru ba, they are all talking at the same time kuma mostly larabci suke yi, ni dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login