Showing 30001 words to 33000 words out of 262297 words

Chapter 11 - Maimoon Hausa Novel Complete

magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my mother" nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother, this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har bom2 dina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are u ready" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje yayin da tawa take tas. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yaroba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da goggoron akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin na isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "kullum na kira Ibrahim zancen sa Maimunatu tace kaza maimunatu tayi kaza, inna yi masa complain akan baya zuwa mana weekend sai yace ai muna karatu da Maimunatu sun kusa fara exams, kullum zancen kenan, shine nace bara inzo inga maimunatun nan dai da ido na" naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yaroba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, ma'ana babana ne mijin mamansa, sunana Efisowa amma zaki iya kira na Efi, nazo in taya shi assessing sabida nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "ina parents dinki?" Nace mata "suna cikin garin abuja" tace "ku 'yan Abuja ne" nace "'yan jigawa ne mu" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Efi ce dai hankali na bai kwanta da ita ba, duk na damu ganin ta kasa dauke idonta daga kan Ibrahim. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Efi ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon efi alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how do you like my mother" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan efi amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, i feel like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da efi is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da efi. A mincewar mama da baba kawai nake bukata. Please Maimunatu don't screw this thing off. Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Efi get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa.

Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishin Efi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem.

Anan zan tsaya inja hankalin 'yammata har ma da matan auren, idan mace ta nuna tana son mijin ki, musamman idan shi mijin ko saurayin baya son ta, don't make an enemy out of her, ki jata a jikin ki kiyi mata kirki sosai, make sure duk sanda saurayin ko mijin yake around kun nuna mata irin soyayyar da kuke yiwa junan ku, ita da kanta zata ji kunya ta ja baya, amma idan kika kama fishi da fada kamar kina tura shi gurinta ne. Ke kuma budurwa da kike neman miji, kar kiga wata da nata kiyi sha'awa kice lallai sai kin raba. In dai har soyayyar tsakani da Allah yake yi mata to ba zasu rabu bafa.

Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shida Efi, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel.
Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Efi nace "this is my Sister, Hafsat" Efi tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur" nayi dariya, Efi tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank u" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a keda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya?

Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits madu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da mama. Ina shiga na gaishe ta, ta amsa min da sakakkiyar fuska sosai tayi min fada akan karatu, naji dadi har raina, na dauko leda ta na bata nace a kaiwa Abdullahi da Abdulrahman, kananan kannen Ibrahim. Taki karba na ajiye mata a gabanta na tafi.

Da daddare Ibrahim yazo yana ta fada wai me yasa na kashe kudi na sayo kaya? In ina son in basu basai inyi masa magana shi ya sayo musu ba? Shi ya dauka siyowa nayi. Bayan kwana biyu sai gashi da kaya niki niki ya kawo min.

Sanda muka fara SSCE kullum in mun shiga exam Ibrahim zai zauna a kofar hall din ya jira ni, har sai na fito ya tambayeni ya paper sannan zai tafi. A lokacin ya koya min jin kida, zai kunna slow music ya saka ear piece a kunne daya ni ma in saka kunne daya muna ji tare. Shakuwa ce sosai kullum take kara shiga tsakanin mu. Har tararradin ranar da zamu gama paper nake yi. A week to gama papers din mu PC ta kira ni tace federal government ta aiko a bada sunan best student za' a biya mata scholarship zuwa university of her choice. Dan haka tana sanar min cewa sunana zasu bayar. Nayi shiru ina tunani. I don't need the scholarship, daddy zai iya biya min karatu zuwa kowacce kasa nake so. Scholarship is meant for bright students din da iyayensu ba zasu iya biya musu school fees ba. Kawai sai Amira ta fado min a rai. Nan take nace da pc na barwa Amira, asaka sunan ta instead of sunana. PC ta nuna bata ji dadi ba, I am the best student that they ever had a school din. Nace mata to tayi contacting daddy ta sanar masa, duk abinda yace shikenan.

Ana gobe zamu yi graduating Ibrahim ya kira ni yace zamuyi magana. Muna zama na lura he is serious. Yace "Maimunatu in kunje gida ina so zanzo in nemi iznin neman auren ki a gurin daddyn ku" zuciya ta ta buga da karfi na kalle yace "yes, ina so in samu permission dinsu saboda insan in da na dosa, just pray for us"

I hope you enjoy this episode. Put on your seat belts because the next episode is going to blow u away.


Episode Twenty three: The Break up 💔

Alright this is another long episode, nayi deciding zan ke yi da yawa ne saboda we have a long way to go.

Na yi shiru na zuba mishi idanu kamar yadda shima ya zuba min. Can ya dan yi murmushi yace "are you scared?" Na gyada kaina alamar eh. Yayi dariya yace "I am scared too, amma dole muyi haka, saboda inaso in kun koma gida in ke zuwa gurin ki kuma kinga bazan ke zuwa bada iznin daddy ba, it's not right" na sunkuyar da kaina nace Allah ya kai mu.

Washe gari har mukamuka fitar da kayan mu bakin gate banga Ibrahim ba, mun dawo hostel muna sallama da mutane sai gashi yazo bakin gate, daga ganin sa nasan cewa he is not OK. Hafsat ce ta tambaye shi "sir, baka da lafiya ne?" Yace mata "wallahi kwana nayi da zazzabi" nan Hafsat ta saka shi a gaba da tsokana wai dan zamu tafi ne, nima kaina zazzabin nake ji. Muka je bakin gate yace shi ba zai karasa ba, wai ko wanka bai yi ba baya son ya shiga gurin mutane. Nan Hafsat ta barmu ta karasa gate. Tana tafiya ya matso kusa dani yace a hankali "so, finally dai zaki tafi ki barni" nace "ba kace zaka ke zuwa ba" yace "ba dole in zo ba, dan ke fa nake zaune a garin nan, only for you, yanzu ma tunanin yadda zanke yin spending days with out you nake yi." Nace masa "ai zamu ke yin waya" yace "bayan ke baki da waya? Kuma in kinje gidan bakya kirana da wata wayar" nace "ai zan kira ka yanzu" "ban yarda ba, ki bani number mommy kawai" "laa to in ka kira ta me zaka ce mata?' "Sai ince mata son in law dinta ne" nayi dariya, a raina nace lallai wannan bai san wacece mommy ba. A fili kuma nace "Allah da gaske nake zan kira ka" ya marairaice fuska "yanzu tafiya zaki yi ki barni?" Nayi dariya ganin yadda yayi da fuskarsa, yace "au dariya ma kike yi min ko? Duk sanda daddy ya bani permission kullum sai nazo" nace "Allah ya kaimu lokacin" Hafsat naji tana kwala min kira, naga tana dago min hannu, nasan anzo daukar mu kenan. Naki tafiya, sai gata tazo tace in ba zaki tafi ba zanyi tafiya ta wallahi, na kalle ta na dauke kai. Sai tace au kuka zakuyi? Bani phone dinka inyi muku hoton tarihi, kawai sai ya fito da phone din ya mika mata, ta karba ta bude camera ta dauke mu. Na dan kwantar da kaina a kafadarsa shi kuma ya juyo da kansa yana kallona. Hoton yayi kyau sosai. Daga haka Hafsat ta figi hannuna muka tafi, ina jinshi a hankali yace "Maimunatu" amma ban juyo ba ballantana in amsa masa.

Muna zuwa gida muka tarar daddy da mommy sun shirya mana surprise party na graduation, duk kowa yana nan har neighbours an gayyato, ga cake kato da hotunan mu a jiki ni da Hafsat. Nan da nan muka chanja kaya zuwa dogayen rigunan da mommy ta bamu as gift din ta, ta Hafsat pink tawa red. Munyi kyau ba kadan ba, mommy tayi mana light make up. Muka fito muka yanka cake tare da daukar hotuna, nan take naji duk na manta da wani rabuwa da Ibrahim. Muna gamawa daddy ya kawo mana nashi gift din. Muna unwrapping muka ga wayoyi ne sababbi fil kirar Samsung galaxy edge ta Hafsat pink tawa red. Ai ji nayi kamar daddy ya saka ni a aljanna. Muka rungume shi muna murna tare da cewa "thank you daddy". Bayan an tashi daga party muka dawo main palo muka dasa sabuwar hira, muna ta basu labarin makaranta su kuma suna bamu labarin abubuwan da suka faro sanda bama nan. Hafiz ya samu admission shima a Oxford inda zai karanci accounting. Anan daddy yake ce min sunyi waya da PC din mu akan scholarship dina, "is that what you really want" nace eh, yace "to shikenan zance a bata din, Allah yasa haka ya zamar miki sadaqatujjariya" nace "amin daddy" nan ya kara yi mana nasiha akan tausayawa na kasa damu da duk wanda muka ga yana bukatar taimako, wanda duk ya taimaki wani Allah zai taimake shi.

Muna komawa daki da daddare mu ka dauko wayoyin mu muka kunna, dama already an saka mana sim cards a ciki. Hafsat ta dauko address book din da muka karbi numbers din friends din mu ta fara saving a wayar ta, ni kuma number da nake so inyi saving tana cikin kaina. Na zauna nayi dialing, bugu daya ya dauka, sai kuma na kasa magana, yayi ta hello3 can yace "maimunatu talk now, ko so kike zuciya ta ta buga ne" da mamaki nace "ya akayi kasan ni ce?" Yayi dariya yace "nasan babu wanda zai kira ni yayi shiru, wato wayo zaki yi min ko? Ke kina jin murya ta amma ni kinyi min rowar taki ko?" Nace "a'a ba haka bane ba fa. Dama so nake ince maka daddy ya saya min waya" da sauri yace "haba? Amma daddy ya gama yi min komai" nace "ya jikin naka?" Yace "na warke yanzu tunda naji muryarki" na lumshe ido na ina jin dadin kalamansa. Dama Ibrahim da magana a hankali balle kuma ana tsara budurwa a waya. Na kwanta lamo a kan gado na rungume pillow, ina ganin Hafsat tana harara ta ni kuma na murguda mata baki. Kalamai Ibrahim yayi ta tsaro min wadanda nake jin su har 'yan yatsun kafata. A haka har bacci ya dauke ni. Da assuba karar waya ta tashe ni, da kyar na bude ido na na duba naga number Ibrahim, tunda banyi saving ba. Ina dagawa yace "a tashi ayi sallah sleepy head" cikin bacci nace "na tashi ai" yace "aa, ban yarda ba, ki shiga toilet ki kunna ruwa inji tikunna" na tashi na shiga toilet na daga sink sannan ya kashe wayar.

Haka rayuwa tacigaba da kasance mana ni da Ibrahim, kullum muna makale a waya. Wannan yasa na rage zaman falo sai bedroom. Da naji mommy ta taho kuwa sai in kashe wayar. Babu abinda Ibrahim bai tsara min ba, ya gama tsara mana rayuwar mu kaf, tun daga design din gidan da zamu zauna, 'ya'yan da zamu haifa, yace duk so yake su yi kama dani amma mazan suyi tsahon sa. Ni dai sai dai inyi dariya ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login