Showing 207001 words to 210000 words out of 262297 words

Chapter 70 - Maimoon Hausa Novel Complete

ina ganinta gabana ya fadi, nayi ta kallonta ina tunanin dawa take yin kama? Kawai sai da tayi murmushi na gane sultan ne, kuma na tuna cewa mamansa balarabiya ce, amma ban tambaye ki sunan ta ba" na sauke ajjiyar zuciya nace "Sunan ta khairat" da sauri Hafsat tace "Allah da gaske? Moon ita ce mamansa kenan?" Nace "I don't know Hafsat, amma baki ganin tayi yarinta da yawa?" Tace "ke dalla can hutu ne fa, kinga sisters dinta data girma kuwa?" Nace "amma me zayed yace miki a dangane ta ita? Ta taba aure a nan ko kuma ya labarinta yake?" Hafsat tace "it is all mysterious Moon, zayed bai san komai a kanta ba, da yake shi kinsan ba'a Riyadh ya tashi ba kawai abinda ya sani shine rayuwar ta take yi ita kadai bata shiga mutane, kuma tunda ya santa bata da aure" na danyi shiru ina tunani nace "please Hafsat can you get her to talk to you?" Hafsat tace "I think so, kinsan hali na da bin kwakwkwafi, kuma daga gani na ta fara sona bansan dalili ba, ga kuma khairat mai sunan ta" sai kuma tayi shiru sannan tace "wai dama sunan ta kika sakawa khairat" na danyi dariya nace "eh sunan ta ne" Hafsat tace "Munafuka, shine kika saka wa yarinya ta sunan surukarki ko?" Nayi dariya nace "to ai gashi nan kema maybe surukar taki ce" Tace "show sultan the picture ki ji abinda zai ce, ni kuma zan fara tambaya inji labarin ta, ko a gurin ummeen zayed ne, daga nan sai mu gane ko ita ce ko ba ita bace ba" na danyi shiru sannan nace "Hafsat bama tare da Sultan yanzu" kamar bata ji sosai ba tace "what?" Na ce ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona "ina gida yanzu" tace "subhanallah Moon wannan wanne irin muguwar magana kike fada min hakan? Sultan din tafiya yayi kika zo gida?" Nan hawaye ya balle min nayi tayi, tana jina bata ce min komai ba, sai da na gama dan kaina sannan na fara bata labarin abinda ya faru gaba daya, na kara da cewa "Hafsat ban san ya zanyi ba, Sultan zafin zuciyarsa yayi masa yawa Hafsat, shima Ibrahim ban san me yake so inyi masa ba, nayi aure kuma ina ruwansa dani?" Hafsat tace "to ai ni sultan yayi min dai dai, cin ubansa ya kamata yayi yadda gobe in ya hango ki a guri da gudu zai fita. Yanzu kina nufin akan Ibrahim din kika baro gidan mijinki?" Nace "Hafsat ba'a kan Ibrahim bane ba, akan Sultan ne, akan bakar zuciyarsa, Hafsat kisan kai fa yayi niyyar yi, da Ibrahim ya mutu me kike ganin zai faru da shi? Me kike ganin zai faru dani? Sannan zargin da yayi min shi yafi komai kona min rai, he should have trusted me" Hafsat tace "tayaya kike tunanin zaiyi trusting dinki bayan ko cikin da kike dashi baki gaya masa ba? Idan da ace yasan da cikin da duk haka ba zata faru ba, idan kakar chocolate kike so zai fita ya sayo miki, in ma ya ganki da Ibrahim din yasan ba purposely kika hadu dashi ba. Idan kika yi la'akari da rayuwar sultan dole yana da trust issues, he is scared of loosing you, gani yake yi kamar kowa is against him" nace "amma Hafsat, upon all what we went through together, ya kamata ace by now ya yarda dani" tace "kin bashi reasons din da zai yarda da ke ne? Mun jima muna tattauna wa da Hafsat a waya, ban ankara ba kawai sai naji wayar ta mutu, ban kunna ta ba kwanta ina lissafa maganganun Hafsat a raina, is what happened my fault? Ban boye wa Sultan maganar cikin nan saboda komai ba sai don ina son inyi surprising dinsa, but I get more than what I bargain for. Naji an fara kiraye kirayen sallah dan haka nasan inna ce zan kwanta bacci zanyi missing din sallah asuba, dan haka na saka phone dina a charge nayo alwala nazo na bude al'qurani na na fara karatu, ina nan har akayi assalatu nayi sallah sannan na kwanta, kafin bacci ya dauke ni na yanke shawarar cewa first thing in the morning zan nuna wa Daddy picture din da Hafsat ta turo min, tunda ya san mahaifiyar sultan zai iya tabbatar min idan itace ko a'a, next thing zan kira Sultan inji halin da yake ciki, my heart can't take hurting him. Amma ga mamaki na ban farka ba sai after 11am, kuma nasan physical and mental exhaustion ne ya kawo min dogon baccin. Ina tashi na kunna wayata, ko wanka banyi ba na saka hijab dina na tafi neman Daddy, a palon sa na same shi shida Mommy, na karasa na gaishe su, Mommy tace "yanzu nake tunanin ko tashin ki za'ayi kichi abinci, sai Daddy n ki yace a barki ki tashi da kanki" na danyi murmushi ina searching picture din da Hafsat ta turo a waya ta, food is the last thing on my mind babu abinda nake so irin inga Sultan, maybe I am weaker than I thought in dai akan soyayyar Sultan ne. Ina samo picture din na karasa gaban Daddy na mika masa nace "Daddy kasan wannan?" Ya karbi wayar daga hannuna sannan ya mike zaune daga kashingiden da yake, ya kalleni sannan ya kuma kallon screen din yawar yace "a ina kika samu hoton khairat? An ganta ne?" Ji nayi wani excitement yana taso min tun daga kafafuwana har cikin kaina, nace "Daddy ita ce mahaifiyar Sultan?" Yace "of cause itace mana, baki ga kamar ba?" Da sauri Mommy ta matso tana kallon hoton tace "Allah mai iko, kamar tasu har ta baci" na tashi da sauri na rungume Mommy ina jin dadi, sai kuma naji kunyar ta na sake ta, Daddy ya tambayeni inda na samu hoton nayi masa bayani, nan suka kara wani mamakin, ikon Allah kenan, wai all this while a she sultan da Zayed 'yan uwa ne babu wanda ya sani. Mommy tace "to yanzu menene abinyi? Zaki gaya masa ne ko zaki bari Hafsat tayi bincikenta a can muji dalilin da yasa duk tsahon wannan shekarun bata nemi danta ba?" Na girgiza kaina , a raina nace "not again, na daina boyewa sultan komai insha Allahu" a fili nace "Mommy zan gaya masa, yana da right ya sani, shi zai yanke decision din me ya kamata yayi" Daddy ya amince, yace "amma ai naga jiya kin kore shi, yanzu kiransa zaki yi? Na dan sunkuyar da kaina ina murmushi, Mommy tace " kar dai kice min shikenan har kin gama horon nashi da zaki yi? Duk kurin zubar da ciki da waye har ya kare kenan, kar ki rako mata mana maimunatu" na rufe fuskata da hannayena, Daddy yace "in kin huce ma ni ban huce ba, sai yazo ya bada hakuri kuma yayi min alkawarin irin haka ba zata kuma faruwa ba. Shi kuma wancan har yanzu fa bai dawo haiyacinsa ba, dan haka nasa anyi wa family dinsa waya a can ibadan an gaya musu halin da yake ciki" bance komai ba saboda bazan iya yiwa Daddy musu ba amma ni kam da zai barni da yanzu zan tafi in kira sultan in bashi labarin mahaifiyarsa, maganar Ibrahim kuma naji babu dadi, it is a pity, naji tausayin mamansa da 'yarsa, a raina nayi masa addu'ar samun lafiya, Daddy yace "ko zaki je ki duba jikin nasa?" Nayi saurin girgiza kaina, there is nothing more between me and him, ni yanzu kawai mijina nake son gani.
Jin basu sake cemin komai ba na gane sun gama magana dani kenan, na tashi na tafi palo ina neman abinda zanci, na faki ido naga babu wanda yake kallona na dauko waya ta nayi dialing number din sultan, amma bansan me zance masa in ya dauka ba, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, a raina nace yayi fushi shima, nafara duba messages wai ko ya turo min message ban sani ba, babu message din sultan sai na Amir, na buda na fara karantawa "your husband is sick, kuma ke yake nema" wayar ce ta zame daga hannuna ta fadi kasa, nima na bita na zauna dabas a kasa, for seconds kaina ya toshe, sannan kuma cikin karkarwar hannu na dauki wayar zuciyata tana wani irin bugawa na kira number din Amir, bugu biyu ya dauka yace "Moon ina kika shiga tun safe ina ta nemanki wayarki a rufe. Muna asibiti da Sultan fa bashi da lafiya" cikin muryar kuka nace "Amir me ya samu Sultan? Ya jikin nasa? Amir na shiga uku" yace "baki shiga uku ba Moon jikin Sultan da sauki, dazu dai babu yadda yake amma yanzu ya samu relief, please amma ki zo yanzu in ya ganki zai kuma jin dadi" na saki wayar na dora kuka na daga inda na tsaya, Sultan babu lafiya amma ni ina gidan mu bana tare dashi, kuma am 100% sure cewa ciwonsa dalilin maganganun dana gaya masa jiya da daddare ne, ni maimunatu na shiga uku, in wani abun ya sami sultan I will never forgive myself. My Darling Sultan. He calls me his love but I didn't act like love, bashi da kowa sai ni and I too pushed him away. What have I done? Amina ce ta sauko ta ganni ina ta rusar kuka ta karaso da sauri tana tabani tace "Moon lafiya? Jikin ne?" Ban bata amsa ba ta koma sama da sauri sai gasu tare da Mommy, Mommy hankalin ta a tashe tace "Moon lafiya" na share hawayena nace "sultan ne bashi da lafiya, yana asibiti" tace "kuma dai? Astagfirullah, Allah in laifi muka yi maka ka yafe mana".
Da kyar Mommy ta matsa min nasha tea kadan, shima ina gama sha nayo mata amansa, tunda na samu ciki ban taba amai ba sai ranar nan. Ni duk burina inga Sultan in san halin da yake ciki, duk wani abinci da maganar ciki ne dani su biyo baya, a gurina lafiyar sultan itace a sama. Ganin yadda na tashi hankali na ya saka Mommy tace mu tafi tare da Amina, in an jima ita sai su zo tare da Daddy, ai kam ban jira komai ba nayi gaba, Amina ma a mota ta same ni, muna zuwa asibitin Amina ta kira number din amir ta gaya masa munzo, ya fito yayiana jagora zuwa dakin da sultan yake.
Tun daga window na hango shi a kwance yana bacci. Nayi sauri na bude kofar na shiga. Shi kadai ne a dakin, babu riga a jikinsa amma an lulluba masa bargo har saman kirjinsa, gani nayi ya rame sosai, fuskarsa tayi fari tas. Duniya kenan, wai sultan ne ciwon kwana daya yayi masa wannan kayarwar. A hankali na karasa na dauki hannunsa na rike a nawa, muryata har ta dashe saboda kukan da nakeyi. Amina ta karaso ta dafa ni tana bani hakuri amma ko kallonta banyi ba. Ni kadai na san me nake ji a raina. Ba wai ciwon sultan din ne yake saka ni kuka ba, abinda yafi damuna shine kasancewar nice sanadiyyar ciwon nasa shine abinda yafi damuna. Ban san ma Amina ta fita ba sai dubawa nayi naga bata nan. Na fara yi masa magana a hankali "Sultan ka tashi dan Allah, menene hakan ne wai kai sai kace ba namiji ba zaka wani kwanta ka kama rashin lafiya. Kace ba zaka iya rayuwa babu ni ba, to ka sani nima bazan iya rayuwa babu kai ba, dan Allah sultan ka tashi kace ka yafe min, zuciya ta ba zata iya jurar ganinka a kwance ba Sultan zuciya ta bugawa zatayi in mutu, kaine rayuwata, kaini jinin jikina, kaine mijina kuma uban 'ya'yana. Sultan kayi hakuri, duk abinda na gaya maka wallahi ba da gaske nake ba. Dan Allah ka tashi, sickness doesn't suit you, ga babynmu kuma yana nemanka yana so ku gaisa." Na dora hannunsa akan mara ta na cigaba da cewa "ka ji shi ko? Kwanan nan zai fara motsi, he is going to grow up to be stronger than you, shi ba zai kwanta ciwo saboda sunyi fada da matarsa ba" na dawo da hannun sama na dora fuskata akai hawayena yana bin hannun nasa nace "my poor darling sultan, my sweetheart my honey, my angel my heartbeat, my life my happiness, my husband my babies Daddy" a hankali naga ya fara bude idanunsa, ya sauke su a kaina, they are the same most beautiful eyes I have ever seen, amma sun dan fada ciki kadan, murmushin gefen baki yayi min yace "indai wadannan kalaman za'a ke gaya min in bani da lafiya to kuwa kullum sai nayi ciwo" na saki hannun sa da sauri gaba daya na fada kansa na zagaye wuyan da hannayena ina sake wani sabon kukan yace "ouch, karki ballani mana baby girl, baki san kin zama 'yar lukuta ba yanzu?" Na dan dake shi kadan a kafada nace "kaine dai dan lukuti, mai kwanciya ya kama rashin lafiya kawai" ya saka hannu daya ya dago ni yana kallon fuskata yace "to ya isa haka kukan in ba so kike a baki gado a kusa da nawa ba" na tashi ina goge hawayena, har yanzu idonsa na kaina yace "you look terrible, da wasu jajayen kunburarrun idanuwanki" na dan harare shi nace "in kawo maka madubi ka kalli kanka kaga yadda ka zama?" yace "no, I don't want to see" ya daga bargon jikinsa, naga daga shi sai gajeran wando da singlet, yace "come here, zo in sammiki zazzabi na" ba musu naje na shige jikinsa na kwanta, ji nayi kamar wacce tayi tafiya nai nisa ta gaji sannan ta dawo gida, irin feeling din nan na finally I am home, na sauke ajjiyar zuciya na kara shigewa jikinsa ina jin zafin jikinsa yana ratsa ni, ya dora hannunsa akan marata yana shafawa a hankali, nace "am sorry sultan, for not telling you about the baby, I wanted to surprise you" murya can kasa yace "it is OK" a hankali yace "do you mean all what you just said. Da gaske abinda kika fada min a dakin ki ba da gaske kike ba?" Na girgiza kaina da sauri nace "wallahi ba da gaske nake ba. Am so sorry I said those words" yace "NO, I am sorry, ni nayi forcing dinki ai kika fada min hakan. Am sorry about what I did Nace "it is OK, ya wuce" mun jima a haka, na dauka ma ya koma bacci, sai naji yace "something weird happened da zu. Takawa yazo dubani" na daga kaina ina kallon fuskarsa da mamaki nace "what?" Yace "yes, i don't know me ya faru, amma ina tunanin Amir ne yaje ya gaya masa, sai dai bansan ya akayi yazo din ba, I just woke up and he was here, he held my hand and then he fainted" nace "fainted?" Yace "yes. Komai ya faru ne da sauri bansan menene ya faru ba, yazo nan, ya kama hannuna sai kuma ya suma, suka dauke shi suka fita dashi, sai doctor yazo ya saka na koma bacci, am just not sure whether da gaske abin ya faru ko kuma mafarki nayi" na mayar da kaina na kwantar a kirjinsa ina sauraron bugun zuciyarsa, na danyi tunani kadan akan abinda yace, we will have to ask Amir menene ya faru. Ba tare dana kalle shi ba nima na fara magana "something weird also happened jiya da daddare" nayi shiru kuma na kasa yadda zan fada masa, sai da yayi magana yace "what happened?" Sannan na cigaba da magana "Hafsat ta hadu da Ummeen ka a Riyadh" farko yi yayi kamar baiji me nace ba, sai kuma ya mike zaune da sauri, taking me with him, yana kallona fuskarsa babu alamar dariya yace "me kika ce?" Na jawo yawa ta na bude masa hoton mahaifiyarsa na mika masa, "Sultan wannan itace mahaifiyarka, you and zayed are cousins". A hankali ya karbi wayar yana kallon hoton, emotions fal a fuskarsa.

Episode Eighty Four : Little Love

Ya dago ya kalle ni nayi masa murmushi ya sake kallon hoton sannan yace " then she is alive. All this time ina tunanin cewa bata raye shi yasa bata neme ni ba, amma tana raye ashe, kawai ta ajiye ni tayi tafiyarta, without a second thought" nace "please Sultan kar ka ce haka mana. Baka san uzurin ta ba. Ka bari idan ka samu lafiya sai mu tafi har Riyadh din mu same ta acan, ka gabatar mata da kanka, na tabbatar zata yi maka gamsashshen bayani a dangane da wacece ita" tun kafin in karasa maganar yake girgiza kansa, yace "I will not go, babu inda zanje, haka kawai muje ta wulakanta mu? Kamar yadda ta wulakanta ni ta ajiye ni ta tafi? If she wants to see me ai tasan a inda ta barni, in tana son ganina tazo inda nake" nayi sauri nace "sultan uwa ce fa, kar ka fadi mata maganar da Allah zaiyi fishi damu kuma" yace "ko menene nace mata Allah ba zai kama ni ba. I don't know much about love but naji ana cewa mother's love is the purest of love, hakan yana nufin ya kamata ace sonda take min yafi son da nake miki yawa, ni kuma nasan a yanzu yadda nake jinki a raina rabuwa dake will be the end of me. Ita wacce irin zuciya ce da ita?" Sosai naga ransa ya baci na tuna cewa bashi da lafiya, na karbi wayar daga hannunsa nace "sultan baka da lafiya, let's not talk about this now, in ka samu lafiya sai mu san abinda zamuyi akai" ya jawo ni jikinsa muka koma muka kwanta, ya jawo bargo zai rufe mu, temp dinsa naji da zafi na yaye bargon, ya rabu dani bai tanka min ba sai kara matse ni da yayi a jikin sa, yace "tell me something nice" banyi magana ba na dora hannunsa akan mara ta, yayi dariya kadan yace "yeah, that's a nice topic of discussion" ya danyi shiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login