Showing 246001 words to 249000 words out of 262297 words
koma bedroom dinta. Tana idar da sallah taji karar wayarta, sai da taji kirjinta ya buga, ta mike ta dauki wayar tana saka ran ganin 'sultan's dad' kamar yadda tayi saving number dinsa, amma sai taga number din mahaifiyarta. Ta zauna a bakin gado ta dauka da sallama. Tace mata "ki zo yanzu ki same mu a gidan babanki Umar" daga nan ta kashe wayar. Ta ajiye wayar ta rike kanta da hannu biyu, ya salam, me ya faru kuma? Kar dai ace sun gano cewa sun shirya da Sadiq zai zo gidanta, tasan halin uncle Umar sosai, abu na farko da zai fara yi shine zai karbe gidanta yace ta koma gidansa da zama. Amma kuma sanda ta kai masa sultan ai bai nuna wani abu ba, nuna wa yayi kamar komai ya wuce. Bata da zabi, duk da shekarunta amma bata kinyin abu in iyayenta sun gaya mata. Dan haka ta tashi ta tafi. Babu kowa a kofar gidan dan haka ta shige cikin gidan direct, tana gaisawa da matan gidan suka gaya mata ta shiga palon uncle din nata ana jiranta, ta gyara lullubin ta ta shiga da sallama. Gabanta ne ya fadi ganin mutane da dan yawa a palon, ba tare data tsaya kallon waye da waye ba ta shiga, ta zauna daga nesa akan carpet ta fara gaishe su. Sai a lokacin ta lura da akwai bakin fuska a dakin, ta tsaya da gaisuwar da take yi tana kallon su, duk da sun dan juya bayansu daga inda take zaune amma ta gane shi ta yana yin zamansa, ya harde kafafuwansa ya zauna a kansu, tun sanda ta san shi haka yake zama duk sanda zai zauna a kasa ba'a kan kujera ba haka yake zama, kuma taga sultan ma haka yake zama, Sadiq ne, he is here. Bata gaishe su ba daga shi har abokin rakiyar tasa , ta karasa gaishe da iyayenta ta zauna kanta a kasa tana jiran taji ta ina za'a fara yi mata ruwan bala'i.
Abokin tafiyar Takawa ne ya bude taron da addu'ah, ya nemi zabin ubangiji akan duk maganganun da za'ayi a gurin sannan kuma ya nemi tsarin ubangiji daga shaidan da mukarrabansa. Yana gamawa Takawa ya fara magana cikin larabci da jefi jefin turanci, yace "sunana Sadiq Abdallah. Ni bakar fata ne mutumin kasar Nigeria. Ni tsohon mijin 'yarku ne Khairat kuma ni ubane a gurin tilon danta, Abubakar. Nazo ne gabanku yau ina neman afuwar ku akan abinda na aikata na rashin kyautawa a gare ku shekaru talatin da uku da suka wuce, sannan ina neman alfarmar a mayar mana da auren mu ni da matata idan kun amince" ya juya ya kalle ta cikin ido, yace "idan itama ta amince" shiru dakin yayi na tsahon lokaci. Khairat kam gaba daya kanta ya toshe , what is he doing? An jima bayan ya gama uncle Umar ya fara magana wacce take cikin larabci mai chakude da turanci "assalamu alaikum. Babu abinda zan iya cewa yau sai Alhamdulillah. A lokacin da Sadiq yazo neman auren khairat a gurina yazo ya nema, amma a lokacin na shafa wa idona toka ba tare da na bashi dama ba nace bazan bashi ba, saboda ina ganin zai zama abin kunya mu aurar da 'yar mu ga wanda ba balarabe ba, ban duba cewa a cikin abubuwan da ubangiji yace a duba kafin a bayar da aure babu kabila ko kalar fata ba, na tauye hakkin sji Sadiq din sannan kuma na tauye hakkin ita khairat din, dan haka zan iya cewa duk abinda ya faru nine sila, saboda na tsallake tsarin addini nabi son raina, wannan shine ya jawo 'yar mu ta bijirewa umarnin mu tabi saurayi ta gudu daga kasar a wancan lokacin, tun a lokacin nasan cewa laifi nane amma pride ya hanani inyi admitting, sai muka tattara laifin duk muka dorawa shi yaron da yazo ya dauke mana yarinya, muka sha alwashin sai munga bayansa. Abin kunyar da nake gudu kar ace mun aura wa 'yar mu wanda ba balarabe ba sai ya zamanto gwara shima akan abin kunyar da muka fuskanta, cewa 'yar mu ta gudu ana gobe daurin aurenta ta shiga duniya. Wannan yasa muka kara kaimi gurin nemansu dan muga mun goge mugun suna a gurin mutane, kuma amma bamu same suba sai bayan shekara uku, sai a lokacin muka fahimci shima yaron dan babban gida ne, jinin sarauta ne, amma duk da haka maimakon mu zauna ayi maslaha sai muka dauki damarar sai mun nuna masa kuskurensa, muka je har gidan aurenta a gaban surukanta da mijinta muka dauko ta, muka raba ta da mijinta muka kuma rabata da dan jaririn danta. Amma Allah shine shaidar mu, bamu taba tsammanin raba sun da mukayi zai tabbata ba, mun raba su ne saboda mu hukuntasu a bisa abinda suka aikata, tunda har 'da ya shiga tsakanin munyi niyyar zamu hakura mu barsu. Amma sai yazo ya same mu ya bamu hakuri kuma ya nemi aurenta properly yadda kowa zai tabbatar cewa aurar da 'yar mu mukayi ba wai duniya ta shiga ba. Munce zamu hukunta shi idan yazo, amma mun san duk wanda yake da courage din shiga gidan mutane ya dauki 'yarsu ya gudu da ita to tabbas yana da courage din fuskantar hukunci a kanta. Amma kuma sai muka tarar da sabanin hakan, maimakon yazo din kamar yadda muka saka rai sai ya aiko mana da takardar sakin ta. Wannan shine abinda yafi komai kona mana rai, mu ana babban cin mutunci shine a auri 'yarka sannan kuma a sake ta. Ga kuma tashin hankalin da yarinyar ta shiga a dalilin sakin da akayi mata, da raba ta da danta da akayi. Tayi ta kokarin komawa amma muka hana ta saboda mu a gurin mu zubar da darajarta ne ace ta koma gurinsa duk kuwa da sakin ta da yayi, pride din mu ya saka muke ganin cewa shi ya kamata ya neme ta ba ita ba. Shi ya kamata yazo ya bata hakuri, ya bamu hakuri gaba daya. To Alhamdulillah yanzu gashi yazo, kuma ya bamu hakurin, kuma mun hakura, sauran magana kuma ta rage tsakanin sa da ita, in ta amince shi kenan ko a gobe sai a mayar musu da auren su".
Tunda aka fara maganganun, khairat kanta yana kasa, tana wasa da 'yan yatsunta, ji take tamkar mafarki take yi amma kuma gashi kamar gaske. Bata dawo daga tunanin taba taji ana ta fita daga palon, zata tashi auntyn ta tace "ki zauna kuyi magana tukunna, zuwa gobe sai ku fadi shawarar da kuka yanke" ta koma ta zauna zuciyarta tana bugawa, tayi sauri tayi wa kanta fada "why are you behaving like a teenager? Ke da za'a haifawa jika very soon?" Nan take ta maida hankalinta guri guda ta juyo tana fuskantar Sadiq da abokin tafiyarsa, sai yanzu ta kalli abokin Sadiq din sosai, he looks familiar, and he also looks like maimumatu and Hafsat, shi ya fara gaisheta, ta sunkuyar da kanta kasa ta gaishe shi itama, ya amsa, sai kuma suka yi shiru, ya mike tsaye yace da Takawa zai jira a waje, har yakai bakin kofa tace "You are Maimumatu's Father, right?" Ya juyo yana murmushi yace mata "that's right" tayi dariya tace "Ina Fatima? Ya baku taho tare ba?" Yana murmushi yace "zata zo itama, maybe daukan amarya zata zo, tunda ni nazo daurin aure" sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta, shi kuma ya fita. Sun jima bayan ya fita babu wanda ya ce komai, sannan Takawa yace "so..., Fatima zata zo daukan amaryar a gaya mata ta shirya ko kuma ba zata zo ba a gaya mata tayi zamanta?" Ta dago suka hada ido, he looks just as she imagined he would, older, stronger and very confident, but then he is still the Sadiq she knows, the Sadiq she fall in love with, her husband, the father of her son, it feels like not a single day has passed. It feels like kamar dazu ne aka tashe su daga bacci aka ce su je ana kiransu a palon Takawa marigayi.
Sati daya chif bayan nan aka mayar da auren Sadiq Abdallah da Khairat Faisal Abdallah. Daurin auren ya samu halartar kafatanin 'yan'uwa da abokan arziki daga barin khairat, a bangaren Sadiq kuwa jirgi guda aka chika da manyan mutane daga Nigeria suka je suka halarci daurin auren. Abin ya kayatar sosai. A take mujallu da jaridu na duniya suka yi ta watsa labarin auren saboda ana ganin wani karin kulla zumunci ne a tsakanin kasashen musulmai. Wannan tamkar wani ci gaba ne ga musulunci da musulmai baki daya. Ana gama daurin aure ango ya dauki amaryarsa suka tafi umra dan nuna godiyar su ga ubangiji akan dawo musu da rayuwarsu da yayi, da kuma neman taimakonsa akan dukkan abubuwan da zasu saka a gaba. Sai da sukayi sati biyu sannan suka dawo Riyadh, daga nan kuma amarya ta fara shirye shiryen biyo angonta Nigeria amma shi kam ango yace ba zai jira wannan fi'ilin sai amarya ta tare ba dan haka shi kawai sai ya tare a gidan amaryar. Ajjiyar da aka yi masa ta three full decades ya zage yake ta karba. It is like nothing has changed, jin su suke kamar sanda suna America farkon auren su. Duk abinda suke kuma hankalinsu yana kan sultan, suna keeping tabs on him. Sai da aka kammala gyaran gidan da Takawa ya saka ayi masa sannan amarya ta tare. Kamar yadda Daddy yayi alkawari, Mommy ya bawa private jet dinsa suka taho tare da Nani da wadansu zababbun mata daga fada suka dauko amarya daga Riyadh zuwa Nigeria. Wannan shi ya kara dankon zumunci tsakanin Ummee da Mommy.
Episode Ninety Seven : The Real Prince
Bikin Amir aka fara. Babu abinda Ummee da Takawa basu yi masa ba. Duk wani gata da 'da yake nema a gurin iyayensa Amir ya samu a lokacin bikinsa, sanda za'a tafi dauko amarya Ummee hana ni zuwa tayi, tace maiduguri yayi nisa bazan je ba, amma sanda aka kawo amaryar direct fada aka kawo ta gurin Ummee, ni kuma ina zaune a hannun daman Ummee. Sai a lokacin naga abinda Amir yake yiwa naci, ba wai kyau ne da yarinyar na kuzo mu gani ba, a'a, nutsatstsiya ce sosai, kana ganin ta kasan she is well brought up, har cikin raina ina kyautata zaton cewa Amir yayi dacen mace ta gari insha Allah. Washegarin da aka kawo Aisha, ni da Sultan muka shirya musu dinner. Takanas na kira saratu da fa'iza suka taya ni organizing dinner din, a cikin fada muka karbi hall akayi, sultan ya zuba kudi sosai, kuma abin ya kayatar sosai. Bayan an tashi daga dinner Amir ya sake kawo min Aisha har gida muka sake gaisawa. Haka kawai naji ta kwanta min a rai.
Saratu da Fa'iza kam by now sun fahimci cewa auren iyayensu ya rabu amma bana jin sun san dalilin rabuwar auren. Ba laifi sun dangana, dan suna yiwa Ummee biyayya dai dai gwargwado, Ummee kuma kullum tana jan su a jikinta, dan komai zatayi sai ta hada da daya daga cikin su. Abbas har yanzu basu shirya da Hajiya ba, dan har yanzu anan gurina yake komai nasa. Yaji shawarata kuwa, dan ya koma makaranta, shi da kansa yaje ya nemarwa kansa admission, saboda sunan Takawa da yake amfani dashi bai sha wahala ba gurin neman admission aka bashi, tunda ya fara zuwa makaranta ya tattara harkar sarautar ya ajiye a gefe ya rungumi karatunsa. Dama ashe ba wai so yake ba tunda ba'a jininsa take ba, kawai dai dan ana matsa masa ne shi yasa yake yi. Ya nuna min rashin jin dadinsa game da kafsa masa da Amira tayi, ni kuma nayi masa alkawarin zan samo masa mata wacce tafi Amira komai.
Na sami wani private hospital mai kyau, likitan su kwararre ne a harkar gynecology, nayi booking anan zan haihu. Sun yi min aune aunen duk daya kamata suyi min kuma sun gayamin zanke zuwa duk sati ana dubani, tunda yanzu edd na saura sati uku ya cika. Likitan yayi noticing high bp na, kuma mun zauna munyi magana dashi akan irin kalubalen da zan iya fuskanta. Na riga na sani, tun sanda na samu ciki, amma so far Alhamdulillah, dan lafiya lau nake bani da wani problem in banda bp din da take high. Rannan muna palona ni da sultan, ina zaune akan kujera shi kuma yana kwance akan kujerar ya dora kansa akan cinyata muna kallo, na saka hannuna absently ina shafa gashinsa, ina jin cikarsa da laushinsa, nace "wannan gashin dai ya kamata a rage shi, in ba haka ba zan fara yi maka kitso" ya danyi dariya yace "bismillah" na fara tsagawa da hannuna ina kitsawa, yace "ouch, da zafi fa" nace "kar ka bada ni mana, ka tsaya inyi maka mai kyau" ya biye min kuwa ya tsaya, nayi ta jagwalgwala masa gashin, nayi masa kitso guda biyar, ya tashi zaume yana shafa kan ni kuma ina tayi masa dariya, shine har da zuwa bedroom ya kalla a madubi, ya dawo ya tsaya yana kallona yace "da ace ni macene da maza sai sun bi layi sannan zan zaba" nayi dariya ina kallonsa nace "Allah yasan nufin jaki shi yasa bai bashi kaho ba" ya koma daki sai gashi da comb ya dawo ya kwanta ya dora kansa a cinyata yace "tsefe min" na karbi comb din ina tsefe masa ina tajewa. Yana kwance yayi shiru kamar mai bacci amma ba baccin yake ba. Na fara magana "I fell in love with you the second time I saw you" ya gyara kwanciyarsa yayi rigingine yana kallona yace "a dinner din Hafsat?" Na girgiza kaina nace "A Hilton" ya dan bata rai alamar tunani yace "that's the first time" na girgiza kaina nace "no, it is the second. The first time dana fara ganin ka a TV ne. Kuna fada da wani akan titi 'yan jarida suna dauka, daga baya aka kirawo police suka zo suka kama ku, they handcuffed you and you were smiling, it was as if you were enjoying yourself" ya danyi murmushi yace "I was" na cigaba "wannan shine dalilin da yasa sanda muka hadu a Hilton, duk da cewa naji wani abu a zuciyata game da kai amma sai na baka wrong information, saboda a lokacin na riga na saka a zuciyata cewa you are a bad person. But my love for you is too strong. A hankali na fara gane ainahin ko kai wanene and the love I have for you grow stronger" duk maganar da nake idona yana cikin nasa hannuna kuma yana kan fuskarsa ina shafawa. Na cigaba "a lokacin burina akan ka gida biyu ne, na farko shine in aure ka, kuma Alhamdulillah, wannan burin nawa ya cika" wani tattausan murmushi yayi min, ya daga gira yace "and how does it feel?" Nace "what?" Yace "how does marrying me feel?" Na mayar masa da murmushinsa nima nace "great, really great, better than I imagined it would" yace "good. Then what is your second wish?" Na danyi shiru ina tunanin ta yadda zan gaya masa ba tare da yayi wa abin wata fassara ta daban ba, nace "burina na biyu shine ina so mutane su sanka kamar yadda na sanka" ya dan bata fuska yace "bangane me kike nufi ba?" Nace "Mu mutane muna da wata halayya, abinda duk muka fara gani ko ji a dangane da wani shine abinda muke rikewa a ran mu, har sai wani abin ya faru da zai chanza mana ra'ayin mu. Ka tuna ranar da na ganka a hanya ka tare hanya da motar ka ka hana mutane wucewa?" Ya danyi murmushi yace "Of cause I remember" nace "a lokacin mutanen da suke gurin gaba dayansu babu wanda yake fadin abin alkhairi a tare da kai, wani a gurin bai ma taba ganin ka ba, dan haka abinda yaji an fada a gurin shine abinda shima zai tafi yana fada a gaba. Wannan misali daya kenan, na tabbatar akwai examples da yawa na irin wadannan abubuwan da suka faru tsakanin ka da mutane. Yanzu da ace zaka yi baddakama ka fita cikin mutanen gari kayi musu tambaya a game da kai nasan da zaka sha mamakin amsoshin da zasu baka. Na san ka chanza, wadanda suke tare da kai ma duk sun sani, amma sauran mutanen gari fa? Ta yaya zasu sani?" Yace "I don't care about mutanen gari. I never care about what people say akaina" nace "but I do. It has always been my dream to clear your name. To make people know you and love you" yace "what are you going to do then? Are you going to change their minds?" Nace "No, but I will do something that will create something that will make them change their minds" ya dan dauke kansa daga kallona yana kallon side, na saka hannu na juyo fuskarsa gurina nace "please sweetheart" yace "Maimunatu bana son kije kiyi abinda zaki shiga trouble a kaina. We are happy the way we are." Na langwabar da kai nace "nayi maka alkawarim abinda nake son yi babu trouble a cikin sa, ina cikin gidan nan zan yi ba tare dana fita ko gate ba. Please just say yes" kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "OK. Amma duk abinda zakiyi sai na sani tukunna" na sunkuya nayi kissing dinsa a goshi nace "Thank you".
Na riga na gama tsara duk abinda nake so inyi, dan haka washe gari tun da nayi sallar assuba ban jira sultan ya dawo daga masjid ba, na fita na tafi dakina. Na dauko laptop dina na dube project din da nayi akan sultan. Na zauna na fara editing, nayi summarizing ya zama page daya kawai, sannan na kara abubuwan da nayi learning recently akan sultan. Sai da na gama kuma sannan nazo na fassara da hausa. Sai ya zama kamar ace front and back ne, front din turanci back din hausa. Sai dana gama sannan kuma nazo na zauna na sake redrawing