Showing 69001 words to 72000 words out of 262297 words

Chapter 24 - Maimoon Hausa Novel Complete

kama rigarsa in rike ina kuka shi kuma yana ture ni har sai na fadi sannan yayi tafiyarsa. Kakana lokacin shi zai daukeni yayi ta rarrashina. Gata kam a lokacin na gani, duk abinda nake so shi za'a yi min, babu wanda ya isa yayi min tsawa ko fada koda kuwa Yaya ce (yaya itace kakata wacce ta haifi babana), dan haka na taso a sangarce, babu mai sani babu mai hana ni, wani lokacin sai in zauna inyi ta kuka ince ni gurin mommy na da daddy na zanje ko wanne yaro yana gurin iyayensa banda ni, a irin wadannan lokutan ne marigayi sarki ya dauke ni ya kaini orphanage ya nuna min yaran gurin yace 'kaga wadannan yaran su basu san uwarsu ba basu san ubansu ba, basu san kowa a dangin su ba, kai kuma kasan babanka, kasanni ni kakanka, kasan dukkan danginka na gurin babanka to kamata yayi ka godewa Allah', a orphanage din na hadu da Amir" na kalleshi da sauri ya gyada min kai "yes, Amir is an orphan. Babarsa tana haihuwarsa ta dauke shi daga shi har mahaifarsa ko cibiya bata yanke masa ba ta ajiye shi a kofar orphanage ta gudu. Kakana shi ya rada masa sunansa Abdallah shine ake ce masa Amir. Sanda yake kaini orphanage ya hada ni da shi, tun a lokacin muke abota da yake shima fitinanne ne iri na, daga baya in zamu taho sai yayi ta kuka yace sai ya bi mu, sai kawai kakana yayi adopting dinsa ya saka mu a makaranta tare, komai tare muke yi dashi har yau. Lokacin da kakana ya rasu ne rayuwata ta chanza gaba daya, I was ten years old then, nayi ta kuka akayi ta rarrashi na naki hakura, Takawa yana zuwa ya kama ni ya daure min hannu da baki na ya saka ni a dakina ya rufe kofar. Haka na kwana ina kukan zuci babu bakin yin kukan ga uban dauri da nasha, sai washe sannan ya aiko aka kunce ni kuma yace in na sake kuka sai ya kuma daureni. Daga ranar nasan na rasa soyayya a rayuwata. Hankali na bai kuma tashi ba sai da aka nada babana sarki, ya dauko iyalansa wadanda ko saninsu banyi ba tunda baya bari inje gidansa ya dawo palace. Ni na riga na saba duk abinda nake so shi zanyi, tun da ya dawo gidan kuwa sai ya zamana duk abinda nayi no matter how small ba zai yi min fada ko nasihaba sai dai ya saka dogaran sa suyi ta dukana, wani lokacin har Amir za'a hada a daka koda kuwa ni kadai nayi laifin. Daga lokacin muka fara koyon fada ni da Amir, in an saka a dake mu sai ya zamana suna dukan mu muna ramawa. Bayan na karasa primary school, Rannan na tambayi Yaya nace dan Allah ta saka a kaini gurin babata sai tace min itama bata san inda take ba, na tambayeta ko ta san dalilin da yasa iyayena duka rabu? Sai tace min saboda ayi protecting family name. Lokacin ina yarinta ban fahimci maganar ta sosai ba. Lokacin Takawa ya sai wata sabuwar mota kawai sai na dauki fenti na shiga garage dinsa na rubuta 'fuck the family name, I want my mother', nasan abinda na aikata dan haka naje na shirya, na saka duwatsun wuta a cikin safa ta na hada da hannuna wanda na daure da karamin towel na daure, neman kawai wanda zan huce temper ta akansa nake yi, ai kuwa sai dashi an turo wani dogari mai tsautsayi akan ya zo ya dake ni, da na dage na fara naushinsa da hannuna mai duwatsun nan har sai da naga baya motsi, haka aka kwashe shi sai asibiti. Washe gari takawa ya kirawo ni yace "tunda ni ka gagare ni zan tura ka inda za'a koya maka hankali" shikenan abinda yace min, babu Sultan me yasa kayi haka? Babu Sultan ya kamata ka dena haka. Kawai ya saka mu a jirgi ni da Amir sai lagos, gidan kangararru. Wasu iyayen suna ganin gidan kangararru a matsayin gidan da zai gyara musu 'ya'yansu basu san cewa kara kangarar da yara yake yi ba. Sanda ya kaimu na tambayeshi 'why?' Amsar da ya bani shine 'to protect the family name'. Babu abinda ban koya a gidan nan ba, babu abinda ban iya ba, acan na hadu da most of the gang bangs, iyayensu sun kasa basu tarbiyya sun turo su nan. Shekarar mu biyu acan uncle dina galadima yaje a fito damu, yana kawomu gida Takawa kallo daya yayi mana yace ba'a gidan sa ba, a lokacin ne Hajiya ta kira ni dakinta ta ce min zata saka a kaini America a saka ni a makaranta amma sai na mata alkawarin bazan dawo Nigeria ba zanyi zama na acan. Ni a lokacin gani nake yi me zai dawo dani Nigeria tunda babu wani abu da na bari anan, nobody wants me, not even my mother. Sai a lokacin naga birth certificate dina da sunanta a jiki 'Khairat Abdallah' da signature dinta, sai a lokacin nasan cewa a america aka haife ni, dan haka ina zuwa America asibitin da aka haife ni na fara zuwa ina bincike ko zan samu wani information akanta amma ban samu komai ba. Takawa ya saya min gida ya saya min mota ya cika min account dina da kudi. Babu wanda yayi tsammanin zamuyi karatu da gaske ni kuwa na dage da karatu kawai saboda ina sa ran maybe in nayi karatu he will love me, na gama sec sch na shiga jami'a amma ko sau daya bai je ya ganni ba, sai dai duk kudin da nake so zai aika min. San da na gama first degree dina na shigo jirgi na zo Nigeria na kawo masa certificate dina ya karba ya duba, abinda yace min shine "good for you" daga nan ya jefo min takardata, alokacin ne na fahimci cewa ba wai halina ne baya so ba ni din ne baya so, Hajiya tace min ina alkawarinta nacewa bazan dawo Nigeria ba? Dan haka na tattara na koma America na koma makaranta. A lokacin nayi hankali sosai kuma na fahimci cewa duk abinda ya faru a rayuwata ya faru ne saboda babana yana so yayi protecting his family name, ni kuma na sha alwashin sai na bata family name din nasa da yake ji dash, duk tsiya dai shi ya haife ni kuma duk abinda nayi dole sunan nasa da yake ji dashi za'a ambata. Ina zuwa Nigeria hajiya ta fara tambayar alkawarin mu and I told her to fuck off, nasan abinda take so, bata so na a kusa da sarauta saboda tana son abbas yayi sarauta ita kuma bata san sarauta is the last thing on my mind ba, dan haka na fara bribing dinta cewa in dai har tana bani goyon baya ina yin duk abinda nake so to I will leave Abbas alone yayi ta sarautarsa.

Aikina na architecture yana kawo min kudi sosai, dan haka a yanzu bana bukatar kudin Takawa dan duk abubuwan da nake yi da kudina nakeyi, yanzu ba zai sa a dakeni ba kuma babu yadda zaiyi dani dan haka sai ya koma ignoring dina, nuna wa yake yi kamar bai san dani a duniyar ba amma nasan cewa sakonni na suna isa gurinsa sosai" ya juyo ya kalleni fuskarsa dauke da wani murmushin dana kasa gane kansa yace "to Maimunatu, I opened up to you, babu wanda na taba zama mukayi irin wannan maganar dashi bayan Amir sai ke. This is me. Yanzu zaki iya yin making decisions dinki yes or no" yana gama fadar haka ya mayar da glasses dinsa ya tayar da motar. Har muka je gida babu wanda ya sake cewa komai. Ni a gurina kaina ne ya kulle, I need to digest duk maganganun Sultan kafin inyi fully understanding din labarinsa. Yana packing nayi masa godiya, kai kawai ya daga min na fita. Sai bayan na gama da kowa nayi sallah nayi wanka na kwanta sannan na fara rewinding duk maganganun sultan ina reviewing dinsu. Duk abinda yake yi yana yi ne dan ya bata sunan family dinsa saboda yana ganin basa sonsa kuma sune sanadiyyar gurbacewar rayuwarsa. Yanzu na fahimci dalilin soyayyarsa da yara da taimaka musu ta hanyar gina orphanage da saka su a makaranta, saboda yasan ciwon rashin samun kulawa daga iyaye, yasan maraici duk da shi ba maraya bane. And suddenly I know what sultan wants, what he needs, LOVE.

Na dauki waya ta na duba time na lissafa naga rana ce yanzu a England, nayi dialing number din supervisor na, yana dagawa nace "sir I think I found the subject for my research project"

*what do you guys think is more important, Family or Family name?


Episode Forty Two : Born for This

Sultan ya jima a zaune a cikin motar bayan fitar Moon, shikenan ta faru ta kare, haushin kansa gaba daya yake ji, menene dalilin da yasa ya gayawa Moon labarinsa, yanzu ya tabbatar she will say NO to him, babu wacce zata so ta hada zuri'a dashi. Wannan shine dalilin da tun tuni ya kasa yin budurwa saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan rejection daga budurwa kuma, plan dinsa shine yazo Nigeria yayi destroying name din familyn sa sai ya koma America ya cigaba da rayuwa acan. A plan dinsa babu budurwa ballantana aure, saboda yasan aure zai ruguza masa plan dinsa ne tunda in yayi aure dole zai haihu kuma 'ya'yansa will still bare family name din da yake yaki da. Out of nowhere Moon ta shigo rayuwarsa, kallo daya yayi mata and he is hooked for life dan yanzu baya jin zai iya rayuwa babu ita wanda hakan yasan wani babban yaki ne ya dauko. Yasan babanta sosai, Ambassador M D, a very well respected man, tsakanin sa da ambassador MD tamkar hanyar jirgi ne da ta mota. Koda ace yayi convincing Moon baya jin zasu iya convincing babanta. Babansa kuwa yasan ba zai shiga maganar ba ballantana a duba darajarsa a bashi ita. Ya runtse idanunsa yana jin zafi a zuciyarsa. She means the world to him, he can't loose her. Ya tayar da motar ya fara tafiya. Yayi mamakin kansa dazu, he don't normally talk about himself amma kawai ya zauna ya saki baki yayi ta zuba mata magana kamar wadda tayi masa asiri, yanzu ya yarda da ake cewa Love is the strongest magic of all. Ya tabbatar cewa yau ba zai yi bacci ba.

Ko da yaje gida ya kwanta ma juyi yayi tayi akan gado amma ya kasa bacci. Sanda baccin ya dauke shi kuwa mafarkai yayi tayi na rayuwarsa a baya. Sai wajen assuba sannan a samu bacci mai dadi. Cikin bacci yaji wayarsa tana kara, da magagin bacci ya dauka ya saka a kunnensa ba tare da ya buda number ba "Assalamu Alaikum" yaji ance "wa alaika assalam, a tashi daga baccin nan haka assuba tayi" tuni yaji baccin ya watstsake, ya duba screen din wayar da sauri, Love, ya sake mayarwa kunnen sa yaji an sake cewa "in baka tashi ba zan kashe in sake kiranka har sai ka tashi" a hankali ya furta "Love, is that you?" Daga cikin wayar yaji sautin murmushinta ya lumshe idonsa yana hango fuskarta da dimples dinta, tace "yes it is me, ka tashi kayi sallah assuba tayi" still idanunsa a lumshe ya ce "then you are not dumping me, right?" ta danyi shiru inda bugun zuciyarsa ya karu sannan tace "no Sultan, am not dumping you". Bai san sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba yaji tamkar an cire shi daga ukuba an saka shi a Ni'ima, murya can kasa yace "thank you, i will never let you down".

Na ajiye wayar ina bin screen din wayar da kallo, nasan na debo babban aiki but I can't stop myself, I feel like I was born for this. Jiya na jima banyi bacci ba kuma na yanke shawarwari da yawa, na farko zanyi accepting soyayyar Sultan dan nima ina son shi kuma ina so in chanza masa rayuwarsa in fito da kyawawan halayensa kowa yasan ko waye real sultan, zan bashi abinda ya rasa a rayuwarsa tun kuruciya, soyayya, zan bashi something to care for, me. Zan nuna masa cewa akwai wanda ya damu dashi kuma zan fahimtar dashi cewa idan har bai gyara rayuwarsa ba zai rasa ni. Matsalata daya shine yadda zanyi family na suyi accepting Sultan a matsayin mijina. Daddy na is soft as well as hard, dole in ina son in gabatar da Sultan a gurinsa sai na nemi soft spot dinsa which for now I don't know. Mommy is as hard as steel dan haka bansan ta wanne barin zan shigar mata da sultan ba, wannan dalilin ne ya saka na yanke shawarar zan cigaba da ganin sultan a boye sannan sai in nemi chance dina kuma inyi ta addu'a. Addu'ar ita na tashi nayi da daddaren nayi istikara na nemi zabin Allah, akan sallaya ta anan nayi bacci kuma ina farkawa da assuba Sultan ne ya fara fado min a rai na shi yasa na kira shi na tashe shi yayi sallah.

Tun daga ranar muka dinke ni da sultan, kullum muna tare dashi a waya dan har komawa nayi saka ear piece saboda bazan yi ta rike wayar a hannuna ba. Wani lokacin muna zaune a falo da 'yan gidan mu muna hira at the same time kuma muna waya dashi. Duk sun san cewa nayi sabon saurayi amma basu san ko waye ba saboda bana yadda in kira sunansa a gabansu. In muna so mu hadu kuwa sai in kirkiri fita unguwa, ko ince zanje kasuwa ko gidan kawaye, sai muyi plan din inda zamu hadu dana fito sai in sallami driver na ince ya tafi yawo in na gama zan kira shi, daga nan sai sultan yazo ya dauke ni. Ni kaina nasan abinda nake yi ba dai dai bane amma na kasa samun wata mafitar. A haka har hutun mu ya kare muka fara shirin komawa england. Ranar da na gaya wa Sultan abinda yace shine "kice tafiya England ta kama ni kenan" nace "ban gane ba?" Yace "wai kina nufin zan zauna a Nigeria ke kina England bana ganin ki? You dey craze? Ai bana jin zan iya sati daya ban ganki ba" dariya nayi sosai nace "Sultan aikin ka fa?" Yace "Daga can ma zan iya yi. To in kin tafi ai tunani ma ba zai barni in yi aikin sosai ba" kuma nasan har zuciyarsa yake wannan maganar, yes Sultan loves me that much, wani lokacin har zama nake inyi tunanin me zaj faru in aka ce za'a raba mu? Ni nasan cewa duk ranar da Daddy da mommy suka ce in bar Sultan to kuwa zan barshi har abada duk kuwa da son da nake masa saboda ban taba yi musu gardama ba kuma bana fatan inyi musu, ina son iyayena sama da komai kuma zan rabu da Sultan in sunce in barshi koda kuwa sansa zai zama ajali na. Ana gobe zamu tafi Amira tazo zamuyi sallama nan na bata labarin cewa sultan fa bin mu zai yi. Tace "bangane ba, daki za'a bashi a gidanku ya zauna?" Nayi dariya nace "ke Amira, da akwai gidan babansa acan, anan zai zauna" ta bata rai tace "ni dai Moon Allah ya gani bana son ki da Sultan wallahi, this is a very dangerous game you are playing. Ita behavior is contagious, idan ke baki chanza shi ba shi zai chanza ki tunda ya fiki taurin zuciya plus kina son shi da yawa. He is handsome na sani, but He is as handsome as sin. Duk wani abin zunubi zaki ga kyakykyawa ne, very tempting, dole sai ka kai zuciya nesa zaka hana kanka" nayi shiru ina lissafa maganar ta, but i know what I feel for Sultan is not lust, it is love.

Bayan munje England ma haka ce ta kasance, kullum muna tare da Sultan a makaranta dan komawa yayi kamar shima student din ne. Kullum in muna tare sai nasan yadda nayi nayi masa nasiha ta sigar lumana, ina nuna masa this is right and this is wrong, amma ga mamaki na sai naga in aya na fara janyo masa sai ya karasa min, in hadisi na dauko sai ya gayamin wani irinsa, wato yana sane da duk abinda yake yi kenan. Abinda na kara fahimta a dangane dashi shine yana da zuciya, muguwar zuciya ma, wannan shi ya saka ya ke da fada, dan a makaranta kullum ina cikin rabon fada da Sultan. Allah yaso makarantar tana da girma shi yasa har yanzu siblings dina basu san da zaman sultan ba. Sannan kuma Sultan yana da mugun kishi dan ko kallona wani namiji yayi indai kallon bai gamshe shi ba yanzu zakuji kansa, ni har dariya yake bani dan ni mai mutane ce kowa nawa ne babu mace babu namiji. Haduwar su ta farko da Mahdi nayi introducing dinsu suka gaisa kamar gaske sai bayan mahdi ya tafi sannan Sultan ya bata rai yace "I don't like him" nace "saboda me? He is nice and shine best friend dina a school dinnan" ya tsare ni da ido yace "amma kin san yana sonki" na sunkuyar da kaina nace "yes, but I don't love him, I love you".

Sau da yawa sai in samu kaina da comparing Sultan da Ibrahim. Sam basu da alaka, kamanninsu sun sha ban ban, yayinda Ibrahim yake da sanyi Sultan kuma zafi ne dashi, Ibrahim ustaz ne sultan is the total opposite of ustaz, amma abinda yake bani mamaki shine lokacin da muna tare da ibrahim har rigima mukayi dashi akan taba ni duk da kuwa lokacin ina kwaila amma sultan ko da wasa bai taba kai hannun sa jikina ba. Situation din da muke ciki da Sultan is exactly wanda muka kasance da Ibrahim, yadda yake bina duk inda na tafi, yadda yake sona kamar ya cinye ni, da kuma yadda duk nake boye su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login