Showing 219001 words to 222000 words out of 262297 words

Chapter 74 - Maimoon Hausa Novel Complete

fushi da kai akanta Sultan, ko ma menene tayi ya kamata ka saurare ta" bai ce min komai ba ya sauke idonsa kasa, amma nasan I got his attention, na jayo hannunsa muka dawo muka zauna akan kujera, yace "ni yanzu inna kira ta to me zance mata? I miss you zance mata ko me?" Nace "I miss you din ma is in order" yace "no, it's not, ban san taba ballantana inyi missing dinta" nace "then let's go to her. In baka san me zaka ce mata a waya ba in muka je ka ganta ido da ido am sure zaka san me zaka ce mata" ya girgiza kansa stubbornly, ba tare da warning ba na hade bakin mu na fara kissing dinsa da zafi zafi, nan da nan kuwa ya dauki zafi, dama abinda yake ta nema ne ido rufe naki in bashi, yau sai gashi har gida, nan na fara sarrafa shi son raina, duk abinda nasan yana so shi nayi masa double, na ruda shi sosai na rikita masa tunanin sa, duk wani stubbornness dinsa sai da na cire masa shi ya dawo a tafin hannuna, a nan kan kujerar muka sauke hajar mu. Ana gamawa Sultan yace shi kari yake so, na bata rai na juya masa baya, ya jawo ni ya kwantar a kirjinsa yayi ajjiyar zuciya yace "why do you care about her? Baki santa ba, baki san halinta ba, for all we know maybe tana zuwa gidan nan ke ce mutum ta farko da zata ce bata so" nace "maybe, maybe not. Maybe tana zuwa gidan nan son da zata yi min sai yafi wanda zata yi maka, we will never find out idan bamu je ba" ya bata fuska kamar zai yi kuka yace "please Love I really don't want to go" nace "then let me go. In kai ba zaka iya zuwa ba ni ka barni inje, Hafsat da zayed suna can, at least in naje muka yi magana da ita zan samo maka duk amsar tambayoyin ka, daga nan sai ka yanke shawarar me zakayi next" yayi shiru yana tunani, ba dan hannunsa da yake shafa cikina ba zan iya cewa bacci yake yi saboda dadewar da yayi a haka. Can yayi magana "zaki je next week, zakiyi three days a can, a gurin su Hafsat zaki sauka saboda bana son a wulakanta min ke, in na fita gobe zan fara processing tafiyar taki" da sauri na mike zaune ina rawar murna, na manta ma babu kaya a jikina sai daga baya na tuna na koma na dunkule a jikinsa, yana dariya ya dago ni yace "amma da sharadi, daga yau duk abinda nake so shi za'a ke yimin, ko yaushe ne kuma ko a ina ne, in ba haka ba an fasa tafiyar" nace "yes sir, an gama" ya mike tsaye ya mikar dani yace "yanzu sai muje daki mu cigaba daga inda muka tsaya".
Washegari duk da farin ciki muka tashi, ni ina murnar na shawo kan sultan shi kuma yana murnar mun dawo rayuwar mu dai dai, dan haka ranar da kyar ya fita office. Bayan mun kammala duk abubuwan al'ada na gyaran gida muka shiga kitchen muna kokarin dora abincin yana, sai ga yarinya tazo tace min wai nayi bakuwa, na leka palon naga Amira na rike kugu nace " au dama ke ce bakuwar zaki wani zauna a palo? Ki tashi ki cire wannan mayafin ki taho kitchen" tana dariya ta ajiye mayafin ta ta taho, a kitchen din muka gaisa sosai sannan ta gaisa da Asma'u da sauran yarana, na lura tayi sanyi sosai kuma naji ina tausayinta har cikin raina. Sai da muka kusa kammala aikin sannan muka bar su Asma'u muka dawo palo muka zauna, muka fara hira, mostly hirar da yadda kawancen mu yake, da yadda tayi ta bani shawara akan sultan ni kuma na rufe idona naki dauka, wani gurin muyi dariya wani kuma muyi jimami, ina sane na sako mata zancen Ibrahim da labarin yanzu Amina yake nema, ina maganar ina kallon fuskarta inga yadda zata dauki maganar amma sai naga babu wani chanji a fuskarta sai ma alamar tana taya Amina murna. Muna nan zaune muka ji sallama, Amira tayi saurin daukan mayafinta ta yafa, a raina nace 'har yanzu ustazancin yana nan kenan' Abbas ne ya shigo cin abinci, da yake shima yanzu anan yake cin abinci tunda har yanzu bai huce da Hajiya ba. Ina sane nace Amira tayi serving dinsa, ta harare ni na langwabar da kai na nuna mata cikina, ta tashi ta bishi dining tana serving dinsa, ina jiyo maganganun su, dan Abbas akwai surutu kamar fa'iza, saratu ce mai shiru shiru dinsu. Bayan ta gama ta dawo gurina muka cigaba da hirar mu, sam ban bata labarin komai da yake wakana a rayuwar mu da sultan ba saboda ance once biting twice shy, bayan Abbas ya tafi muma muka je muka ci abinci tare sannan ta tafi gida. Bata jima da tafiya ba sai ga Abbas ya dawo, ina ganinsa nace a raina tarko na yayi kamu kenan, yazo ya zauna yana shafa kai yace "babbar yaya wacece dazu tazo gidan nan?" Na hade rai amma cikin wasa nace "ina ruwanka da ita?" Yace "please ki dan shigar dani mana" na wara hannuna nace "a nawa? Kasan ni bana aikin banza" yace "zanyi ta yi miki addu'ah kullum idan nayi sallah. Please" nace "ni ba zan shigar da kai ba, zan dai baka number dinta ka je ka shigar da kanka" yayi godiya ya karbi number din ya fita. Asma'u tana daga kitchen ta leko tace "dama nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya" muka yi dariya tare.
Na kira Hafsat na gaya mata an bar ni zuwa, nace ta gaya wa Ummee cewa zanzo amma ni kadai, anan take gaya min cewa khairat ta hana ta komawa gidan su zayed tun da tasan dangantakata da ita, anan gidan yanzu take sai dai zayed yazo gurinta, tace min itama tana murnar zuwan nawa nan da sati daya. Satin da sauri yazo, tun kwana uku tafiya ta na fara hada kaya, sultan kam sai kumbura yake yi, kullum sai ya tsara min yadda tafiyar zata kasance, yace gurin Hafsat zan sauka, sau daya zanje gurin Ummee, in naga babu fuska kar in sake zuwa, ni dai to kawai nake ce masa amma ni na gama plan dina, ana gobe tafiyata naje gida na wuni gurin Mommy, Daddy dama baya nan lokacin, na gaya wa Mommy komai yadda ake ciki da kuma plan din da nayi, farko ta fahimta kuma ta yarda, sai kuma daga baya ta zama alarmed, "kin ga neman takawa dama suke yi suyi masa hukuncin sace musu 'yarsu da yayi, kar kije kuma su kama ki ke" nayi dariya nace "Mommy ba abinda zasu yi min, shekara talatin fa da yin abin, besides, gurin Hafsat zanje". Sai dare sultan yazo daukana, tun a mota yake cewa shi ya akayi ya bar ni wannan tafiyar ne, a ranar yadda muka ga dare haka muka ga rana, sultan yayi nadamar bari na yafi cikin charbi, sai kara jaddada min yake yi "three days kawai, babu kari, make sure wayarki a kunne take all the time, in kinga zasu daga miki kai ko su Hafsan ne ma ki rabu dasu kije ki kama hotel ki kwana da safe kiyi tahowar ki" ni dai sai to kawai nakr ce masa. Da safe saura kadan ya saka inyi missing plight kuma nasan yana sane, so yake in fasa tafiyar amma naki. Muna zuwa airport yace "ko dai ince na fasa barinki tafiyar nan ne?" Nace "nasan ma ba zaka fadi haka ba" yace "saboda me kika ce haka?" Nace "because you are a man of your words" ya girgiza kai kawai ya fito min da akwatina, har sai da aka fara cewa za'a rufe kofar jirgi sannan sultan ya sake ni na tafi. Ina shiga jirgin ina zama naji na fara missing dinsa, na dauko waya na kira shi nace "already missing you Darling" yace "then come down ki fasa tafiyar nan please" nace "no, na riga nayi niyyar, just pray for me" ya kashe wayar bai ce min komai ba.
Wajan asr jirgin mu ya sauka a birnin Riyadh. Ina fita reception na hango Hafsat da Zayed suna jirana, na karasa da sauri na rungume Hafsat da naga ta kara kiba da kyau, jin dadi sosai ya bayyana a tare da ita, Zayed ya karbi akwatina yana cewa "welcome to my home town sister In-law, kin zama in-law dina ta two sides" muka yi dariya a tare. Muna shiga mota yace "gidan khaloo (Aunty) zamu je ko?" Nace masa "eh" ni dai duk ina feeling nervous, ban san ya zata karbe ni ba, what if sultan is right? What if ta wulakanta ni?" A hanya Hafsat take ce min wai khairat har fenti ta saka aka sakewa gidan ta na tara ta, wai yau tun safe take kitchen tana girki, ta rasa me zata dafa min, jiya kuma sam bata yi bacci ba saboda anticipation. Wannan maganar ce ta dan kwantar min da hankali.
Tun daga gate din gidan nasan an ajiye dukiya a gidan nan. Ya hadu karshen haduwa, dan bazan iya tsayawa fassara haduwar sa ba. Ni dai kawai bin su Hafsat nake a baya da sakakken baki ina kallo, mun wuce palo sunfi uku sannan muka zo inda suka ce min shine palon ta, zayed ya bude kofar da sallama sai kuma yaja baya ya bani guri yayi min alama da in shiga, na hadiye yawu da kyar sannan na daga labule na shiga da sallama. Tana zaune akan kujerar da take facing din kofa, bakar abaya ce a jikinta da rolling irin na larabawa, gashin kanta ya fito ta kasan mayafinta ya sauka har gadon bayanta, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta, ta bude idanuwanta tana kallona, she looks more like sultan in reality than in the picture. Kallo daya nayi mata naga extreme of innocence a fuskarta. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta, idonta ya sauka akan dan karamin cikina, naga kwalla ta fara taruwa a idonta, ta kasa cewa komai, na karasa shiga palon a hankali, kafin inyi magana wayata tayi kara, ina dubawa naga sultan, na dauka da sallama, bai amsa ba yace "kin fasa yin kwana ukun, na duba naga gobe da akwai jirgin safe daga nan Riyadh zai dawo Nigeria, ki biyo shi ki dawo" nace masa "an gama" na katse kiran, na kashe wayar gaba daya na saka ta a jaka ta. A hankali tace "Sultan ne" Nace "eh shine" Tace "he is already regretting letting you come ko?" Nace "yes" take naga fuskarta ta chanja kalar tashin hankali, tace "fushi yake yi dani and I don't blame him, sai dai bansan me zanyi masa ya hakura ba. Cewa yayi ki koma Nigeria ko?" Nace "yes. But if he wants me, he will have to come and get me?" A hankali naga damuwar fuskarta tana washewa, farin ciki yana replacing, ta karaso gurina da sauri ta rungume ni tace "thank you my daughter".
Afuwan jiya kun jini shiru, abubuwa ne suka dan sha kaina amma lafiya lau nake Alhamdulillah, nagode da kulawarku sosai. I feel loved.

MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty eight :Khairat
Ta sake ni ta kama hannuna muka karasa kan kujera, ta zaunar dani sannan ta zauna a kusa dani still tana rike da hannuna, tana min murmushi from ear to ear, na dan sunkuyar da kaina saboda kallon da take min, ta saka hannu ta dago habata, tace "masha Allah, you my dear are very beautiful" naji kunyarta na sunkuyar da kaina. Ta dora hannunta akan cikina tana dariya excitedly, tace "wata nawa?" Ni dai duk kunya ta ishe ni, na kasa bata amsa, tace tana karkata kai "please kar ki yi min haka mana, talk to me, ki dauke ni kamar kawar ki kinji?" Na gyada mata kai, ta sake dora hannunta akan cikina tace "wata nawa?" Ina murmushi nace "almost four" ga mamaki na kawai sai naji babyn yayi motsi, itama taji a hannunta, ai kuwa murna kamar me, tace "shima yasan yazo gida, welcome home my little love" ni dai sai taya ta dariyar ta nake yi, sai da ta gama murnarta sannan tace "how is he?" Na san wa take nufi da he din, to amma na kasa sanin ta ina zan fara bawa uwa labarin danta wanda rabonta dashi shekara talatin? Jin bance komai ba yasa tace "ya kamannin sa suke yanzu" na dago kai na kalle ta nace "you just need to look in the mirror, he looks just like you" ta fadada murmushinta tace "but he has his father's built and temper" nace "yes, he do" ta sake juyo wa tana kallona tace "har yanzu yana da hot temper kenan? Sanda yana baby in yana son abu na hana shi sai yayi ta buga kansa a jikin bango, in na bashi abin ma daga baya sai ya karba ya jefar wai yayi zuciya" nayi murmushi, ta sake cewa "tell me menene yafi so duk duniya" na san me yafi so duk duniya amma am not going to tell her that, dan haka nace "food" ta bude baki da mamaki tace "har yanzu bai daina son abinci ba? Sultan har cikin dare yake tashi yaci abinci, sanda ina feeding dinsa sai da na hada masa da madara saboda tsabar cin sa, da ya fara yawo kuma babban abincin da yake so shine nama, daga nan sai fresh milk" nace mata "har yanzu ma, yana son nama sosai" tace "is he still making troubles? He was a trouble maker as a baby, yana da kiriniya sosai dan sanda ya fara crowling duk abinda nake so sai dai in dora a sama, a saman ma in ya samu abin takawa sai ya dauko, yayi ta faduwa yana jin ciwo amma sai ya koma" ina jinta ina ta murmushi a raina ina hango baby sultan yana ta kiriniya da wannan thick gashin kan nasa, tace "please tell me all about him, nuna min pictures dinsa in gani" na dauko waya ta na zare sim card din dan kada sultan ya kira, na kunna na nemo mata wani hoton sultan wanda yake looking very good and decent, na mika mata, tana karba tasa hannu ta rufe bakinta tace "Ya Allah, he is so grown up and handsome" sai kuma hawaye ya fara zuba a idonta "my son, my darling baby" daga hoton dana nuna mata maimakon ta dawo min da waya ta sai ta fara scrolling tana kallon pictures din mu, mostly na sultan ne da ni, sai few na yan gidan mu, in tazo kan wanda bata gane ba sai ta nuna min ta tambaye ni in bata amsa, har yanzu hawaye bai daina zuba a idonta ba, kuka take kuma tana dariya duk ita kadai, ni dai ji nake kamar in karbe waya ta saboda da akwai hotunan da bai kamata ta gani ba, amma ita babu ruwanta, kalli take yi kawai tana dariya, ta dago kai ta kalleni tace "he really loves you, I can already see it in his eyes" na gyda mata kai nace "yes, he does" sai can kuma ta ajiye wayar tace "oh dear, ko ruwa ban baki kin sha ba" nayi dariya kawai bance komai ba, hannuna ta kama ta jani har dakin da na fahimci cewa bedroom dinta ne, ni dai kawai kallonta nake yi, she is really beautiful and amazing, in ka ganta daga nesa ba zaka taba tsammanin babba bace ba, sai in kun zauna da ita ka kalle ta sosai sannan zaka ga shekarunta a fuskarta, jikinta kam babu alamar girma a tare dashi.
Anan dakin nayi sallah, ina idarwa sai ga Hafsat tazo kirana in fito muci abinci, sai a lokacin na kalli Hafsat sosai, nace "yanzu Hafsat dama ciki ne dake baki gaya min ba" ta murguda min baki, nace "yanzu khairat din watanta nawa har zaki ji mata sibling" tace "ke watanki nawa aka haifi faruk? Ni wata na nawa aka haife ki? Me ya ragu a jikin mu? Ko wani mugun ciwo babu wanda yake dashi a cikin mu, itama khairat babu abinda zai same ta" na bita muka tafi ina tambayar ta "wai duk wannan gidan ita kadai take zaune?" Tace "sai ma'aikata, sai kuma 'yan'uwa duk wanda yake so zai iya zuwa ya zauna" ni dai har yanzu kallon gidan nake yi, Hafsat ta dan dakeni tace "kar ki bamu kunya mana, ke tsiya ta dake kyauyanci" muna zuwa dining naga an cika shi da kayan abinci, nan take kwadayi na ya tashi, ina zama Ummee ta taso ta fara serving dina, komai sai da ta zuba min tace dan ni ta dafa dan haka komai sai naci, yi take kamar zata bani a baki, ni kuwa na saki jiki nayi ta zurin abinci, sai kuma naji ina missing sultan, ina ma dai yana gurin nan da sai dai a dauke shi saboda yawan abincin da zai ci. Muna gama ci Hafsat tace min ta kai min akwatina dakin da take, nan take Ummee ta bata rai tace zayed yaje ya dauko ya dawo dashi dakinta, tace yau a gado daya zamu kwana babu mai raba ta dani. Bayan mun tattare gurin muka tashi muka zagaya gidan, ita take tayi mana bayanin ko ina na gidan. Kafin mu gama na gaji sosai, dama ga gajiyar hanya, muna shiga mukayi sallama da Hafsat muka tafi dakin ummee, ina zuwa tace min inyi wanka inyi sallah sai in kwanta, ai kuwa hakan nayi dan Sallar da kyar nayi ta dan idona har rufe wa yake yi saboda bacci, amma ina kwanciya sai na tuna sultan, na tabbatar yau ba zai yi bacci ba, bana nan kuma na kashe wayata ballan tana ko murya ta yaji. Nima sosai naji ina missing dinsa, kamar in dauki wayata in kira shi kuma sai na daure zuciya ta, na runtse idona ina addu'ar bacci yazo amma ina, Sultan kawai nake so. Ranar ba karamin yaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login