Showing 12001 words to 15000 words out of 262297 words

Chapter 5 - Maimoon Hausa Novel Complete

with you, just report to me or any other senior staff" nace masa tom.

Har aka tashi daga school ban yanke shawarar ko zanje library gurin Ibrahim ba. Saida akayi ringing bell sannan na tuna cewa ban yanke shawara ba. Kamar Hafsat tasan tunanin da nakeyi sai naga ta zauna a kusa dani, na juyo na kalli fuskarta naga babu wasa a cikin ta. In a serious tone tace min "me yace miki dazu? " na gane maganar da take yi kuma ga mamaki na sai na samu kaina da fada mata gaskiyar yadda mukayi da Ibrahim. Ta girgiza kanta alamar gamsuwa tace "i expect as much. Babu inda zakije, yau a hostel zakiyi karatun ma ko class ba, zaki zo ba ballantana library. Green snake under green grass kawai. Sumi sumi dashi kamar wani na Allah. Ni dama duk ustazan nan bana yadda dasu..... ". Duk da nasan Hafsat tana kokarin protecting dina ne amma sai na samu kaina da jin haushin maganganun da take fada akan Ibrahim. Na dakatar da ita nace "bafa wani abun ba yace min ba Hafsat, he just asked me to meet him in the library. It might be totally different from what you are thinking. Please Hafsat ki bar ni inje inji abinda zai ce" nayi ta lallaba Hafsat amma taki bari na inje. Haka ta tusa keyata har hostel. Ranar haka na wuni jikina da zuciya ta babu dadi. Ina tunanin ban kyauta ba dana barshi yana jira na, kuma deep inside me ina son inje din saboda insan me yake so dani, nima kuma in wanke duk wani kokwanto dake zuciya ta a game dashi. Amma Hafsat ta kasa ta tsare ta hanani sakat.
Washegari da assuba ina tashi gaba na yake ta faduwa saboda nasan yau dai dole zamu hadu da Ibrahim a islamiyya. Hafsat ta hade ranta sosai ta kora min warning akan koya yimin magana kar in kulashi. A haka muka je masallaci mukayi sallah sannnan muka tafi islamiyya. Muna zama sai gashi ya shigo. Na kasa daga kaina in kalleshi har muka gaishe shi duk ya ajin. Kawai sai ganin sa nayi ya zo ya tsaya a gaban seat dina yace "maimunatu" na daga kaina a hankali na kalleshi, bacin ran da na gani a idonsa shi yasa nayi saurin saukar da idona kasa ba tare da na amsa kiran da yayi min ba. "Maimunatu am talking to you " ya sake cewa cikin tsawa-tsawa. Jikina ya fara karkarwa saboda tsoro, nace "am sorry sir " "sorry for what? I clearly asked you to meet me after school yesterday but you didn't. Why? " kawai sai naji hawaye yana zubo min, sai na fara sheshshekar kuka, ni dama akwai saurin kuka. Tsayawa kawai yayi yana kallona da mamaki sannan yace "why are you crying? For God's sake I only asked you a question" cikin fada yake min magana. Wani kukan na sake rushewa dashi, ni babu abinda bana so a rayuwata irin a yimin tsawa ko fada. Shi bai san cewa fadan da yake yi min shi ne ya ke sakani kuka ba. Hafsat ce tace masa "she was sick sir, that's why she didn't meet you in the library " duk da kukan da nake yi sai da nayi mamakin yadda Hafsat ta shirga masa karya. Kuma na gane motive din ta, so take yace min in tafi hostel tun da bani da lafiya. Ya sunkuyo dai dai fuskar ta sannan cikin sanyin murya yace min "are u sick? Na girgiza kaina. "Do u want to go back to hostel? " na sake girgiza kaina alamar a'a. "OK stop crying for God's sake, or else I will have to send you back to hostel" ya fada da dan karfi wanda hakan yasaka na sake rushewa da wani kukan. Tsaki yayi sannan yace "OK, that's it, u are going back to hostel" yana fadin haka Hafsat ta mike tare da kamoni kamar wata marar lafiya. Ya dakatar da ita tare da cewa "where are you going to? " nan ta kama inda inda tana kokarin yi masa bayanin cewa rakani hostel zatayi. Shi kuma ya ce mata tunda nace lfy ta kalau ta barni inyi tafiya ta ni kadai ita kuma tayi karatun ta. Ta koma ta zauna tana zumburar baki, ni kuma na kama hanyar fita. Ina tajin surutan mutane a ajin nidai nayi tafiya ta. Na dan yi nisa da class din kenan naji takun mutun yana bina, ina juyawa na ganshi a kusa dani ya kamo hannuna ya jani da sauri zuwa wani class da babu kowa ya rufe ajin tare da tare bakin kofar. Duk wannan ya faru ne cikin seconds. Wani kukan na sake saka masa ina rokon sa "please let me go, i will never disobey you again, please let me go" kallona kawai yake cikin mamakin yadda nake ta rusa kuka. Ya rungume hannayensa a kirjinsa sannan yace " do you want me to let you go? " na gyada masa kai "then stop crying like a baby, for God's sake I just walk out of my class just to talk to u. Why are you crying? What have I done to u? " nayi shiru ina sheshshekar kuka, ya sake maimaita tambayarsa " did i do u anything wrong ". "You are shouting at me" na amsa ina kara sautin kuka na. Dariya ya fara yi kasa kasa yana girgiza kansa ni kuma dariyar ta kara bani haushi, yaya bayan yayi min tsawa ina kuka kuma zai saka ni a gaba yana min dariya? Dan haka sai na rufe fuskata da hannayena biyu na kara rushewa da kuka. Ya tako a hankali ya tsaya agaba na sannan ya sunkuyo kansa dai dai kunne na yadda har inajin saukar munfashinsa a wuya na yace "I am sorry for shouting at you. I promise to never do it again " na bude fuskata na turo baki ina goge hawayena da bayan hannuna. Ya chiro handkerchief a miko min, nasa hannu na karba na karasa goge fuskata dashi, sannan na daga kaina na kalleshi naga yana kallona yana murmushi. "OK cry cry baby, tell me why didn't you come to the library yesterday? " na kalli windon class din naga gari ya fara haske sannan na tuna cewa ya baro students suna jiran sa zai yi musu dori. Na kalle shi naga ni kawai yake kallo yana murmushi daga dukkan alama ya manta da 'yan class din da suke jiransa. Nace masa "we, will talk about that later, now your students are waiting for u, time is running out " ya danyi frowning face dinshi alamar tunani sannan yace "good lord! I totally forgot about them." Ya shafa gashin kanshi sannan yace "just PROMISE that we will talk tomorrow " na ce "not tomorrow sir, we will talk on Monday " yace "why not tomorrow? " Nace "I don't want to be taking time from our Islamic class time. I will talk to u on Monday if u promise that you will not talk to me during our Islamic class " yayi shiru yana kallona sannan yace "OK I promise "nayi murmushi nace masa OK. Daganan na bude kofar class din na fita na koma hostel.
Yayi keeping promise dinsa kuwa dan bai kuma yi min magana a islamiyya ba, karatu kawai mukeyi dashi mu tashi. Ranar monday muna da class dinsa kuma nasan dole zai ce min mu hadu a library after school. Yana shigowa bayan mun gaishe shi sai ya dauko wata 'yar jotter ya rike yace yau discussion za'ayi, zaike mana tambayoyi muna amsawa. Kawai sai ya taho kan desk dina ya zauna kuma ya juyo yana facing dina kuma yana facing sauran 'yan class din, tunda a front row nake. Nayi sauri na kalleshi sai ya sakar min murmushi, na sunkuyar da kaina kasa duk naji na takura. Yana ta questions dinsa sauran 'yan class suna amsawa amma ni ban san ma me suke yi ba, saboda yadda yake zaune gab dani kuma duk numfashin dana shaka saina ji kamshinsa. Na rasa inda zan sa kaina. Chan ya ce min "Maimunatu are u OK " sai da na dan firgita kadan saboda nayi nisa a cikin tunani, na manta ma a ina nake. Nace"yes sir, i am alright " "are u sure" Hafsat ce tace " I am sorry sir, but dont you think you are making her uncomfortable? " gaba daya ajin akayi shiru yace mata "what makes you think I am making her uncomfortable? She is not complaining, is she? " ta kalle shi ido cikin ido tace "i know she is uncomfortable because she is my little sister " "ohhh" shine abinda Ibrahim yace sannan ya juyo ya kalleni ya sake komawa ya kalleta kamar mai comparing din mu, yayin da ita kuma ta tsare shi da ido.


Episode Twelve : This is Me

Note: duk maganar da akeyi da Ibrahim da turanci akeyi, amma zamu keyi da hausa saboda a samu sauki fahimta. Ayi karatu lfy

"Da gaske sisters ne su? " ya fada yana kallon sauran 'yan ajin. Duk ajin ya dauka "eh sir sisters ne, baka ga suna kama ba? " ya sake kallon mu yana girgiza kai, "ni ban ga kama ba" Hafsat ta kara kulewa ta hade rai sosai, shi kuma sai ya kalleta yayi dariya yace " ok Big Sister, kiyi hakuri na takura ma kanwarki. In babu damuwa to in dawo desk dinki mana maimakon nata? " Hafsat ta bude baki tana kallonsa da mamaki, sannan tayi sauri tace "a'a yi zamanka anan" yayi dariya sosai har habarsa ta lotsa sannan yace "dama nasan zaki ce haka, nima kuma nafi son zama anan" nidai duk ina jinsu bance komai ba. Sai da period dinsa ta fita sannan yace min "kar ki manta alkawarin mu, ni kadai nasan abinda zanyi miki in kika yi min irin ta rannan" da haka ya fita daga ajin. Yana fita Hafsat ta jawo kujerar ta kusa da tawa tace " alkawarin me mutumin nan yake magana akai? Yaushe kuka hadu har kika yi masa alkawari ba tare da nasa ni ba? " na kalleta nace " wani lokacin Hafsat ina mamakin mutane in suka ce na fiki surutu, sa idonki yayi yawa Hafsat " nan Hafsat ta kuma kuluwa tace " au haka ma zaki ce ko? Duk abinda nakeyi fa dan ke nakeyi. Mutumin nan daga ganin sa ba mutumin kirki bane, bana son kowacce irin alaka a tsakanin ku. I am trying to protect you" nace " ni kuwa Hafsat kina bani mamaki duk sanda kika ce Ibrahim ba mutumin kirki bane ba, how do you know? Kin san kullum daddy yana ce mana never judge a book by it's cover, ba dai dai bane ba kawai ki yanke hukunci akan mutum ba tare da kin fahimce shi ba" tace "OK kina so ki gayamin cewa ke kina so ki fahimce shi kenan ko? " nace mata "exactly " Amira ta taso tazo gurin mu tace "pls guys not here, zamuyi maganar in munje hostel" Hafsat ta cigaba da balbalin fada ni kuma na tashi kawai na fita daga class din. Kan veranda na zauna ina tunanin yadda zan bullowa wannan lamarin, nasan Hafsat akan gaskiyarta take fada, duk da ina da karancin shekaru amma na gane duk abubuwan da Ibrahim yake min da duk kwana kwanar sa nasan inda ya dosa. Kuma ni kaina basai wani yayi min fada ba nasan nayi kankanta da zuwa inda ya dosa. Abu na biyu kuma Ibrahim bayarabe ne, ni kuma bafulatana bana jin tarayyar mu dashi zatayi kyau. Murmushi nayi sanda na lissafo fuskar mommy inta samu labarin ina dating yaroba guy. Amma koma menene zai kasance yau zamu zauna muyi magana da Ibrahim, zan bukaci ya fada min duk abinda yake zuciyar sa ni kuma zanyi masa bayanin cewa abin ba me yiyuwa bane. Ina so mu samu maslaha a tsakanin mu.

Da aka tashi bayan munyi sallah munci abinci Amira ta jamu dakin su tana so ta daidaita tsakanin mu da Hafsat. Na zauna a nutse na yiwa Amira bayanin abinda yasa nake son muyi magana da Ibrahim. Muna ta maganar mu Hafsat tayi banza ta rabu damu, saida Amira tace mata "baki ce komai ba Big Sister" ta fadi big sister din da tsokana, irin yadda Ibrahim ya ce mata dazu a class. Ta juyo ta kallemu tana yamutsa fuska tace "She can do as she wants, ni dai tasan cewa komai tayi kamar tayi a gaban mommy ne dan wallahi sai na gaya mata" Amira tace "Haba Hafsat pls let her go, inta dawo zata gaya mana duk abinda sukayi dashi daga nan za muyi shawarar me zatayi next" Dakyar Amira ta lallaba Hafsat ta barni na tafi da sharadin cewa duk abinda yace min zanzo in gaya mata.
Naje nayi wanka na shirya a tsanake, dama ni ko a gida ba kwalliya nake ba ballantana a school na saka hostel wears dina, har na nada vail dina sai kuma na chire na dauko dogon hijab din Hafsat na saka. Ina fita na nufi library, tun daga nesa na hangoshi a zaune a side din library din da table a gabansa dauke da littattafai, amma kuma ba karatun yakeyi ba waya yake dannawa. Na karasa da sallama, ya dago kai ya kalleni da murmushi a fuskarsa, daga gani ya dade a zaune a gurin. Ya nuna min kujerara kusa dashi yayi min nuni da in zauna. Maimakon in zauna a kusa dashi din kamar yadda ya bukata saina dauki kujerar na zagaya daya side din na zauna ina fuskantarsa. Ban gaishe shiba nace masa "am here, what do you want ?" Ya sake yin murmushi yace min good evening ma'am" sai kuma naji kunya ban gaishe shiba nace "good evening sir" ya cire glasses din idonsa yana murza idon yace "har na fara tunanin bazaki zo ba, na dauka yau ma Hafsat ta hana ki zuwa" na kalleshi da mamaki nace "ya akayi kasan ita ta hanani zuwa rannan? " yace "da ban sani ba, sai dazu data cemin ita sister dinki ce sannan na fahimci ita ta hana ki zuwa" muka yi shiru baki daya na wani lokaci sannan ya cigaba da magana a hankali " am sorry for shiga rayuwarki da nayi kwana biyu. Nima bansan mai yake hawa kaina ba tun zuwa na makarantar nan, ina so ki fahimci cewa bani da wani mugun nufi a kanki sai alkhairi insha Allah. Tun ranar da kika amsa question dina a class naji kin burgeni, bayan na fita daga ajin ku na je staff room nayi tambaya akan ki anan na fahimci cewa you are a genius " nayi saurin katse shi nace "am not a genius " yayi dariya yace "research ya nuna cewa babu genius din da ya taba yarda cewa shi genius ne" ban bashi amsaba na sunkuyar da kaina kasa. Ya cigaba da cewa "tun daga nan na zama interested akan ki, lokacin ne nayi miki offering friendship. Kuma ina saka ran babu wani abu da zai rusha friendship din mu" ya sake yin shiru kamar ya gama magana sai kuma yace "ita zuciya tana da wahalar fassarawa, na kasa fahimtar me zuciya ta take nufi dake. Kullum sai inji ina so in ganki, inna ganki kuma sai inji bana so mu rabu, in ban ganki ba kuma sai inji na rasa farin ciki na" ya sake yin shiru yana shafa gashin kansa. "What do you want from me? " na sake tambayar sa a karo na biyu. Ya yi tagumi da hannayensa duk biyun ya sauke lumsassun idanuwansa a kaina sannan cikin muryar rada yace " ina so ki kara kahuri dani mu cigaba da friendship din mu, nasan wannan feeling din da nake ji akanki zai wuce wata rana. Ina so please kiyi tolerating dina for the time being. In kina ignoring dina zan iya aikata wani abun da ba dai dai ba". Duk bayanin da yake yi ina jinsa kuma ina analyzing duk maganganun sa. Na bude baki zanyi magana kenan sai ya daga min hannu ya dakatar dani yace "kar kice komai yanzu, ki bari sai kinje hostel kinyi tunani akai tukunna. Ina so mu cigaba da zama a friends but i have feelings for you. Nace masa to zanje inyi tunanin kamar yadda yace.

Muka danyi shiru na wani lokaci sannan ya ce " kafin kiyi tunanin amma ina so in dan baki brief labari na saboda ki fahimceni sosai. Kamar yadda na sanar dake ni bayarabe ne full blood. A yanzu shekaruna ashirin da biyar da haihuwa. Mahaifina ya rasu tun ina five years old. Nine babbar a gurin parents dina, sai kanne na mata su biyu. Bayan rasuwar mahaifina mamana ta sake aure ta haifi maza su biyu. Step father dina babban malamine a garin Ibadan, a gurinsa na koyi karatu sosai. Ya rike mu ni da sisters dina tamkar shi ya haifemu dan idan ba gaya maka akayi ba ba zaka san ba shine baban mu ba. Daga mamana har step father dina basu yi wani karatun boko sosai ba, baban mu dai yana dan taba kasuwanci kadan sai kuma islamiyya da yake koyarwa a unguwar mu, dan haka mu ba masu arziki bane sosai sai rufin asiri dai dai gwargwado. Allah ya bani kwakwalwar karatu na arabi da boko, wannan yasa baban mu ya sakani a makarantar kudi dan insamu ilimi mai kyau kuma Alhamdulillah na samu. Duk kudin babanmu akan karatuna yake karewa, sauran siblings dina duk a makarantun government suke, a cewar baba ni zan kula dasu inna samu aiki. Bayan na gama secondary school ne na samu na fara aikin teaching a wata primary school dake unguwar mu. Shekara ta uku ina teaching ina samun salary na baba yace lallai saina koma makaranta nayi degree, Allah ya taimakeni na samu admission a university of Ibadan nayi degree na a fannin mathematics. Na samu kyakykyawan sakamako na fita da first class shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login