Showing 171001 words to 174000 words out of 262297 words
sai da yayi sallah sannan ya dawo inda still nake kwance ba tare daya ce min komai ba ya dauke ni ya kai toilet, da gaske ciwon nake ji ba wai shagwaba bace, dan kafafuwana jinsu nake kamar lagwani, da nayi alwalar ya dawo dani daki ya sakamin doguwar riga ta da hijab dina ya zaunar dani akan sallaya nayi sallah, ina idarwa ya shigo da tea a hannunsa ya zauna ya fara bani, naki sha sai da yace min inna shanye zai kira Hafsat, na sha kamar rabi nace na koshi, kan gado ya sake mayar dani ya lullubeni. Ya dauko min wayata ya dawo kusa dani ya kwanta yace "to kira Hafsan, tunda kince ita kike so" na duba time naga 6:30, na kira number din Hafsat, ringing biyu ta dauka, sai kuma na rasa me zance mata, tace "I know u will call me dama, check your messages, na bar miki sako" daga nan ta kashe. Sultan yace "me tace?" Na gaya masa, ina duba wa kuwa naga message daga Hafsat 'you once asked me what it feels like, yanzu nasan kin sani. Was Sultan gentle? If he isn't please knock his big head for me. I left something a bedside drawer dinki and I also left you farfesu a cikin fridge, for you alone, kar ki bashi ko loma daya' ina gama karantawa na tattaro dan sauran karfin daya rage min na rankwashi Sultan aka, ya rike gurin yace "ouch, me nayi kuma?" na nuna masa message din Hafsat nace "sako ne inji Hafsat" ya shagwabe fuska "was I not gentle?" Nace "you weren't" yace "to ai ba laifi na bane ni kadai, why do you have to be so damn good. I always thought it will be good but did not expect it to be this good" nace "so it is my fault kenan ko?" Yayi dariya bai amsa ba ya mike yace "let me get sakon nata". Few minutes later ya dawo da leda a hannunsa, ya zauna a gaban gadon ya bude, magunguna ne a ciki, mostly pain relievers ne, sai wani farin gari a leda da instruction din a ruwa za'a zuba a shiga ciki, sai kuma wani paste shi kuma na shafawa ne. Yana gama dubawa ya dauki na ruwan ya tafi dashi toilet, nasan ruwa zai hada min dan haka duk na tsorata, nasan zafin dana ji a ruwan jiya, yana dawowa na saka masa kukan ni bana son shiga ruwa, da kyar muka je toilet din, amma shiga ruwan ya gagara, a karshe dai sai tare muka shiga, kayan kuwa sai a cikin ruwan aka cire su. Bansan me yake faruwa ba sai da na gama jin zafin ruwan sannan na lura da yadda muke, ai kuwa nace sai ya fita amma yaki, a dole muka gama zaman cikin ruwan tare muka fito, muna fito wa na rufe ido na wai bazan kalle shi ba tunda babu kaya a jikinsa, yayi ta tsokanata amma still naki bude idon, muna dawowa daki ya dauko na shafawar wai sai ya shafa min, na fara kokawa ya saka hannu daya ya rike ni kuma ya shafa min din. Na kwanta ina kumbure2 ya fita, har na fara bacci sai gashi ya dawo da bowl a hannunsa da kuma kwalin fresh milk, ya tashe ni zaune yace sai naci, ina ta shagwabar ni bacci nake ji amma haka ya matsamin sai da muka ci tare, muna gamawa ya dauko min magungunan wajan Hafsat ya bani nasha sannan na koma na kwanta, ban jima da kwanciya ba naji shi ya kashe fitilar dakin ya hawo gadon shima, ya jawo ni jikinsa kamar zai tsaga kirjinsa ya sakani ciki, nayi 'yar kara, yayi dariya yace "ya jikin?" Nace "da sauki" yace "Maimunatu" nayi mamaki saboda yau ne rana ta farko daya kira ni da wannan sunan, nace "Na'am" yace "thank you, I really mean thank you, for yesterday, for everything, bansan me zance miki, bansan sunan da zan kira ki dashi ba, I will continue calling you my love, saboda you are the love of my life, amma ki sani ba wannan ne kadai matsayinki ba, you are my everything, I was nothing kafin in hadu dake kuma I will be nothing without you" bance komai ba amma ina jin dadin maganganunsa har cikin raina, ina kara jin sansa yana shiga har cikin bargo na, he is mine, and I am his, forever and ever.
Ni na sake riga shi tashi wannan karon ma, na farka naga still dakin duhu, wato shi wannan dakin na sultan koda yaushe a dare yake kenan, sai mutum yayi ta bacci bai san me duniya take ciki ba. Na tashi zaune, ga mamaki na sai naji babu ciwon sam, sai dan ciwon jiki kadan, na kunna bedside lamp, na duba agogon wayata, 1:15, oh my God, nasan mutane sunyi ta zuwa suna ganin gidan a rufe, na juya na kalli sultan da yake bacci a gefe na, sai naji na kasa tashin sa, he looks so handsome, hasken lamp din yana reflecting a golden skin dinsa, na koma na kwanta a side dina ina kallonsa, I have never see him this peaceful before, na tuna maganar hausawa da ake cewa wai angwaye suna kwallin goshi, to ko dai da gaske ne? Na kai dubana kan kirjinsa, Ya dan yaye bargon ya bar kirjinsa a waje, gashin da yake kwance a kirjinsa yafi na fuskarsa kyau da sheki kamar yadda fatar gurin tafi da fuskarsa haske, a hankali na gada hannuna, na sake kallon fuskarsa naga baccin yake yi, I couldn't stop myself, a hankali na sauke hannuna akan gashin na fara shafawa ina jin laushinsa a hannuna, I was so consumed in doing what I was doing kawai naji maganarsa "hey woman, you already had me, if you want more all you have to do is ask" nayi sauri na dauke hannuna na rufe fuskata dashi, ya mirgino ya hade fuskarmu guri daya yace murya can kasa "do you want more?" Na girgiza kaina da sauri, yace "but I do want more" nace "ni fa tashinka zanyi, lokacin sallar azahar ya kusa, kuma kaga ko bude kofa bamuyi ba kar mutane su yi ta zuwa gida a rufe" yace "so what? Duk wanda bai zo jiya ba yayi wa kansa, an gama ganin gidan amarya. Let's not open the door forever, let's not get out of this bed forever" nayi dariya na dan dake shi a kafada nayi kokarin tashi ya sake dawo dani baya nace "Sultan, ka bar ni inje dakina in saka kaya, inje in samar mana abinda za muci kuma, we can't stay here forever" ya saka fuskarsa a wuyana yace "sai kace girkin ta iya da gaske. Za'a kawo abinci, za'ake kawo wa daga cikin gida har nan da seven days, kafin nan sai mu nemi cook. Yau bana son ko tashi inga kinyi, I want to treat you like the queen you are, komai kike so ni zan yi miki, duk abinda kike so shi za'ayi".
Da kyar na samu ya dauko min kayana a dakina na saka, daga nan ya tafi masallachi sallah ni kuma nayi sallah ta anan, miracle maganin Hafsat yayi min amfani sosai dan bama na tuna wa da wani ciwo sai in na yi motsi da sauri. Man sa na shafa na saka tunarensa, banyi kwalliya ba, na zauna akan kujera ina duba messages din wayata, yawanci sakonnin taya murna ne daga mutanen da basu samu damar zuwa bikin ba, anan naga sakon mahdi, yace min ya cigaba da karatunsa bai dawo Nigeria ba, na rufe WhatsApp kenan naga sakon Amira ya shigo, na koma na bude "Moon dan Allah ina so muyi magana, can I come to your house please?" Ban yi mata reply ba Sultan ya shigo, tray din abinci ne a hannunsa amma idonsa yana kaina, na karaso na karba na ajiye, bai ce komai ba ya sake fita ya dawo da still da wani abincin, na kuma karba nace "Sultan wannan abincin ya zamuyi dashi?" Yace "I don't know which one you will like, shi yasa na debo kowanne. Sun kawo abincin yana dining. Da akwai Baba Gaji Yaya ta turo ta gurinki, I told her ba zaki samu ganinta yanzu ba amma ta zauna duk wanda yazo ta raka shi yaga gida amma ta gaya musu amarya is not available" nace "ayyah, da ka barni naje baka san menene sakon Yayan ba" yace "ba zai wuce zancen masu aiki ba" zan kuma yin magana ya jawo nikan cinyarsa yace "me zaki ci?" Mun ci abincin sosai daga ni har shi duk ashe yunwa muke ji, sam ya hanai fita da kayan shi ya dauka ya fita dasu, kafin ya dawo na gyara gurin na kara freshner a dakin, yazo ya jani muka koma gado yace "ya ciwon? In duba in gani? Nayi sauri na hade kafafuwana nace "bai warke ba ai" yace "OK, kin san me za'ayi masa ya warke da wuri? Wani za'a kuma yi, nan da nan zakiga ya warke" na fara matsawa baya ina zaro ido "please Sultan, wallahi mutuwa zanyi, dan Allah karka tabani" dariya yayi sosai yace "harda mutuwa? Am just kidding, amma babu wani mutuwa da zaki yi, an gama mai zafin ai" na sake matsawa baya, ya jawo ni yace "trust me bazan miki wannan ba, I just want to feel your warmth and smell your scent" na dan saki jikina kadan amma kuma ba abinda ya fada kadai yake yi ba, sai da naga yana neman wuce gona da iri sannan na saka masa kuka, ya sakeni ya gyara min rigata sannan ya gyara min kwanciya, har na dauka yayi bacci sai naji yace "tell me about him" duk da bai fada ba nasan wa yake nufi, kuma nasan dama dole zamuyi maganar amma sai naji bakina yayi min nauyi na kasa magana, jin nayi shiru ya sake magana "I just want to know, shi kadai ne ko kuma akwai wani daban da ban sani ba" na girgiza kaina nace "shi kadai ne, sunan sa Ibrahim, he was a copper a sec sch din mu when I was in SS2, I was 14 years then" daga nan na bashi labarin duk rayuwar mu da Ibrahim him, da yadda muka rabu, da irin zaman jiransa dana zauna yi kafin haduwar mu shi (sultan), na bashi labarin har ranar da muka kuma haduwa da Ibrahim da labarin daya bani na rayuwar da yayi bayan rabuwar mu da irin abubuwan da Amira ta kulla mana, ban boye masa komai ba har wayar da mukayi dashi a phone din Amina da duk bayanin dana yi masa ya kuma nuna ya gamsu, na karasa da cewa "bansan me yasa ya aikata abinda ya aikata ranar nan ba. Am sorry na boye maka duk wanan maganar, at first I never thought zamu sake haduwa dan haka nake ganin there is no point in telling you, daga baya kuma bayan mun hadu dashi na kasa gaya maka ne saboda bana son in bata maka rai". Har na gama maganar baice komai ba,har na fara tunanin ko yayi bacci, na kalle shi sai naga yana kallon ceiling, can yace "promise me you will never see or talk to him again, my heart cannot take it" na dago kaina ina kallon cikin idonsa nace "I promise" yayi murmushi yace "thank you" sannan ya jawo fuskata ya hade bakin mu.
Episode Seventy Three : His Father's Son
Washe gari bamuyi missing sallar assuba ba kaman jiya, Sultan ne ya fara tashi, sai da yayi alwala sannan ya tashe ni shi kuma ya fita masjid, ya jima bai dawo ba har nayi sallah na dan taba karatun al'qurani sannan nayi morning azkar dina, ji nayi duk na gaji da kwanciya, I want to do some work, na tashi na gyara dakin na wanke toilet, na dawo palo ina cikin gyarawa ya shigo, ya tsaya yana kallona "wato matar nan kin warke ko? Shine zaki kama aikin da assubar nan ko?" Nace "na gaji da kwanciya ne kawai, I want to do something" ya fara tahowa yana min murmushin mugunta yace "You want to do something? I have got something for you" na ajiye duster din hannuna na fara ja da baya ina jin tsoro har cikin raina dan na warke amma ban manta azabar da nasha ba. Nace "Sultan Allah ban gama warkewa ba, dan Allah kayi hakuri wallahi na daina aikin zan koma in kwanta" ya karaso in da nake yace "really baki warke ba? Can I see?" Nayi saurin girgiza kaina nace "you are not a doctor how will you know if a wound is healed or not?" Yace "am not a doctor but ni mijin doctor ne, dan haka believe me I will know" idonsa kawai na kalla nasan kona roke shi it will be to no avail, jikina har karkarwa yake yi saboda tsoro, me yasa nayi aure ne wai? A kunne na ya rada min "believe me, it will not hurt". And it didn't, at least not as I expected. Yana cikin bacci na zare jikina na tashi, a hankali na lallaba na saka kayana na fice, da sauri na karasa dakina ina shiga nayi locking kofar, finally nazo dakina after two days, da sauri sauri na gyara dakin duk da ba wani datti yayi ba, na shiga toilet na shiga shower ina wanka, at last zanyi wanka without sultan standing and watching. Na fito na zauna na shirya a tsanake cikin atamfa ruwan hoda, nayi 'yar kwalliya kadan na fesa turare na fito. Ina fita palo na tarar da wata tsohuwa a zaune a kan carpet da wadansu 'yammata su biyar daga can bakin kofa, ina fitowa duk suka mike tsaye kansu a kasa, 'yammatan kamar harda tsoro a fuskarsu, sai da na zauna sannan suka durkusa suka fara gaisheni daya bayan daya, na saki fuskata sosai na amsa musu. Babbar matar ce ta matso tace "ranki ya dade, Allah ya taya miki, Allah ya dora ki akan makiyanki duniya da lahira, Allah yaji kan magabata, Allah kuma yasa albarka a zuriya" nace "Ameen" ta cigaba da magana "ranki ya dade ai jiya ma munzo, muna nan har magriba bamu samu ganin ki ba. Dama mai babban daki (yaya) ce ta turo mu, tace tana gaishe ki sosai, kuma tace duk mu shidan nan mu dawo nan gurinki mu zauna muke yi miki hidima. Ni sunana Gaji, tun asalin kakanni na bayi ne a wannan gidan, anan aka haifeni anan na girma nayi aure na hayayyafa, 'ya'yana ma suka yi aure suka haihu duk acikin gidan nan, guda biyu daga cikin 'yammatan nan jikokina ne. Kamar yadda aka kawo 'yammatan nan gurinki yanzu haka aka kaini gurin mai babban daki sanda tana amarya, wannan shi yasa nake daga cikin amintattun bayinta, kuma wannan shi yasa ta zabe ni akan in zo in zauna a gurinki, saboda tasan zan rike mata amana. Suma wadannan duka yaran da kika gani zababbu ne dan ni ta saka in zabo mata masu tarbiyya da rikon amana kuma na zabo su. Insha Allah zamu rike ki da amana Allah kema ya baki ikon rike mu da amana." Kawai naji matar ta kwanta min araina, na tambayi yaran duk sunayensu suka fada min, naga duk sunki sakin jikinsu sai na fara yi musu wasa, ba'a jima ba suka fara dariya. Da kaina na tashi na kaisu har bq din mata na nuna musu komai sannan muka dawo tare. Nace "Ku dauke ni a matsayin yayar ku kunji, dama ni bani da kanne mata kunga shikenan na samu, duk abinda kuke so kuyi min magana in dai ina dashi zan baku, abinda bana so shine kazanta, ku kula da tsaftar gidan nan ku kuma kula da tsaftar jikin ku, ku kame kanku banda shiririta. Allah ya bamu ikon zama lafiya". Sunji dadin yadda na karbe su, kuma daga dukkan alamu sunji dadin bq din dai sai murna suke sunzo gurin 'yan gayu. Nan take baba Gaji ta raba mudu kowa aikinsa, jikokinta guda biyu su ta bawa part dina, sauran kuma sauran parts din gidan. Banda part din Sultan. A take suka tashi suka fara aikin su. Ina zaune sai ga abinci daga cikin gida, suka je suka ajiye a dining room sannan suka zo suka gaishe ni, wai hajiya tace ayi min sannu da jiki, na amsa musu, naga suna ta kallon 'yammatana da Baba Gaji da naga ta hade rai. Na tashi na koma part din Sultan na tarar ya tashi yana wanka, na zauna na jira shi ya fito, yana kallona yace "shine kika gudu ko?" Bance komai ba, ya tsaya yana goge jikinsa, ya juyo ya kalleni muka hada ido nayi sauri ya sunkuyar da kaina, yayi dariya yace "ana so ana kaiwa kasuwa. You are welcome to watch" nace "an kawo abinci, nan za'a kawo ko kuma zaka fito dining?" Yana kokarin shiga closet yace "bara kawai in fito, dama zan dan fita" har ya kai bakin kofa kuma ya tsaya ya juyo "bazaki zo ki tayani shiryawa ba?" Na rufe fuskata da hannuna, yayi dariya "wannan kunyar naga har yanzu da akwai saura, zanyi maganin ta ne" ina nan zaune inda ya bar ni har ya sake fitowa, kananan kaya ne a jikinsa yayi stocking rigar ya saka belt, da comb a hannunsa yana taje kansa, na tashi na karasa inda yake na karbi comb din na cigaba da taje masa, nace "ina zaka je?" Yace "orphanage. Yanzu zan dawo. Tunda aka fara bikin nan banje na gansu ba" na gama gyara masa gashin nace "let's go eat then".
Sai bayan ya tafi sannan na dawo palo gurin baba gaji, ina zama tazo ta fara yi min tausa a kafa ta, naji dadin tausar saboda dama kafar ba dadin ta nake ji ba, cikin girmamawa ta fara yi min magana "ranki ya dade ni kam wadannan masu kawo abincin nan ina ma za'a ce musu su daina kawowa? Mu sai mu ringa yi anan" ban