Showing 186001 words to 189000 words out of 262297 words
ganshi yanzu yasan da akwai banbanci. Wata rana ina fatan kuma zaku ganshi kamar yadda nake ganinsa." Sai a sannan Khulsum tayi magana bayan tayi tsaki tace "tana magana kamar wata psychologist" na juya na kalle ta nace "I am a psychologist, I have a first class degree in psychology from the second best university in the world. I know exactly when someone is lying to me. I can read your mind as well as I can read time from an analog clock" na bi fuskokin su da kallo, kamar an tsiyaye musu jinin su daga jikinsu, na hango kiyayyata karara a rubuce akan fuskokin su. Kusan minti biyu babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu. Hajiya ce ta kirkiro murmushi tace "ku tashi mu tafi, mun bar ango yana ta jiran amaryarsa" Khulsum ce ta fara tashi ta fita ba tare da ta kalli inda nake zaune ba. Har mota na raka su na daga musu hannu sannan suka tafi. At least nasan yanzu tsakanin mu is clear, babu munafunci babu yaudara. Ba zasu sake zuwa su ce zasu gaya min wata magana akan Sultan ba, amma kuma nasan na kunno wata wutar kuma. Na gaya musu nasan secrets din su dan haka na kara wutar kiyayyarda suke yi min. But am ready, Allah yana tare dani and am not scared. Na yarda da Allah na yarda da kaddara, nasan su basu isa suyi min komai ba, duk abinda ya same ni daga Allah ne ba daga gare su ba. Kuma komai nisan jifa kasa zai dawo, duk kuma abinda ka shuka shi zaka girba, in khairan khairan in sharran sharran.
Ina komawa cikin gida na koma part dina nayi wankan da ban samu nayi ba, ba fito na shafa special mai na, na kuma fesa turaruka daban daban. Na shiga closet dina, na jima ina neman kayan da zan saka, daga baya na dauko wasu deep red kaya, robber, three quaters wando da half vest. Na saka su ba tare dana saka komai a ciki ba. Ni kaina dana kalli madubi sai da naji kunyar kaina, kayan sun bi jikina like a second skin, kalar ta kara fito da haske da kuma kyan fatar jikina. Na dauko deep red lip stick na shafa a lips dina. Na dauko dogon hijab har kasa na saka, sannan na fita. A palon sa na tarar dashi, yana zaune da fararen singlet da gajeran wando a jikinsa, ya kunna TV ya rike remote a hannunsa amma kuma ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani yana kallon sama. Na jima a tsaye ina kallonsa amma bai ma san na shigo dakin ba. Na dan daga murya nace "wanne film kake kallo ne?" yayi sauri ya kalle ni sannan ya kalli TV din, ya daga kafada yace "I don't even know wanne film suke yi. Ba'kin naki sun tafi ne?" Ban bashi amsa ba, ya fara kokarin chanza station, na chire hijab din jikina a yar a gefe nace "pss" ya juyo da sauri yana kallona, a hankali remote din hannunsa ya zame ya fadi kan carpet, ina kallon idonsa naga duk wani tunani da wata damuwar sa suna disappearing har sai da ya zamanto babu saura. Ya saki ido da baki da hanci duk yana kallona, a hankali ya furta "ya Ilahi save me, wannan rayinyar so take ta haukata ni" sai kuma naji kunya nadan rufe idona kadan da hannayena wadanda suka sha jan lalle tun na biki na. Yace "come here" babu musu na taka naje gabansa na tsaya, tun daga fuskata ya fara kallona har 'yan yatsun kafata. Ya hadiye wani mugun yawu daya sa na kara jin kunyar sa. Ya gyara zamansa yace "sit here" yana nuna min cinyarsa, nan ma babu musu na zauna. Ina zama na fahimci sako na ya samu karbuwa dan message din yaje har inda nake so yaje, na danyi dariya kadan, ya saka hannu yana shafa bare fatar cikina, murya can kasa yace "dariya kike yi min ko? Zan rama ne nima" na saka hannayena duk biyun na zagaye wuyansa sannan nace "sai dai ka rame" yayi murmushin gefen baki yace "really? Wanna bet?" Nace "yes" ya dora hannunsa akan kirjina ya fara shafawa a hankali, na lumshe ido na jikina yana amsar sakonsa na bude su akan fuskarsa mai dauke da murmushin mugunta yace "you still wanna bet?" Wannan karon ban bashi amsa ba, ya cigaba da abinda yake yi, nace cikin sarkewar murya, "ka takura musu da yawa fa" ya dan bata fuska yace nine na takura musu ko sune suka takura min?" Ya saka both hannayensa ya kama straps din half vest dina ya jawo ta kasa ya dawo da ita kan cikina, yace "better, yanzu sai muga waye ya takura wa wani a tsakanin ni da su" ina kallon cikin rinannun idonsa nace "in suka rame bashi kenan ba" yayi replacing half vest din da hannayensa yana kara lumshe ido, yace "wa yace miki ramewa zasuyi? A cikin 'yan kwanakin nan baki ga har girma suka kara ba sabida kulawar da suke samu? Nine dai nake ramewa saboda takura min da suke yi, sun hanani sakat, sam bana iya dauke ido na daga kansu, bana samun nutsuwa sai ina tare dasu, in ido na biyi tunanin su nake, in bacci nake mafarkin su nake......" Tun ina jin abinda yake cewa ina kuma fahimta har na daina fahimtar abinda yake cewa, na daina fahimtar komai, shima kansa mai maganar bana jin yana fahimtar me yake cewa, daga baya ma maganar ta gagara gaba daya. Mun manta da duk abinda ya faru a ranar, babu Takawa and his threats, babu Hajiya and her hypocrisy, babu khulsum and her food, a lokacin hatta Mommy da Daddy basa gabana, Sultan ne kadai a gabana, only him existed in my world kamar yadda shima ni kadai ce a tasa world din. Sai da akayi first round aka zauna break sannan na bashi labarin yadda mukayi dasu Hajiya, ban boye masa komai ba na gaya masa duk abinda suka ce min da amsar dana basu. Kamar yadda nayi tsammani, bai nuna damuwar sa koya tada hankalinsa ba sam, sai nuna min jin dadinsa da yayi akan yadda nayi tackling maganar da kuma trusting dinsa da nayi. Daga nan muka bar maganar muka cigaba daga inda muka tsaya. Hint ga matan aure, irin wannan time din shine best time discussing sensitive issue da mai gida, especially mai gidan da yake da temper ko kuma wanda baya daukan shawara, a lokacin he is relaxed, in body and in spirit, kan sa is fresh,and he is very excited, da wahala ki fadi abinda zai bata masa rai a lokacin. Amma fa bance ayi using time din wajan roko ba, ko kai tsegumin kishiya ba, gwara ayi amfani da time din gurin bawa mai gida shawara mai kyau wacce zata kara kafa miki fadar ku a gurinsa.
Washegari kamar yadda Sultan ya saba, in ya tafi masallachi baya dawowa sai gari ya waye, wanda na lura yana zama ne acan yayi karatun al'qurani, ni kuma wannan time din nake using in gyara dakunan sa, mostly daga nan bacci muke koma wa amma yau kitchen na tafi na barshi, yana ta mita wai shi bai ga amfanin in ce sai na koyi girki ba, tunda dai shi zan ke yiwa girkin nan kuma yace baya so ba shikenan ba sai in hakura. Ina shiga kitchen na tarar already Asma'u tana ciki, yau ma cewa tayi in cigaba da watching and learning, tana yin komai tana yi min bayani, ni kuma na bude kaina sosai ina fahimta, in naga abin tambaya in tambaya, har muka gama komai muka jera a dining sannan na tafi zanyi wanka. Ina shiga dakina wayata tana fara ringing na duba naga Daddy. Duk da cewa tun da nazo gidan kullum sai ya kirani ko kuma ni in kira shi mu gaisa amma yau sai da naji gaba na ya fadi. Nayi bismillah na dauki yawar, muryarsa naji wasai babu alamar damuwa a cikin ta, na sauke ajjiyar zuciya na gaishe shi, mun jima muna hira yana gaya min gobe zai tafi England kuma zai dan jima kafin ya dawo, nayi masa addu'ar fatan alkhairi, sai da muka gama maganganun mu sannan yace "jiya da daddare ai nazo palace, mai martaba sarki ya kira ni akan maganar ku, ya nuna min wasu pictures da banji dadin su ba, amma abinda na sani shine na yarda dake, tunda har baki kira ni kin gaya min menene ya faru ranar nan ba hakan na nufin kina ganin zaki iya handling koma menene, amma ina so ki sani, as much as I like sultan I like you more, amma hakan ba wai yana nufin bana son sultan ba, ina sonsa sosai kuma ina alfahari da abinda kike yi a rayuwarsa, but be very careful my daughter, your picture with a gun almost give me a heart attack, idan kinga abin yana kokarin yafi karfin ki just give me a call, ko ina kasar nan ko bana kasar nan I will always be there for you. Idan wani abin ya same ki a dalilin auren nan I will never forgive myself, saboda ni na amince ba saka ki a ciki duk kuwa da sanin sarkakiyar da take ciki. Zan yi yawa da Sultan din shima zamuyi magana dashi." A hankali nace "to Daddy, nagode. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" yace "Ameen" na jima a zaune a gurin bayan mun gama wayar, kawai sai naji hawaye suna zubomin bansan dalilin su ba. A duniya mutum bazai taba samun mai sonsa ba sama da iyayensa, kuma babban dace a duniya bayan kasancewarka musulmi shine samun iyaye na gari. Iyaye na gari sune ginshikin samun rayuwa ta gari.
Amina
Tun ranar da tabar gidan Moon kullum sai ta kira number din Ibrahim sau ba adadi amma har yanzu bai dauka ba. Wani lokacin sai ta ji haushi ta jefar da wayar tace yayi wa kansa, amma kuma in ta huce sai ta kuma dauka ta kira shi, still no response, kuma karin jin haushinta shine number din tana shiga dauka ne ba'a yi. In tayi tunanin ta rabu dashi kawai sai kuma ta yi tunanin to ko bashi da lafiya ne, he might be dying on a hospital bed ko kuma alone a gida for all she knows. Ranar dai da akayi kwana biyar ta shirya da niyyar yau dai zata yi finding out ko ma menene ya same shi. Ta shirya tsaf ta hau sama dakin Mommy ta gaya mata zata fita tana son siyan wasu 'yan kaya, Mommy ta bata kudi tace kuma ta dauki driver amma kar ta dade. Tana shiga mota ta gayawa driver supermarket din Ibrahim, tasan dole zata samu labarin sa a gurin staff din gurin. Tana shiga ta danyi 'yar siyayyar ta kadan tazo gurin cashier ta biya sannan tace "please manager dinku kuwa yana nan? I am a friend of his ina son ganinsa" matar ta danyi jim tana tunanin me zatace sannan tace "eh yana nan ma'am, amma I don't know ko zai ganki, in kina da number dinsa ki kirashi mana in yace ki shiga kinga shikenan" Amina tace "ai number din nasa bata shiga ne, I would have call him, just ki je kice masa Amina tazo tana son magana dashi" matar tayi saurin girgiza kanta "am sorry ma'am, bana son inyi laifi" Amina tace "OK, just show me ina office din nasa yake sai inje ni kadai" nan matar tayi mata kwatance. Ta hau saman benen da aka nuna mata tana kallon kofar offices din da suke a jere, a kofa ta uku taga an rubuta "manager" sai data sauke ajjiyar zuciya sannan tayi knocking, babu response, ta sake yi sannan ta murda hannun kofar, ga mamakin ta sai ta ji kofar a bude, ta tura ta shiga da sallama. Yana zaune akan kujerar sa yana danna laptop din gabansa. Looking as handsome as ever. Ya dago idanunsa ya dora akanta, sanyin AC office din ya saka ta dan rungume hannayenta tana shakar daddadan kamshin sa. Bai ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanu. Ta dan kirkiro murmushi ta karaso gaban desk din sa, tace "Can I sit down?" Nan ma babu amsa, ta dan zauna tana kallon haduwar office din, ta na feeling nervous, damn you Moon da kika saka nayi miki wannan alkawarin. Kamar daga sama taji yace "What do you want?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa, babu dariya sam a fuskarsa, zuciyar ta taji ta fara tafasa, a ranta tace "what am I even doing here? In Moon tana son ta san halin da yake ciki she should come by herself" ta mike tsaye cikin zafin rai tace "am sorry I bother you" da sauri ta fice daga office din kamar zata tashi sama. Har ta fara sauka stairs din sai kuma tayi wani tunani, wannan mutumin kar fa ya dauka wai ta damu da shine ya saka take ta kiran sa a waya kuma har tazo office dinsa, da sauri ta koma saman, ba tare da sallama ba ta kuma bude kofar ta tsaya a bakin kofar tana kallonsa tace "ba wai dan na damu da kai nake kiranka a waya ba, ba kuma wai dan na damu da kai nazo office dinka ba har da zaka wulakanta ni. Moon ce ta roke ni inyi haka, har kasa ta durkusa akan guiwoyinta sannan na yarda zan yi, dan haka save your arrogance for her not me, ka tattara duk wani guntun wulakancin ka and shove it up your handsome face" tana gama fadin haka ta buga kofar da karfi ta juya ta tafi tana murmushin jin dadin ta rama wulakancin da yayi mata, sosai taga yadda expression din fuskarsa ya chanza sanda ta ambaci sunan Moon, ita wannan soyayyar mamaki take bata. Ji tayi ya bude kofar da sauri ya biyo ta, bata waiga ba taci gaba da sauka stairs din yace "Amina wait please" ta juyo tana kallonsa tace "saboda me? Saboda kaji nace sakon Moon ne zan gaya maka? Wait, ya akayi ma kasan sunana? Ka yiwa kanka ai, zan koma in gaya mata kace baka son jin komai daga gareta" ta juya ta cigaba da sauka, tana jin sa ya biyo bayan ta yana kiranta amma bata waiga ba, tana gama sauko wa tayi hanyar fita, sai da takai bakin kofa sannan ta juyo, bai biyo ta ba, the mighty manager ba zai zubar da ajinsa a gaban yaran sa ba. Ta fita ta shiga mota suka koma gida. Tana ta tunani a ranta, wannan wacce irin soyayyace haka, wanne irin so ne Ibrahim yake yiwa Moon, duk da cewa kiri kiri moon ta zabi Sultan, duk irin abinda ya faru ranar nan amma har yanzu mare ambaton sunan ta ya chanza masa lissafi. Ita kam bata jin zata iya yiwa wani irin wannan son. Ta fara tunanin abinda ya faru ranar da aka kai Moon, bata taba tsammanin wai maganar zata wuce shikenan kamar ba'a yi ba, amma Moon wai ko Daddy ta hana a gaya wa, wanne irin so ne haka itama Moon take yi wa Sultan?.
Tana shiga gida ta dauko wayar ta, 6 missed calls from Ibrahim. Dariya tayi a bayyane, she got him right where she wants him, sai ta rama duk abinda yayi mata, sai ta ja ajinta san ranta. Kwanan su biyu a haka, ya turo messages sunfi a kirga, ya kira ta sau ba adadi amma bata kula shiba. Ranar kwana na ukun dai ya gaji, zuciyar sa tana ta yi masa sake saken menene sakon Moon din da Amina zata bashi? Is she OK? Kar dai ace wani abun ya faru da ita ranar nan bayan tafiyarsa. Yana tashi daga office ya biya ta restaurant ya ci abinci daga nan gidan su Moon ya wuce, direct ya doshi gate din gidan yayi horn, mai gadi ya leko ya ga motar bai bude gate din ba ya fito ya taho gurin sa, ya sauke glass din sa yana kallon mai gadin yace "Amina tana na kuwa" mai gadi yace "eh tana nan" ya cigaba da kallonsa, Ibrahim yace "zan iya shiga in ganta ko kuma in tsaya anan za'a kirawo min ita?" Da da sauri mai gadin yace "a'a bara a bude maka ka shiga ciki" still amma yana kallon Ibrahim, sai kuma ya dan yi gaba kamar zai tafi ya kuma juyowa ya kalli Ibrahim, sai ya dawo da baya, yace "ni kuwa bawan Allah kamar kaine ka taba zuwa nan a shekarun baya ka bani sako in bawa maimunatu" Ibrahim yaji yawun bakin sa ya bushe, yace "eh nine baba, ashe baka manta ni ba" baba habu ya washe baki yace "yauwa har naji dadi, ai bana manta fuska, in dai naga mutum ko mai tsahon shekaru ina iya gane shi" ya danyi shiru sannan yace "abinda yasa kaga na tambaye ka shine, bayan na bata sakon, lokacin zasu tafi England, ta bani wata katarda tace in baka. Tunda kuwa suka tafi kusan kullum sai ta kira ni ta tambaye ni kazo? Daga baya ni nace mata ta hakura ta daina kira, in kazo da kaina zan kira ta in baka ita kuyi magana" Ibrahim ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya runtse idonsa yana jin zafi a ransa, baba habu ya cigaba da cewa "ina fatan dai ba wajan ta kazo ba yanzu ba, saboda anyi auren ta satin daya wuce" Ibrahim ya bude idonsa yace "No, ba wajanta nazo ba, wajan Amina nazo, nasan anyi bikinta. Amma baba takardar da ta baka tana nan kuwa har yanzu?" Baba habu ya danyi tunani yace "ai shekarun ne da yawa, amma zan duba maka, inna ganta kafin ka tafi sai in baka" daga nan ya bude wa Ibrahim gate ya shiga sannan ya tafi kiran Amina. Tun da Ibrahim yayi packing idonsa yake rufe yana jin dachi a ransa. She trusted that he will come back shi yasa har ta bayar