Showing 18001 words to 21000 words out of 262297 words

Chapter 7 - Maimoon Hausa Novel Complete

samu kaina da kin zuwa islamiyya. Nasan ba Ibrahim ne ya daki Hafsat ba amma still ina ganin duk a sanadin alakata da shi ne komai ya faru.
Sai da na gama shiri zan kwanta sannan nazo kan gadon Hafsat na zauna na fara yi mata magana da harshen fulatanci. "Hafsat nasan yadda kike ji a ranki yanzu, kina jin tamkar duniya duka ta juya miki baya amma ina so ki sani ba haka bane. Ita duniya tana zuwa maka ne a yanda ka dauke ta, inka dauke ta da zafi to babu shakka zata zo maka da zafi. Ina so ki san cewa ni bani da komai a raina a game dake sai alkhairi, bana miki fatan komai sai na alkhairi, ban taba rukon ki a raina ba kuma kema ina rokon yafiyar ki idan na taba yi miki wani abu. Please Hafsat tunda muke ban taba neman alfarma a gurinki ba, dan Allah wata alfarma nake nema as a sister, idan kika yi min wannan nayi alkawarin bazan sake rokon wani abu a gurinki ba, please ina so komai ya wuce dan Allah kiyi abinda mommy tace, kizo muke yin karatu tare da Ibrahim, I assure you you will like him. Please sister just give us a chance" duk maganganun da nake bata cemin komai ba amma ni na tabbatar tana jina. Na tashi naje na kwanta nayi adduoi nayi bacci. Washegari ma duk mu biyun bamu je islamiyya ba, nayi wanka ina saka uniform sai ga Hafsat ta fito daga wanka ta bude fridge ta dauko fresh milk tana sha sai ta miko min tace "do you want some?" Nayi murmushi na karba nace mata "thank you" daga nan muka shirya muka fita class tare. Tun daga lokacin muka daidaita da Hafsat, muka koma yin alamuran mu kamar da. Hafsat ta fara zuwa gurin karatun mu da Ibrahim sai dai ba kullum ba, in taje su kan danyi magana kadan ba sosai ba.
Shakuwa ce sosai take shiga tsakanina da Ibrahim. Kullum muna tare tun daga 3pm har magrib. Kofar library ya zama permanent gurin zaman mu. Abin mamaki shine, kusan duk interest din mu daya; a duk subject nafi son maths shima haka, sport din da nake yi shi ne basketball kawai ranar sport shima sai na ganshi a gurin basketball, duk kanin mu muna da fara'a da surutu kuma bamu da fada. Kullum in aka tashi daga class Ibrahim sai ya rakani har bakin hostel, haka zalika in aka tashi daga islamiyya ta dare ko ta assuba sai ya rakoni har sai na shiga hostel sannan zai koma. Tun ana min surutu ina damuwa har na saba. Zan iya cewa kusan komai na Ibrahim na sani, duk wani abu da yayi idan bama tare in muka hadu sai ya bani labari. Rannan muna zaune a gurin zaman mu sai sister dinsa ta kira shi a waya, ya dauka suka fara hira da yarabanci, ni sai abin ya bani dariya saboda ban taba jin yana yarabanci ba dan har manta wa nake yi shi yaroba ne, daga dukkan alama fada yake mata. Sai da suka gama sannan ya miko min yace mu gaisa, na karba tare da yi mata sallama ta amsa min da accent din yaroba. Muka gaisa babu yabo babu fallasa na mika masa wayar sukayi sallama ya kashe. Nace masa "what is her name?" Yace "Maryam" na sake tambaya "how old is she?" Yace "23" sai a lokacin na sake realising age gap din da yake tsakanina da Ibrahim. Nan yake bani labarin cewa maganar auren ta ne ya taso, ta kawo miji step father dinsu baiyi approving ba shine take so shi Ibrahim din ya shiga cikin maganar shi kuma yaki. Anan na fahimci cewa Ibrahim yana mugun yiwa step father dinsa biyayya like shi yake da final say a duk abinda ya shafesu.
Ibrahim sam ba mai yawan abokai bane dan ban taba ganinsa ko jin sa yana waya da wani aboki ba. Rannan mun tashi daga islamiyya. Nace " why aren't you going into town? Yace "I have nothing to do in town, ni ban san kowa a garin nan ba, school din nan ta bani gurin zama a cikin quarters, tana bani abinci kullum" ya tsaya da tafiya ya juyo yana kallona "and you are here also, so mai zai kaini cikin gari?" Nayi murmushi naji dadi har cikin raina nace "amma tunda har kazo Abuja, why not baza kayi using this chance ba ka ga gari, it is a very nice town, besides, u never know wa zaka hadu dashi a cikin garin. Ka sani ko kayi budurwa. Dariya yayi sosai yana kallona da lumsassun idanuwansa, ya langwabe kai gefe kamar mai shirin yin shagwaba yace "ni nayi kankanta da yin budurwa. Baki ganin ni yaro ne" yadda yayi maganar ne ya bani dariya nima nace "yaro a ina? I thought 25years kake? To in bakayi budurwa ba sai ka fara furfura tukunna? Ya kalleni da serious look yace "Allah da gaske nake bani da budurwa, sai later, da nace sai na gama service amma yanzu ina tunanin anya zan iya jira kuwa? In na tsaya wasa zuciya ta zata iya fitowa daga kirjina" yadda yake maganar a hankali da yanayin da yake kallona yasa naji tsigar jikina tana tashi. Banyi aune ba sai ji nayi Amira ta kama hannuna tana jana gefe tare da cewa "to love birds, times up, goodnight sir, sleep tight " da sauri da sauri take jana muna tafiya hostel ni kuwa har yanzu ido na a kansa suke shima kuma ni yake kallo, sai da muka je bakin gate din hostel sannan naga yayi min alamun 😘 nayi sauri na dauke kaina ban kuma kallon inda yake ba. Muna shiga hostel Amira ta jani gefe "what are you doing Moon? Kinga kallon da yake miki kuwa? Shaidan fa is real komai iliminsa kema kuma komai kame kanki da saka hijabin ki ba guarantee bane na cewa shaidan ba zai yi nasara akan ku ba" raina ya baci da accusation din Amira nace mata "Amira mutumin nan fa ba saurayina bane, we are just friends, sannan kuma bama kebewa mu kadai ni dashi, kullum a waje muke inda kowa zai gan mu" tace "ni ban taba ganin inda saurayi da budurwa za'a keyin friendship ba, you are deceiving yourselves, ko makaho ya shafa fuskokin ku yasan cewa something is there" nace "saurayi da budurwa kika ce. He maybe saurayi amma ni ba budurwa bace" tayi min kallon sama da kasa tace "oh ke 'yar jaririyace kenan ko? Ji nake yanzu haka ma period kike yi? Wanne girma kuma zakiyi nan gaba bayan already hormones din adolescent sun fara aiki a jikin ki. You are a woman now whether you are full breasted or not, dole akwai attraction tsakanin ki da shi" nayi sauri nace mata "am not attracted to him" tace "really? " tayi tafiyarta ta barni.

Episode Sixteen : The Letter

Har na karasa dakin mu ina tunanin maganganun Amira. Tabbas duk abinda ta fada gaskiyane. I know my biology and I know I am in adolescent stage. But am I really attracted to Ibrahim? It is not as if we are in love or anything amma kuma do i even know what love is? Am I ready for this? Har na kwanta ina ta lissafi a raina. Soyayya da Ibrahim ba abu ne me yiwuwa ba. Wata tafiya ce mai tsaho. Family na, family n shi, everyone will be against us. Hatta Hafsat ta saurara masa ne yanzu saboda nace mata ba soyayya tsakani na dashi. But i know what I am feeling. Ba zance ina son shi ba saboda ban san menene son ba. Amma nasan ina son kasancewa tare dashi, yana sani dariya, kuma duk sanda bana tare dashi inajin kamar ina missing wani abu. Is this love 💟? Ni na san ba zan iya yiwa Hafsat wannan tambayar ba in ba so nake in tsokano tsuliyar dodo ba. Tambayar da nake yiwa kaina itace: if abinda nake ji shine love din, am I willing to take the chance for him? And more important, is he willing to take the chance for me?
Tun daga lokacin sai na samu kaina da yin baya baya da Ibrahim. Bana barin mu hada ido dashi sam, in ya taho zai rako ni kuma nakan jawo Amira mu tafi tare, ita ma kuma Amiran ba ta ki saboda ta fahimci maganar da tayi min rannan ne ta saka nake gyarawa. Kullum in muna tafiya kuma maganar mu bata wuce ta karatu ko labari gida.
Muna haka har muka fara exams komai ya koma serious, Amira ma tayi joining karatun mu, kullum tare muke karatu mu uku shi kuma Ibrahim in mun gama sai ya dunga yi mana questions muna amsawa. Ana gobe zamu yi hutu mun fito daga Exam sai Ibrahim yayi kirana, muka tafi ni da Amira. Muna zuwa muka tarar dashi yana waya gida da yarabanci. Amira da sunkuyo dai dai kunnena tana dariya, kawai sai na samu kaina da jin haushin ta. Sai da ya gama wayar sannan ya kallemu yace "so u guys are going home tomorrow, right?" Amira tace "yessir" yayi dariya yace "oh su Amira harda saurin amsawa ko? Wato kin gaji da ganin mu ko? Dadinta dai muma gidan zamu tafi muma mu huta" sai a sannan nayi magana nace "are u going home also" ya kalleni da seriousness yace "yes, i am going tomorrow, there is nothing for me to do here in kun tafi" na hadiye wani kululu da ya tsaya min a wuya na nace a hankali "ok". Mukayi shiru for sometimes sannan yace "i will see you guys tomorrow before you go" Amira ce kawai ta bashi amsa da ok
sir. Daganan muka tafi hostel. Duk jikina a sanyaye nake shirin tafiya, tamkar wacce ta tashi daga jinya haka nake ji na. Washegari tun a assembly ground nake ware ido ko zan ganshi amma babu shi babu alamarsa. Gashi wannan abun da ya tsaya min a makogwaro na har yanzu yaki wucewa. Wajen karfe goma aka bude get motoci suka fara shigowa. Hafsat sai ware ido take tana neman motar gidan mu ni kuwa adduah nake yi a raina kar suzo yanzu sai na ganshi. Muna cikin haka na hango motar mu tana shigowa, na lura Hafsat bata ganta ba sai nayi sauri nace mata "Hafsat zan danje toilet kafin azo daukan mu" batare data kalli inda nake ba tace "ok" na juya da sauri nayi hanyar classes ina ta waige waigen ko zan ganshi, har naje get din hostel ban banshi ba, kuma na tarar har an rufe get din dan haka na juyo, hawaye naji mai zafi yana tahowa daga kirjina amma naki na barshi ya karaso idona saboda kar a gani a tambayeni dalilinsa. Ina tafiya kaina a kasa naji an kama hannuna an jani da sauri cikin wani class, da sauri na kwace hannuna ina neman hanyar gudu sannan naji wannan mayataccen kamshin nasa ya ziyarci hancina, na juyo da sauri muka hada ido. Ya saka complete kaki na NYSC a jikin sa, p-cap din ya juya ta tana kallon bayansa, da wata katuwar school bag a goye a bayansa. Fuskarsa babu murmushi. Mun jima muna kallon juna sannan nace"i thought ka tafi" ya hadiye yawu adams apple dinsa ya motsa sannan yace "I am sorry, an kira mu meeting ne tun safe, i was really pissed na dauka bazan same ki ba" naji dadin maganarsa har cikin raina, take naji wannan kululun da ya tsaya min a wuya ya narke yana tafiya. Nayi murmushi nima nace "I was afraid ka tafi without saying goodbye" ya matso gaf dani yanda har muna iya jin lumfashin juna, sa saka hannayensa biyu ya ruko fuskata idonsa cikin nawa yace "I will never" a can kasan zuciya ta nake jin tana min warning cewa in kwace fuskata daga hannunsa in matsa daga kusa dashi amma jikina yaki yayi responding, na kasa koda dauke ido daga cikin nasa ballantana in matsa. A hankali ya sauke idonsa daga ido na zuwa kan lips dina sannan ya fara sauko da fuskarsa zuwa ta wa. I was screaming at myself from the inside, nasan what he was about to do, nasan kuma it is wrong but I failed to stop him. Kamar wanda akayi wa shocking sai kuma yayi baya da sauri sannan ya juwa min baya yana furta "A'uzubillahi minash shaidanir rajim" sannan ba tare da ya kalleni ba yace "go maimunatu, just go" sai a sannan naji jikina da dawo dai dai, da sauri na bude kofar class din na futa jikina yana ta rawa. Ina fita na hango Hafsat tana tahowa daga hanyar hostel, daga dukkan alama ni take nema, gurinta na tafi da sauri ina kiran ta. A tare muka karasa gurin motar mu Ya Walid yana ta fada wai na bata masa lokaci, ni kuwa hankali na har lokacin bai gama dawowa jikina ba. Muna shiga mota sai ga Amira da sauri tana tsayar damu. Muna tsayawa ta bani wani littafi wai inji Ibrahim. Wani novel dinsa ne Sands of time. Abin mamakin shine ni ban ce masa ina so ba, asali ma ni ba ma'abociyar karatun novel bace. Na karba na saka a hand bag dina muka yi sallama da amira muka tafi.
Kafin muje gida har na ware, Ya Walid yana gaya mana su Inna sun zo tare da Amina (wata cousin din mu sa'a ta a 'yalleman) dan haka muna zuwa gida da murnar mu muka tafi gurin mommy, daddy baya kasar a lokacin, muka tarar an shirya mana abinciccika iri iri, nan muka hadu gaba daya a falon su inna har daada muna cin abinci muna hirar yaushe gamo, Ya Walid yayi tayi mana hotuna saboda washegari zai tafi England hutun sa ya kare. Gaskiya ba abinda yafi Family dadi. Kowa yabar gida gida ya barshi. Har dare muna tare ana ta hira, ga mamakina Hafsat bata yi zancen Ibrahim ba. Sai mommy ce ma tace " Hafsat kina zuwa extra lessons din kuwa?" Hafsat tace "Eh, mommy ina zuwa" mommy tace "good, saboda bana son Moon take zama ita kadai tare da wannan malamin naku, kuma bana son in hana ta saboda naga tana benefitting" sai a sannan na gane manufar mommy ta hada mu da Hafsat, lallai ance abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala ba zai hango ba.
Sai da dare yayi sannan muka koma part din mu. Na hada ruwan wanka na shiga tub sannan na fara lissafa abubuwan da suka faru. Tabbas maganar da Amira ta gayamin gaskiya ce. Shaidan yana iya shiga tsakanin 'yan uwa ciki daya ma ballan tana mu. Kuma tabbas I am attracted to Ibrahim kamar yadda ta fada, tunda gashi dazu ya kusa kissing dina kuma ban hana shi ba. I am weak. Zuciya ta is too soft. Ko zan cigaba da alaka da Ibrahim sai na dage sosai. Daganan na tuna da littafinsa a cikin hand bag dina. Bayan na fito daga wanka da shirya cikin riga da wando na bacci sai na dauko littafin na kwanta ina dubawa kawai sai naga takarda ta fado. Ina dauka naji kanshin turarensa a jiki, na bude naga rubutun sa kamar haka.
MAIMUNATU
I CAN NO LONGER STOP MYSELF FROM SAYING THIS, BELIEVE ME I TRIED. MAIMUNATU I LOVE YOU. I NEVER KNOW WHAT LOVE FEELS LIKE BUT I AM 100% SURE THAT THIS IS IT.
I AM NOT SURE IF YOU FEEL ABOUT ME AS I FEEL ABOUT YOU. PLEASE MAIMUNATU, IF MY ANSWER IS NO, CALL THE NUMBER AT THE END OF THIS LETTER JUST SAY NO, THEN I WILL ASK FOR TRANSFER BEFORE YOU RESUME. I CAN'T KEEP SEEING YOU KNOWING YOU WON'T BE MINE.
YOURS IN LOVE
IBRAHIM

An zo gurin, will Moon say yes knowing the consequences or will she say no knowing she will never see him again?


Episode seventeen: Reply

Na jima ina karanta takardar hannuna ina maimaitawa. Amma Ibrahim baka yi min adalci ba, yanzu me kake so ince maka? Yes or No? Ni dai nasan koda wasa bazan tunkari Hafsat da sunan neman shawara ba. Na saka karanta takardar kamar me saka ran ganin ganin chanji a rubutun. Tabbas handwriting dinsa ne, kuma kamshin turarensa ne. Na kai ido na kan number daya rubuta a kasan takardar lokaci daya na haddace ta. Na ninke takardar na mayar cikin littafin, a lokacin Hafsat ta shigo tana hamma, ta kalleni tace " kasa, a gidan ma sai kinyi baccin wuri" nayi dariya ban bata amsa ba saboda I am not in the mood. Ina kallonta tana shirin wanka na dauko littafin Ibrahim na fara karantawa saboda nasan sa idon Hafsa, tana shiga wanka na rufe littafin na saka a kasan filona na kwanta akai. Har ta fito ta shirya ta kwanta banyi bacci ba ina ta sakawa da warwarewa. What should I do? Ni nasan ina son Ibrahim har cikin rai na, wannan bani da tantama akai, amma nasan abu ne mai wahala kasancewar mu tare. Bani da problem da daddy sai mommy nake ji, kallo daya idan tayi min sai na gwammace ban taba ganin Ibrahim ba, Inna da baffa da kawunnai na na 'yalleman zasu iya haka rami su binne ni akan su barni in auri Ibrahim. Ina son family na fiye da komai dan haka maganar inbijire musu ma bata taso ba. A daya side din kuma inna cewa Ibrahim no nasan ba wasa yake yi ba akan maganar barin school din mu, kuma bazan sake ganin saba har abada sai dai wani ikon Allah. Anya zuciya ta zata iya daukan haka kuwa? Anya zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba kuwa? What should I do? A haka bacci barawo ya dauke ni. Cikin bacci nayi mafarki wai gashi muna tafiya da family na a mota a nata hira ana dariya sai naga Ibrahim yana tafiya a kasa shi kadai, sai yayi mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login