Showing 222001 words to 225000 words out of 262297 words
nayi ba kafin in samu bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai kusan assuba, na tashi zaune naga ummee a kusa dani tana bacci, abinda ya fara fado min a raina shine sultan, ko zai iya tashi sallar asuba yau? Dan nasan ba bacci zai yi ba kar yazo kuma yayi missing masallaci. Na tashi nayo alwala nazo na dauki alqurnin dana gani a gurin sallah na fara karantawa a hankali dan kar in tashi ummee, har sai da naji anyi assalatu sannan na tashe ta ni kuma na tayar da sallah. Da safe duk jikina babu dadi, na dauki waya ta da niyyar kiran sultan yafi a kirga ina ajiyewa, daga karshe dai na bawa Hafsat sim card dina nace to nace ta bani kar ta bani, tana dariya tace "ai kuwa ba zan baki ba ko zakiyi kukan jini". Tare muka shiga kitchen da Ummee, she is an amazing cook, muna aiki muna hira, nan na bata labarin cewa kafin inyi aure ban iya girki ba, sai daga baya na koya, ai kuwa tayi min alkawarin sai ta mayar dani kwararriya a girki. A kitchen din muka zuba abincin a kwano daya muka ci, ban san me yasa ba kawai naji na saki jikina da ita, ji nake yi kamar dama can nasan ta all my life.
Bayan nayi sallar azahar, ina zaune a dakin ummee ina tunanin ko me sultan yake yi yanzu? Sai ga ummee ta shigo, ta samu guri ta zauna a bakin gado, na dan juyo na kalleta tayi min murmushi. Tace " maimunatu so nake ki bani labarin sultan, tell me all about him, I want to know everything bana son ki boye min komai" na gyara zama na ina tunanin ta ina zan fara ne, she is his mother, she deserves to know everything. Nan na fara daga labarin da Takawa ya bamu na abinda ya faru bayan an dauke ta daga gidan, na gaya mata abinda sarki abdallah yayi, tun anan ta fara sharar hawaye, na dora da bata labarin rayuwar da sultan yayi tare da mahaifinsa, ban boye mata komai ba har zamansa a gidan kangararru da rayuwarsa a America, na gaya mata past drinking habit din sultan amma na tabbatar mata cewa yanzu ya daina, amma ban gaya mata dalilin fara shan giyar tasa na, na gaya mata haduwata dashi da yadda Daddy ya dauko shi ya dawo dashi gidan mu, amma ban gaya mata kiyayyar da Mommy tayi masa faga farko ba, na bata labarin auren mu da kuma sanadin karyewar asirin Takawa zuwa halin da muke ciki a yanzu, na dora da cewa "Sultan is emotionally not stable, shi yasa yaki zuwa, har yanzu kullum yana tunanin cewa mutane basa sonsa, da kyar ya yadda cewa Takawa yana sonsa da gaske, kema kuma yana tunanin ba sonsa kike ba saboda yana ganin kinyi abundaning dinsa tsahon shekaru baki taba neman sa ba, he is just scared to get his heart broken" bata cemin komai va saboda kukan da take yi, ta tashi ta fita daga dakin. She needed to be alone and I understand. Har bayan la'asar ban kuma ganin ta ba. Zayed yazo ya dauke mu ni da Hafsat muka tafi yawo, ya nuna min birnin Riyadh, garin ya hadu fiye da tunani na, lallai larabawa karshe ne gurin dukiya, ga tsari ga doka. Da magrib muka je gidan su Zayed na gaishe su, sun karbe ni sosai a matsayin kanwar Hafsat, Zayed yace mu bar Khairat ta gaya musu da kanta when she is good and ready. Muna komawa gidan Ummee muka same ta ita kadai a zaune a palon ta, akan kujerar dana sameta jiya, idonta akan kofa, na lura ta dan rame kadan akan jiya. Muna shigowa tayi mana murmushi, tace tana kallona "na dauka kin gudu" na karasa da sauri nace mata "I will never" .
Da daddare sai ka wayar sultan a wayar Hafsat, ta nuna min screen din, na daga kafada, ta dauka da sallama, daga ganin yadda Hafsat take yamutsa fuska nasan masifa yake mata, sai da ta barshi ya gama sannan tace "kana magana da Hafsat ne ba da maimuna ba" sun jima suna ta rigima daga alama cewa yake ta bani wayar ita kuma taki, da ta gaji ta kashe wayar tana kallona "he is really pissed off, yana neman ya kashe min dodon kunne" and my heart went out to sultan, yana can nasan ya hargitsa gidan mu gaba daya, poor Amir shi zaifi kowa dandanar zafin sultan. I hate hurting sultan amma shi zuma ne sai da wuta, he will never come to his mother in ba haka nayi masa ba. Duk hirar da muke yi Ummee tana jin mu amma tayi shiru, she seems deeply in thoughts. Sai bayan munyi sallama da Hafsat naje nayi shirin kwanciya na kwanta ina ta tunanin sultan sai gata ta shigo, ta zauna a bakin gado tana kallona tace "yana son yasan abinda ya hanani zuwa wajansa ko? Yana son yasan ko ina sonsa ko bana son sa? To ga labari zan baki ki gaya masa" na tashi zaune na jingina da jikin frame din gadon ina sauraron ta. Tace "bayan an dauko ni daga Nigeria, ban taho da komai ba, babu miji babu da, bani da ko hoton sa, daga ni sai kayan bacci a jikina sai abaya da hijab, babu wanda zai gane halinda na shiga a lokacin sai uwar da aka raba da mijinta da kuma dan karamin danta, suna farkon duniya ita tana karshe. Nayi kuka kamar raina zai fita, gaba daya family aka taru a kaina telling me cewa na basu mamaki, na zubar musu da mutuncin su a cikin jama'ar, saboda ba karamin abun kunya bane ace 'yarka budurwa ta gudu da saurayi, kowa abinda zai fada daban. Gashi an samu matsala da familyn wanda aka yi niyyar hadamu aure da shi. Aka sake sakani a daki aka rufe. Babu abinda yayi keeping dina alive a lokacin shine maganar sadiq da yace he will come for me, so I waited, not patiently but I waited. Kwana daya sadiq bai zo ba kwana na biyu shiru, a kwana na ukun ina dakina ina aikin dana saba wato kuka sai ga ummina tazo tayi kirana, ina zuwa palo na samu babana da uncle dina a zazzaune, na gaishe su sai suka miko min takarda suka ce daga Nigeria, da sauri na da bude ina so inji labarin Sadiq da Sultan amma me zan gani, wasika ce daga Sadiq cewa ya sake ni, bai yi stating dalili ba kawai dai ya sakeni, in his own handwriting, after all what we went through together, after irin rabuwar da mukayi da kuma irin alkawarin da yayi min cewa he will come for me, amma abinda na samu daga gare shi shine saki. I list everything, the trust of my family, my dignity, my husband and my son. I was totally broken. Na shirya akan lallai sai naje Nigeria na tambayi sadiq dalilin da yasa yayi min abinda yayi min, kuma in karbo dana, amma family na suna ganin yin hakan bashi da amfani, ya wulakanta ni ya yaudare ni ya rabani da iyayena, sannan kuma ya sake ni, to me zanje inyi masa kuma, sunce matsoraci ne shi, nusari wanda ba zai iya fighting for his family ba. Na nuna musu ni ba ta sadiq nake yi ba ta Sultan nake yi, amma still suka hana ni xuwa, abinda ummi na tace min shine inna je ma ba bani shi zasuyi ba, kuma nasan gaskiya ta fada ba zasu bani shiba, ta gaya min cewa inna dauko shi ba taho dashi gurina what kind of life zan bashi a matsayin dan mace babu uba? Duk abinda mutane suke fada akaina cewa yawon banza na tafi sai su tabbatar kenan in suka ganni da 'da babu uba, tace duk tsahon shekaru sultan shi zai neme ni da kansa. Duk na nuna musu kamar na yarda amma suna sakin jiki dani na gudu, unlucky for me wani friend din babana ya ganni a airport ya kira waya ya fada, aka zo aka sake mayar dani gida, nan take magana ta fara fita a cikin mutane, cewa khairat 'yar faisal abdallah ta fara yawon banza, ance na gudu da saurayi shekara uku sannan aka samo ni, fada da nasiha babu irin wadda ba'a yi min ba amma ni hankali na yana Nigeria, na gwada guduwa yafi a kirga, daga baya family na suka hadu suka yanke shawara, aka yi bannin dina daga fita daga kasar saudiyya gaba daya, ko baje airport da zarar anyi thumb printing dina shikenan ba za'a barni in shiga jirgi ba. Tun daga lokacin har yau ban taba taka kafata outside Saudi Arabia ba. I tried everything i can to get to sultan, I wrote him letters but they all turned back. My family made sure sunyi cutting duk wata hanya da zanyi contacting Nigeria. Su a ganinsu gurin sadiq nake son komawa, inna yi musu maganar sultan sai suce min zai neme ni da kansa. Da addu'ar da nasiha na fara hakura da zuwa Nigeria, amma ko dai da rana daya ban taba dauke hankali na daga kan sultan ba. Na yadda da abinda ummi na take gaya min cewa sultan zai neme ni da kansa, saboda nasan da ya fara hankali zai fara neman ina mahaifiyarsa take, kuma nasan Sadiq zai gaya masa labari na kuma nasan zai neme ni. I waited years in and years out amma shiru. Babu irin abinda ba'a yi min ba akan inyi aure amma naki, ba wai sadiq nake jira ba, bana son sultan yazo ya tarar na sake wani family din, kar yayi tunanin na manta dashi ko bana sonsa, I stayed alone for him, very lonely. Ina kallon 'yan'uwana maza da mata kowa yana yin aure yana barin gida amma ni naki inyi aure. Ina ta lissafa shekarun sultan, lokacin da na san cewa he is old enough ace ya mallaki hankalinsa ya fara nema na, a lokacin na kara saka ran zuwanshi, ban taba tsammanin cewa dana bai ma san wacece ni ba, ban taba tsammanin Sadiq ya manta dani ba. Da shekaru suka ja sai na fara tsoron ko wani abun ya same shi shi yasa bai neme ni ba har yanzu" kuka yaci karfinta tayi shiru, sai data tsagaita da kukan sannan taci gaba "I was so lonely and depressed, sai babana ya bani jari yace in fara business, it will keep me busy as I waited for my son, nan na fara kasuwanci, from small scale ina dan siyan kayayyaki ina siyarwa, Allah ya saka min albarka a ciki, nan take arzikina ya fara habaka, within few years na fara aikawa kasashen waje ana saro min kaya ina siyarwa, har na zama dealer nake supplying manyan shagunan garin nan da kaya. Amma dai dai da rana daya ban taba cire ran sultan zai zo ba, tunda na gina gidan nan na dawo duk sanda mota ta tsaya a bakin gate sai gaba na ya fadi ina saka ran shine yazo, amma shiru. Na kebe kaina daga cikin mutane ne saboda bana son maganganun da akeyi a kaina. Nasan Zayed yayi aure amma bansan wa ya aura ba, lokacin da yazo nan shida sister dinki naga cewa she is African kawai sai naji ina sonta, I told her about sultan. You have no idea how I felt sanda kika ce min ke matarsa ce" ta goge hawayenta ta juyo tana kallona "How long do you think zaiyi taking kafin yazo?" Nace "one week, at most, two weeks, shima saboda sai ya nemi visa ne" . Tayi murmushi tace "then we will wait for him, together".
Episode Eighty Nine : Khairat 2
Na taso na dawo kusa da ita na zauna nace "yes Ummee, we will. Nayi miki alkawarin Sultan zai zo gidan nan, kuma in yazo zaki yi mamakin sa, dan duk wannan zuciyar da wannan fushin na dan lokaci ne, haka yake, akwai saurin hawa kuma akwai saurin sauka, I assure you yana ganinki shikenan komai zai wuce, he is just not sure of yadda zaki karbe shi ne, duk wannan girman jikin da wannan kwarjinin a ido ne kawai, in side him he is the kindest man I have ever known, yana da tsananin tausayi da kuma kokarin kyautatawa mutane, ko da kuwa wadanda suka zalince shine bai damu ba, he said kyautatawa mutane makes him feel good shi yasa yake yi, ballantana ke da kika haife shi, kallo daya zaiyi miki and it will all be over, he will take you in his arms and cry on your shoulders, he will love you fiye da yadda kike tsammani, zai zamar miki 'da daya tamkar da dubu, he will feel Lucky to have you as his mother" sosai Maganganu na sun kwantar mata da hankali dan har murmushi na gani akan lips dinta, ta kama hannayena duka biyun tace "Maimunatu bansan me zance miki ba daga ke har iyayenki, you are really an angel a rayuwar dana, bani da bakin da zan gode miki sai dai in dawwama har karshen rayuwata ina yi miki addu'ar" na dora hannunta daya akan cikina tace "ubangiji Allah ya jagoranci rayuwarki, da duk kanin zuri'ar ki, ya baku kyakykyawar rayuwa fil duniya wal ahkhira, Allah ya daga garajarki da duk kanin ahlinki, Allah ya kade duk wani sharri dake cikin rayuwar ku ya tabbatar da alkhairi a duk al'amuranki, Allah yayi miki sakayya a bisa duk abinda kika yi a rayuwar sultan. Allah ya albarkaci zuri'arki yasa su zamo sanyin idaniya a gare mu baki daya. Allah kuma ya kara soyayya a tsakanin ki keda mijinki, ya dauwamar da zaman lafiya a tsakaninku, ya sa ku kasance tare har karshen yaruwar ku" duk abinda take fada ina cewa amin, kuma ina jin dadi har raina, sai da ta gama yi min addu'ar sannan ta jawo ni jikinta ta rungume tace "Nagode Maimunatu".
Kwana biyu bayan nan, ni gani nake yi ma kamar nafi sultan damuwa, komai nake yi hankali na yana kansa, da kaina nace Hafsat ta bani sim card dina amma taki, kullum sultan yana cikin kiran wayar Hafsat, tun yana yi mata masifa har ya koma bata hakuri yana lallashinta, ita kuma tace sai ta rama fadan da yayi mata, innaji suna waya sai in ji kamar in kwace wayar amma nasan muna yin magana da sultan zai kalallame ni yace in dawo Nigeria, I don't think I can resist him in inajin muryarsa. Little khairat ce ta zama babbar kawara, tana ta rarrafenta ko'ina har ta fara tsayawa, in tana gurina babu abinda yake kaita gurin Hafsat sai in zata ci abinci. Ummee kuwa sosai muka kara sabawa da ita. Kamar yadda tayi min alkawari haka ta zage wajan koyamin girki, irin abincin larabawa iri iri haka take koyamin, babu abinda take so irin in zauna inyi ta bata labarin sultan, wannan kullum shine abin hirar mu. Hotunan sa kuwa na waya ta ta gansu yafi a kirga. A wayar Hafsat na hada ta da Mommy suka gaisa, nan take suka kulla kawance. Mommy ta gaya min ta yaba da ita tun kafin ma ta ganta.
Ranar dana kwana biyar a Riyadh, muna dinner da daddare sai ga kiran sultan a wayar Hafsat. Ta nuna min screen din sannan ta daga. Sun danyi magana sannan tace min "yace in ba zaki karbi wayar ba in saka shi a speaker zai yi miki magana, na kalli Ummee naga alamun anticipation a fuskar ta, she has never heard her son's voice tun da suka rabu, na gyada wa Hafsat kai, ta saka wayar a speaker ta ajiye a kusa dani, naji muryarsa "Moon please listen to me, why are you punishing me for the crime I didn't commit? Ni laifin me nayi wai? Kina so zuciyata ta buga in mutu ko?" Na danyi murmushi, dadin baki yake so yayi min, ya cigaba da magana, "Love please, nasan kinaji na, kuma nasan me kike so, I promise you zanzo amma kinsan it will take time, dan Allah na wahala haka, kar kice ba zaki yi min magana ba sai nazo, I can't take it kin sani" Ummee ta taso ta dauki wayar da fitar daga hands free ta miko min, na karba na ajiye khairat da take bacci a kan cinya ta, na mike na fita veranda, ina jiyo Hafsat tana gyaran muryar tsokana amma ban kula taba, na saka wayar a kunne na nace "My Love" kamar ba zaiyi magana ba amma ina jiyo numfashinsa a hankali, sannan yace "why are you doing this?" Nace "I just want you to come and see your mother, shikenan" yace "you should have talk to me ai, ki gaya min ga abinda kike so, you know I can do anything for you love" nace "nayi maka maganar ai kaki yadda, babu yadda zanyi da kai ne" ya dan yi shiru sannan yace "you have no idea how damn good it feels to hear your voice" Nace "me too" yace "ba wani nan, da kin damu dani ai da baki kashe wayarki ba, you always say kina sona but nasan ko rabin wanda nake miki ba kya yimin" nace "kai ma kasan ba haka bane ba. Kawai dai we show our love ne in different ways ni da kai. Zuwa na garin nan da kashe wayata da nayi are all ways of showing you how much I love you. Sometimes you have to sacrifice something to get something better" yace "zaki yi min dadin baki ko?" Nayi dariya, nace "tun da nazo garin nan bana samun bacci me dadi saboda babu kai, ba karamin dauriya nayi ba these five days" yace "uhmmm, na ji ki dai amma ban yarda ba, kina can kina sharar baccin ki kin barni da rungumar pillow da mafarkai ko?" Nace "sorry" yayi ajjiyar zuciya yace "so, how is she?" Nace "come and see for yourself" yace "hmmm baza ki fada min ba kenan ko?" Nace "eh