Showing 138001 words to 141000 words out of 262297 words

Chapter 47 - Maimoon Hausa Novel Complete

never find out" Amira tace "ni fa har yanxu ban sayi gown din da zan saka ranar bridal shower ba, kowa ya gama shirin sa ban dani, bayan itama da akwai abubuwan da ban saya ba" nayi sauri na zauna kusa da ita nace "kinga kawata, kuje ke da Amina gurin Mommy ku lallabata ta barni in fita, sai muje in kaiki ki siyo, wallahi na gaji da zaman gidan nan. Tunda sunce rana ce basa so in shiga ai yau babu ranar ma" Amira tace "ni kinsan Mommy yanzu ba shiri muke yi da ita sosai ba, sai dai ko Amina" na juya gurin Amina nace "please yaya Amina, kije ki tambayar min" ta bata rai tace "to in kun fita me zaki siyo min?" Nace "duk abinda kike so" nan ta jera min uban list na abubuwan da take so in siyo mata, duk nace naji na yarda. Ta fita muka zauna zaman jira. Sai da tayi wajen minti talatin sannan ta dawo tana bata fuska, har na sare, sai kuma tayi dariya tace "an barki, amma ki saka dogon hijab da nikab" murna kamar in cinye Amina, dan ji nake gaba daya na tsani kaina saboda zaman gida. Na kira Sultan a waya na gaya masa zamu fita da Amira, yace "OK, in kun gama ki yi min magana, nima ina son zamu je wani guri" nayi shiru bance komai ba, yace "please say yes mana, yaushe rabon da in ganki wajan three days" nace "ina zamu je?" Yace "where it all began, ina so muje muci abinci a Hilton, anan na fara ganinki" kawai sai naji ba zan iya ce masa no ba, nace "OK" yana ta murna na kashe wayar. Da sauri na shirya muka fita, har wadanda suke palo basu gane ni ce na fita ba saboda na rufe fuskata, daya daga cikin motocin Sultan na gani na leka naga key a jiki kawai na shiga na tayar, Amira ta shiga muka tafi. A gate mai gadi kin budemin yayi sai da nayi magana yaji muryata sannan ya bude yana dariya. Wani supermarket tayi min kwatance, ni ban taba shigar sa bama ina dai ganinsa a hanya, ita ma tace bata taba zuwa ba an dai ce mata akwai kaya masu kyau a can. Muna zuwa muka yi packing, na chire nikab dina na ajiye a mota, muka shiga, karshen haduwa gurin ya hadu, kaya kam akwai su, ga shi komai a tsare, nan da nan Amira ta fara lodar kaya, ni kam ban sayi komai ba saboda babu abinda nake bukata, a wajen siyan gown tayi ta ruwan ido, nace "wallahi in ba zaki dauka ba zan tafi in barki, Sultan fa yace zamu hadu in anjima" ta tsaya ta saki baki tana kallona, tace "dama rakonin da kika yi na munafunci ne? Dama gurin sultan zaki tafi? Wallahi kinsan ba karamin aiki na bane yanzu in kira Mommy in gaya mata" nayi ta bata hakuri ina lallabata "ba wani gurin zamu je ba fa, abinci kawai zamuje muci a Hilton, kuma motar sa daban mota ta daban" tace ta hakura ba zata fada ba amma sai in barta ta gama siyayyar ta a hankali. Sai da ta gajiyar dani sosai sannan tace ta gama, muka tafi gurin biyan kudi. Da POS ta biya kudin, aka bamu receipt muka fito, muna shiga mota na dauko waya ta da niyyar kiran Sultan naji Amira tace da karfi "what?" Na juyo ina kallonta da waya a hannuna naga wayarta take dubawa, nace "ya akayi?" Ta nuna min screen din wayarta naga alert ne na siyayyar da tayi yanzu nace "menene?" Ta nuna min receipt din, ni har lokacin ban fahimci me take nufi ba, tace "duba ki gani, sun kara min 10k a cikin kudina" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amira, let it go, wallahi na gaji" tace "wallahi bazan hakura ba sai sun biya ni kudina, haka kawai dubu goma a banza, zo muje sai sun biya ni kudina" kamar zanyi wa Amira kuka haka na fita na bita muka koma ciki. A gurin cashier ta fara masifar sai an biya ta kudinta "How can you guys be so incompetent, ku kara min kudi har dubi goma?" Cashier kaman zata yi kuka tana bawa Amira hakuri amma Amira ta shafa wa idonta toka tace sai an biya ta, ni dai ina ta kallon agogo naga har karfe biyar, nasan duk inda six tayi Mommy zata kira ni tace in dawo gida, kuma gaskiya bana son missing date din mu da sultan, na karasa gurin rigimar naji cashier din tana cewa da Amira "madam kudin sun riga sun shiga account din shagon nan, ba zamu iya fitar dashi ba sai dai ki dau wani abun na kudin ki" Amira tace "ni na gama siyan duk abinda nake so in saya, babu abinda zan dauka kuma, kawai kudi na kawai nake so a bani" cashier tace "I can't do that madam, only the manager can do that, sai dai in zaki yarda in kaiki gurinsa inyi masa bayani sai ya biya ki kudinki" naga tsoro karara akan fuskar cashier din, daga alama tana tsoron manager din, nace "Amira ki zo mu tafi, ni zan biya ki 10k dinki" tace "wallahi bazan tafi ba chafdi, nasan sauri kike ki tafi gurin Sultan, in ya kira ki bani shi in yi masa magana" ni dai duk raina a bace, tausayin cashier nake yi, mistake tayi muka maybe zata iya loosing job dinta akan haka, da har nayi deciding inyi tafiya ta in bar Amira su karata amma sai na sake tunanin maybe in na bisu gurin manager din zan iya bashi hakuri kar ya kori cashiet din. Sai da ta fara yin waya ta tabbatar yana office sannan tace muzo muje, ta shige gaba muna binta a baya, ta hau stair muka bita zuwa hawa na uku, da kyar na karasa ina ta haki, taje bakin kofar tayi knocking, aka yi magana daga ciki, ta bude tayi mana alamar mu jira a waje sannan ta shiga ciki, Amira kam ba zata jira ba dan haka ta tura kofar ta shige ciki, nima na zo kofar na tsaya.

Cashier na hango tana ta kokarin yin bayani, muryarta sai rawa take yi, na dan shigo daga ciki dan in hango wannan manager da matar take tsoro haka. Ya dan juya side dinsa, dan haka banga idonsa ba, amma tsaf na gane shi. Familiar scent dinsa ne ya kara tabbatar min da cewa shine. Na kara taku daya cikin katon office din. He is still tall but no longer thin. Yayi kiba, jikinsa ya murje sosai, hakan sai ya bashi almost a giant frame. Doguwar fuskarsa ta cika, siririn sajensa ya kara fadi dan ya tafi da fadin da fiskarsa ta dan yi, dan karamin gemon da da yake dashi yanzu babu, meaning the ustaz part of him is gone. Amira naji tayi catching breath dinta very sharply. Fatarsa ta kara haske, tana kara nuna alamar hutun daya samu. He looks so different but still the same. Lokaci daya ya juyo ya kalleni idonsa ya fada cikin nawa dana bude ina kallonsa. His eyes look the same, babu abinda ya chanza. Suna nan a lumsassun idanun da nayi falling in love with all these years ago. Gabadaya yanayin fuskarsa ya chanza lokaci daya. Da sauri na juya na nufi kofa, bansan sanda ya sauko daga kan kujerar saba har ya zagayo table dinsa ba, ina dora hannuna akan doorknob naji nasa hannun akan nawa, ya jawo ni baya da karfi, cikin tsawa naji ya ce da cashier din data kawo mu "out" na fara kokarin kwace hannuna amma maimakon ya saki hannuna sai ya hada ni da kirjinsa ya matse. Na fara kokarin kwace wa amma sosai ya matse ni, kuka na saka sosai, still bai cika ni ba, ban san adadin tsahon lokacin da muka dauka a haka ba dan har sai da nayi kuka na na gaji dan kaina nayi shiru sannan ya sassauta rikon da yayi min. Ina kwacewa na rarumi wani file akan table dinsa na fara dukansa dashi, har sai da takardun ciki suka tarwatse sannan na kuma daukan wani na cigaba da dukansa ina cewa "why? Why? Why?" Bai hana ni ba har sai da dan kaina na gaji da dukansa na durkushe a gurin na sake wani sabon kukan. A hankali a durkusa a baya na yace "am sorry" na juyo a fusace nace "sorry? Abinda zaka ce kenan? Sorry?" ya sunkuyar da idonsa kasa yace "am sorry, i shouldn't have hug you like that, bai kamata in taba ki ba kina matar aure, am sorry i lost control of myself bayan ganin ki after all these years" na juyo da mamaki ina kallonsa dan ban fahimci me yake cewa ba nace "me kake nufi da matar aure kuma?" Yanayin yadda nayi tambayar yasa ya mike tsaye da saurinsa yana kallona gaba daya ya rude yace "ance min kinyi aure a shekarar da muka rabu, kwanan nan akace min kin haifi danki na uku"


Episode Sixty Three : Amira 3

Cikin tsananin mamaki nace "what? Waye ya gaya maka haka" gani nayi yana kallon office din kamar me neman wani abu, nima na taya shi dubawa, sai a lokacin na tuna cewa tare da Amira muka shigo office din, babu ita babi alamar ta. A zuciye naga yayi hanyar kofa yana cewa "I will murder that bitch" jiri naji yana kokarin dibana, nayi sauri na zauna a kujera, nasan da za'a gwada jini na a lokacin za'a tarar ya hau, Amira, why? Me yasa zata yi min haka? I trusted her. Babu abinda banyi mata ba kuma babu abinda ba zan iya yi mata ba. Ina zaune rike da kaina Ibrahim ya dawo cikin office din idonsa kamar garwashin wuta, ya fara zagaye office din da alama jinin yarabawan ne ya motsa. "She told me lokacin da Daddy ya san alakar mu ya hada ki aure da wani cousin dinki a 'yalleman, she even showed me the wedding invitation, after a year ta turomin message tace kin haihu" sosai kaina yake juyawa dan sama sama nake jin maganar sa, lokaci daya kuma naji wani realisations yayi hitting dina, Hafsat, oh dear God no, not Hafsat, i can take betrayal from Amira but not from Hafsat, na juyo na kalleshi nace "kaima ance min kayi aure, ka auri Efi" ya tsaya a zagayen da yake yi, yazo ya tsugunna a gaba na, expression din fuskarsa na kalla naji wani dadi a raina, at least Hafsat gaskiya ta fada. Yace "yes, na auri efi shekara daya bayan rabuwar mu, amma ban karbi auren ta ba sai bayan da na samu labarin kinyi aure tukunna..." Na katse shi nace "and kawai daga Amira ta gaya maka nayi aure you just believe her, ba zaka bincika ba, ask around, ba zaka kira ni ba kayi confirming daga baki na ba" na danyi shiru ina controlling temper dina, sannan na cigaba "you switched off your phone, you didn't even call me, you just left without a second look" Ya mike tsaye ya koma ya zauna akan kujerar da take kallon tawa, har yanzu bai ce komai ba, na dago kai na kalleshi muka hada ido na mayar da ido na kasa, a hankali naji yace "kin chanza sosai, you look more beautiful, more beautiful than I kept imagining you would be" a hankali nima nace "it doesn't matter, abinda nake so kawai in sani shine 'why?' Dama tun farko bada gaske kake sona ba ko kuma bayan ka tafi ne ka chanza ra'ayi?" Ya kara jawo kujerar sa kusa da tawa yace "Maimunatu kema kinsan amsarki, I love You, more than life itself. Ki tsaya ki saurari labarin abinda ya faru bayan tafiya ta, ina tabbatar miki da cewa zaki yadda cewa it hurt me more than it hurts you. I was fooled by your friend, totally fooled" na sake dago ido ina kallon rinannun idanunsa da suke kaina. Nace "OK. Ina jinka, tell me, what happened"
"Bayan na bar gidan ku a ranar nan, na koma makaranta, ina zuwa na kashe wayata na ajiye saboda nasan zaki kira ni, ni kuma a lokacin gani nake yi as long as ina jin muryar ki I cannot stay away from you. I thought i was strong, na dauka zan iya zama babu ke har sai na samu abinda nake nema, har sai nasan na isa in zo in nemi auren ki. I had your number in my memory, dan haka plan dina shine duk sanda naga cewa it's OK to return sai in kira ki. Ranar sam banyi bacci ba, washegari na tashi da rashin lafiyar da har sai da aka kwantar dani a clinic din school. Sati da daya ina jinya sannan na dan samu sauki nace su sallame ni, suna sallamata na shiga office din PC na bata takarda ta ta barin aiki, bana son duk sanda na tashi dawowa neman aurenki ya zamanyo ina jingine da babanki ne. Kayan da suke gidana duk na hada na sayar na dau jakar kayana na fita daga makarantar, gidanku na fara zuwa na bada sakon CD a gurin mai gadi sannan na wuce tasha, .nadabazan iya misalta miki yadda nake jin raina ba a lokacin maimunatu, ina jin haushinki a lokacin sabida kin gaya min gaskiya da kika yi kuma ina jin wani irin sanki a raina, sannan ga alhinin rabuwa dake kuma, ji nake kamar na chire wani bari na jikina na ajiye. I was tempted to call you then, na dauko waya ta na saka sim na kunna, sai kuma na sake kashewa na cire sim din na jefa shi ta window din motar. Kafin muje ibadan zazzabi ya sake rufe ni, da muka je sai mai motar ne ya karbi number din baba a wajena ya kira ya gaya musu halin da nake ciki, nan suka zo suka dauke ni sai asibiti, na jima shima ina rashin lafiya a can, hatta mama bata san abinda yake damuna ba ballantana su Hadiza, na gaya musu na ajiye aikina na Abuja, kawai dai sun fahimci cewa it has something to do with you. Bayan na samu lafiya an sallamoni sai na yanke shawarar tafiya Lagos, da akwai wani uncle dina a can wanda kudin inheritance din mu yake hannunsa yana business dashi, mama taso ace na zauna a ibadan na nemi wani aikin amma naki, gani nake aikin government babu abinda zai kawo min. Ina zuwa lagos uncle dina ya fara koyamin harkar business, cikin 'yan watanni na koya sosai, ya dauki kudaden mu gaba daya ya bani na fara nawa daban. Duk abinda nake yi kowacce rana, kowanne hour, kowanne minute kowanne second kina cikin raina maimunatu. A lokacin na fara trying kiran number dinki da sabuwar number ta, at least duk da cewa ina ganin lokacin dawowata bai yi ba amma ina so in san ya kike, amma ga mamakina your phone was switched off, kullum na kira a kashe, bani da number din kowa kuma a gidan ku sai taki. Tun a sannan na fara zama very frustrated. A haka har shekara ta kusa ta zagayo. Ban wani tara kudin kirki ba amma bazan iya jure zama babu ke ba, a dole na fara shirin tahowa Abuja in neme ki. Kamar hadin baki, ina zuwa ibadan baba ya shigar min da maganar auren Efi, a take nace masa a'a, wannan ba karamin bata ran mama yayi ba, saboda bata taba zaton zan iya cewa da baba a'a ba, tunda ban taba ce masa a'a ba. Ta fara fada baba yace a tambaye ni uzuri na, nan na gaya masa maganar ki, na nuna masa sosai irin yadda nake sonki, shi kuma ya goya min baya yace inzo abuja muyi magana da daddy in ya amince sai inzo in fada su kuma sai suje ayi maganar manya. Washegarin da muka yi maganar dashi na taho Abuja, har a lokacin wayarki bata shiga. Nazo unguwarku naga gidan ku babu alamar movement kamar wancan zuwam nawa, bana son wulakancin securities din ku dan haka na tsallaka gidan opposite dinku na tambayi me gadin kuna nan kuwa? Sai yace min ai kun tashi daga kasar ma gaba daya, sosai hankali na ya tashi, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa wayarku bata shiga. Bansan a gurin wa zan samu labarinki ba ballantana contact dinki. Na tuna da kawarki Amira itama a abuja take da zama kuma nasan tabbas zan samu labarinki a gurinta. Na tafi tsohuwar makarantar ku gurin principal na roke ta ta nemo min file din Amira, a ciki na samu address din gidan su, ina zuwa gidan su na aika a kirata aka cemin ta tafi makaranta, anan na zauna nayi ta jiranta har magrib sannan ta dawo. Sosai tayi mamakin ganina a kofar gidan su, kuma tayi murna sosai. Sai yanzu na fahimci dalilin murnar ta, ta dauka gurinta naje, ni na manta ma da cewa tana da wani feelings for me, na dauka tunda na gaya mata baki da baki cewa bana sonta shikenan magana zata wuce. Bayan mun gaisa ta kawo min ruwa nasha sai na gabatar mata da abinda ya kawo ni gurinta, cewa ina neman hanyar da zan same ki ne ko kuma number dinki. Abinda tace min shine 'au baka sani ba? Na dauka ta gaya maka ai' nace mata 'me fa?' Tace 'zancen auren ta mana, ai ranar da kaje gidan su Daddy n ta ya ganka, kana tafiya ya tambayeta waye kai ta gaya masa yace babu ita babu kai, shi ba zai bawa bayarabe 'yarsa ba, data takura ta daina cin abinci ta daina yiwa kowa magana sai ya dauke ta ya kaita 'yalleman, bata fi two weeks acan ba aka hada auren ta da wani cousin dinta a can' ji nayi tamkar ta zuba min fetur a jiki na ta kyatta a shana. She is your best friend, how can I not trust her words? Besides, nasan dama ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login