Showing 195001 words to 198000 words out of 262297 words
AC naji yana ratsani. Nayi kokarin bude idona naji yayi min nauyi sosai, na motsa hannayena kadan ina son in dawo da karfin jikina, muryar Mommy naji tace " Maimoon? Maimunatu kina ji na?" Na dan bude ido na kadan na kalleta, da sauri ta taho ta rike hannuna fuskarta tayi ja alamar tayi kuka, na danyi kokarin yi mata murmushi amma ciwon da kai na yake min yasa murmushin ya zama kamar gyatsine. Na fara duba dakin da nake, asibiti ne, ga drip a hannuna, Mommy tana zaune gefena, Daddy yana tsaye a gefenta, Sultan yana daga can baya ya jingina da jikin bango, tsantsar tashin hankali ne a rubuce a fuskarsa. Motar Ibrahim na tuno yadda tayi ta adungure kafin ta fada cikin ramin. A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idona, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah kasa mafarki nake yi yanzu za'a ce min ba gaske bane ba, amma yanayin fuskar sultan ka dai ya tabbatar min da cewa ba mafarki nake yi ba, Sultan yayi kisan kai a gaba na, Sultan ya kashe Ibrahim. Allah sarki Ibrahim why? Menene kake tunani me yasa ka biyo mu? Nasan bacin ran daya gani a fuskar sultan da yadda sultan ya fara acting a cikin store din shi ya saka ya biyo mu, he was looking out for me, amma banda abin Ibrahim koma me Sultan zaiyi min ai munfi kusa ni da shi, ballantana ma Sultan babu abinda zai iya yi min. Yanzu shikenan Ibrahim ya bar duniya, because of me, Sultan yayi kisan kai, because of me, na tuna da little Moon, na tuno fuskarta a hotonta dana gani a office din Ibrahim, she looks so happy, yanzu ta zama marainiya babu uwa babu uba because of me, sultan da yake ta faman kula da marayu kullum maganar shi bata wuce ta marayu yau muguwar zuciyarsa da bakin kishinsa ya nawo yayi making marainiya da kansa. Kuka nake yi sosai inajin ciwon kaina yana karuwa. Muryar Mommy naji tana cewa "Haba Moon, kukan menene kuma wannan? Daga rashin lafiya sai kuka? BP dinki ne fa ya hau idan baki daina kuka ba kuma tayaya zai sauka?" Daddy ya kalli sultan yace "kace a kitchen ta fadi ko?" Sultan ya dan kalleni kadan sannan ya gyada kansa ba tare da yayi magana ba, Daddy yace"amma menene zai sa BP dinta yayi wannan hawan haka? Bai taba hawa kamar haka ba" Sultan ya sunkuyar da kansa fuskarsa kamar zai yi kuka amma sultan never cries, Mommy tace "may be zafin kitchen ne dear, dama masu hawan jini ba'a so su ringa kusa da wuta sosai" Daddy ya karaso ya rike hannuna yace "maimunatu kukan me kike yi?" Kafin inyi magana sai ga doctor ya shigo, yana murmushi yace "finally ta farka ashe, ya jikin?" A hankali nace "da sauki" yace "menene kuma na kuka? The pregnancy is intact ai, munyi nasarar tsayar dashi bai fita ba" a tare Mommy da Daddy suka ce "pregnancy?" Na juyo na kalli sultan naga gaba daya fuskarsa tayi fari tas kamar babu jini, ya juyo da sauri ya kalle ni, na kalli su mommy naga gaba daya hankalinsu yana kan doctor yana musu bayani, na gyada masa kai nace "shi yasa nace ina son chocolate din" hannu biyu ya saka ya rike kansa, Mommy naji tana magana cike da fara'a tace "I suspected as much, bana son in saka rai ne ko ba haka bane inzo inji babu dadi shi yasa na dora wa zafin kitchen" doctor din ya gama yi musu congratulations ya fita, Sultan har yanzu kallona kawai yake yi sannan da sauri kamar wanda aka jawo ya taho gurina, kara na saka da duk dan karfin da ya rage min, wannan ya jawo hankalin Mommy da Daddy kaina, Mommy ta taho da sauri kusa dani tace "lafiyar ki kuwa? Ciwon kan ne?" Na nuna Sultan nace "kar ka karaso inda nake, it is over between us" cikin muryar abin tausayi yace "Moon dan Allah kar kice haka, bazan iya rayuwa in babu ke ba mutuwa zanyi please" nace "then so be it" bai hakura ba ya sake taku daya, na dunkule hannuna na daga dai dai kan mara ta nace "kana kara wani takun zan fitar da abinda yake cikina in baka kayanka" a tsorace ya tsaya, he looks scared, I have never see Sultan scared tunda na san shi. Mommy ta rike hannuna da sauri tace "baki da hankali maimunatu? Me ya hada ku haka?" Fuska ta babu alamar wasa kwata kwata, na kwace hannuna daga hannun Mommy na kuma dagawa a saman mara ta, da sauri sultan ya ja baya, yanayin fuskarsa kadai ya isa ya saka mai karamar zuciya ya fashe da kuka. Daddy ya tafi kusa dashi yana cewa "Sultan me ya faru?" Bai amsa ba ya juya da sauri ya fice daga dakin.
Yana fita na kifa kaina akan pillow na fara rera kuka, Allah kai kasan me kake nufi damu, Allah ka shiga lamarin mu. Ko kadan abinda Sultan ya aikata bai chire min ko digo na soyayyarsa daga raina ba. Amma abinda na fahimta shine; Sultan is too hard for me to break, diamond ne shi kafin a narka shi sai anyi amfani da ice da fire, I have used the ice bai yi min amfani ba, now I have to use the fire. Daddy ne yazo ya zauna kusa dani yana shafa kaina yace "Maimunatu talk to me" na dago kaina naga Mommy tana ta sharar kwalla, na runtse idona ina tuna duk abubuwan da suka faru a ranar, na kwalli agogon bangon dakin naga 3:30 na dare, hakan yana nufin an dauki hours da yin abin, hakan yana nufin Ibrahim yayi spending hours a cikin ramin day fada, wani kukan ne ya taso min, na dora kaina a kafadar Daddy nayi mai isa ta sannan na share hawaye na, tiryan tiryan na basu labarin duk abinda ya faru, na karasheda wani kukan "yanzu Daddy sultan ya kashe Ibrahim, ya zanyi? Shima hukuncin kisa ne akansa in aka san maganar nan, idan kuma nayi shiru ban fada ba kuma kamar na daure wa cin zali gindi kenan, ya zanyi Daddy? Mommy ki taimaka min" Mommy ta jawo ni ta rungume ni tana kuka tana salati "mun shiga uku mun lalace ni Fatima" Daddy kuma cike da mamaki yace "waye shi Ibrahim din ne?" Mommy tace "wannan copper din da yake sonta da a makaranta" Daddy yace "That yaroba guy?" Kai kawai na gyada masa, yace "a dai dai ina abin ya faru? Kamata yayi muje first mu dauko shi, maybe yana da rai yana bukatar taimako, in ma bashi da ran kamata yayi ai muje mu dauko shi" nayi musa kwatance ya mike yace "bara in nemi sultan shima inji me yake ciki, I don't want him hurting himself kuma" na girgiza kaina nace "he won't. He would want to see his child".
Tunda Daddy ya fita babu wanda yayi magana ni da Mommy, kowa da abinda yake zuciyarsa. Mun jima sannan naji Mommy ta fara yi min magana, ga mamaki na maimakon inji tana fadan abinda Sultan yayi sai naji tana addi'ar Allah yasa babu abinda ya sami Ibrahim. Muna cikin haka wayar ta tayi kara, ta dauka tace " wannan number ce ma babu suna, waye zai kira ni cikin daren nan kuma" ta daga tare da sallama, take naga yanayin fuskarta ya chanza, tace "Amina slow down kiyi min bayani yadda zan gane. Kina ina?" Ta jima tana sauraron Amina tana kuma kallona, na mike zaune ina jiran inji abinda ake gaya mata, tace "OK, kinyi kokari sosai Amina, ki zauna anan inda kike bara in kira daddyn ku in gaya masa" ta kashe wayar, bata yi min magana ba sai tayi dialing number din Daddy tace "ba sai kunje gurin ba dear, su Amina sun dauko shi sun tafi dashi general hospital. Yes, he is alive, zan yi maka bayani later" ta kashe tana kallona, wata ajjiyar zuciya na saki na koma na kwanta, duk da bansan details din me ya faru ba amma na fahimci cewa Ibrahim is alive, wannan information din kadai ya isa ya kwantar min da hankali. At least Sultan is safe now, amma kuma dole zai fuskanci hukunci daga gurina, sam ba zan yi masa da wasa ba, he must learn to control his temper especially yanzu da zamu fara ajjiye zuri'a. Daga baya Mommy tayi min bayanin cewa ashe duk abinda ya faru a store Amina ta gani, taga fitowa ta da kuma fitowar Sultan, bayan ta fito itama waje sai taga tafiyar mu a guje, sai kuma taga Ibrahim ya biyo bayan mu shima a guje, shine taji tsoron kar wani abin ya faru ta hau taxi tace yabi yaban mu, munyi musu nisa dan haka basu ga sanda abin ya faru ba amma sunga motar mu tana juyowa amma bata ga ta Ibrahim ba, suna zuwa gurin suka ga alamar anyi accident, ita da mai taxi suka fito sannan suka ga inda motar Ibrahim ta fada, mutane masu wucewa ne suka taimaka masu aka fito da Ibrahim, lucky for him shima ya saka seatbelt kuma motar sa akwai airbag dan haka bai wani ji mugun ciwo ba amma still he is unconscious, sun kai shi asibiti an kaishi emergency.
Gari yana wayewa Daddy ya shigo, ya gaya mana cewa har lokacin Ibrahim bai farfado ba amma doctors din sunce he is stable. Sultan daga bakin kofa ya tsaya yana kallona, kallo daya nayi masa na dauke kaina gefe, ya gaji da tsayiwa ya juya ya fita. Da la'asar aka sallame ni, direct gida aka nufa dani, naji dadin haka dan dama ina ta addu'ar Allah yasa kar Daddy yace a mayar dani gidan Sultan. Shima kansa Daddyn naga ya hade wa Sultan rai sosai. Muna zuwa gida Daddy ya saka ni a gaba yace "zaki dan zauna a gida Moon, hakan ba yana nufin zan raba ki da mijinki ba, a'a, so nake mijinki ya gane cewa abinda yayi ba dai dai bane, for him to think cewa zai iya daukan ran mutum koma me mutumin yayi masa is very bad. Zaki koma amma sai na tabbatar da cewa something like this will not happen again" na share hawayen ido na nace "na gode Daddy" yace "yanzu so nake dake ki nuna masa kuskurensa sosai, kar ki raga masa ko kadan. Ke ce abinda yake so fiye da komai a duniya, kuma yana takama ne cewa kina sonsa, show him you can leave him in dai har ba zai iya controlling kansa ba" na gyada kai na sake cewa "na gode Daddy".
Dakina aka gyara min, na shiga ina karewa dakin kallon, I never thought zan kuma dawowa dakin in kwana a ciki. Dare yana yi nayo alwala nazo na fara jero salloli ina godewa Allah daya ta kaita abin, sannan kuma ina sake neman guidance dinsa akan abin da na saka a gaba na. Na duba agogo naga karfe daya da rabi na dare, na kashe fitila na zauna akan gado ina kallon kofar balcony, I know he is coming, and I pray for God to give me the strength to do what I plan to do. Ban jima a zaune ba naji ana taba kofar, sannan aka bude ta, duk da cewa dakin da duhu bai hana ni gane shi ba, ya jima a tsaye yana kallona amma ya kasa cewa komai, nace "me kazo yi nan?" A hankali ya karasa shigowa dakin yace "Maimunatu dan Allah ki tsaya kiji abinda zan gaya miki" nace "me zaka gaya min, a gaba na kayi kokarin kashe mutum, you almost make me miscarry our child" da sauri yace "how can you say that, ke ma kinsan bansan dashi ba" nace "how can you say naje store ne dan in hadu da Ibrahim bayan bansan yana gurin ba" yace "am so sorry" nace "don't be. Rayuwa ta da taka ba iri daya bace ba. Ka tafi, ni bazan iya zama da mutumin da yake ganin cewa it is OK yayi kisan kai ba, bazan iya haifar 'ya'ya da kai ba, wannan ma da yake cikina in naga baka chanza ba I will make sure cewa bai san kaine babansa ba" da gaske magana ta ta shige shi dan fuskarsa koma wa tayi kamar an chire masa spirit din jikinsa, na mike tsaye nace "now get out of my room" ko motsi bai yi ba, na kunna fitilar dakin, yanayin da naga fuskarsa yasa nayi saurin dauke idona daga kansa tun kafin zuciyata ta karaya, na sake cewa "ka fita ko in kira security su fitar min da kai" a hankali yace "you won't" ban kuma ce masa komai ba naje na danna security button, ba'a jima ba sai ga David da wasu guda biyu sun shigo dakin, David da bindiga a hannunsa. Na nuna Sultan nace "ku fitar mun dashi daga nan" David yace "with pleasure ma'am" dama har yanzu David yana da grudges for sultan saboda dukan daya yi masa rannan ya kunyata shi a gaban yaransa. Ga mamakina ko motsi sultan baiyi ba ballantana yace zai yi fada dasu, suka kama shi suka fita dashi ta gabana, na dauke kaina ban kalle suba, amma suna fita na bi bayansu na tsaya a kofar dakina ina kallon yadda suke jansa akan stairs, ji nake tamkar zuciyata suka fito da ita waje suke ja a kasa, ina kallon su har suka bude kofar palo suka fita dashi waje. Na hango Daddy a kofar dakinsa shima yana kallon su. Na koma dakina da sauri na bude kofar balcony na shiga na cigaba da kallonsu suna jansa a kasa kamar babu rai a jikinsa, har suka bude gate suka fita dashi waje, a gaban gida na biyu bayan namu na hango motar sa, nan suka nufa dashi suka jefar dashi a gaban motar suka juyo, na tsaya ina kallon duhun inda yake a kwance a kasa, a raina ina cewa 'get up sultan' amma shiru bai tashi ba, bayan kamar 20 minutes na koma dakina na dauko waya na dawo balcony din, na kira wayar Amir, yana dauka nace "Kazo gidan mu yanzu, your friend needs you" na kashe wayar, ban bar gurin ba har sai da naga shigowar Amir unguwar mu, har ya wuce inda Sultan yake sai kuma yayi reverse, ya fita da sauri yana taba sultan, sannan ya daga shi, naji wani dadi a rauna ganin sultan din yana kokarin tafiya da kansa, a bayan mota Amir ya saka shi sannan ya koma ya rurrufe motar sultan din sannan suka tafi. Na rufe fuskata da hannayena ina kuka, I really hope cewa abinda nayi is the right thing to do. Waya tace ta fara kara, duk a tunani na Amir ne amma sai naga sunan Hafsat. Nace a raina 'har ta samu labari kenan' na dauka nayi mata sallama cikin sarkakkiyar murya, excitedly ta fara magana "Moon am sorry na kira ki yanzu nasan dare yayi sosai a Nigeria, what ever you are doing ki ajiye ki hau WhatsApp na turo miki hoton wata auntyn zayed, she looks exactly like Sultan, her name is Khairat, Moon I think she is his mother".
*when everything seems lost, have hope and trust in Allah, He will always find a way out for you. Remember, there is always darkness before dawn.*
Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
A lokacin da su David suka ajiye shi a kusa da motar sa, kasa tashi yayi daga gurin, jira yake mutuwa ta karaso ta dauke shi, dan shi a ganinsa bashi kuma da sauran rayuwa a gaba. To menene sauran rayuwa in babu Moon? Dama itace farin watan data haskakae rayuwar ta sa da hasken ta, to yanzu tunda babu ita kuma menene yayi saura in banda duhu, a cikin duhun zai yi ta lalube har yaje ya afka ga halaka, he is sure that he will be lost without her. Yana kwance yaji tsayuwar mota a kusa dashi, a tunanin sa ma robbers ne kuma he didn't care. Sama sama yaji muryar Amir yana yi masa magana, ya dan bude idonsa ya kalle shi ya mayar da idon ya rufe. What is this man doing here? Me ya kawo shi? Yana jin Amir ya fara kokarin tashin sa, ya kwace, Amir yace masa "Sultan menene hakan kake yi wai? Moon ta kira ni tace inzo gurin ka, me ya faru? I really hope you are not drunk kuma? Sultan ya bude ido ya kalle shi sosai sannan yace cikin murya kamar ba tasa ba "Moon ce tace kazo nan?" Amir yace "eh, me ya faru haka" Sultan ya fara kokarin tashi Amir ya taimaka masa ya bude masa mota ya shiga suka tafi. Me yasa Moon ta kira Amir? Shin hakan yana nufin she still care about him ko kuma just tana so a dauke mata shi daga kofar gida saboda bata son ganin sa?. Ya lumshe idonsa yana tunanin abubuwan dasu ka faru tsakanin su, she even said zata tabbatar da cewa dan da yake cikin ta bai san cewa shine mahaifinsa ba, she hates him that much kuma bai ga laifin ta ba, koma menene ya faru laifinsa ne. Na farko ta ya akayi ma zuciyarsa ta raya masa cewa Moon sun hada plan da Ibrahim zasu hadu? How can he even think that? Kishinsa ya rufe masa ido kawai ya fadi magana without thinking kuma wannan maganar ita ce tafi komai bata wa Moon rai. Shi shine mai bad past, amma ita ko yaushe tana kyautata masa tsammani, ya tuna case din khulsum, tun kafin ma moon ta tuntubeshi da maganar har ta yanke hukuncin karya suke masa, amma shi bai showing mata the same courtesy ba. Wannan shine babbar nadamar sa ba wai ture Ibrahim ba, that bastard, he deserve that, uban wa yace ya biyo su? Har cikin gidansa ya shiga gurin matarsa and he let him go, sannan kirikiri ya ganshi ya rike hannun matar sa a cikin store and he still ignore him,